Showing 21001 words to 24000 words out of 53214 words

Chapter 8 - Hafsat Ilham Book Complete by Billy Galadanci .pdf

20 Mar 2025

3501

ana saidawa" da sauri ta wani daka tsalla tace "Yauwa bara na saka hijab kin na"
Murmushi yayi yafara tariyo tsallen datayi yanda mazaunan ta ke girgiza san ransu,Shifa harga
Allah ya kusa ajiye zancen Khamis gefe, idanma asiri suka masa aiba laipi bane danya kusanci
matarshi kumama koda zasu rabu ai Gara yasan ya Mora,beside kyautuwa ma yayi a karya
taba sakin matarshi,tunda ai zab:in momy ce,da wannan tunane tunanen har tace "Yar megadi
na jiran Sarki me jiran gado,nafa kimtsa" beji dad'in maganar taba amma seya basar ya Mik'e
kawai ya zura jallabiya rsa ya ce "muje" haka suka jeera suna tafiya ba mewa wani magana
acikinsu,suna karya kwanar layin ya rik'e hannunta,kallon shi tayi batace komai ba,acan suka
siyo suka k'aro juice suka juyo,har suka iso ba wanda ke magana,anan suka bace tare suka cin
ye kazar tatas,mikewa tayi ta wanke baki ta dawo ta haye gadon ta kwanta abinta cikin nutsuwa
bacci barawo shine ya sungumeta suka ware..... Ba ita ta farkaba se Wuraren karfe biyu na
dare dama tana tsammanin zuwan period nata,aikam ciwon mara me tsanani ne ya tasheta,a
razane ta tashi sai kuka,se Innah take kira tana yarfe hannaye,a k'asa ya kwanta dama saman
carpet acikin bacci yaji kukanta ya farka da sauri yazo ya dagata ya daurata akan cinyarsa
"Hafsat lapia menene ya sameki haka" tana kuka tace "Yaa Abdul na Shiga uku mtrl pain ke
damuna mutuwa zanyi" tsoro yaji sosai ya rasa me ze mata,acikin rudu yace "Me ake baki Idan
yana miki ciwo ne?" Kasa ansashi tayi tayita kuka se tambayoyi yake mata amma sa. Ta kasa
amsashi sabida azaba,kan kace me wannan tafara amai me tsanani da gudu take zuwa toilet
yin aman,a haka har kusan asuba dawowa tayi ta kwanta akan cinyarsa duk ya damu tanata
kukan,hannu ya sanya yana d'an patting bayanta a hankali,da kad'an yaji shiru koda ya duba
tayi bacci sosai ta bashi tausayi yalwataccen gashinta duk ya baje ya rufe mata fuska se gumi
take had'awa hannu ya saka ya janye mata gashin a hankali ya sunkuya ya sumbaci goshinta
yace "sorry my wife, u will soon be well" kasa d'agata yayi ya barta anan tana bacci nta har
bakwai ta gota sannan ya lallab'a ya ajiyeta ya je sallah,kuma dawowa yayi kasan cewar flight
nasu se dare ze tashi ya sanya ya shige cikin jikinta ya rungumeta sosai suka ci gaba da baccin
Su,har cikin ransa yakejin wani dad'i jinshi ajikinta wanda ya kasa gane ko dad'in menene.


