Showing 33001 words to 36000 words out of 50228 words
Chapter 12 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf
tsokane idon......" Nice na dakatar dashi
saboda dariyar da nakeyi.
*Comment*
*&*
*Share*
*By*
*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*MENENE MATSAYINA ?*
*(fictional story)*
*Written by*
phatymasardauna
*í ¼í¾ˆMrs Sardaunaí ¼í¾ˆ*
*Dedicated to my lovely sister Maryam*
*í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*í ½í²ƒí ¼í¿»JIKAR HAJIYA í ½í²ƒí ¼í¿»* ```bansan mai zance miki ba, amma gaskia kina sani nishaÉ—i da
comment ɗinki, Inasonki Sosai tawan, kiyi farinciki har ƙarshen rayuwarki, wannan page ɗin
kyautane a gareki ke kaÉ—ai...```
*PAGE 5⃣6⃣to5⃣7⃣*
Gudu kawai Hameed keyi akan titi burinshi baiwuce yaga yayi ido huÉ—u da Sarah ba,,
dayake yasan gidansu, domin kwanakin baya yataɓa kai Farhana, don haka bai wani shan
wahala wajen nemanta ba kaitsaye ya nufi gidansu,, daga É—an can nesa da gidansu Sarah
yayi parking motar tasa, jingina yayi da motar bayan yafito yana mai kafe ƙofar gidan nasu
da'ido.. Mintuna bakwai da isowarsa ƙofar gidan, yaga wata mota tayi parking a ƙofar gidan,
Sarah ce tafito daga cikin motar, carab idanunta suka sauƙa akan Hameed dake tsaye jikin
nasa motar, sake waro idanunta tayi domin tabbatar da abun data gani, "shine dagaske
wallahi Hameed ne" tafaÉ—a lokacin da take murje idanuwan ta da hannayenta duka biyu,,
"Kaddai har aikin boka naguru yasoma ci ? tatambayi kanta, domin dai yanzu haka daga wajen
boka take, tanar ka masa maƙudan kuɗaɗe yakuma bata wani ƙullin magani yace duk yanda
za'ayi tasan yanda zatayi tasanya mawa Hameed acikin abinci yaci, yakuma yi mata wani aiki
wanda Hameed ɗin da ƙafarsa zaitako yazo gareta,, wani irin tsallen murna tayi haɗe da cewa
"Yes Boka wallahi aikinka har ya soma ci domin ko gashi yazo da ƙafafunsa " take Sarah
tasauya takunta zuwa rangwaÉ—a, tanufi inda Hameed ke tsaye, kafeta yayi da mayun idanunsa
wanda suka ƙaɗa sukai ja dasu tsabar bala'i da ɓacin rai dake damunsa, tana ƙara sowa tayi
masa wani murmushi mai É—auke da sigan jan hankali, cike da kisisina tace " Yaya Hameed yau
kai ne agidan mu, Allah yasadai wajena kazo ?" taƙare maganar tana maiyi masa fari da'ido,,
kallonta yayi na tsawon minti É—aya kafun yasaki wata Æ´ar guntuwar murmushin datafi kuka ciwo,
tsab yakaranceta don haka yace " Shiga mota a kwai abun da nakeso mutattauna dake mai
mahimmanci " jikinta har rawa yake jin yace tashiga mota zasuyi magana mai mahimmanci,
Azuciyarta tace "Allah kasa zancen soyayya zaiyi mini" (kuji shegia hatta manta aika aikan da
tayi) da sauri tashige cikin motar tasa haÉ—e da hakimcewa a gidan gaba, shiga cikin motar
shima yayi haɗe da sawa duk wata ƙofar fita daga motar luck key yayi mawa motar, da ƙarfin
tsiya ya figi motar harsai da Sarah ta suɓalo gaba kanta kuwa yayi wani irin mummunan
bugewa,, a matuƙar tsorace ta juyo ta kalleshi haɗe da cewa " Nashiga Uku na Yaya Hameed
ina zaka kaini !! ? " baiko kalli inda take ba balle tasa ran amsawarsa, gudu kawai yake
shararawa,, tafiya sosai yakeyi akan titi tamkar wanda zaifita gari, yayinda Sarah ke ta yi masa
