Showing 9001 words to 12000 words out of 50228 words

Chapter 4 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf

kallon gefe Daya yace
"Tashi kisaka hijjab dinki"
Kuka nakeyi nace
"Wallahi bazan iya tashiba bayana ciwo yakeyi kamar zai balle" Jin muryar datayi magana
yasakashi karasowa cikin sauri Yana fadin

"Nafeesat Nafeesat kece meya kawoki nan mesukayi Miki please Nafeesat kibani amsa
mesukayi Miki kuma suwaye wadan nandin?" Tambayar yakeyi cikin tashin hankali da firgici
hijjab din ya dakkomin yazo yasakamin tare da daukata gabaki Daya fitowa yayi wurin Babu
kowa don mutane Basu fiya wucewa tananba don haka yayi motarshi Dani da gudu Yana kara
maimaitamin tambayoyin suwaye mesukayimin,

Banda kuka Babu abinda nakeyi harya sakani cikin motar shiga yayi sannan Yakima yashiga
tare da tada mota,

Tuki yakeyi cike da rashin kwanciyar hankali tare kuma da tunanin abinda yakawoshi unguwar
tasu Yama kasa tantancewa yasandai Babu abinda zaiyi dazu yazo kuma yadan juma awurinsu
don haka yaketa tunanin abinda yasakashi zuwa unguwar tasu kuma ya ajiye motarshi yataho
akafa, Cikin tunanin barkatai harmuka karasa asibitin dake kusa da unguwar mu shiga yayi Nan naga
anata karasowa wurinsa anamasa sannu da zuwa baiko amsaba yakaraso inda nake zaune
don naji dama dama yabude tare da kallona yace" Zaki iyayin tafiyar?"

Daya kaina nayi alamar eh sannan nafito ahankali nake tafiya harmuka karasa ciki wani office
yabude yace
"Shiga ciki inazuwa" shiga nayi Ina tunanin Daman wannan mutumin yadakkoni Allah
yataimakeni dazo ya kwaceni ahannun wadan Nan mugayen datuni yanzu sungama ketamin
haddina sun zubarmin da mutuncina na 'yamace hamdaoa nayi sannan nadora da fadin
"shikuma yatashi yawani dakkoni kamar wata baby Sai wani rawarkai yakeyi....." Bude kofar da
akayine yasakani nayi shiru shigowa yayi tare da sallama wata mata abayanshi Tana rike da
kayan aikinsu na likita karasowa yayi ciki Yana fadin
"Baki zaunaba kenan Kika tsaya haka?" Shiru nayi Ina sunkuyar da kaina kasa juyawa yayi
Yakima baking kofa yace
"Sister gatanan kifubamin ita sosai please kitanbayeta komai" Yana kaiwa Nan yayi waje,

Kallona tayi tare da murmushi tafara tambayata Ina Bata amsa Nan nafada mata Babu abinda
sukayimin kawaidai bayana ke ciwo Amma yasaki Nan tace shikenan tafita zaune nake har
yakara shigo namike nace
"Zantafi gida kar Innarmu taking shiru" magana nakeyi Amma kaina nakasa nakasa had a
idanu dashi,

Kallona yakeyi cike da tausayi sannan yace "muje to" fita yayi nabi bayanshi,

Take muke Babu maiyiwa want magana harmukaje kofar gidanmu Sai lokacinma natuna da
buhun wakena dakuma Mai dazan karba wurin maikantin layinmu Nan nafara hawaye naki fita
Daga motar shirune yarats motar nawani lonaci sannan yace
"Yada kuka kuma meyafaru?"
"Waken da Innarmu ta aikeni siyowa yanacan nabarshi". Sai lokacinma yatuna yaga buhu
awurin don haka yace
"Jeki gida nakawo Miki" to nace tare dayimasa godiya nasauka shiga fitowa yayi yace
"Kishiga gida in nadawo zanyi magana"to nace tare dayimasa godiya nashiga gida,

Ina shiga nasami Inna tsaye baking kofar soro tanata tunanin ina natsaya kukan dataga
inayine yasakata fara jefomin tambayar,

