Showing 30001 words to 33000 words out of 50228 words
Chapter 11 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf
Badata nayi Ina dariya nan nafara chatting na dora pic din namu a WhatsApp da Facebook
mutane nata tayani murna wanine Wanda ban taba chatting dashiba Naga yayimin magana a
Facebook messenger yace min
"Ke meyasa Kika saka pic dinki aduniya kowa ya gani bakisan hakan nada matsalabane?"
Kallon sunan nakarayi abin yabani mamaki ganin sunan wai *Uncle* to waye hakan kuka,
Katsemin tunani yayi danaji yace
"Dazaki Kama Dora pic dinki kekadai akaiwa haihuwar ne ko Wanda amayiwa nagadai pic
baby kawai yasaka Banda nashi Amma ke ga gwana kinwani saka naki" haushi maganar tashi
tabani dakuma mamaki to a Ina yasan Yaya Kuma no yaushema na amsa friend request dinshi
gyara zamana nayi sannan nafara typing nace "Malam waye Kai Kuma dazaka yimin wannan maganar haka?"
Shiru yayi zuwa can yace
"Mutumne ni Kuma kiyi saurin gogewa hanason kikara saka pic dinki aduniya"
"Tab lallai yau Naga karfin Hali barawo da sallama, nida abuna sannan wanine zai nunamin Isa
akanshi to naki nacire din ai Allah yasa pic dinane bana waniba ehe"
Typing yafara zai maidamin amsar maganar danayi Masa naji Innarmu nayimin magana tace
"Kinga nafisa zanje gidan kafin ta farka nayi girkin da za,a kawo nandin"
"To Inna adawo lafiya Allah ya tare hanya"
Da ameen ta amsa ta fita.
*Comment*
*&*
*Share*
*By*
*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*
[10/4, 7:46 PM] Hayat: *ν ½νΉν ½νΉ RAYUWATA CE*ν ½νΉν ½νΉ
*Na*
*Khadeejah Sani (Journalist)*
*ν ΌνΌKAINUWA WRITERSβν ΌνΏΌ ASSOCIATION*ν Ύν΄ν ΌνΏ»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*ν Όν΅Ώ49_50*
Innarmu ce tafita Nan nadawo kan wayata da kallo amsa yabani da fadin
"Ke inayi Miki magana kina maidamin to kiyi gaggawar cireshi kafin ranki yabaci, shikenan
bakusan inda za,a kaimaku pic ba kidunga sakawa sukuma wadan can masu Kama da
bunsuran harsun fara yimiki comment to kiyi sauri kicireshi kafin na nuna Miki asalin kalata"
Ai ganin abinda ya fadamin yasakani saurin zuwa na guge pic din banawa kadaiba harda na
babyn Saida na cire sannan na kashe datan na rafka uban tagumi Ina tunanin waye wannan
haka Mai kokari dazai hanani abinda nakeso,
Wama yasani ko aljanine baisaniba,
Aikuwa Dana shiga uku da aljanine nake magana dashi,
Tsorone ya kamani natashi da inda nake nakoma kusa da nafisa daketa bacci inata raba idanu
don atsorace nake kamar ace Tak nazura aguje,
Bata farkaba har mama tazo don haka nadan saki jikina Amma duk da haka Saida tagane
tacemin
"Waini tunda nazo naganki wata kala kodai bakida lafiyane?"
"Mama kaina kemin ciwo kadan kadan shiyasa"
"Ayyah sannu mamana ai Naga alama tunda nazo naganki wata kala sannu"
"Yawwa" Sai lokacin nafisa ta farka Nan mukayi mata sannu mama ta hadamat tea tafarasha,
Muna haka sunata fira nidai bana tofa komai Sai murmushi kawai nakeyi,
Muna haka Yaya yadawo Nan yakira likitan data karbi haihuwar tazo ta dubata sannan tabamu
sallama fitowa mukayi baki dayanmu mukayi gida a motar Yaya,
Lokacin da mukaje hidan Innarmu harta Gama girki don haka tasakani nakaimusu daki,
Bayana nagama duk abinda zanyi nayi sallah tare da wanka nadawo daki kan kujera na
kwanta sannan na kalli Innarmu nace
"Innarmu yaushe za'a kwasomin kayana daga wancan gidan inason nayi amfani da sauran
kayana Kinga Koda Yaya yaje ya dibomin ba dukkansu bane akwai wasu" kallona tayi tace
"Ai dama baban naku yayimin magana jiya yace Wai aurenshi yakusa aje akwashe Miki
kayanki nafadawa yayanku da yace yau zakuje ke dashi da nafisa to gashi Kuma ta haihu
saidai kibari idon gwagwanku tazo kwaje, tunda anyi haihuwa nasan cikin satin nan zatazo"
"Allah ya kawota lafiya, Amma anfada musu ko?"