ihu da magiya akan yataimaka ya tsaya ta sauƙa,, amma kollonta bayayi,, gaban wani gini
wanda aka fara ba a ƙarasa ba, yatsaya da motar tasa, cire luck ɗin daya sanyawa ƙofofin
motar yayi haɗe da ficewa daga cikin motar, ƙofar da Sarah ke ciki ya buɗe haɗe da sanya
hanunsa yadam ƙota, haka yashiga janta tana ihu har cikin wannan gidan, kitsaye wani ɗaki
da ke cikin gidan ya nufa da'ita, bakomai acikin ɗakin sai zallan ƙasa, amma akwai rufi asaman
ɗakin hadda winduna,, cikin turbuɗin ƙasan dakw ƙasan ɗakin ya wurgata, haɗe da zare belt
É—in jikin wandosa, yayi kanta, batare da tunanin komaiba Hameed yashiga dukan Sarah baji
babu gani, ihu sosai Sarah takeyi na neman taimako, amma bawani mahaluƙin dake jinta, duka
sosai Hameed yayi mawa Sarah harsai da jikinta yafaffashe, fuskarta kuwa raga raga tayi da
jini, saida Hameed yaga Sarah ta daina numfashi kafun yadaina jibganta, bayan yagama illata
mata jiki da duka, ruwa mai sanyi ya É—ebo ya kwara mata, afirgice tafarfaÉ—o daga suman da
tayi, motarsa yakoma ya ɗauko wata gorar Fanta, danne sarah yayi da ƙarfin tsiya yaɗura
mata wannan fantan dake cikin gora, saida tashanye tas kafun yayi wulli da goran gefe, wani
irin kallon tsana yayi mata haÉ—e da cewa " Banza sakarya wacce batasan mutumcin abota ba,
ke atunaninki zaki kashe jinin Hameed kuma kizauna lafiya ? wallahi yau saikin gwammace da
uwarki bata haifeki ba, Æ´ar iska mahaukaciya " yawun dake cikin bakinsa yatofa mata akan
fuskarta, haɗe da ɗaukan kaca yaɗaure mata hannayenta da ƙafofinta gamdashi, "Nan da 5
minute ki saurari baƙon yanayin dazai zo miki, wallahi saikinji fiye da azaban da kikasanya
Farhana aciki, saikinji fiye da zafi da raÉ—aÉ—in da kikashayar da Farhana" yana kaiwa nan a
zancensa yasakai yafice daga cikin ɗakin haɗe da danna mawa ƙofar ɗakin kwaɗo yajefa key
É—in acikin aljihunsa,, cikin motarsa yakoma haÉ—e dayi mata key, kaitsaye yaÉ—auki hanyar
asibiti.....
Yanazuwa asibitin yasamu doctors suna shirin sallaman Farhana, domin har su Ummie da Abba
sunzo, nan aka sallamesu suka tarkato suka dawo gida, koda Farhana tagama zayyane
mawa su Ummie abun da yafaru tsakaninta da Sarah, Salati Ummie da Abba suka somayi cike
da alhinin abun " lallai duniya, wanda kayarda dashi shike cin amanarka, lallai zuciyar É—an
adam cike take da baƙinciki da kuma hassada, zamani ya lalace wanda kabawa yarda da
amana shike yaudaranka, ya Allah karabamu da sharrin maƙiyanmu nafili da na ɓoye, Ameen
".......
Minti biyar da tafiyan Hameed Sarah dake ɗaure, tasoma jin mararta na wani irin ƙullewa,
yayinda cikinta ke wani irin ƙugi tamkar hanjinta zasu tsistsinke haka takeji, ihu tafara kurmawa
daduka ƙarfinta, tana mai neman agaji amma ina bamaijinta balle yakawomata agaji, wani irin
masifaffen ciwon ciki da na mara ne suka addabeta tamkar zata mutu haka takeji, haka tashiga
murƙususu acikin ƙasa tana kwarara ihu, iya azaba da raɗaɗin duniyarnan Sarah tajisa, gashi
babu wani maijinta balle yataimaketa, saboda tsananin azaba da Sarah keji, yasanya
numfashinta É—aukewa baki É—aya......
