Showing 27001 words to 30000 words out of 53214 words

Chapter 10 - Hafsat Ilham Book Complete by Billy Galadanci .pdf

20 Mar 2025

3498

mara nauyi tazo ta sameshi yana adu'a
Sosa kanta ta d'anyi ta tsaya sanda ya idar,tasowa yayi ha zauna a bakin gadon tace dashi

"Yaa Abdul ina so zanje na kwanta idan baka buqatar komai,na rigada na rufe ko ina na gidan"
hannunshi ya saka ya janyota ta fad'a jikinshi kwantar da ita yayi akan gadon yaje daidai saitin
kunnenta yace "Bana tunanin ina buqatar komai seke Elham na,yaya zaki tafi Kibarni ni kad'ai
kin manta banida lapia?" Wani irin kasala ya saukar mata kasa cewa komai tayi har cikin
b'argon ta takejin wani abu dabaza ta iya fassara ko meye ba,hannun shi yakai ya shafi mararta
lokaci d'aya numfashin ta ya soma barazanar d'aukewa da sauri ta d'aura hannunta saman
nashi se kuma ta soma kuka tace "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri" hancinshi ya saka a saman
nata yana gogawa a hankali batare daya janye hannunshi a saman marar tata ba,ita ma kuma

ta kasa d'auke nata,sannan ya kai bakinshi wurin kunnenta yace "Menene yake sakaki kuka
Elham na? Bakyaso nake zuwa kusa dakene ko me?" Cikin kukan tace "Nidai Kayi hakuri tsoro
nake ji" sakinta yayi yaje kashe fitilar d'akin ya d'are kan gadon,janyota yayi sosai jikinshi ya
lalubo bakinta yafara kissing nata passionately, kasa tureshi tayi kurin dai bata dena kukan
ba,seda yagaji dan kanshi sannan ya pulling out,yace cikin sigar rarrashi hannunshi na saman
kanta "Elham na menene? Bakyaso?" Gyad'a masa kanta tayi alamar e,janyota sosai yayi ya
rad'a mata a kunne

"To kiyi baccinki Na dena kinji,ko bakyason ki kwanta ajikin mijinki?" Banza ta masa yace "Ean
Elham na bakyaso?" Cura fuskarta tayi acikin k'irjinshi duk da suna cikin duhu,cikeda shagwaba
tace "To nidai ban ceba" Murmushi yayi ya k'ara k'ank'ameta a haka bacci me dad'in gaske yayi
awon gaba da Dukkansu.
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

16
Abdul kamma kuka ya saka ya zauna yana ta bata hakuri,dakinta ta koma ta k'ulle kanta,ta
zauna tanata rusan uban kuka,tama rasa me zatayi,kiran momy tayi tayita kuka tamata ta'aziyar
Ameer amma ta kasa gaya mata sakin da Abdul ya mata,bayan sun gama ta share hawayenta
ta kira Aunty husna,komai sanda ta sanar mata,nisawa Aunty husna tayi tace
"Kinga Elham,bazamu bari aurenki ya lalace haka a banza ba,karki kuskura kowa yaji wannan
zancen, koda yace ze dawo dake karki yarda amma ki Barshi wlhy ze kawo kanshi
ne,hujjojinshi basuyi karfin da zeyi wasa da saki har Hakaba,duk da yake yanada ban tausayi
amma wlhy bazamu aminta ya lalata rayuwar kiba,yanzu ki nutsu Elham saki akwai ciwo ba
kad'an ba, kuyita hakuri Koda yace ki dawo Nigeria karki yadda,ki roqa a sama miki makaranta
anan" shiru tayi sabida tanaji wannan karon bazata bi zancen Aunty Husna ba kuma sam tama
tsani ganin Abdul,se can tace

"Aunty Husna nifa wlhy na tsaneshi bana san a gyara auren,ni sena sanar wa momy" sassauta
murya husna tayi cikeda rarrashi

"Haba Elham Karki yiwa momy haka mana,kinsan yanda take k'aunarki d'innan Zata iya yanke
jiki ta fad'i ga kuma an mata mutuwar Ameer na damunta,dan Allah na rok'eki ki gyara aurenki
da kanki batare da sanin kowa ba" nisawa tayi tace "Idan haka ne Aunty ina da shawara"