"Eh dazo nayi waya da ita dakuma anty larai duk since zasuzo Amma ita cewa tayi kafin suna
zatazo"
"Allah ya kawota lafiya"
"Ameen"
Duk firar Nan da mukeyi hankalina yanacan wurin tunanin chatting dina da Uncle Wanda
nakasa gane wayeshi Kuma naje don naduba friends dinsa banga Wanda nasaniba haka Kuma
Babu pic ko guda Dana sani, daukar wayata nayi nasake bude data nashiga Facebook,
Har yanzu Yana online sainaga ya turomin Tex yace
"Ya gida ya Inna ya mahbub dakuma antynki nafisa da new baby din mu?"
Duk yajero min wannan tambayar Saida na nisa sannan nabashi amasa atakaice nace
"Duk suna lafiya"
"Masha Allah, kekuma ya karatunki Ina fatan bakya Wasa dai ko don banason Wasa da karatu"
yakara fada shiru nayi Ina Kara maimaita karanta message din sannan nace
"Alhamdllh"
"Ya kawarki Ayshat yarinyar kirki ai Babu laifi tanada tarbiyya"
Cikin mamaki nake Amma nadaure nace
"Tana lafiya lou"
"Shine yau Kika gudo daga makaranta ko waike kinyi baby to idon Kuma akayi muku test kiyi
Yaya kenan"
"Mahadu a exam ai"
"Hahaha lallaine yarinya"
Yakara da fadin
"Kinga nikuwa da ace nine dasaina kadaki kuwa"
Uhmm" kawai nace nayi shiru,
Hakadai mukaita fira dashi nakasa sauka ga tsoro fal cikina ganin danai duk kusan abubuwan
dake faruwa a makaranta yaketa fadamin harda yimin maganar wani yaro dan department
dinmu dake Sona yayimin Wai karna yarda da soyayyar makaranta Kuma karna yarda yaji ko
yaga Ina kulashi don bayason shashanci idon karatun zanyi nayi bayason kule kule, Kainane ya kulle bayan na kashe data Nan nafara tunanin lallai bazai wuce Aysha ba itace ta
fadawa wannan mutumin wani Abu akaina don haka na kirawo number dinta bayan gaisa nace
"Aysha wanene wannan uncle din da kike fadawa abubuwa akaina?"
Shiru tayi zuwa can tace
"Ke kawas banfa gane me kike nufiba meya faru ne haka?"
"Kinga Yar rainin wayo bansaniba, inace kinfini sanin duk abinda yafarun"
"Ke Wai meye haka wallahi bansan abinda yafaruba kiyimin bayani don Allah"
Nan nafada mata yadda mukayi da Kuma Abubuwan dayake fada akaina Wanda Kuma nasan
ita kadaice tasani tunda idon naje makarantar tare muke komai ko maganar saurayin iata aka
fara Tara aka fadawa Wai yanasona Amma yakasa yimin magana, abin yabata mamaki don
haka tace "Wallahi wallahi Allah kuwa bantaba magana da waniba akanki, kinji na rantse Miki inba da
mamarmuba Babu Wanda yasan Ina tare dake Sai Sadiq dina shikuwa har gaisawa kunshayi
dashina inace koyau shine yazo yadaukeni amakaranta yace kina Ina nace anmaku haihuwa
kintafi har yacema zamuzo barka tare dashi, Amma wallahi kiyarda Dani Babu Wanda mukayi
wannan maganar dashi"
Shiru nayi zuwa wani lokaci sannan nace
"Nayarda dake wallahi shikenan nagode saimun hadu Monday kenan ko?"
