Showing 45001 words to 48000 words out of 53214 words
Chapter 16 - Hafsat Ilham Book Complete by Billy Galadanci .pdf
bata
sunan momy,dama a fada suke zama tunda cikinta ya tsufa,se Wuraren 9 Abdul ya qaraso a
fusace yazo gidan yana zuwa yaganta zaune a parlor itada wasu hadimai
"Sannu da zuwa yaa Abdul?" Tace dashi tana me kallonshi ko duban inda take beyiba yace
"yauwa" atakaice ya wuce ciki abinshi,mamakine ya kamata ta miqe ta baiwa dayar babyn ita
kuma tabishi ciki yana daga cikin wardrobe tace "yaa Abdul lapiya dai kashigo cikin gida ranka
abace?" Cikeda fusata yace
"Bansaniba tsabar rainin hankali shine tun karfe hudu nake kiranki amma baki daga ba kuma
har yanzu baki kirani back ba,ko kinaso...ya zaro kanshi daga wardrobe d'in yana mata magana
atake yayi hooking gani ba ciki a jikinta,da sauri yazo ya riqeta da mamakinshi yace " Blossom
yadai?" B'ata rai tayi "kaci gaba da masifan da kake mana,banda haka ina fama da labour zaka
zo kanamun masifa,Allah ni banmasan inda na wurgar da phone naba,kuma fa nasha
wuya,shine kokace ina Baby" wara idonshi cikeda mamaki "Blossom wai da gaske kin haihu?
Wlhy babu wanda ya sanar mun hasalima ban lura ba ciki ajikinki ba se yanzu,me kika haifa
mun ina babyn?" Murmushi tayi "Baby girl tana hannun hadima adama" wani uban tsalle ya
daka yana ihun murna da gudu ya ruga parlor hadimanma sunsha mamakin yanda ya manta da
wani girman kan mulki ya sungume y'arsa yana tsallen murna..
*ku taya Nu'aiym da adu'a wlhy bashida lapiya*
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: HAFSAT ELHAM*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
29
Zanen Elham ta duqufa tanayi na wani kata faren kamfanin da za'a bud'e a qasar Saudi wanda
aka baiwa Abdul kwangila Shikuwa haka kawai yace lallai itace zatayi wannan zanen,yau kusan
sati biyu tanayi,tausayinta yaji yabata wahala har kusan k'arfe biyu na dare tana abu d'aya dafa
kafadar ta yayi yana daga kwance yace "Blossom mana ki kwanta inyaso da safe kya qarasa
kinji?" Batare data dakatar da abinda takeyi ba tace "Hubby sauramun befi 30mnt ba plss
kabarni na k'arasa" bece komai ba ya kwanta abinshi..... Lokacin da Abdul yaje gabatar da
wannan zanen aka karb'a cikin jin dadi be boye musu ba akan cewar matarshice tayi zanen
lokaci d'aya suka buqaci ganinta inda suka jinjina wa k'okarin datayi tare da kyaututtuka masu
tsoka ciki kuwa harda gida sukutum kuma suma d'auketa aiki a babban kamfaninsu na Zane
Zane, wannan abu ba karamin dad'i yayi Abdul ba alokaci d'aya ya nema mata gurbin karatu a
jami'ar dake birnin London tafannin Zane,tana karatun tana aikinta haka suka rayu da juna
cikeda Aminci kuma princess har wannan lokacin tana wurin momy susu kad'ai suke zaune a
london d'in suna sha'anin su,wani yammaci suka shirya zuwa yellow London Beach, dogon
wandon jeans ta saka blue sa top red,sannan ta daura qatuwar rigar sanyi light brown a sama
ta saka hula brown da shade ruwan k'asa shima, ba k'aramun kyau tayi shima kusan irin
shigarta yayi suka d'auki hanya a beach elham matashin kai tayi da cinyar shi tana cin
strawberries,hannunshi ya d'aura a saman kanta yace "Blossom dama fa inaso muyi wata
magana dake" batare data baiwa abun muhimmanci ba tace "To bismillah ina jinka" d'an shiru
yayi sanda ta qara cewa "Enhm hubby inajinka menene?"
