Showing 39001 words to 42000 words out of 50228 words

Chapter 14 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf

da dukkan makiyanku ameen, tashi kije nasan anata jiranki"
Kuka nake tare da rike hannun Innarmu hakan da tagenine yasakata kamani ta fito Dani tsakar
gida Nan suka kamani muka fita wajen mota,

Motane duk sungama shiga cikin motoci don haka muna shiga aka bar layinmu inata kuka,
Gwagwo ce takemin fadan Wai nadaina kukan haka ai taga yanzu Yan birni sundaina kukan
aure nidai inajinta nayi banza da ita don nasan tsofane ke damunta,
Bansan inda aka kainiba Saida naji suna cewa mufito zamu shiga gidan uwar mijina agaidata
Nan nagane gidan hajiya mukazo,
Munsameta afalo Nan muka zauna aka gaggaisa nidai Ina kudundune banbude kainaba hajiya
har kusa dani tazo tadafa kaina tace
"Diyata kiyi hakuri kinji kibar kukan Nan haka karya saka Miki ciwon Kai"
Sassautawa nayi da kukan Jin abinda tace Nan suka gama maganarsu Mika fito don tafiya
gidan,
Babu wani nisa don haka Babu wuya mukaje can,
Shiga akayi mutane nata shiga suna ganin yadda gidan yake,
Nan mutane sukaita santin gidan Ayshat mAh dake kus Dani itama Sai fadamin take wai gidan
ya hadu sosai mantawa tayi bamuyi maganarba lokacin da sukaje jere nidai Ina jinta nayi shiru,
Bayan sallar magriba saiga abokinshi yazo yace da Nafisa za,a kaini gurin kwalliya dagacan
za,a wuce dinner Suma sushirya kafin karfe bakwai da rabi za,a turo mota,
Nan tazo ta fada Mana nida Ayshat neh zamuje it zata zauna da kawayenmu dondaima
dukkansu sun sakko kayan ankon nasu,
Munje wurin kwalliyar maisuna tafida itace zatayi Mana kwalliya,
Saida nayi sallah sannan na canja kayana nazauna don afarayimin dama ita Aysha tuni anfara
yimata,
Kwalliya aka yimini sosai don tun wurin karfe bakwai akemin har karfe tara don lokacin Aysha
tayi waya da Nafisa tace mata suna gurin dinner din mutane duk suncika sosai,
Suma bangaran angwaye suna waje suna jiranmu Muslim neh da Mahmud sukazo tare Ayshat
tanacan wurin mijinta Wai yunwa yakeji shine ta tafi rakashi jikin wajen kwalliyar zaici abinci
hakan yasa Muslim zama acikin motar Yana jira,
Saida aka Gama yimin sannan nakirata tace gata nan zuwa,
Samuna tayi zaune Ina danna wayata tana shigowa tafara fadin
"Wow wow Amarya Kinga yadda kikayi kyau kuwa wallahi kinhadu sosai wow gaskiya kinyi
kyau nifa nama rasa abinda zance dake wallahi" turo Baki nayi sannan nace
"No ke barni kawai wallahi duk agajiye nake kamar zanfadi nakeji"
"Ayyah sannu Bari nabaki magani kifarasha akafin mufita" Jakarta ta bude ta dakko tabani
nasha sannan mukayiwa Mai kwalliyar sallama mukayi gaba,
Amota muka samesu ni baya nashiga itakuma ta shiga gaba.