Kasancewar bansaba boye mata komai nawaba yasaka nafara Bata labarin komai Daya faru
har Muslim Daya taimakeni dakuma kaini asibitin da kawoni gida dayayi yanzu harma da
dakkomin buhun waken Dana bari acan,
Salati kawai takeyi tare da fidda hawaye tace "nagodewa Allah Daya kawo wannan bawan
Allah Daya taimakeni ya taimakeki yauda bansan yadda zanyiba aikuwa wannan awarar anbar
yinta insha Allah baza,a karayi a Allah yabamu yadda yadda yadda,ayi gaskiya bazamu
karayiba ahakura kawai munemi wata Sana,ar" tana kaiwa Nan tayi shiru donjin Ana kwada
sallama Jin muryarshi yasa innarmu cew
"Jekice Masa yashigo" wucewa nayi na fada Masa don haka muka shigo tare,
Shimfida tabarma Innarmu tayi yazauna itakuma ta tsugunna agefe buhun waken nakai
kitchen nashige daki,

Mahbub nasamu kwance don haka nakarasa tare d tabashi jinai jikin yakara zafi don haka
natadashi don nabarshi magani,


Bangaransu Innarmu kuwa gaisawa sukayi tare da jajanta abinda yararu Nan Innarmu
tayimasa godiya akan abinda yayimin tadora d cewa
"Ai tunda abin yazo da haka Sai ahakura da awarar dama tafadamin yadda sukayi d
wadannan yaran tun kwanaki" Nan Innarmu tashiga bashi labarin yadda mukayi dakuma abinda
najisu suna Fadi,

Bakaramin mamaki yayiba donjin nasanma wadanda sukayi yunkuri ketamin haddina don
haka yace insha Allah bazai barsuba saiya bimin hikkina kuma arabani dasu don irin wadannan
abin tsorone,

Nan suka Dade sunata fira Shima yace d Innarmu abaryin awarar adunga yimasa t dubu uku
kullum zaidunga karbar ta dubu daya sauran kuma adunga sadaka da ita,

Sallama sukeyi zantafi daidai lokacin mahbub yafito ya tsugunna Yana kwara amai nikuma Ina
rike dashi inamai sannu,

Saida yagama nagyara wurin Yakima gefe yakwanta don haka Muslim yakarasa wurinsa Yana
dubashi fita yayi yace yanazuwa yadan juma awake sannan yadawo dauke d Leda kallona yayi
Ina zaune ga hawaye afuska ganin yadda mahbub yaketsa wani mikewa Innarmu tana shafa
Masa ruwa tacemin Suma yake don haka duk atsorace nake,
Jin muryarsa nayi yace "Inna akaishi inda zai kwanta zandaka mishi ruwa yadda zaifijin dadin
jikin" to tace tashi tayi tashiga dakinmu tafara gyara gadon inda za,a dorashi,

Bayan tashinta ya kalleni yace
"Kekuma hawaye baya Miki wuyar zuba Naga alama, yanzu meye na kukan?"
Kallonshi nayi tare da kara matso wasu hawayen nace
"Uhm................



*Kuyi hakurin rashin jina kwana biyu, hakan yafarune dalilin rashin lafiyar danake fama dashi
kwana biyu, kuyi hakuri yanzuma kokari nayi nayimuku wannan, please Ina bukatar addu,arku
bisa wata Yar matsala data faru Dani please my fans I need your prayers*👏👏👏👏👏


*My lovely mom inamai kara tayaki Al,ajabin abinda yasameki Allah yakiyaye gaba Allah ya
tsare my Mom da dukkan yan,uwa musulimi baki daya*ν ½νΈ­ν ½νΈ­ν ½νΈ­ν ½νΈ­ν ½νΈ­


*By*



*Khadeejah (Ummu Fu,ad & Afnan)*
[9/7, 6:11 AM] Hayat: ν ½νΉ†ν ½νΉ† *RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†

*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*




*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


*Dedicated to Ayshat m zazzau*



https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

ν Όν΅Ώ *15 - 16*



"Uhm kana ganin yadda yakeyifa" wani hawayenne yazubo min nakara shareshi da hannuna,
Innarmu ce tafito tace
"Yawwa bari akaishi dakin saika saka mishi"
Mikewa yayi yace
"Bari nadaukeshi Nafeesat shigomin da kayan Nan" tashi nayi tsaye nabishi da kayan Innarmu
tabiyo bayana itama,

Gadona danake kwanciya naji Innarmu tace anan za,a dorashi nandin kuwa aka sakashi aka
daura Mai Kari ruwan sannan ya nunamin yadda zancire Masa idon ruwan yakare sannan
yanuna min maganin nashi da yadda za,a bashi,

