Showing 9001 words to 12000 words out of 53214 words

Chapter 4 - Hafsat Ilham Book Complete by Billy Galadanci .pdf

20 Mar 2025

3487

d'acin murya

"Hafsat kin sani ni d'innan ba sa'anki bane ko? Kuma sarai kin sani yarannan rainani zasuyi
Idan har sukaga namiki magana kin k'i ji,plss mana hafsan momy Fulani,tashi ki shirya muje"
murya na rawa cikin shagwabar daba ta ma san tanayi ba harda kwallanta tace

"Allah ni yaa Abdul bazan biku ba,yanzunnan zaka disgani su feenah kuma sumin dariya,ni ba
wanda yake sona kowa ma ya tsaneni" fashewa tayi da kuka shi abinma dariya ya so
bashi,zuwa ya mikar da ita tsaye yace hannayenshi biyu duka a kafad'un ta "Bazan disgaski ba
I promise,jiya d'in ma Aina ce dake sorry,kuma yau ma nan zan kama dakin Nima,waye ma
yace dake ba me sanki? Kowa ma yana sanki Elly, baga momy ba dasu Inna?,plss kije ki shirya
muje kinji?" D'an tsukakken bakinta ta turo takuma yamutse fuska dama wanan dabi at tace
tace "kaje waje yanzunnan zan watsa ruwa na shirya mu tafi" Kallonta yayi yana dan kasalallen
Murmushi yace "zan jiraki a parlor and plss karki wuce 10 mnt" daga nan ya bar d'akin a gurguje
ta shirya cikin doguwar riga me santsi kalar sararin samani ya,ta yane kanta da guntun mayafi
pink color, jakar ta yar k'arama kalar pink takalmi nta masu uban tudu ma pink ne,powder kurun
tasaka da lipstick pink and purple dan tsukakken ba kinnan ya had'e karshe,kwalli ta saka take
manya manyan fararen Ida nuwanta suka k'ara girma hasken su yakara bayyana,tasowa yayi
domin yaga abinda ya tsaidata kusan 30 mnt,yasani su Ashraf ma sun gaji sabida kurun suna

tsoron sane suka k'i kiransa,a daidai lokacin daze Shiga d'akin ita kuwa lokacin take kokarin
fitowa,karo sukayi take ya bangajeta taje taga taga zata fad'i da sauri ya tarota jikinshi,kasa
magana yayi ya k'urawa tsukakken mitsitsin bakinta ido,ita kuwa ta tsare shi da manyan
idanuwanta yana kallon su kuwa ta lumshe su wanda hakan ba karamin saukar masa da kasala
yayi ba,take kuma kamshin turaren ta ya gama rud'ashi,saurin saketa yayi yace "I'm sorry Elly,
bansan kina zuwa ba" wara manyan idanu Wanga tayi akan nashi tace "Ba komai Nima ban
kula kana zuwa ba I'm sorry" janye wa yayi ta wuce yabi k'ugunta da kallo gani yake tamkar
danshi take Wannan rausayar,Murmushi yayi aranshi yace " yarinya bazaki rud'ani da Wannan
rangwadar da shagwabar muna funcin dakike ba wlhy" koda suka fito kowa ya gama k'osawa
Raihan ce sarkin baki tace a fusace "Wai mutum shiba kowa ba galadiman tsumma,yariqa
d'aukar kansa wata tsiya,kawai zaki mana iko a karin banza ki barmu anan for more than an
hour" batace komai ba,Ashraf ne me tuki,baba k'arami yana dayan gefen,yan matan susu uku
suka Shiga baya,yayinda Abdul ya zaga gefen da Elham take ya zauna,lura yayi da yanda
tsukakken tommy d'inta ya lafe ya kulleta yace "Elham have you eating?" D'an lagwabe kai tayi
batace komai ba,Raihan ce yar iyayi tace " yaa Abdul bafa abinda Wannan taci tun zuwan mu
anan,kasan halinta da k'yank'yamin masifa,yoghurt tasha jiya yauma haka" d'an Kallonta yayi ta
d'auke kanta daga dubanshi yace,yana meso ya b'atawa Raihan rai karta gane baya san
Elham,ko basason juna

"Elham mesa? Ban hanaki zama da yunwa ba? Kalli fa yanda flat tommy naki ya k'ara shigewa
ciki,Ashraf plss take us to a near by restaurant" d'an narkewa tayi harga Allah ita batasan cin
abincin wani restaurant arna ne fa sukeyi kuma ba tsarki sukeyi ba tace