"To ina jinki Hafsat" daga nan ta zayyane mata komai yanda take ganin za'ayi dashi,ta k'ara da
cewar "Aunty wannan ne kad'ai hanyar danike ganin zamu bi,Abdul be kyauta wa kanshi ba
aganina kuma beyi jarumta ba amaimakon yayi jarumta ya nemi mafita seya sakarwa yan
uwansa ragamar rayuwar sa gaba d'aya"
"To Elham ina fatan Allah ya sanya wannan tsarin namu yayi working kinji" sallama sukayi ta
ajiye wayar cike da bacin rai,har kusan kwana ki biyar bata k'ara ganin Abdul a gidan ba da
wannan take tunanin bata yanda za'ayi plan nasu yayi working,a maimakon ta kira
Husnah,kurun se fushin zuciya ya d'ebeta ta kira momy ta saka mata kuka,cikeda wauta ta gaya
mata komai tsaf daya faru,B'acin rai me tsanani ya ziyarci momy,rayuwarta ta b'aci,bak'in ciki ya
lullub'e ta hankalinta ya tashi,kuka kawai ta saka ta kashe wayar,a fusace ta kira Number
d'inshi.....

Yana office zaune yana tunanin yanda zeyi da Elham so yakeyi yace ze maida aurenta amma
yasani bazata aminta dashiba,yana tunanin yanda zeyi rayuwa batare da Elham ba,yanzu ya
haqiqancewa kansa rayuwarshi batada wani amfani idan ba Elham,Mema zesa yayi wannan
tunanin har ya biyewa san zuciyarsa ya saketa,yana tsakiya da wannan tunanin wayarsa ya
soma ringing, gabanshi ne yayi mummunan fad'uwa ganin sunan momy domin kuwa basufi
awanni biyu da gama wayar ba,yakuma sani banza bata kai zomo kasuwa,jiki a mace ya d'aga
wayar....

"Baba na na gode da abinda ka sakamun dashi na sakar mun mama na da Kayi, ka mayar mun
da ita k'aramar bazawara,ka tozar tar dani,baka dubi halin rashin Ameer danake ciki ba ka
sakar mun yarinya,me kake so nace da iyayenta? Wlhy ka wulakanta ni fiye da tunaninka,kuma
ka sani sena rama da yardar Allah Mamana Zata auri miji wanda ya fika lallai ka Turo mun ita as
soon as possible sabida ta sanar dani ba iddar ka a kanta zamanku tare yanzu had'arine Babba
ba k'arami ba" kafin yayi magana ta kashe wayar koda ya kuma kira wayarta a kashe gashi
feenah bata gida yanzu bare ya kira ta bata,dafe kanshi yayi yata kuka tamkar k'aramin
yaro,seda yayi me isarsa sannan ya tashi zuwa gida,d'akin Elham ya wuce kai tsaye ya tarar ta
idar da sallah tana adua zama yayi harta idar,juyowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta

"Hafsat mesa kika mun haka? Mesa zaki zab'i had'ani da mahaifiyata? Menene ban miki ba a
rayuwa? Sabida kawai ki dauwama a farin ciki na sadaukar da nawa farin cikin,Ashe ban
cancanci ki rufa min asiriba? Bayaga haka na gama yanke hukuncin zan kama aure na,Mesa
bazaki fara tambaya na tsarin dana mana ba" wani mugun kallo ta wurga masa tace a fusace
"Wlhy Kayi kad'an na kuma zama matar har abada,da kake zancen kama aurenka sekace wata
tinkiya kokuma dabba,bakada labarin cewar Na gama idda,dole ne se an sake daura mana
aure,kuma bana buk'atar k'arasa rayuwata da ragon namiji,mutumin daze bar ragamar gidansu
ta lalace sabida rashin lissafi,aure na ya kare dakai har abada,banida iddar ka kuma Baba me
gadi ya kaini islamiyyah,an sanar dani cewar idan idda ta yanke baza'a k'ara komawa aure ba
se an d'aura kuma da waninka zan d'aura bada kaiba,na gama dakai har abada" duk girma irin
na Abdul kasa daure wa yayi ya saka kuka

"Elham wlhy bazan iya rayuwa batare dake ba,kuskure ne nayi kuma na gane kuskurene plss
give me a second chance" dariya ta kwashe dashi "Off course I can give u one big another
chance to destroy my life" matsawa yayi kusa da ita yace

"Ba haka bane Elham,wlhy kece rayuwata gaba d'aya, banajin zan iya rayuwa baki" ka tayi
magana wayarta ya soma ringing, dauka tayi taga yaa Ibrahim ne,d'agawa kurin tayi,t wani
shagwabe murya