Kwance suke akan gado rungume da juna, idanun kowannensu nakan É—an uwansa, wani irin
kallo Hameed kejifan Farhana dashi, mai cike da tsananin soyayya da kulawa, itama irin kallon
da takeyi masa kenan, a hankali yakawo bakinsa kusa danata ya haÉ—esu waje guda, wani irin
kyakkyawan kiss suka shiga mawa laɓɓa da harshen juna, kiss suke mawa juna, wanda bakow
keyin irinsaba sai ga babban masoyinsa, a hanakali yagangaro da hannayensa kan breast
É—inta wanda aÆ´an kwanakinnan suka sake cika da girma, yanda yakeshafa breast É—inta
yasanya taƙara lafewa a cikin jikinsa domin kuwa sosai hakan keyi mata daɗi, a wannan dare
wani irin gangariyar soyayya Farhana da Hameed É—inta suka gudanar, Hameed ya shayar da
Farhana'nsa daÉ—i son ransa, yayinda itama tashayar dashi daddaÉ—an zumanta wanda babu
algus acikinta.......
****
Cikin muryan kuka Beedah ke cewa " Dan Allah kasanar dani *MENENE MATSAYINA* acikin
gidannan ? ka ƙauracewa shimfiɗata, baka saurarata, baka shiga duk wani al'amurana, nasan
cewa nayi maka babban laifi, amma maiyasa bazaka yafemin ba ?? " wani irin mugun kallo
Hameed dake tsaye a gabanta ya watsa mata, haÉ—e da cewa " Koki bani hanya na wuce kona
tattakaki anan wajen " yaƙare maganar cikin kakkausar murya, cikin matsanancin tashin
hankali Beedah ta zame a wajen tashiga rera kuka, Hameed kuwa tsalleketa yayi, yayi tafiyarsa
abunsa,,, koda yaje gidansu bai ɓoye mawa Ummie da Abba komaiba yagaya musu cewa
yakama Beedah tanashan ƙwayoyin planning,, sosai ran Ummie yasosu da abun da Beedah ta
aikata, taji zafin abun sosai, amma tunda ta fuskanci cewa É—annata yanason matarsa, yasanya
ta shanye ɓacin ranta cikin zuciyarta,, Abba ma yaji zafin abun, amma sai ya taushi Hameed
haɗe da basa haƙuri akan kada yasake yaɗauki wani tsattsauran mataki a kanta, duk da cewa
tayi laifi, kada ya yi mata tsastsauran hukunci, Abba yayi masa nuni da yayi mata nasiha mai
ratsa jiki, ko hakan zaisa ta kiyaye gaba,, yanda Abba yayi ta bawa Hameed shawarwari a
game da rayuwa, yasan yashi jin zuciyarsa tayi sanyi....
Tunda Hameed ya kulle Sarah a cikin wannan kangon baisake waiwayarta ba, saida tayi kwana
Uku, koda ya je a wani irin mummunan yanayi ya isketa, tamkar gawa, murmushin mugunta
yayi haÉ—e da cewa " Nasan kinÉ—anÉ—ana azabar da Farhana ta É—anÉ—ana alokacin dakika zubar
mata da ciki, ke ƙaramin mugunta kikayi mata nikuma namiki babba, idan kin rayu ruwanki idan
kin mutu duk ɗaya" kiiii haka yajata a ƙasa, yacusata cikin mota, bai zarce da'ita ko inaba, sai
ƙofar gidansu, ƙafansa yasanya ya tangaɗata waje daga cikin motarsa, haɗe da bamawa motar
tasa wuta, yafice daga area'n nasu,, ƙanin Sarah dayazo shiga gida shiya fara yin tozali da ita
yashe a gefen titi kamar wata gawa, ai dagudu yayi cikin gida haɗe da ƙiran mamansu, kuka
maman Sarah ta sanya, ganin ɗiyarta yashe a ƙasa jikinta duk jini bata ko numfashi,, da
taimakon mai gadinsu aka sanya Sarah acikin mota, aka wuce a sibiti da'ita.........
Duk iya ƙoƙarin da doctors sukayi wajen ceto numfashin Sarah abun yaci tura, domin dai
abincikensu sun gano cewa "Maganin zubar da ciki tasha mai ƙarfin gaske, batare kuma da
tanada ɗauke da ciki ba, ƙarfin maganin kaɗai ya isa ya sanya numfashinta ɗaukewa na har
abada, maganine mai haÉ—arin gaske, Allah ne dai kawai yasa kwananta na gaba, amma ita da
farfaÉ—owa bayanzu ba, kuma side effect na maganin yasanya mata wani ciwo a mahaifa,,
koda doctors sukai mawa iyayen Sarah bayanin halin da ƴarsu keciki, baƙaramin tashin hankali
suka shiga ba, bama kamar mamanta......