*kumun uzuri Kuyi hakuri da wannan ina busy ne*

Mom Nu'aiym ce.
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

13

Basu suka farka ba se after 11,shine ya fara farkawa mamakin yanda suka k'ank'ame juna
yakeyi,itama sarai ta farka amma seta kasa b'anb'are kanta daga cikinshi,haka kurun taji
kwanciyar ajikinshi na saukar mata wata nishad'i dajin dad'i,duk sanda yayi yunk'urin tashi se
yaga tana k'ara rik'eshi,gyara mata kwanciyar ta yayi ajikinshi ya rungumeta da kyau,k'urawa
fuskar ta ido yayi yana murmushin dabesan dalilin shiba,hannunshi ya saka ya yaye mata
gashinta daya rufe kyakyawar fuskar,idonta yake kallo yanda gashin idonta ya kwanta luf luf
gasu zara zara,sumba ya manna mata a cute lips d'inshi.seda ta gaji da baccin k'arya sannan ta
bud'e lumsassun idonta a hankali ta saukesu akanshi,Murmushi ya sakar mata ita d'inma ta
mayar masa martanin Murmushi,yace "Sannu Elly how are u feeling now?" Wani narkewa tayi
dak'yar tace "I'm feeling much better now but am seriously hungry" d'an gyara mata kwanciyar
ya kuma yi yace "To ai ked'ince kin iya san jiki da yawa,baki bari ma na motsa ba balanta na na
nemo miki abinda zakici nanfa ba gida bane" magana yakeyi d'auke da Murmushi a fuskarsa
wanda shima besan tame ye yakeyi ba,lumshe ido tayi ta yamutsa fuska tace "Nidai abinda
zanci plss" hannunshi ya d'aura akan gashinta yana shafawa a hankali yace "Elham to dake zan
tashi kid'an tashi mana" a hankali ta raba jikinshi da nata tayi cikin toilet wanka tayi ta dawo
d'akin ta tarar baya nan,ta zauna duk jikinta a mace yake ko man ta kasa shafawa, a haka
yashigo ya sameta ta kwanta ta k'urawa saman d'akin ido,zama yayi kusa da ita yace "Chinese
rice and meat balls, kokuma fried rice da paper chicken?" Turo baki tayi tace "Yaa Abdul shin
kafa da safennan ni indomie zan ci" k'ura mata ido yayi yace " Elham a ina zan samo indomie
yanzu? Dan Allah Kici wannan kiyi hakuri " batace komai ba ta sauko ta d'auki Chinese rice
d'inta da meat balls ta fara ci sanda ta cinye tatas sannan ta sha lemo ta kalleshi "Yaa Moris kai
bazaka ci abinci bane?" Murmushi ya sub'uce masa jin sunan data kirashi dashi yace "I'm OK
nasha coffee yanzunnan" tashi tayi ta Shafa manta sannan tayi brush ta zo ta kalleshi tace "Yaa
moris kaje parlor zan saka kaya" kwanta yayi ya bata baya yace "keda kika damu kya iya zuwa
can ki shirya abinki ni ba inda zani" ya mutsa fuska tayi ta tab'e baki ta kwashi kayan taje parlor
ta saka sannan ta dawo, wayarta ta d'auka ta juya zuwa parlor d'in taje ta kira Aunty husna,suna
gaisawa tace "Aunty da kunya wlhy da kunya abinda kike cewa Senayi,jiyafa cewa yayi banida
kunya" dariya Husna tai tace "kinga bawai rashin kunya nake Saka kiba gaskia ce kurun nake
d'auraki akanta,kisani mijinki baze kawo kanshi gareki ba a wannan yanayin se kin janyo shi
sosai ajiki,inasone ki saka abubuwan dakike a mizanin k'uruciya u stop being too serious kin
gane ai?" Murmushi tayi tace "Yauwa Aunty Husnah na gode zanyi yanda kikace" daga haka
sukayi sallama tana shigowa d'akin yace da ita " Elham zonan" batayi masa musu ba taje kusa
dashi ta zauna yace "sanar dani menene ake baki idan kina kalar wannan ciwon dakikayi jiya?
Na tsorata gashi bansan maganin dakike sha ba" d'an wara ido tayi irinna k'uruciya ta d'age
kafad'unta tace "Lipton ake had'amun me d'acin gaske ba sugar kokuma nasha cock amma fa
sam sedai yarage baya sauka kuma haka Innah tace se idan Nayi aure ze denamun ni banma
yadda ba yanzu ita da momy duk haka suke cewa amma har yanzu be dena ba,gashi kuma
Nayi auren kaga ni bara ma na kira momy na sanar mata Nayi auren amma mestral pain be
dena munba" ta saka hannu ta janyo wayarta da sauri ya k'wace yace "ke bakida hankaline
wai?" K'ura masa ido tayi irin cikin mamakin nan tace "Menayi kuma yanzu,ina Sune suka ce
haka gashi yanzu nayi auren amma yamafi damuna" gano yayi kuruciyarta yayi yawa yace
"How old are you Elham?" Kallonshi tayi tace "Kamanta kwana ki goma sha biyu na bawa
Feenah August zan yi 17 nanda watanni shida masu zuwa yanzu ina 16/2 sha shida da Rabi"