"Yaa Ibrahim dan Allah fa tun yaushe na kiraka shine se yanzu kake kirana?" Daga d'aya
bangaren kuma Murmushi yayi najin dad'i yace

"Kiyi hakuri Rose kinji,inata aiki ne yanzunnan na shigo gida go lunch ban ciba" K'ara langwab'e
murya tayi tace "Yaa Ibrahim kai kuwa seka riqa wani tunamun da yaa faruk na,shine yake
kirana da Rose" Murmushi yayi shi yakasa gane kan Elham yanzu kuma tace dashi wai aurenta
ya mutu,kuma batada Idda dama auren dole akayiwa dukkansu
"Ehn love one tintin Kodai yanzu da yaa faruk za'ayi aurenne?" Dukda tasan cewar Abdul bawai
yana jiyo me Ibrahim ke cewa bane,amma seta tsinci bakinta da furta Kalmar "Bazan kuma aure
a gidan sarauta ba,indai yaa faruk ne na hak'ura gaba d'aya, kawai dai sunanne yake
zuwarmun da good memories damuka kasance a tare,he's such a nice person,nasan da ace
Shina aura,da Banyi zaman zawarcin k'uruciya ba a yanzu,baze tab'a saki naba sabida yana
sona sosai"

"To kiyi hakuri wata rana se labari,idan na kammala abinda nake zanyi kiranki" sallama sukayi ta
wuce bathroom kai tsaye tana me jin zafin yanda zuciyarta keso ta bata kunya akan
Abdul,mesa takejin tausayin sa ne?" Wannan itace tambayar data kasa samun amsarta tuni.....

Juyin duniya Abdul yayi amma Elham takasa bashi fuska,hasalima zagine ke Shiga
tsakaninsu,a haka a rikice ya dakatar da duk abinda yakeyi ya kwaso ta suka dawo Niger.......

Zagi na wulakanci momy ta masa,yashiga magiya amma fir taqi saura rarsa,iyayenta sunyi
bak'in cikin wannan wulakncin sedai wannan karon a wurin momy ta dawo da zama gaba
d'aya,d'akin feenah shine ya zama nata,hankalin Abdul be kara tashiba seda yaga har me
martaba Fushi yake dashi, shirya wa yayi yaje fadar me martaba,a durk'ushe yake agaban me
martaba yana kwasar gaisuwa,daga gaisuwar kuwa me martaba yamata banza,seda ya raina
kanshi sannan yace

"Abba dama nazone akan zancen Hafsat,dan Allah a taimaka a dawo mun da ita,tunda saki
daya ne,Inshaa Allah,wannan kuskuren baze sake faruwa ba" yafi mintuna sha biyar da gama
magana me martaba be kulashiba,ga bahalin cewa komai,se can yace

"Ina so kasani,mahaifiyata Hafsat ta kasance me rauni tun kafin zuwan tsufanta kasancewar

batada lapia ko kadan,mahaifiyar Elham itace ke d'awainiya da ita kasancewar a b'angarenmu
bamuda macen dazata kula da ita,bata tab'a gaji yawa da kulawa da itaba kazalika bata tab'a
karb'ar sisin kwabon mu na ladan d'awainiyar da take da ita ba, alokacin datake fama da
matsananciyar rashin lapiya Asabe baro mijinta take ta dawo ta kwana a wurinta,itace da kanta
ta samo mata maganin hausan datayi ta sha harta samu lapiya,tafara tafiya bayan tayi shekaru
takwas bata taka k'afafuwanta,sabida yaa d'aukar Mahaifiya ta matsayin mahaifiyarta tana
haihuwa ta sakawa yarta suna Hafsat!!! Yarinyar da shekara da shekaru Allah be basu
haihuwaba se daga bisani suka haifeta,soyayya me tsanani mahaifiyata keyiwa Elham wanda
wannan shaida ne kowa yasani" "shiru yayi yad'anja fasali sannan yaci gaba

" Anya Abdurrahman kayiwa Mamana adalci daka saketa da k'uruciya? Bakada labarin matsalar
da wannan sakin ya jamun awurin Mahaifiyata akan na bada auren takwararta akan mijin dabe
dace da ita ba? To ka sani gangan cin danayi abaya bazan k'ara maimaita irinshi ba har
abada,Elham ta kawo mana yaron dazata aura me suna Ibrahim kuma mun bashi aurenta
nanda sati biyu masu zuwa" zabura yayi tamkar wanda aka tsikara ya saka kuka agaban
mahaifinshi