*Bayan Sati Biyu*
Gaba É—aya hankalin Hameed yau a tashe yake, domin kuwa tun safe Farhana keta kwarara
amai, gashi taƙi sanya komai acikinta, uwa uba gawani zazzafan zazzaɓin dayayi mawa jikinta
rubdugu,, ganin abun nata na ƙara da ɗuwa yasan ya shi ɗaukanta, suka nufi asibiti.....
Zama yayi akan wani benci dake bakin ƙofar ɗakin da aka shigar da Farhana, kallo ɗaya zakai
masa kafuskanci cewa yana cikin damuwa,
Doctor Rasheed ne yafito fuskarsa ƙunshe da murmushi, Hameed na ganinsa yayiyo kansa
yana cewa " Doctor yajikin nata ?" " jiki Alhmdlh, tama samu bacci, saidai a gaskia.....
"Saidai me doctor dan Allah karkacemin wata matsala ne yasameta, Hameed yakatsesa da
hanzari,, murmushi doc Rasheed yayi haÉ—e da cewa " Bawata matsala, ina mai tayaka murna
Mr Hameed matarka tana É—auke da juna biyu !!!"
Waro idanunsa Hameed yayi cike da tsananin mamaki yace "Dan Allah doctor dagaske kake ?"
" Ƙwarai kuwa Mr Hameed matarka na da ciki !!" Rasheed yasake maimaita masa,
"ALLAHU AKHBAR ! ALLAHU AKHBAR !! Allah bawani sarki bayankai, kaike isar mawa bawa
ako wani hali, Ya Allah inamai miƙa godiyata a gareka " Hameed yafaɗa idanunsa cike da
ƙwallan farinciki, Sujja yayi awajen haɗe da sake gode mawa Allah, daya sake a zurtashi da
kyautar É—a ko Æ´a,, yana É—agowa daga sujjada ya rungume doctor Rasheed cike da farinciki
yace " Kayimin albishir wanda bazan taɓa mantawa ba, haƙiƙa zansaka maka da kyauta wanda
kaima bazaka taɓa mantawa ba,, yana kaiwa nan azancensa yacusa kansa cikin ɗakin da
Farhana ke kwance,,, murmushi kawai doc Rasheed yayi, domin ya fuskanci cewa Hameed É—in
yanacikin farinciki......
*13/October/2019*
*MRS SARDAUNA*
*í ½í¹†í ½í¹† RAYUWATA CE*í ½í¹†í ½í¹†
*Na*
*Khadeejah Sani (Journalist)*
*í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*í ¼íµ¿65_66*
Agurguje
Biki yazo anata shirye shirye naje gidan amarya Aysha nasameta lafiya kalau saboda muna
haduwa a makaranta shiyasa bamuyi kewar junaba Nan muka kara shirya yadda bikin zai
kasance don saura kwana biyar daurin auren,
Zaune nake falon Aysha ita Kuma tana daki take dakkomin dinkin da akayi mata zangani na
bikin,
Dawowa tayi ta zauna kusa Dani tace
"Ke waima Ina Zaki zaunane haryanzu banji unguwarba Allah yasa kusa damune madunga
tahowa tare da makaranta"
Murmushi nayi nace
"Uhm kinsan abinda har yanzu banma saniba kenan Kuma jiya naji ana maganar jere Yaya
Yana cewa gobe za,aje ayi Amma wallahi bansan ko wacce unguwa bane" dariya tayi sannan
tace
"Kajini da 'yar duniyar amarya Wai da gaske kike Baki saniba?"
"Wallahi Allah bansaniba nifa bamu tabayin maganar anguwar da yake giniba kawaidai nasan
yanayin gini Amma bansan unguwar ba"
Hade Rai tayi sannan tace
"Malama banson rashin kirki kirashi muji inane" kallonta nayi sannan nafara dariya nace
"Kinjiki kawai kibari idon kukaje kyagani ai dake za,aje gobe ko bazakiba?"
"Au waidama hardani za,aje jere?"