"Noo plss yaa Abdul,zansha yoghurt I'm sure it will be OK" d'an mayarda dubanshi yayi kan
hanya yace "Ashraf muje restaurant kawai" shiru ta masa ita harga Allah batasan cin komai na
wuri,Mr Biggs ya kaisu kowa yafita shikuma ya riko hannunta haushi duk ya gama kashe
Raihan,har k'arami ya fahimci hakan,shima hannun nata ya kama yace "kema zakici abinci ne
habibty?" Da sauri tace zataci,koda sukaje suka zauna waiter yazo Elham se cewa tayi wai
popcorn da ice cream takeso se fayrouz,hannunta Abdul ya riko yace murya k'asa2 "menene
haka kike zama da yunwa? Sanar dani me Wannan k'walamar zasu miki' zuba mishi idonta tayi
tace

" I'm sure zasu k'osaddani,so worry not plss" kallon waiter din yayi yace "fried rice with fried
chicken plss" juyawa yayi aka Wadata su da abinda suke buqata d'in,cikeda yanga Elham kecin
popcorn d'in kai kace tilastata akayi,tana wani yamutsa fuska,itafa wannan abin dake baiwa
mutane haushi akanta bata masan tana yin shiba,hasalima haka Allah ya halicceta,matsa
kujerar sa yayi kusa da tata ya sanya hannu ya kwace kwalin popcorn d'in yace "Hafsat bazaki
bari momy tace nazo dake Kano na bari yunwa ze halla ka ki ba,so maza bud'e baki shinkafa
zakici" spoon din ta kaiwa kallo taga cewar na roba ne alamar dispose one ne,tamkar zatayi
kuka ta wara bakin ya saka mata,tana tauna shinkafar tamkar mecin magani,shidai bebi ta
kanta ba,haka yayita bata sanda taci kusan Rabi ya kara ebo wa ze bata ta janye kanta,kallonta
yayi alamar me hakan yake nufi,ta langwabe kai kurun,kara matsawa yayi da spoon din bakinta
ta karayi baya "Elham Sefa kin cinye shinkafar nan tatas" bata fuska tayi tace "yaa Abdul Allah

na k'oshi kuma fa kagan inaso zanci popcorn na da ice cream" Murmushi ya sub'uce masa
aranshi yace"kini babbiya kyadaiji dashi kike wani mun karairaya sekace anga ya miki ni
Wannan yana tasiri ne akaina" ita kuwa aranta se cewa tayi

"Mugu Wato sabida kurun suyi tsammanin yana kulawa dani,ta yanda ko aure mukayi nace
yanamun wani mugun abin ba wanda ze yadda dani"bece komaiba,kurun ya mike yabar wurin
Raihan se cab'e fuska takeyi,amota suka taddashi ya zauna inda yake zaune d'azu,tun daga
nesa ya kurawa flat tommy d'inta ido,sosai yake mamakin duk abin cinnan data ci Tommy d'in
nanan yanda yake dazu tamkar ba abinci aka zuba masa ba yanzu,Idan kaga tsukakken cikin
bazaka yadda ka sanshi ke dauke da wayannan manya manyan Heeps da duwawun ba,dukta
yanda ta cira kafarta tana tafiya ilahirin bayanta da gefen cinyoyinta motsi sukeyi,shi wasu
lokutanma tsoro take bashi wlhy,a hankali ya d'aga idonshi zuwa dukiyar fulanin ta, yaa ilahi ya
furta adaidai lokacin da suke kokarin shigowa motar ganin Raihan ta zago gefenshi yasanya
yafito da sauri ya nufi shagon tamkar yayi mantuwa yaje ya dawo,ya zauna gefen Elham ya riko
hannuta,wayarta yake kallo k'aya taccen pics nata data saka wall paper ya kurawa ido harga
Allah yana san hoton,ba karamin kyawu hoton ya masaba,a haka suka isa shop na sammanin
fatihu,mamakin yanda su feenah suka dage sunata kwasar kaya yakeyi ita kuwa ya kula she's
too materialistic,and tana da high test ba komai bane yake burgeta sedai batada zalama, ta ebi
jallabi yu masu kyau da tsada black ones dakuma coloured one's sunfi kala talatin,kawai taje ta
zauna,kallonta Abdul yayi yace "Elham kin gaji ne?" D'an yamutsa fuska tayi tace "yaa Abdul ba
gajiya bane ina wayannan sun isa" harara ya wurga mata yace sauran su Lace's fa da atamfa
material,shaddoji?" Murmushi tayi "bana saka shadda sam,Lace's kuma da atamfa,hmmm
aikawa nadan duba suma sun isheni" haushin tane ya cikasa yace "kinga bazaki hadani da
momy ba wlhy,dukkanin kayan da kika eva sunfi kala hamsin ne? Kuma acewarta 150 set za'a
miki nikuwa anawa ra'ayin 200 zanyi so maza muje har abinda be mikiba ki Zara,naga wasu
dresses a shop na friend d'ina jiya suma muje ki kwasa" kallonsa kurun ta tsayayi,a haka yaja
hannunta ya dinga jibagar kaya tamkar besan darajar kudaden sa ba,haka kowa ya siya kayan
ba laifi,saura aka barwa gobe kurun...... Yamma sosai suka dawo masauki,Elham ce tafara yin
wanka da Sallah sannan sauran ma sukayi,batare da sun sanar mata inda zasu ba, suka caba
ado suka fice,bata wani damuba tayi kwanciyar a dakin tana dannan wayar ta,kira ne
yashigo,taga bak'uwar lamba,d'agawa tayi da salkamarta,shi d'inma ya masa,suka gaisa yace
"sunana Ibrahim,nine wanda namiki katsalandan jiya,ma ina sone muyi sallama,karna bar gari
bamuyi sallama gobe asubar fari zamu juya zuwa abuja,Idan bazaki damuba mu hadu a inda na
ganki jiya" batayi masa musuba ta saka dress ta roba da siririn mayafi sosai surarta ta bayyana
a hakan tafito,zama tayi abinda ta sameshi suka kara gaisawa,yace dama ze mata sallama
ne,yayi mata wa'azin yanayin shigarta a kaikaice sannan yace "Hafsat inasan sanin menene
yakawo ki Wannan wurin ke kadai hotel ne fa" Murmushi tayi tace