"A,a gobe da yamma zanzo Naga babynmu ai"
"To saikinzo goben agaida mama da Sadiq"
"Zasuji sosai, Nima agidan Inna da maman baby da baby"
Nandai mukayi sallama cikin mutunci,
Tunani nakeyi akan maganar da mukayi har nahukara na barwa Allah kawai zan dage da
addu,a Allah ya bayyana minshi nagan ko waye haka,
****************
Kwanaki sun tafi ansha shagalin suna yarinya taci Sanu Fatima wato sunan Innarmu za,a
dunga kiranta da zahra,
Su gwagwa sunzo daga katsina ansha shagalin suna munje munkwaso kayana komai Saida
nakwaso hatta tv Dina banbartaba saina nasmu Mai kwancewa ya banbaromin kayata duk
nakwashe kayana gidan tsaf dashi anata Kara gyaranshi saboda za,a saka amarya,
Kwanaki nata tafiya nafisa harta Gama wanka tana Shirin dawowa tunda Daman washegari
suna takoma gida wanka,
Da baba yaso yahana Sai Innarmu tabashi hakuri tunda taga yarinyar nason komawar, Kuma
itama mama tanaso kawaidai tayi karane Kuma tunda tazo ganinta a asibiti aka sallameta
mukazo gida Bata Kara zuwaba don haka Innarmu tabashi hakuri ya yarda takoma gida wanka,
Tadawo lafiya Zahra takara girma fa wayo tasan mamarta idon wani ya dauketa tadunga kuka
kenan bta yadda da kowa Sai mamarta da mahbub saikuma ni,
Amma kar tasani da zarar Innarmu ta dauketa zata saka kuka hakama babanta bata yarda
dashi,
Haka rayuwa keta gudu yanzu gamunan har munshiga nce2 karatu yakara yawa don haka ko
chatting bana samunyi sosai dondaima banason naki Hawa online saboda uncle munyi wata
kalar shakuwa dashi sosai har jinake kamar so shi nakeyi don yanzu ko tunanin Muslim banayi
sosai kamar yadda nake tunanin Uncle,
Yauma kamar kullum bayan nadawo daga makaranta nagama abinda zanyi nakwanta Ina
kallon chat Dina dashi don yanzu har WhatsApp mukeyi dashi,
Kawai saina kunna data natafi muna firar bikin Aysha don bikinta ya matso saura sati uku,
Sakonahine Naga yashigo don haka nayi sauri fitowa dakoma wurinsa,
Pic Naga ya turamin kala kala abinda na Dade inaso ya turan Amma yaki saiyau tsaki nadanyi
sannan nafara kokarin budewa kawai sainaga fuskar da bazan taba mantawa da iataba har
abada Amma takara kyau haske hutu kallon pic din nakarayi nafara magana afili nace
"Anya kuwa wannan pic din na .................."
*ν ½νΈ³ν ½νΈ³ To ni journalist pic din waye Nafisa tagani kodai pic din Yaya Adam neν ½νΈν ½νΈ kokuma
naν Ύν΄ Babu ruwana kartace nafiya shishigi Kuma Sai zura kaina nake nagani Amma Taki barina
don haka nace muzuba idon dani daku dasu ma gani a nex page*
*Comment*
*&*
*Share*
*By*
*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*
*ν ½νΉν ½νΉ RAYUWATA CE*ν ½νΉν ½νΉ
*Na*
*Khadeejah Sani (Journalist)*
*ν ΌνΌKAINUWA WRITERSβν ΌνΏΌ ASSOCIATION*ν Ύν΄ν ΌνΏ»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*ν Όν΅Ώ59_60*
'Yan matane suka fito da abokanan ango don shiga da amarya fitowa sukayi daga motar Nan
aka jera nice agaba Sai uncle agefan ango,
Amarya da ango ne kebin bayanmu nan muka shiga tare da sauran mutanen tafe muke ana
daukarmu a hotuna da video,
Ina lure da Uncle ransa a bace yake Sai wani hade fuska yakeyi Yana shankamshi kamar
Wanda akayiwa wani abu ganin yadda yake jeromin harara yasakani daina kallon ko inda yake,
Ahaka mukaje mukasami wuri mukazauna Ina zama natashi don zuwa wajen kawayenmu nan
nafara gaisawa dasu Daya bayan daya,
Taro ya fara kankama don wajen Banda tashin kida Babu abinda kakeji awurin,
Saida nagama yimusu sannu sannan nasami kusa da Nafisa nazauna nan nake tambayarta
Yaya tace
"Yana waje ai dama baishigo ba kinsanshi bayason irin wannan abun"
"Okay ashe Yana can aikuwa banganshiba dazamu shigo kokuma Yana nesa da wurin da
mukayi parking ne"
"Kila bawuri Daya kukayi parking ba"
Muna nan munata fira kawai Sai jinayi ana Kiran sunana Wai nazo nabada tarihin amarya
atakaice kallon Nafisa nayi tare da dafe kirji nace
"Nashiga uku kinji abinda kawas tayimin ko?"