dariya ta sub'uce masa yace "Ban gaba jin inda mutum yace yana shekara kaza da Rabi ba just
admit it ur just 16,kinga baki gane zancen Su momy bane suna nufin se i dan Kinyi aure kinada
shekaru ashirin ne bazakiyi ba amma yanzu ur just 16 ai" dafe kirji tayi ta wara ido "yanzu kana
nufin duk month Senayi haka se nan da shekaru uku da rabi?" Se kuma tasa kuka wiwi shi
abinma dariya ya bashi janyota yayi yace "Kinga Elham bafa abin kuka bane,idan kin haihu ma
kan nan da shekaru ukun ze dena" k'wace kanta tayi daga jikinshi tace tana kuka "Bayan Aunty
Husnah data haihu tace da wahala daukan ciki sanda tazo aihuwa ma sumanta biyu Allah ni
bazan haihuba" hannunta ya riqe "Yanzu dai ki dena kukan haka,idan mukaje London zance
abaki maganin daze hana kiyi ciwon kuma tunda bakyaso ma bazaki haihuba so be it kinji?"
Gyad'a masa kai tayi hadda share majina ya ce yana kwantar da ita "oya zoki kwanta da
yamma zamuje yawo flight namu karfe 11pm ze tashi" wani patting bayanta yakeyi ita kuwa
dama haka takeso sun shirya bashi wahala idan har ya kuskura ya kawo kanshi...... Ya Zata
bacci takeyi jin yakira sunan ta kusan so biyu bata amsa ba,janyo wayar shi yayi yakira Khamis
yana d'agawa yace

"Khamis Yarinyar nan Zata rikitar dani wlhy,kaga k'uruciya zallah wai Ashe dama rashin zama
wuri d'aya ne ya sanya ban gane tanayi ba nifa inaga bazan iya rabuwa da itaba sam wlhy"
d'biar sace idan ba headphone tofa hansfree yake saka waya seji tayi khamis yace " Baba wlhy
duk cikin tsafine wayannan mutane naji ana fad'in ko gadin dasu keyi agida nku shekara da
shekaru asirce iyayenku sukayi dama so suke Su k'wace muku sarauta kaga idan ta haihu in
one way or the other d'anta ze gaje sarautar daga nan kuma kaga Su sun zama jinin
sarauta,wlhy ai kawai karka yarda da wani kirsa nata kuna zuwa kamata k'azafin bin maza ka
Turo da takardar saki uku awuce wurin tunda ba gyara,ni dazaka bi magana na ma ka saketan
yanzu ka Adana takardar dakunje da wata d'aya ka sako Shegiya ka turota gida" nisawa Abdul
yayi yace "Khamis zanbi sha'awararka amma dai se idan zan korotan zan rubuta" sallama
sukayi khamis se murna yakeyi, da yamma sukace yawo cikin dare suka cira zuwa birnin
London...... Had'adden gidan dabata tab'a ganin irinshi ba ya kaisu taga hadimai turawa se kira
masa sir sukeyi ana gaidashi,ahaka ya nuna mata d'akinta ya barta nan,yana wuce dama rata
ne bata samu ba ta ciro wayarta takira Aunty Husna,suna fara magana yana danno kanshi
domin shigowa d'akin,da kukanta take magana
"AUNTY Husna nashiga ukuna,wani abokin Abdul me suna khamis naso ya mayar dani
k'aramar bazawara,wai cewa ya masa asiri mahaifina ke musu danta gaji sarauta wlhy Aunty
Husna mahaifina ko mahaifiyata sabida gudun irin wannan ba wanda yakesan aurennan kurun
biyayya suka yiwa me martaba sabida k'imarsa ya wuce haka sannan kuma ya mutuntasu shi
baya kyamar talaka wa ko kad'an,ni wlhy banasan yaa Abdul kodan wulakancin daya kemun
Amma banaso na zama bazawar karfi da yaji,wlhy Aunty bamu masa asiri ba, mezamuyi da
mulkin da zamu mutu mu Barshi a duniya? Me iyayena suka nema suka rasa dazasu ce dole se
jininsu yayi sarauta,nifa a ganina Kobata hanyar ba idan Allah ya kaddara ze faru" nisawa
Husna tayi

"Nasan da tashin hankali amma kiyi hakuri,da yardar Allah baze sakekiba,sanar dani in details
me kikaji da kunnen ki?" Kwashe komai na wayar dataji sunayi ta fad'awa Husnah ta k'ara
dacewar