"Yaa Ibrahim ban t'aba zuwa hotel ba sam,Wannan ma daka ganni nida yayyu na maza
nazo,dakuma yan mata irina susu biyu Munzo hada kayan lefene daga Adamawa muke,yan
gidan sarkin Adamawa ne yayin da Nike yar me gadin gidan sarkin tuni,babban d'ansa zan
aura,shine mukazo da kannensa maza da mata dayake auren gida Zakuyi dukkansu hadin
kayan lefe" gyad'a kanshi yayi alamar gamsuwa da baya ninta yace

"Se yanzu nakejin saukar nutsuwa akaina,da farko harga Allah na tsorata nazata cewar wani
abinne yasanya kike gudo daga Allah ya albarkaci auren da Zakuyi, ina fatan zumun cinmun
baze yanke daga nan ba" gyad'a masa kanta alamun ba abinda ze tsinka musu igiyar
zumunci,ya zaro wani kwalin har guda biyu ya mik'a mata,godiya sosai ta masa,sukaci gaba da
hira tamkar dama can sun saba,se dariya yake sakata,can ta hango Abdul ajikin mitarshi ya
hard'e hannayenshi a k'irji yana kallonsu ya murtuk'e fuskarnan tamau,ta abin ma tsoro ya bata,
sauri tayiwa Ibrahim sallama tajuya dakinsu....bayanta yabi yana zuwa ya banke kofar d'akin ya
shiga,bata nan tana bedroom, kai tsaye yabita can fin cikota yayi yace a fusace.

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).


*Aunty Mejiddah Musa,Wannan shafin nakine kyauta duk ke kadai,na gode da kaunarki
agareni*

05
Tana zuwa tayi Sa'a ba kowa kai tsaye dakinta ta wuce,fadawa tayi kan gado a rigin gine ta
saka kuka me tsuma zuciya....duk'awa yayi ya dauki kwalin wayar da sim card d'in yabi bayanta
dashi,da sallama ya isa gidan bakowa se k'anwarta Halima,tana ganinshi ta mik'e tsaye daga
wanke kwanukan datake tace "Yaya Yarima Barka da zuwa ina wuni?" D'an kallon yanayin gidan yayi ba laifi Ba kazanta sedai
warin dabbobin dasuke kiwo a gefe d'aya, yace "lapia ina Elham?" Dan Sosa kai tayi tace "Ni
kadaice agidan amma inaga sanda nashiga Sallah kamar naji shigowarta bara na duba d'akinta"
batare data jira cewar saba ta juya zuwa d'akin, dage labulen kofar tayi tace "Aunty Hafsat ga
Yaya Yarima yana magana dake" d'an saisaita kanta tayi batare data juyo ba ta ce,banasan
tsayuwa a waje,ki kawoshi cikin d'a kinnan" juyawa kurun tayi domin tasan da matsala taje ta
kawo shi har kofar dakin tace ya Shiga.....A yanda ta kwanta kife haka yazo ya sameta still
kukan takeyi mara sauti sosai,sosai yaji ba dad'i,harga Allah kukan mace na karyar masa da
zuciya ya sani kuma sam be kyauta ba yanda ya sakar mata maganganu,Shifa Wannan kurin
da nuna cewar ita watace shine yake bashi haushi dashi,dakin yafara bi da kallo komai k'al
k'al,gashi bazakace d'akin acikin gidan yakeba se tashin kamshi yake ya hade da Air
conditioner dake dakin,kai dubanshi yayi zuwa ga mirror nata,mamakin manya manyan
turarukan dake kai yakeyi,albashin ubanta baze siye daya daga cikin suba,lallai momy ta
sangartar da Yarinyar nan,a hankali ya tako yazo daf da ita zama yayi kan gadon ya sanya
hannunshi ya d'ago ta,batayi musu ba ya dauki kafarshi ya daura har saman gadon ya juyota ta