"Eh Mana abinda nazo fada mikifa kenan Innarmu tace afada Miki kishirya da wuri Yaya zasu
biyo shida Nafisa da anty safnah"
"Okay Allah yakaimu aikuwa nidai before hakan kikiramin shi kitambayeshi" dariya nayi nace
"Kefa dadina dake naci"
"Eh naji nidai akirashi kawai"
Wayata nadauko kallona takeyi cike da mamaki sannan tace
"Yaushe Kika canja waya bansaniba"
"Ohhh namanta Ashe Baki ganiba ranar Friday ya kawomin wallahi"
Dariya tayi take
"Lallaima wannan angon bayajin garin Nan wato harda canja waya"
Murmushi kawai nayi tare da kiranshi,
Har takatse bai dagaba Sai yabiyoni dagawa nayi tare dayin sallama ya amsa nan nace
"Ya weekend?"
"Alhamdllh y Innarmu ya gida?"
"Inna tana gida tana lafiya kalau"
"Ina kikaje?"
"Gidan Ayshat"
"Da izinin wah kikaje?"
Tambayar tabani mamaki Amma sainace
"Banganeba"
"Zaki gane ai kibani amsa wa Kika tambaya?"
"Innarmu"nabashi amsa atakaice Sai yace
"Uhm bakijin magana ko shine Zaki fita bazaki tambayi mijinki ba Sai bayan kinje sannan
kiwani fadamin"
Dariya nayi nace
"Wai nufinka idon zan fita Saina fada maka? Kabari lokaci yayi Wanda Dole Saida izininka zan
fada maka"
Dariya yayi sannan yace
"Zan kamakine ai Zaki gane kurenki"
Murmushi kawai nayi sannan nace
"Ayshat keson magana dakai"
"Okay Bata wayan ai yanzu muka rabu da mijinta yazo office dina ya Dade"
"Ayyah Allah sarki gata"
Namika mata hararata takeyi sannan takara kunnen nata gaisawa sukayi sannan ta
tambayeshi maganar unguwar da gidan yake sukayi maganarsu bansan me yake cemataba har
suka Gama sannan tamikamin wayan,
Karba nayi nakara akunne yace
"Wai dama bakinsan inda gidanki yakeba?"
"Ai baka fadaminba"
"Ohhh kekuma kinwuce kitambayeni wato Sai nine zan fada Miki"
Uhm kawai nace sannan yadora da fadin
"Wallahi ni nama manta ban fada mikiba ai anan GRA yake"
"Okay Ashe anan yake?"
"Eh nanne Babu nisa da gidan hajiyata ai"
"Ayyah Allah sarki ya hajiyar take?"
"Tana lafiya kalau"
"Masha Allah"
"Yaushe Zaki tafi gida"
"Sai da yamma"
"Okay kijirani zanzo na daukeki"
"Allah dama kabarshi kawai karna baka wuya"
"Ohho komadai menene nidai sainazo"
Yana fadar haka ya kashe wayar,
Kallon Aysha nayi nace "ashema Sai anwuce ta Nan"
"Eh Nima haka nace Kinga idon za,aje GRA Sai anwuce ta hauran wanki"
Kasancewar nanne unguwar da aka kawo Ayshat,
*****************
Yaune zamuje kunshi Amma Saida mukaje makaranta don wata lecture zatayi Mana test don
haka muka fara zuwa bayan angama nida Ayshat muka wuce wurin kunshi,
Sai dare sannan muka taho daga gidan kunshin don daima Mahmud din Aysha ne yaje ya
daukomu Saida suka kawoni gida sannan suka tafi munrabu Akan Sai gobe zatazo don gobe
jum'at Kuma ranar za,ayi daurin aure,
Gida nashiga nasami Baki sunzo Amma bawasu masu yawa bane gwagwo da anty jummala
Nan muka zauna nafara gaidasu sunata tsokana ta Wai amarya nasha kamshi dariya kawai
nayi nashige daki nace
"Wallahi nagaji wanka zanyi"
Bayan nayi wanka Nan aka hadu da Nafisa Yaya da Innarmu akayita fira kamar kar arabu,
*********************
Rana Bata karya saidai uwar Diya Taki kunaya,
Yau andaura auren *Nafeesat Adam jigo da Muslim Muhammad* bature akan sadaki naira
dubu dari da hamsin Wanda dubban jama,a suka shaida bayan ansakko daga sallahr juma,ah,
Lokacin da mahbub yazo Yana murna Yana tsalle yace
"Innarmu andaura auren" gabanane yayi wata kalar faduwa saikuma