Innarmu tayimasa godiya sosai sannan yafita wajen na rakoshi tare dayi Masa godiya Nan
yace Saida safe zaizo yaga jikin nashi,
Najuya ina niyyar komawa cikin gida yace
"Nafeesat" juyowa nayi tare da amsawa,
Karasowa yayi kusadani yace
"Kibani phone number naki saboda anjima naji yaya jikin nashi"
"Wallahi wayana babu sim" kallona yayi cike da mamaki Wai wayana Babu sim menake nufi to
ahaka nake ruke da wayan Babu sim,
"Kamar yafa banganeba"
Murmushi nayi nace
"Bansaka sim bane da akabani wayar Amma zansaka insha Allah"
"Okay ga wannan wayar kiyi amfani dashi kafin goben nataho Miki da SIM card din" murmushi
nayi nace
"A,a kabarshi kawai"
"Saboda me kikace haka?"
"Innarmu zatayimin fada"
"Okay yayi to kibani number din Innaryamu inyaso saina Kira anata naji"
Karba nayi narubuta Masa Sannan mukayi sallama,

Kulle gidan nayi nashiga nasami innarmu zaune kusada mahbub Nan nafada mata yakarbi
number dinta zuwa anjima zaikira yaji ya jikin nashi Nan tace nadakko wayar narike awurina
inya Kira muyi maganar to nace nadakko,


Kwance nake kusada mahbub Wanda ruwan da akasaka Mai harya kare nacire Masa bacci
take hankali kwance nikuwa nakasa bacci tunani barkatai yayimin yawa fargabata tayadda
zankara fita waje naje wani gurin mainisa don harga Allah tsoran fita nakeyi daga gidan su
Musa sungama bani tsoro gaskiya,
Karar wayar Innarmu ce tafarkar Dani daga tunanin danakeyi Nan nafarka firgigit nadauki
wayan bakuwar number ne don haka nagane shine ke Kira,

Saida takusan tsinkewa nadauka tare da karawa akunne nayi sallama,
Ajiyar zuciya yasauke sannan ya amsamin sallamata gaidashi nayi dukda dazu mungaisa ya
amsa tare da tambayata jikin mahbub nace
"Jiki yayi sauki bacci yaketayi baima tashiba"
"Ayyah Allah yakara sauki"
"Ameen mungode Allah yasaka da Alkairi Allah yabiya"
"Irin wannan addu,a haka nagode sosai Amma banason yawan godiyar Nan kinji tayi yawa ai
idon nayimiki Abu kamar nayiwa kainane" shiru nayi don banganeba meyake nufiba dorawa
yayi da fadin,

"Tunda Allah yayi nadora idona akanki Sai naji duk yan mata duniya basa burgni kece
tauraruwa guda daya acikin su haskenki yana sa nasu ya dushashe hakika Allah yayi miki
baiwar daba kowacce mace gareta ba, sai an laluba gaki da tarbiya, ilimi, ladabi, uwa uba kuma
biyayya gana gaba dake, kinada wadatar zuciya, haka kuma tarbiyyar da aka doraki akanta
itace kowanne namiji yake burin matarshi takasance da ita, sannan tadora yaranshi bisa kalar
tarbiyyar da aka dorata agidansu, tunda nadora idona akanki nagane nayi dace mata tagari,
nayi facen abokiyar rayuwa, Alhamdllh, Alhamdllh, Alhamdllh, Ina godiya ga Allah ne Daya bani
damar sauke nauyin dake cikin zuciyata na tsayin watanni masu yawa, inaso kiyiwa maganata
kyakyawar fahimta kuma kifadamin abinda ke ranki karki boyemin komai please my baby kiduba
maganar Dan marayan Nan, kifadamin abinda kikeji game dani"

Shiru nayi Jin kalar kalaman dayake antayomin Yama sakani jikina dukkanshi ya mutu Baki
Daya nama kasa Koda motsin kirki kuma narasa menake ciki farin cikine kokuwa akasin
hakanne,

Cikin tunanin danakene naji yakara magana yace
"Kiyimin magana please kozanji sanyi cikin raina, kifadamin ko menene duk abinda yake
zuciuarki inasonji my baby Fadi wani abun"