fuskance shi ya sanya hannunshi ya tallafo kanta ya sanya hannunshi ya share mata
hawayenta,so yakeyi yace mata tayi hakuri amma girman kai ya hana,tausayinta yakeji amma
yanajin kiyayyarta can kasan zuciyar sa,yayi iya yinsa harshen sa ya furta Kalmar hakuri amma
ya kasa,ganin haka ya sanya yanjanyota zuwa kirjinsa,a hankali yake patting bayanta,shida ita
bazasu fad'i tsawon lokacin da suka dauka a haka,kawai dai gani yayi jikinta duk ya mace
dagotan dazeyi yaga tana bacci,mayar da ita yayi kirjinshi yana mamakin kanshi bayaso ya
motsa yakasance bacci nta beyi nisa ba ta farka,yakusa 30 mnt tana jikinshi yana jin yanda har
lokacin take shasheka tana sauke ajiyar zuciya, ganin baccin nata yayi nisa ya sanya ya
kwantar da ita da kyau ya mik'e tsaye yana kura mata manya manyan dara daran
inuwanshi,lumshe ido yayi yana mamakin dalilin dayasa yake Kallonta, waige waige ya soma yi
a d'akin can ya hango sckool bag nata ya dakko ta ya zaro paper da pen ya rubuta dakyar "I'm
sorry Elly,plss call me as soon as u wake up" ya dakko wayar ya zura mata layinta ya kunna
sannan ya jona caji ya bar gidan gaba d'aya..

Wanka yayi ya shirya kwanciya,har ya Hau gado ya kwanta yayi adu'o insa Amma ya kasa
bacci, duk motsi d'aya tunano yanayin da suka kasance atare dazu yake,dogon tsaki yaja yace
a sarari "Wannan er iskar Yarinyar ta gama sabawa da maza,har ta samu damar yin bacci a
jikina muna fukar banza,tagama nuna wa momy itadin ta kwarai ce" har bacci ya daukeshi yana
mamakin kanshi yanda ya kasa manta Wannan moment din,dakuma yanda kwalwarsa keta
tariyo masa uban tsallen da ta doka a shop dasukaje dazu,yarasa dalilin daya sanya tsallen ke
bala'in bugeshi.

Elham ba ita ta farka ba se asuba da mamakin kanta ta duba agogo,tayi mamakin baccin
datayi iya saninta bazata tunano sanda tayi bacci sanye da kaya ajikinta ba,ga kuma fitila a
kunne,tunano abinda ya faru tayi jiki a san yaye ta tashi taje tayi wanka ta daura alwala tazo tayi
sallah,nan ta zauna tana ta adu'a, Idan aurenta da Abdul ba alkhairi bane kar Allah ya tabbatar
dashi,tana aduar neman gafarar kwanciya da tayi ajikinshi har tayi bacci alhalin hakan ya
haramta a tsakanin su,nan dai ta ga saqon shi,taga wayarta,banza ta mishi se Wuraren karfe
bakwai da Rabi ta fito ta gaisa da mahaifiyarta ta daura musu breakfast soyayyen dankalin
hausa da kwai,ta hada ruwan shayi ta kai dakin Innah sannan ta dauko nata tazo tadan
tsakura,ta ajiye....wayar tane tana yana ringing tana dubawa taga Abdul ne,d'agawa tayi tamkar
bata san magana tace "Yaa Abdul ina Kwana" gyaran muryarsa yayi "lapia lau kin tashi lapia
elly?" Shiru tamasa yace "karfe tara ki shirya zamuje Kano dake da feenah da Raihan,se bayan
sati d'aya zamu dawo Idan munje,zan koma ne nanda wani satin kuma da siyayyar da zamuyi"
langwabe kai tayi tace