"Sanar wa Abdul ne kurun banyiba,tunda suka zo gidana yake yawan kirana wai in kwantar da
hankalina shi idan Abdul bayaso ze aureki,nace ina ka samo number na,wai Abdul ne ya ajiye
wayarsa be saniba ya kwasa,idan shi Abdul besan darajataba shi ya sani,wai nayita yiwa Abdul
rashin kunya idan ma ya sakeni shi ze aureni" mamakine yacika husan tace "har yanzu yana
kiranki?"
"Nasaka number d'inshi a black list ai,haka kawai se inga kamar Abdul ne ya turoshi dama ni
bansan meyake tunani ba akaina" jinjina kai Husnah tayi tace "Ki nutsu ki saurereni so yake ya
kashe miki aure sabida shi ya aureki,ai Abdul bazeyi wannan gangancinba sabida haka ki san
abinyi koda bakya sansa ki koyar dashi yanda ze soki,bazamu bari yaci galaba akanmu ba
kinji,anjima da kaina zan kiraki in sanar miki hanyoyi masu sauqin bi" godiya tayiwa Husnah ta
kashe ta zauna tana hawaye da kuka me d'an sauti tana magana "Allah ya isa khamis
wlhy,inajin muryanka na gane Kaine tunkan ya ambaci sunanka,kazafin daka mun se anwa
yarka wlhy" juyawa Abdul yayi yana mejin zafin abinda khamis ya masa aranshi yace Senayi
uwar khamis kuwa wlhy,dama burinshi ya had'ani da momy tome na masa,Kodai zargi nane ya
tabbata so yake na saki Elham yaa aura? Dama mana ranar se kallonta yakeyi kuma seyata
matsayin akan zasuzo gidana,k'wafa yayi yashiga d'akin da sauri ta goge fuskarta tace tana
murmushin yaqe

"Yaa Abdul yanzu nake shirin kiranka,yunwa fa na nakeji" kamo hannunta yayi yace "Elham
kukan me kikeyi daga zuwanmu" k'ura masa ido tayi tace "Inna da momy nake missing da gida
gaba d'aya" tausayinta yaji ga k'uruciya ga damuwa yace " keda kike da yaa Abdul d'inki a kusa
mezai dameki kuma?" Murmushi tamasa kurin ya sanya hannu yaja hancinta yace "Idan na
kuma jin kukannan bulala zan miki" maqe kafad'a tayi "ehmm ni banasan bulala fa ko askul idan
za'a dakeni kula nake tayi inankiran momy" Jan hannunta yayi "muje our food is ready"....

Da dare zasu kwanta se tsoro takeji ita kad'ai a d'akin gashi wani irin qatoton d'aki
ne,b'ingilalliyar riga ta saka iya cinya tazo parlor d'in ta zauna,kallonta yayi yana danna laptop
yace " Elly dear baki kwanta ba?" Murmushi tamasa sannan tace "I'm scared"
"Of what Elham?" Murgud'a baki tayi ta tsuke fuska "I mean the bed room is very big can't sleep
in there me alone" Murmushi yayi yace "Muje na tayaki kwana a d'akin kinji?" Binshi tayi abaya
ya kashe laptop din ya kashe side lamp, edge d'in gadon taje ta kwanta tanata takure wa shi
dariya ma tabashi,sanda ya bari tayi bacci sannan ya janyota jikinshi....
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*wannan shafin nakine mom humaid*

14

Wuraren k'arfe uku na dare ta farka,mamakin take sanda tazo jikinshi har haka,fitsari takeso tayi
amma ta kasa koda motsi sabida yanda d'imin jikinshi ke saukar mata da kasala,a hankali ta ce
"Yaa Abdul ka d'aga ni ina so zanje bathroom ne" be motsa ba sanda ta maimaita so kusan uku
sannan ya bud'e idonshi a hankali ya sakar mata lallausan Murmushi dukda acikin duhu
suke,hannu yakai ya kunna side lamp dake d'akin sannan ya sake riqon daya mata yace "Sorry
na hanaki tashi bacci ne yamun nauyi" Mik'ewa tayi kurun ta gyara gashinta daya yamutse taje
toilet d'in tayi fitsarin ta dawo,zaune ta taddashi tace