Gyara kwanciyata nayi sannan nafara magana cikin sanyin murya kamar banason magana

nace
"Nagode da wannan yabon dakayimin kuma agaskiya naji dadi sosai Allah yabiyaka da
mafificin Alkairi, Abu nagaba kuma naso ace kafadamin wannan maganar tunkafin lokaci yakure
mana, Amma saidai baka fadaba har lokaci hakure Mana don ayanzu bani da damar amsar
soyayyarka saboda......" Katseni yayi cikin sauri yana fadin "Saboda me kina nufin kice kin mallakawa wani zuciyar Dana Dade Ina tunanin tazama
mallakina don Allah karkicemin haka wallahi Ina kaunarki bazan iya rayuwa Mai dadiba inba
tare dakeba please karkiyimin haka" yakarasa maganar cikin sanyin murya,
Bakaramin tausayi Yabani ba kuma Nima kaina naji tausayin kaina don ganin nasami maimin
so irin Wanda bana tunani gashi lokaci yakuremin ajiyar zuciya nasauke nace
"Yau kwana biyu kenan babana wato yayan babana yakirani da maganar aure kuma
yafadamin zai hadani da yaronsa aure nanba da dadewaba kojiya yazo gidanmu sunyi maganar
da Innarmu don haka inamai baka hakuri kuma inaso kasani kasaka aranka ni Nafeesat Ina
sonka Ina kaunarka saidai banida yadda zanyine da bazantaba aurar waniba inbakaiba, kayi
hakuri nagode da kalar soyayyarka gareni" inafadar haka nakashe wayar tare da fashewa da
kuka,

Bangarenshi Shima kukan yakeyi kamar wani karamin yaro azuciyar ya kudurce bazai iya
rayuwa da kuwaba Sai ita Amma ya akayi akarigashi akayimasa irin wannan shigar Allah
yadafamin abinda yake maimaitawa kenan ganin dayayi Babu wata mafita kawai yatashi ya
dauro alwallah yafara fadawa Mai kowa Mai komai,
Bangarena Nima hakance tafaru Dana kasa bacci natashi nafara salloli.



*By*


*Khadeejah (Ummu Fu,ad & Afnan)*





[9/8, 12:47 AM] Hayat: ν ½νΉ†ν ½νΉ† *RAYUWATA CE* ν ½νΉ†ν ½νΉ†


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


ν Όν΅Ώ *17 - 18*



Washegari da safe muntashi jikin mahbub dasauki sosai,
Hakan bakaramin dadi yayi manaba saidai Babu kwari jikin Yana kwance duk yarame kamar
aanda yayi jinyar watanni,

Nagama duk aiyukana dazanyi nayi gyaran gida nahada Mana breakfast dafaman tea nayi
saikuma taliya da manja dayaji (ν Ύν΄ͺ kwakelenki zazzau) dakkosu nayi nakawo Mana dakinmu na
ajiye,

Wanka nashiga nafito nasami Innarmu zaune zata hadawa mahbub tea din don harda Madara
aka siyamasa tunda bashida lafiya ballalai bane ya iya cin taliyarba,

Saida nagama shiryawa sannan nadawo falon nazauna tare da daukar cup zandibi nawa
nasha kwankwasa kofar gidanmu akayi don haka natashi naje don nabude hijjab nasaka tunda
bansan ko wayeba,

Ina budewa naci Karo dashi tsaye Yana murmushi fuskarshi ta Kara kyau ajiyar zuciya muka
sauke atare sannan nayi saurin dauke kaina Ina fadin
"Inakwana"
Murmushi yakarayi yace
"Lafiya kalau yajikin mahbub?"

"Dasauki bara nafadawa Inna" inafada najuya cikin gidan,

"Innarmu ga wannan mutumin yazo duba mahbub" kallo tabini dashi saikuma tace
"Waye kuma wannan mutumin banason shashancifa?"

Murmushi nayi nace. "okay Muslim zance mantawa nayi" hararata tayi sannan tace yashigo
tafada tare da saka hijjab dinta,

Saminsa nayi tsaye jikin motarsa Nan nace Masa yashigo,

Shigowa mukayi nice agaba Yana biye Dani abaya har muka karaso dakin,

Zama yayi a kasa tare da tankwashe kafa Yana gaida Innarmu nidai cikin dakin nashige don
kunyarsa nakeji,
Bayan sungaisa yake tambayarta yamai jiki tace
"Wallahi jiki Alhamdllh kaganshi yanashan tea saidai rashin karfin jikin danaga baya iyazama
sosai saidai kwanciya"