*Comment*
*&*
*Share*

*By*



*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*



*🙆🙆 RAYUWATA CE*🙆🙆


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*🅿69_70*



Zaunawa nayi tare da gaida Mahmud amsawa yayi Yana tsokanata Wai amarya Bata laifi
murmushi nayi kawai sannan nayi shiru,
Tafiya aka fara motar tayi shiru kowa da abinda yake tunani saikuma can Ayshat suka fara fira
ita da mijinta,
Abinda bansaniba Ashe shi gogan naku Yana nan yayi suman zaune da ganin yadda nayi
kyau nagama burgeshi yakasa ko dauke Ido daga kaina Sai zuwa can naji ya riko hannuna
kallonshi nayi Sai Naga ya dagamin gira murmushi nayi sannan nace
"Barka da warhaka"
"Ohhh wato da Baki ganniba ko?"
Girgiza kaina nayi batare danayi maganaba jawoni yayi jikinshi sannan yace
"Baby kinyi kyau kyawun da bazan iya fadarshiba don idon zan fadeshi bansan mezan fara
fadaba, abinda zan iya fada shine Ina kishin wasu mazan su kallemin wannan gayun wallahi
Amma babu yadda zanyi dole nahakura"
Murmushi nayi sannan na kalleshi nace
"Aidai kafini yin kyauma" nakarasa maganar cikin sigar shagwaba,

Murmushi yakarayi sannan yace
"Karkiji zancen Wasa wallahi tunda nake bantaba kallon mace Mai kyawun kiba Kuma haka
bantaba ganinki kinyi min irin kyawun da Baki taba yiminba, kinyi kyau da kalar wannan shiga ta
fararen kayan Amma ni nasani kece Kika haskaka shigar ba shigarce ta haskakakiba baby
wallahi Ina yimiki kaunar da bana tunanin.........." Katseshi Mahmud yayi inda yace
"Kai malama wannan bayani haka kabari idon kuka koma gida kwayu yanzu lokacin mutanene
don haka Bismillah tun dazu muka karaso Baku saniba"
Kallon wurin nayi azuciyata nace wow *meenah event center* yayi kalli wurin kamar rana
bazaka taba tunanin dare bane idon kana ciki saidai idon ka daga kanka sama zaka gane
hakan,
Fitowa mukayi sannan aka Gama gyara yadda za'a shiga cikin wurin taron,

Shiga mukayi ciki taro yayi taro mutane sun cika wajen ni abunma mamaki yabani ganin yadda
wajen ya cika da mutane bayan mudai bamuyi rabon invitation hakaba,


(Kasan cewar ni journalist Ina cikin wajen dama tun da wuri nazo don kar arugani cin kaji😋🤣
don haka nazo da wuri can na gano Yan groups kala kala sunsha ankonsu irinsu *kainuwa
writers, can na gano su, Ayshat m zazzau, Zarah Abdul, Anty fauzah 'yar amana, Nana Ayshat,
Zarah Faruq, official khadyy*, da duk Yan kainuwa don Nafeesat tabani invitation nabasu don
haka sun ziyarci wannan shagali, can na gano *RAYUWATA CE fans 1&2* su *anty fareeda
anata kwaso shoki dasu sa,adatu Aliyu, hauwa ayuba, hidaya, mmn hanan, mmn mus'b, mmn
haidar, mmn habib, anty Salma, anty shukrah,* da sauran masoyan Nafeesat duk suna cikin
wannan taro, Sai sauran groups din Dana ganosu Suma irinsu Rayuwar muce haka fans, home
of novels, da duk sauran masoyan wannan littafi dama masoya Nafeesat Baki Daya anata
kwasar kaji anaci da kuma girke girke iri iri, Sai kwasar gara akeyi, nimadai ba,a barni abayaba
wajen kwaso shoki don jikina har gajiya yayi)

Alhamdllh biki yayi Dadi yadda akeso anci ansha haka taro ya tashi cikin farin ciki da
annushuwa,
Amotar Mahmud muka dawo Nan suka kawomu gida sukuma suka tafi nasu gidan,
Muna shiga nazauna kan kujera shikuma Saida ya kulle kofar falo sannan ya karaso kusa
dani ya zauna tare da fadin
"Wash Allah Alhamdllh anyi biki lafiya angama gani ga masoyiyata akusa Dani yau ga mafarkin
dana Dade inayi yauga burina dana Dade inaso yacika ya cika, Kai Alhamdllh" ya fada Yana
daga hannnu sama,
Kallonshi kawai nayi sannan nayi murmushi tare da mikewa tsaye nace
"Saida safe zanje nayi Shirin bacci don agajiye nake" kallona yayi sannan yayi murmushi yace
"Lallaima baby me kike nufine da hakan wai?"
Kara kallonshi nayi sannan na kauda kaina nace
"Bacci fah nakeji"
Mikewa yayi tare da rikoni mukayi hanyar daki Yana fadin