"Lapia dai yaa Abdul?" Murmushi ya sakar mata " Ai komai Nisan dare idan aka tashe ni bana
iya komawa baccin " b'ata fuska tayi tace "Ohhsh Allah dana sani ban tashe kaba wlhy,yanzu
haka zaka yita zama kenan??" Kishin gid'a yayi yace parlor zanje inyi kallo kawai" zaunawa tayi
kusa dashi tace "To nima zan bika muyi kallon tare" "Noo plss karki damu,ki kwanta kiyi baccin ki kinji" mak'e kafad'a tayi "ehmm ni bazan kwanta
d'inba zanje mu zauna tare kawai" Mik'ewa yayi yace "if u insist" Murmushi kurun tayi tabi
bayanshi,Jennifer's diary yake kallo dai itad'ima zama tayi se dariya sukeyi sabida anata yin
abin dariyar,bacci ne yafara fizgarta,ganin tana d'ingishi ya sanyashi dariya ya janyota jikinshi
kanta ya datura akan cinyarshi yashiga Shafa lallausar sumanta "Kiyi bacci Hafsat,bacci kikeji
naga alama" batayi musuba tashiga lumshe ido,har cikin ribs nata take receiving saqonnin
dayake aika mata,a haka bacci barawo ya kwasheta,gogan shima a zaune yayi baccin basu
suka farka ba se 7 wannan ma ita d'ince ta fara farkawa k'urawa fuskarsa ido tayi tana mamakin
kyakyawar fuskarsa har acikin bacci,tana so ta tasheshi yayi sallah,taga alama ma kwanciyar
na bashi wahala sosai sabida a saman kujera kanshi ya tafi sosai kasancewar a k'asa suke,tuna
wa tayi da yanda Husnah ta koyar da ita yanda zatana tashin mijinta a bacci,Murmushi tayi
aranta tace zan iya kuwa?? A hankali ta tashi daga jikinshi ta sanya hannunta tana Shafa
kanshi a hankali,bud'e idonshi yayi ya sau kesu a kanta,da Murmushi ta tare shi tace "Kayi Latin
sallah yaa Abdul ka tashi" Mik'ewa yayi a hankali batare da yayi magana yabar gurin, itama ta
miqe tawuce d'akin ta,wanka tayi ta shirya tsaf cikin wata doguwar riga mara nauyi me santsi da
kyawun gaske kalar sararin samaniya ta tufke gashin kanta a tsakiya tayi masa style na donut,
ta feshe jikinta da turaruka dama gashi tayi wanka da ruwan miski se tashin k'amshi takeyi tako
ina. Parlor tafito har wannan lokacin be dawo ba,se can ya shigo cikin Shiga ta kananun kaya
riga da wando,wandon jeans blue sa shirt kalar sararin samaniya shima yayi kyau matuka se
tashin k'amshi yakeyi,zama yayi kusa da ita yace yana mai janyo hannunta

"Ur looking beautiful Elham" Murmushi tamasa tace "u too" hancinta ya d'an ja "ohh Really?"
Langwab'e kanta tayi tace "yea Kayi kyau sosai,ko wurin budurwar ka ta nan k'asar zakaje?"
Murmushi yamata yace "Ai itane zatazo karki damu da wannan" cikeda isa ya nuna
wannan,gabanta ne ya yanke ya fad'i ta yi Murmushi tace "zanji dadi idan na ganta kuwa"
kallonta kurun yayi ya mik'e ya bar wurin......

Rayuwa tayiwa Elham k'unci kasancewar tunda sukazo bata sake saka Abdul a idon taba tun
kwanan farko, tsoro me tsanani ya shigeta,gashi se yan matan turawa masu masa aiki take gani
suna kai kawo a part d'in shi,takuma tambayi d'aya daga cikinsu inda yake tace mata fitar asuba
yakeyi ya dawo late,yau kusan kwananta shida kenan bata ganshi ba abinda ta rasa amma
batajin dad'in rayuwarta sam!!! Ganin ya Shigo da sauri ta miqe taje gunshi "Yaa Abdul lapia
kuwa? Kwana biyu bana ganinka?" Hannunshi ya sanya ya tureta yace cikin maye "Zaman
uwarki nake a garinnan dazakice Sekin ganni kullum,wlhy ki Shiga taitayinki" zaro ido waje tayi
jin muryarshi se a sannan ta kula da yanayinshi sarkace k'atuwa a wuyanshi da wando iya
gwiwa daka ganshi kaga zararre kuma a buge yake,kafin tayi wani yunkuri ya fad'o ajikinta,tare
shi tayi sannan cike da k'arfin hali taje ta kwantar dashi a d'akin shi,wannan ne karo na farko
data fara Shiga d'akin kuma ya tsoratar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login