Dariya tayi sannan tace
"Hahaha wallahi kinbani dariya kuwa kawai tashi kije kiyi abinda aka bukata malama"
Niyyar Bata amsa nakeyi naji Ankara kirana don haka namike jiki a sanyaye nayi wurin kowa
dake wurin sunzuba min idanu karasawa nayi cikin nutsuwata da takun hankali Ina tafiya anutse
Amma alokacin zuciyata Banda bugawa Babu aminda takeyi kirjina Sai dukan uku uku yakeyi
harna tsaya tare da karbar abin magana nagyara tsayuwata sannan nafara tunanin da wanne
yare zanyi magana hausa ko turanci,
Tunawa nayi ai turanci ba yaranmu bane gwara mudunga yin amfani da yarenmu a kowanne
wuri bawai ba'a iyaba a,a Koda ka iya kawai kayi yaren kasarka,
(Wannan babban kuskurene waanda muke fama dashi acikin kasarmu Wai idon mutum baiyi
yaren turanci ba Sai adaukeshi Mara ilimi, uhmm Amma abin duba anan shine yadda kowacce
kasashe suke amfani da yarensu Kuma suke alfahari dashi, don hakan yakamata muma
mugyara gaskiya mudunga koyi da sauran kasashe munayin yarenmu a wurare irin wadan Nan
tonda acikin wannan taron kusan dukkan mutanen dazasu halarci wajen hausawane ko akwai
turawa Basu da yawa don haka saikayi yarenka da kowa zai fahimta maza da mata yara da
manya, Allah yasa mugane Ameen)
Bayani nafara kamar haka
"Assalamu Alaikum warahamatullahi wabara katahu, dafarko Ina Mai fara mika sakon
gaisuwata dakuma godiyata gareku, iyayena,yayyane,kannena da Kuma kawayena, muna
godiya ga dukkan Wanda yasami halartar wannan shagali Kuma munsan ku masoyanmu ne
nagaskiya don haka saidai muyi muku fatan Alkairi tare da addu'ar Allah yakai kowa gida lafiya,
Allah yabar zumunci, wannan sakone daga kawata masoyiyata Kuma 'yar uwata Allah yasaka
da Alkairi, bayan haka sunana Nafeesat Adam jiggo Kuma Ina Daya daga cikin kawayen
Ayshat, itadai Ayshat Muhammad modibbo yarinyace Mai hankali ilimi nutsuwa uwa uba Kuma
ladabi biyayya da sanin yakamata, anhaifi Ayshat a mumbila tafara kataunta na primary a
mumbila Saida takai aji hudu sannan mahaifanta suka dawo Kano dalilin aiki Daya dawo dasu,
anan tadora katunta har zuwa lokacin da tayi candy, sannan tafara kokarin shiga makarantar
gaba da sandiri Alhamdllh lillah ansami abinda akeso tasami admission a FCE inda take
karantar computer maths yanzu haka tana karatunta anan saidai fatan Allah yabada sa'a
sabada abinda ake nema Ameen, (juyawa nayi na kalli wurin da suke zaune sannan nadora da
cewa) ango inamai Kara tayaka murnar samun Aysha amatsayin mata don hatta ni kaina
nayaba da kalar Alkunyarta, hakurinta, dakuma tarbiyyarta, ko shakka banayi nasan kayi dacen
mata ta gari zakaji dadin zama da ita insha Allah, Ina Kara tayaka murnar samun 'yar uwata
amatsayin mata saidai nabiku da addu'ar Allah yabaku zaman lafiya da zuri'a dayyiba Ameen,
Alhamdllh wannan shine takaitaccen tarihin rayuwar amarya Kuma uwar gida agidan Alhaji
Salis, Ina Kara Mika godiyata gareku da kuka bani aron hankalinku nagode Allah ya maida
kowa gidansa lafiya Ameen" Ina kaiwa Nan namika abin maganar na koma wurin amarya inda
aka tanadamin wurin zama,
Acan bangaran kuwa Yaya Adam ne yayi suman zaune Jin yadda nake magana kallona kawai