"Nima inajin baccin don agajiye nake muje muyi wankan bayan mun fito Sai muci abinci don
Ina lure dake awurin dinner bakici komaiba Sai lemo kawai don haka dura zan yimiki yau
dinnan"
Shiru nayi nidai nama rasa abinda zance dashi Wai muyi wanka tare da shi, tab babbar
magana kenan,
Muna shiga dakin na Sami bakin gado na zauna sannan nace
"Please kaje dakinka kawai Nima kabarni nayi abuna" kallona yayi zuwa can yace
"Okay shikenan jeki kiyi Nima Bari naje nayi"

Fita yayi daga daki don haka na Mike tsaye tare da dakko jakata don daukar abinda zanyi
amfani dashi don akwai wani sirrin da nasamu a group din *gyara kanki* na *Anty khadeejah
journalist* don haka na dakkosu na shiga toilet,
Bayan na Gama wankan na dawo daki na dakko kayana Dana tanada Wanda zansaka dama
tun kafin yau na tanadi kayana saboda *Anty khadeejah journalist* tabamu sirrin kalar kayan da
yakamata ace mace zata saka ranar da ta tare agidan mijinta don haka nasaka kayana na
Kuma fasha turarurrukan da nahada sannan na yafa mayafina na Sami saman gado na Dane
dama Saida nayo alwallah tah kafin na fito daga bandaki,
Ina zaune najishi zai shigo nayi saurin jawo mayafina na Kara rufe fuskata,
Shigowa yayi bakinshi dauke da sallama yasamu kusa dani ya zauna Yana Dan dariya yace
"Ohhh Wai kice sainayi sabon siyan Baki kenan ai nadauka dinner ta karbarmin Ashe abin ba
haka bane?"

Shiru nayi hakan yasakashi matsowa kusa dani ya ciremin lullubin fuskata sannan yafara
magana yace
"Baby Ina Kara godewa Allah Daya mallakamin ke amatsayin matar aurena Allah nagode
maka, irin farin cikin da nake ciki bazai misaltuba tunda nake bantaba tsintar kaina a farin cikiba
kamar na jiya da yau saboda nasami abar Sona wadda na dauki shekaru Ina dakon soyayyarta,
nayi tsammanin zan Kara rasaki a Karo na biyu Amma Sai Allah ya dagamin ya cikamin burina
ya taimakeni ya mallakamin burin zuciyata, don haka inaso kitashi muje muyi sallah don mukara
Mika godiyarmu agurin Mai kowa Mai komai" Yana kaiwa nan yatashi tare da dagoni da kanshi
ya dakkomin hijjabi babba nan muka tada sallah,

Bayan munyi sallah yayimana addu,o,I sannan ya tashi da kanshi yaje ya dakko ledar da
Mahmud ya shigo da ita don Saida suka shigo har cikin gidan yayimana nasiha akan zaman
aure tare da addu'o'i sannan sukayi Mana sallama suka tafi,
Zama yayi ya bude ledar tare d budewa yace
"Bismillah muci" kasa saka hannu nayi hakan yasa ya matso kusa dani ya jawoni jikinshi inata
nukewa da mannani da jikinshi sosai yafara bani abaki har Saida na koshi sannan ya kyaleni
Shima yadanci kadan,
Toilet na shiga nayi brush nafito,
Samu nayi baya dakin don haka na koma bakin gado nazauna,
Saigashi ya dawo Shima toilet din dakin nawa yashiga fitowa yayi da alama brush yayi,
Karasowa yayi kusa dani yazauna yace