"Alhamdllh to Allah yakara sauki ai yanzuma sakamasa za,a karayi saikiga yasami karfin jikin
insha Allah"
"To madallah nagode Allah yasaka da Alkairi yabiya da gidan aljanna nagode Dan nan nagode
badan kaiba dabansan Yaya zanyiba jiya kila da saidai ya mutu bamu da yadda zamuyi sannan
ga taimakon dakayimana na wadancan yan iskan datuni sungama ketamana haddi don idon
sukayiwa Nafisa want abun kamar nisuka yiwa Allah yasaka da Alkairi" takarasa maganar da
kuka,

"Inna Babu komi wallahi ai anzama Daya Allah yakiyaye gaba kawaidai Sai akiyaye saboda
irin wadan Nan mutanan basuda mutunci kwata kwata kuma insha Allah za,asan abinyi akansu
baza,a kyakesu hakaba"
Fira sukeyi inadaga daki inajinsu banyi yunkurin fitowaba Jin muryar Innarmu nayi ta
kwadamin Kira tace

"Nafisa Wai Inace kece Kika zuba ruwan shayin Nan Amma kikawani shige daki kamar garar
kunya bazakizo kidaukaba Kisha karya huce"
Tashi nayi nafara leken falon zaune yake inda nabarshi bisa darduma fitowa nayi gashi kofin
Yana kusadashi don haka nakarasa cikin sanda tare da dauka Ina niyyar komawa daki nayi
Innarmu tace
"Kizo kizubawa yarona Shima Mana kinata wani sanda ohh ni narasa meke damunki yau dinan
tunda safe kiketa wani lakwai lakwai" komawa nayi nadauki cup nafita waje nawanke nadawo
nazubamai tare da mikamai,

Shikuwa zaune yake idonsa nakaina yazubamin ido Sai wani lumshe idanu yakeyi Yana kara
kallona,
Mikamai nayi yakarba tare da yimin sannu cikin siririyar murya wadda bana zaton ko innarmu
taji maganar da yayimin,

Mikewa nayi zankoma takara cewa
"Waike komai sainace Miki kiyi toki zubamai taliyar yaci saidai bansaniba ko yanacin taliya da
manja" takarasa fada Tana kallonshi,
Murmushi nan nashi yayi yace
"Inacinta Inna Amma yanzudai nakoshi wallahi wannan ma ya Isa nagode"
"Ohh Dana Kodai kaima ta yayansu Shima yace bayacin taliya da Mai shiyasa indai Yana Nan
bamayi" gyara zama yayi yace
"Wai nikuwa Inna a Ina yake aikene naji mahbub yacemin Wai Yana Abuja hakane kuwa"

Murmushi tayi tace "bawani aiki yakeba yadaiyi karatun yayi degree Amma baisami aikiba
shiyasa yake zuwa can irindai yan bige bigen nan nasamari yakeyi acan"
"Amma Inna maizai Hana yadawo yanemi aiki anan garin Ina ganin kamar zaifi zuwa can din"
"Umm banki tatakaba kasan yanzu aiki akasarnan yazama abinda nazama saikana da hanya
mukuma wallahi bamu da wata hanya dazamu nema tanan shiyasama danaga yafara nema
yanazaune nace yahakura yanemi wani aikin zaifi Masa kawai"

"Hakane gaskiya yanzu abun yazama abinda yazama Amma inason kisakashi yadawo insha
Allah za,a Sami aikin yadawo cikin satin Nan idon da dama insha Allah za,asan yadda za,ayi"

"To insha Allah zanfada masa yau dinnan mungode dana Allah yabiyaka"
Ameen yace Yana kurbar ruwan tea din,
Nidai inadaga daki har lokacin Daya tashi tafiya sukayi sallama da Inna kirana tayi tabani
wayarshi Daya manta tace nakaimai,

Fitowa nayi nasameshi zaune saman motarshi karasawa nayi nace
"Gashi kamance wayanka" dariya yayi yace
"Wallahi ina sane nabarta nasandai kece Zaki kawomin ai" murmushi nayi kawai yadora da
fadin
"Yanzuma zandawo ai zanje nadakko drip nadawo, kuma dama nace zamuhadu shine jiya
Kika kashemin way to?" Rufe fuskata nayi da tafin hannuna Ina dariya.



*By*


*Khadeejah (Ummu Fu,ad & Afnan)*
[9/8, 8:57 AM] Hayat: *ν ½νΉ†ν ½νΉ†RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Saudaukarwa gareki mamana Allah yajamin da ranki yakara girma*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login