yakeyi tare da juyawa duniyar tunani,
Tun bayan rabuwarshi Dani take cikin tashin hankali don wannan aurenma dazaiyi bawai don
Yana sonta bane a,a kawaidai zai aureta ne saboda tafi karfinsa Kuma shidai bazai iya budar
Baki yayi wata maganaba akan maganar bikin Sai yadda tace haka za,ayi gashi kwana biyu
baya iya bacci kullum kwana yakeyi da tunanin Nafisa haka Koda baccine ya daukeshi tofa
Babu abinda yakeyi Sai mafarkinta bai Gama yadda da cewa sona yakeba Sai yanzu Daya
ganni Ina magana Ashe nasan amaryar shi angonne abokinsa don wurin aikisu Daya office
dinshi Yana kallon nashi shinema dalilin zuwanshi wurin bikin Amma yayi Daya sanin zuwa
wurin bikin nan,
(Nidai nace kwalelanka to don uncle ya ruga ya kwace abarsa aha baka isaba eheν ½νΈ‘ν ½νΈν ½νΈ)
Bangarena kuwa Ina karasawa nazauna tare da sauke ajiyar zuciya nace
"Washshsh Allah nah wallahi nasha wuya fah bakini har muryata tafara rawaba Allah kiris nake
jira nayi kuka kinsanni bana iya magana cikin mutane" murmushi tayi tace
"Ai wallahi ina Nan Ina maganarki nace nayi mamakin yadda Kika tsaya kinayin bayani Shima
dariya yagama yimiki" murmushi nayi nace
"Allah yasa dai nabaku kunya nayi abinda yadace"
Tashi nayi nace
"Bari naje nayi magana afara rabawa mutane abinci" sakkowa nayi Kuma lokacinne aka Kira
abokin ango Shima inajin sunayin magana da Uncle yace asaka wani shi bayajin Dadi bazai
iyaba nace oho maka dai nayi gaba,
Nayiwa masu zuba abincin magana sunfara zubawa don haka nafara duba uncle don Naga
baya wajen da naganshi a kusa da angon don haka nayi waje don naduba,
Ajikin mota naganshi don haka nakoma nakarba Masa abinci da lemo nakoma don nakai Masa
Saida naje nayimasa sallama Amma yaki amsawa don haka Sai kawai na ajiye nakoma
dakkowa Yaya don naganoshi cikin mota,
Nafisa nasamu tana shirin fitowa nace
"Ohhhh kaimasa zakiyi ne?"
"Eh gashi nan zankai"
"To wanna ya isheku kenan"
"Eh saidai ki Kara Mana drink din"
Ciki nashiga na nakko musu nafito don kaimusu bayan nabasu na koma kamar zan wucesa Sai
jinayi yace
"Zonan" kallonshi nayi yawani hade Rai kamar bashine yayi maganarba nakarasa wani na
tsaya nace
"Gani"
Ko kallona baiyiba yace
"Shiga ciki muyi magana"
Daukar kayan Dana ajiye nayi nakarasa nashiga nazauna a bayan motar ganin hakan
yasakashi karasowa Shima yashigo bayan yazauna tare da barin kofar abude kamar yadda nayi
sannan yafara magana yace
"Nafeesat kina sane kikemin wannan abun ko saboda kinsan kalar soyayyar da nake yimiki
shiyasa kike yimin haka ko?"
Kallonshi nayi Naga idanunshi sunyi jajur sunkara kankancewa daga gani kasan kishine kawai
yake damunshi don haka nace
"Uncle menayi maka Kuma?"
"Okay Baki saniba kenan?"
"Allah bansani ba"
Nafada cikin shagwabe fuska kamar zanyi kuka kallona yayi sannan yace
"Uhm shikenan"
Kara kwabe fuska nayi nace
"Please kayi hakuri to"
"Kinsan bazan iya fushi dakeba shiyasa kikemin duk abinda kikeso"
"Allah bansan abinda nayiba"
"Shikenan yawuce to, shine kika wani bude Baki dazu kinata zuba bayani mutane sunata
kallonki wani kamar yazo ya rungumeki Ina kallonshi Sai wani yake Baki yakeyi wani Kuma
yanata wani kwalalo Miki idanu saura kadan ai na