"Bacci fah kikace min kinaji Amma naganki azaune"
Hawayene ya wanke min fuska hakan yasakashi saurin fara tambayata menene me akayimin
meya faru menene
Nikuwa Babu abinda ya sakani kuka Sai yadda Naga ogan yanata wani rawarkai Yana
lallabani shine abinda ya kashemin jiki nafara hawaye,
Ganin yadda ya rudene yasakani cewa
"Kainane yake ciwo" kanshi ya dafe sannan ya dago Yana Fadi
"Amma Kuma shine Zaki Kama kuka basaiki fadamin ba Bari nabaki magani kisha" tashi yayi
ya dakko magani yabani nasha sannan ya kwantar Dani ya lullubeni yatashi yafita,
Ajiyar zuciya na sauke sannan na gyara kwanciya,
Harna fara bacci sama sama najishi ya dawo ya kashe wutar dakin yadawo ya kwanta kusa
dani sannan yajawoni jikinshi Yana shafamin bayana,
Gabana ke faduwa don jikina harya fara rawa hakan Daya gani shine ya sakashi yimin
magana yace
"Kiyi baccinki babu abinda zanmiki kinji?"
Hakan yasakani sakin jiki nafara baccinah,

Amarya da ango asuba ta gari,


******************

Washegari da asuba nice nafara farkawa Amma Jin yadda nake a jikinshi yasakani kwantawa
nayi shiru har Saida ya farka da kanshi sannan yatashi Yana addu,ar tashi daga bacci sauna
yayi tare da taba kafata yace
"Baby tashi muyi sallah zanje nayo alwallah a dakina indawo" to nace sannan ya fita nikuma
na tashi nashiga toilet alwallah nayi sannan nazo nafara nafilah Saida na idar da sallah sannan
yashigo kallona yayi yace
"Kardai kinyi sallahrki ke Daya Baki jiraniba?"
Murmushi nayi sannan nace
"A,a nayi nafilah ne"
"Ohhh yayi hakan tashi muyi sallah"
Tashi nayi muka gabatar da sallahr asbah tare da addu'o'i,
Kallona yayi yace
"Bacci bazai barmu yin karatuba muje mu kwanta "
Sunkuyar da kaina nayi sannan nace
"Ina kwana?"
"Lafiya kalau ya gajin bikin Yakima kan yadaina ciwon?"
"Eh ya daina"
"Masha Allah naji dadin hakan"
Tashi mukayi muka koma saman gado,
Yanzuma kamar dazu jawoni yayi jikinsa,
Ammafa sainaji labari yasha banban don jinai kafara wani abunda banganeba hakan yasa

nafara hawaye,

Nidai nace Allah ya inganta hajiya Nafeesat🤪

*****************

Bangaran su Yaya Adam anacan anatashan amarci shi harya gaji da wannan Abu ita Bata
gajiya idon taganshi agida ta dunga takurashi kenan tana damunshi da tabe tabe idon yace
mata yagaji Sai tace ita Bata gajiba don haka Saida yayi hakuri ya kyaleta,
Yauma kamar kullum suntashi da asuba yanasamu yashiga toilet don yayi wanka yayi sallah
kawai yaga mata acikin toilet din tace
"Shine kagudo kabarni to muyi tare wankan" babu yadda ya iya dole suka farayin wankan
amma ana cikin hakan sai wasa ya canja nan yafara niyyar kwace amma ina saidai taji ta
gamsu sannan ta rabu dashi sukayi wanka suka fito,
Suna idar da sallah ya kalleta yace
"Dear Bari naje nadan duba Abu Ina zuwa"
Kallonshi tayi tace
"Kayi sauri don Allah dear don Ina bukatarka gaskiya"
Kallonta yayi cike da mamaki yace
"To Bari nazo"
Yana fita yashige dakinshi tare da rufe kofar da makulli Yana magana a fili yace
"Shikenan kinmaidani kamar wani dabba saikiyita damuna keba wani dadinki nakejiba bana
samun biyan bukata yadda ya kamata Amma kiyita takurani, tsaki yayi sannan yace kawai kinsa
na rabu da matata wadda nake masifar sonta yanzu gashi wani shege yaje ya auremin matata
ai wallahi sainaji ajalinsa na dawo da matata na huta, kekuma Ina fatan Allah ya rabani dake
inhuta ace mata ko irin Yar kunyar nan Bata da ita saidai mannewa namiji tayita takurashi ni
wallahi duk maitata da mata wannan tafini, Allah neh kawai ya hadani da wadda tafini masifa"
hakadai yayita surutun shi shikadai cikin hakan ya jiyo maganarta tana buga Masa kofa ya bude
mata Amma yaki budewa yayi kwanciyarshi Yana jinta,