"Dan Allah Abba kamun rai,na rokeku kubani wata damar nayi alkawarin zan gyara kura
kuraina,na baya,zan kula da ita zan rayu da ita cikin Aminci" Murmushi me martaba yayi irinna
manya yace

"Abdurrahman ka rigada kafara haduwa da darasin rayuwa, da wannan zakasan muhimmancin
tunani me zurfi kafin yanke ko wane irin hukunci" da kuka yabar wurin..... Sanye take da
doguwar rigar less ash color tayi rolling da red d'in mayafi,fuskar nan tasha makeup tamkar
babu abinda ke damunta,nan kuwa tunanin Abdul ya tayar mata da hankali matuka,tarasa
nutsuwar ta gashi sam ta gayya ta gayyato Ibrahim a rayuwar ta bata taba zaton cewar ze
gabatar da kanshi da sauri har hakaba, Dukda bata sonshi, amma a yanda Abdul ya wulakanta
ta Zata koyawa kanta san Ibrahim ko yaya ne......kamar wanda k'wai ya fashewa aciki haka
yake tafiya,a garden yazo ya sameta zauna kusa da ita,waigowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta
gaba d'aya,cikin sanyi murya ya furta

"Hafsat zuwa nayi muyi magana akan zancen aurenki da naji,dan Allah ki taimakamun karki
barni" wani malala cin Murmushi tayi tace

"Kamar yanda Kayi dogon nazari akan sakina kafin ka sakeni,haka nayi dogon nazari akan
auren masoyina Na haqiqa,Abdul bakada hurumin dazakace wai na fasa auren shaqiqina na
dawo hannun wanda bema san darajar iyaye na ba,inaso idan mafarki kakeyi toka farka,sabida
bazan tab'a auren kaba" k'ura mata idonshi yayi da suka sauya launi zuwa jajaye yace murya
na rawa

"Hafsat nasani ban miki adalci ba ko kadan,kuma ban isa in hanaki komaiba,nasani wannan
hukuncin dakika yankemun Na cancanci wanda yafishi,zan miki fatan alkhairi idan har kika zab'i
yin hakan amma wlhy duk halin dana Shiga kece sila,mutuwa zanyi ada na hakura dakene

sabida wasu yan dalilai,yanzu kuwa bayan munyi aure mun rabu na fahimci kece rayuwata tsaf
zan mutu idan nayi rashin ki my Elly,ina miki....se kuma tari ya sarqeshi janyo handkerchief yayi
ya tare wanda atake ya soma aman jini,gigicewa Elham tayi ganin wannan tashin hankali tazo
ta riqeshi " Yaa Abdul Sannu,meke faruwa da kaine? Aman jini na Shiga uku " ganin fa be
kulata ba kuma gashi se aman yakeyi ya matukar tayar da hankalinta,a rikice taje part d'in
momy ta sanar mata,a tare sukazo aka kwashe shi zuwa asibiti Elham se kuka takeyi wanda ita
kanta bata san kona meye ba,tsoro takeji karta rasa yaa Abdul d'inta wannan aman jini idan
yayi irin shi so biyu toko tabbas tsaf mutuwa zeyi dominnko ba abinda ze hana wa jininshi
tsiyayewa ta tas.....abin mamakin kuwa shine yanda doctors suka tabbatar musu cewar lallai
daga zuciyarshi har b'angaren ulcer lapiyarshi qalau,me martaba be yadda ba yasanya aka
masa general check up nan ma Lapiyar shi qalau.....haka ya shafe kwana ki goma cur besan
inda kanshi yake ba idan kuma yasoma aman jini baya tsayawa seya kusa amayar da yayayen
hanjinshi,Elham ita kad'ai setaje d'akinta tayita kuka daba tasan dalilin shiba,Gashi me martaba
yace aurenta ba fashi sora kwana ki 4 tunda ba biki za'ayiba daurin aurena kawai kuma Abdul
bashi bane angon kazalika ba waliyinta bane da har za'ace ajira warkewarsa,a yanzu an dawo
dashi gida sabida likitoci basu gane komai ba,inda ake zargin asiri aka masa,momy dukta ya
mutse ba itaba ba Elham ba,a haka ranar d'aurin aure tazo ba amarshi haka aka gangama
daurin auren......