"Yaa Abdul banida wanakken kaya fa,mafi akasarin dogawen riguna suna gun wanki plss Abari
gobe mana,Idan na karbo" sosai ta bashi haushi yace

"Kinga nifa ba laifi na bane,momy ce ta ce lallai yau zamu tafi so kije da kanki ki sanar mata
uzurinki" da sauri tace

"Kayi hakuri yaa Abdul bara kurin na ebi laces da atmfa,momy ta hana ni tara wanki fa,kuma

kaga jiya na kammala exams ban samu na kaiba"
"Karfe 9 ya miki a mota kinji bana san Wannan African time na kau yanci" kantayi magana ya
kashe wayar sa ya kama hanyar part din momy,a gurguje taje ta sanar da Innah da Baba anan
takejin seda aka tambayi baban ta ma,har hada ka yanta tayi ta fito waje kai tsaye part din
momy ta nufa taje kusa da ita ta zauna tace " momy na shirya" Shafa kanta tayi tace "Allah ya
kiyaye Mamana,dan Allah ki kula da kanki sosai ki tsare mutun cinki kamar yanda nasan
kinayi,kuma ki kula da mijinki daidai gwargwado,kai kuma Babana lallai ka kular mun da
Mamana amana ce na baka kakuma san yanda amana take ko" girgiza kai yayi,ta zaro wayar
daya siya mata tace tana kallon momy tana Murmushi "Momy kinga wayar da yaa Abdul ya
siyamun jiya,momy ki tayani godiya dan Allah jiya jiyannan tawa ta fadi ta cinye screen d'in"
Murmushi momy tayi,har ranta taji dad'i tace "Angode Babana Allah ya saka da alkhairi ya kara
bud'i" shima yaji dadin adu'ar ta matuka,a haka sukazo wurin mota dukkansu,Abdul ne ya kalli
kannenshi Baba karami da Ashraf gasu feenah yace "Baba karami,Ashraf,feenah da Raihan ku
karbi key din range dinnan ku biyo ni abaya,da mota biyu zamu tafi ni zan tafi da Elham" yana
fad'a tamkar yayi kuka,Wannan tsarin momy ne,su kuwa masoyan dama haka sukeso se murna
sukeyi zasusha hira soyayyah,Ashraf d'ane wurin yayan momy daya rasu kuma a hannunta
yatashi, shine ze auri Feenah a yanzu haka yana aikine da kamfanin MTN,kayan lefe ne akace
suje hadowa shine zasuje.....

Yamma likis suka isa Kano,a Tahir guests palace hotel sukayi masauki,kallon Baba karami
yayi yace"k'arami wayannan matan a kama musu suit Babba,ku kuma kujewa d'aki d'aya "
kallon shi yayi yace "Yaya Abdul kaifa?" Wrist watch nashi ya kalla yace "Ba anan zan sauka ba
ku dai ku zauna anan,kuma dan Allah banda shishirta,kusan wayannan yaran matsayin kannen
ku suke ku kula da mutuncin su" haka kawai Elham taji ba dad'i tace tana shagwabe wa "yaa
Abdul dan Allah kaima ka zauna anan" kura mata ido yayi nay'an dak'ik'u yace yana mayarda
kallon shi ga Baba karami "Zan muku waya goben ku shirya early,zamu fita da range dukkanin
mu" Da sauri ta sake jakarta tazo ta rike masa hannu "yaa Abdul dan Allah ka zauna anan hotel
d'in" cikin fad'a ya warce hannunshi yace "ke Wannan wane irin rashin hankaline,kece zaki
gayamun inda zan zauna kokuwa,bakida hankali" take idonta ya ciko da k'wallah su feenah
suka kwashe da dariya sosai Wannan ba karamin bata ran Elham yayi ba,har ranta taji
zafi.....bece komaiba ya ja motar shi yabar harabar hotel d'in, dakin da aka saukesu kowa tayi
wanka aka kawo musu abinci suka ci banda Elham yoghurt kurun tasha tace ta koshi,silent ta
saka wayarta ta fito waje,tasamu wurin flower bed dake zagaye wurin ta sadda kanta tana kuka
me ban tausayi,kyakyawan saurayin datun fitowarta ita yake kallo yazo ya zauna wurin
yace,cikeda iya tsara kalamai

"K'anwata duk abinda yayi zafi magani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login