*******************


*Comment*
*&*
*Share*



*By*

*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*



*🙆🙆 RAYUWATA CE*🙆🙆


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*🅿71_72*




Kwance nake asama a saman gado Banda ciwon jiki da kai Babu abinda nakeji gawani kalar
zafi da yake tasomin daga kasana don haka tunda na fito daga wanka na kasa ko motsawa
nake kwance Ina hawaye,
Shigowa yayi dakin don lokacin dana fito ban same shiba, shine ya hadamin ruwa ya sakani
aciki Yana kokarin yimin wanka nasaki kuka nace yafita zanyi da kaina hakan yasakashi tafiya
dakinshi Saida yayi wanka sannan yadawo dakin dauke da tea acikin cup Sai magani,
Karasowa yayi kusa dani yazauna abakin gadon tare da dagoni Yana fadin
"Haba baby nace kiyi hakuri kibar kukan nan haka karya saka Miki ciwon Kai please"
Kukan na daina Sai hawayen dake zirarowa ta idona kawai bani yayi nafarasha yasakamin
maganin abaki nashanye sannan na koma na kwanta,
Tashi yayi yafita zuwa can Kuma Sai gashinan yadawo ya kwanta kusa dani tare da jawoni
jikinsa cikin tsora nafara kokarin kwacewa ganin hakan ya sakashi cewa
"Please kiyi baccinki Babu abinda zanyi miki, idon kikayi bacci Kika tashi zakiji jikin yayi Miki
sauki"
Jin abinda yace yasakani yin shiru Ina raba idanu don har lokacin a tsorace nake,
Bacci ne ya daukeni Ina Nan kwance bansan me yafaruba Sai karfe shabiyun Rana sannan
nafarka,
Tashi nayi ganin baya dakin yasakani mikewa nayi toilet yanzu Babu laifi naji dadin jikin ba
kamar dazuba haka nayi wanka nayo alwallah,

Fitowa nayi nasaka atamfa ajikina Riga da zani sannan nayi sallah don lokacin har Daya
takusa kasancewar Saida na Dade a toilet nakara gasa jikina,
Baya na idar da sallah nazauna nadan gyara jikina nayi simple makeup sannan nagyara dakin
sosai in Banda kamshi Babu abinda dakin yakeyi da jikina,
Fitowa nayi falon na sameshi zaune Yana danna system dinsa dagowa yayi Yana kallona Jin
kamshin turarena yasakashi kallona har nazo kusa dashi na zauna tare da gaidashi kallona
yake nikuwa nayi kasa da kaina don Banda kunya Babu abinda nakeji shiyasa nakasa hada Ido
dashi, Jawoni yayi jikinsa yace
"Lafiya kalau baby ya jikin naki?"
"Da....da....sau...ki"
"Allah sarki baby dazu nayi babban laifi ko ayimin afuwa bazan kara irin wannan laifinba Allah
yayi Miki Albarka, saidai abinda nakasa yarda dashi shine ya akayi haka ta faru bayan nasan
kintaba yin aure?"
Shiru nayi Ina Wasa da yatsun hannuna hakan yasa yace
"Kiyimin bayani Ina cikin wasi-wasi akan hakan don abin da abin mamaki"
Cike da Jin kunya nayi Masa bayani yadda zai gane akan zamana da Yaya Babu abinda ya
shiga tsakanina dashi Sai suka da zagi,
Rungumeni yayi Yana murna tare da yiwa Allah godiya yafara fadin
"Gaskiya naji dadin hakan Allah na gode maka daka nunamin wannan rana Dana sameki
matsayin da ko wanne namiji yake murnar yasamu matar aurenshi Allah na gode make dakasa
wannan wawan bai samarmin matataba Allah Kaine ka tsare wannan baiwa taka Allah ka Kara
tsaremin ita duniya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login