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

18

Tun asuba ta farka taga baya nan,ga alama ma sallaci yaje ita d'inma sallah taje tayi,ta wuce
kitchen kai tsaye ta d'aura musu egeg yam with beef paper soup, ba jimawa ta kammala ta
hada masa coffee ita kuma ta had'a kayan tea nata ,a dining ta Jere komai ta wuce toilet kai
tsaye tana idar wa ta fito ta shafe jikinta da mai tafara sanya sure spray follewed by body splash
nata,ta bayanta ya rungumota ta na tsaye ajikin mirror d'in rufe idonta tayi jin saukar hannunshi
saman breast nata, dukda a saman towel ne seda taji wani yarrrr,bata gane menene yake mata
yawo a duk sanda ya rab'eta irin haka,jikinta ta janye da sauri ta sadda kanta k'asa,hannunta ya
janyo ta dawo jikinshi ya manna mata hot kiss a wuya yace "Elham na,ina kika Shiga ina ta
nemanki?" Murmushi tamasa

"Ina kitchen ne ina had'a breakfast"
"Dama yunwa ya addabeni oya saka kaya da sauri muje muyi break fast d'in" yaudai Hafsatu

kasa koda motsi tayi bazata iya saka kaya a gabanshi ba,kallonta yayi ganin tayi tsaye ta
sunkuyar dakai
"Bakiji ba nace ki shirya mu tafi ko" d'an ya tsanta ta saka a baki tace "Yaa Abdul ka bani wuri to
mana,zan sameka a dining d'in" Murmushi yayi ya fice batare da yayi magana ba,yau ma sanda
ta bashi abincin yaci sannan suka dawo parlor a saman cin yarta ya d'aura kanshi shi adole wai
ga mara lapia, ita kuwa kunyarshi take ji matuka yanzu......
Tun da safe Hafsat ke fama da wani matsanan cin ciwon kai amma bata sanar masa ba da
rana ma haka ta daure ta girka masu spaghetti da miyar Hanta kurun se ice tea, zuwa yamma
kam Hafsat jiki ya tsananta domin kuwa kasa yin girki tayi,Shikuwa baya gidan yaje ya gaisa da
mahaifanshi kasancewar jikinshi yayi k'wari.....sosai momy taji dad'in ganinshi agidan Ras da
shi tace

"Mamana fa? Ina fatar tana lapia?" D'an Sosa kunne yayi yace "Tana nan lapia lau momy tace
ma na gaidaki ai" Murmushi tayi "To Babana kadaiji tsoron Allah ka kula da yar mutane tsakanin
ka da Allah dan Allah na rokeka karka kuskura ka wula kanta musu 'ya,sunmaka halacci sosai"
"Inshaa Allah momy zan kiyaye komai da kika ce zan kula da ita" al Barka ta zabga masa ya
tashi ya fita......Koda ya dawo Elham bata parlor kuma yaje kitchen bata nan,kai tsaye bedroom
nata wuce ya tarar ta k'udundune a bargo se rawar sanyi takeyi,da sauri ya Hau saman gadon
ya d'an yaye duvet d'in "Hafsat lapia dai meya sameki?" Kasa bashi ansa tayi kurin dai taci gaba da zubar da zafafan
hawaye,dagota yayi ya d'aura ta saman cinyarshi yaji jikinta zafi rau "Hafsat plss Sanar dani
meyake damunki haka,jikinki zafi fa sosai" dak'yar ta iya cewa "Kainane yakemun masifar ciwo
sarawa yakeyi tamkar ze rab'e gida biyu" kan ya kama yaji zafi rau yace "subhanallah Elly tashi
muje asibiti,bazan barki gida da zazzabi haka ba gaskia" kasa cewa dashi komai tayi da kanshi
ya saka mata doguwar riga ya kinkimeta se asibiti, zazzab'in cizon sauro ne ke damunta aka
mata aluurai aka bata magunguna suka dawo gida abinsu,salar isha ma dak'yar tayi tayita ya
samu tasha tea kawai suka koma d'aki suka kwanta,janyota sosai ajikinshi ya rungumeta
yanata rarrashi nta se hawaye kurun takeyi sabida ita kad'ai tasan yanda kanta ke masifar Sara
mata,har bacci ya d'aukeshi ita bata rutsa ba,can Wuraren karfe ukun dare kukanta ya
tasheshi,"Hafsat har yanzu kanne?" Cikin kuka tace "yaa Abdul dan Allah ka k'ananun kaina
ciwo yakemun sosai wlhy,kuma ka matsamun k'afana suma suna mun nauyi saramun komai
yakeyi" haka ya tashi yamata kamun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login