"So nakeyi ki haqura da karatun nan da kikeyi" sarqewa tayi da Berry d'in da takesha ta miqe da
sauri ta juyo ta kalleshi "meya faru hubby? Meya sameka? Meye zesa na dena karatuna ? Wani
abin na maka ne? Kokuwa dai haka kawai?" A rud'e ta jero masa wayannan tambayoyin, d'an
murtuqe fuska yayi yace "Ba abinda kikamun kawai dai banaso ne ya isheni haka ke har aikin
ma ki dena banaso" shiru tayi ta qura masa idonta da a wannan lokacin har sun sauya launi
zuwa ja tamkar gaushin wuta,dak'yar ta furta
"Yaa Abdul dan Allah kayi hakuri ka barni na qarasa karatuna kuma inajin dad'in aikina" harara
ya wurga mata "Bazan haquraba naga alama kinaso ki maidani qaramun mutum sabida haka
daga yau dukka biyun na dakatar dasu bazaki yiba" kasa riqe hawayenta tayi
"Yaa Abdul lapiya lau fa muka fito daga gida kuma bansan menene ze shafi aiki na da karatuna
da sauri haka ba mena maka?? Sauramun shekaru biyu kacal fa na kammala" k'ara tamke
fuska yayi
"Nasani sarai lapiya lau muka fito kuma ai wannan ba wai shawararki nake nema ba umarni ne
nake baki,daga yau na dakatar dake daga zuwa skul d'in aikin ma ki rubuta resignation later ki
basu,ke gaba d'aya ma Nigeria zaki koma da zama, shekaru biyun dakike cewa Sune suka rage
miki bansan abinda zaki zamar mun ba idan na barki kika karasa sabida haka bazakiyi ba" zaro
idonta tayi waje cikeda tashin hankali
"Yaa Abdul to yanzu nikam mena zama arayuwa?? Konayi maka wani laifin ne hala?" Tsawa ya
daka mata "Ba abinda kikamun kurin dai bazakiyi bane,kuma kinji na fad'a miki Karki k'aramun
maganar skul d'innan kuma kafin hutun dakika d'auka ya qare lallai kiyi resigning" bata qara
cewa komai ba haka ta share hawayenta a zuciyarta tana da d'a nanata innalillahi wa Innah
ilaihirraji'un ba adadi,har suka bar wurin ba wanda ya kuma qara cewa komai,koda suka je gida
kowa part dinsa ya nufa,a can Elham ta zauna ta dirza kukanta ma ishi,ko bayan isha bata fito
ba haka Shina bebi ta kanta ba sabida abinda tamasa ba karamin b'ata ranshi tayi ba,yaga
alama idan yayi wasa London din Zata haukatar masa da ita......washe gari ma bata fito ba
sabida bataji dad'in yanda ya wofintar da itaba bayan kuma ba haka ya saba mata ba kuma ba
rashin kunya ta masa ba,a part nata kurun tasha fresh milk ta shirya zuwa skul se time da
takeda lecture sannan ta fito,a parlor ta same shi taje ta durkusa kaman yanda ta saba tace
"Sabahul khair hubby" kallonta yayi fuskarsa a daure yace a dakike "kin tashi lapiya?"
"Lapiya lau zan tafi skul ne inada test" da mamaki ya d'ago ya kalleta amma seyayi kokarin
Kawar da mamakinshi yace "Allah ya sanya ayi a Sa'a" "Ameen" tace a taqaice taje ta dauki
key a inda suke ajiye key na motocinsu tafice,wannan abin ba qaramun tunzura Abdul yayiba
aranshi yace "Wato ma ban isa ba kenan? Lallai kuwa zan shayar dake mamaki" ita kuwa harga
Allah bata dauka komai ba batayi tsammanin kawai sabida yace Zata dena zuwa skul ba
shikenan Zata dena zuwa ta Zata zeje skul d'inne ya sanar musu Zata dakata tukunna,da
wannan tayi hakan, wannan kenan.
*Washe gari*
Koda Elham tayi wanka tazo ta d'auki key ba key kona mota d'aya a wurin dasuke ajiye
Key's na motocinsu d'akinshi ta nufa nanma bayanan,d'aga wayarta tayi tayi kiranshi yana
d'agawa suka gaisa tamkar ba komai tace "hubby ba key na mota ko d'aya awurin ajiyewa?"
"Ina dukkanin motocin nine na siya da kudina?" Mamaki maganarshi ta bata a hankali tace "To
hubby me kuma ya kawo wannan maganar?" Katse kiran kurin yayi batare dayayi magana ba
ita kuwa tabi kan wayar tata da kallo,sam bata fahimci inda ya dosa ba kuma ta kasa gane kan
wannan fushin nashi batasan dalilin suna zaman zaman su lapiya ze tsiri masifa ba,haka tayita
fama har sukayi wata fiye da d'aya baya kulata,wannan ya sanya tayi resigning dukda company
d'in basuso hakan ba Amma ba yanda zasuyi kasancewar tamusu alqawarin bayan gama
karatunta zata dawo wa aikinsu.......A parlor yana zaune yana karatun news paper yana kurbar
coffee a hankali ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya da madubi Sanye a idonshi tazo ta
zameshi,kusa dashi ta zauna a k'asan kafafunshi tace cikin sanyin murya
"Yaa Abdul dan Allah magana nakeso muyi dakai" beko kalli inda takeba bare ta saka ran ze
saurareta hawayene ya soma sintiri a akan fuskarta takuma cewa "Yaa Abdul dan Allah Kayi
hakuri wlhy nayi dukkanin abinda kakeso, karatun ma Kaine kawai nake jira kaje ka dakatar
dani" rausayar da kanshi yayi D'auke da Murmushi akan fuskarshi me nuna irin kanki akeji
kenan sannan yace yana me zummar barin wurin "Hafsat dama ke nake jira kiyi Hutu muje
gida,so na kammala shirye shiryen da komai ranar Tuesday zamu wuce" kukan tane ya
tsananta taje tasha gabanshi tana kuka ta qanqameshi "yaa Abdul wayene yake k'ok'arin shiga
tsakanina dakai? Mena maka arayuwa dana cancanci wannan horon,ai kinnan dakaina na
dakatar dashi karatunnan kuma qarashen hukuncinka kawai nake jira dan Allah Kayi hakuri"
hannunshi ya saka ya b'amb'areta ajikinshi sannan yace bayan ya qura mata ido "A zatonki kin
fini wayo,a tunaninki kin fini kwarewa a rayuwar turai a tsammanin ki bazan tab'a gano mugun
abinda kike aika tamun ba,Toki sani wlhy nasan komai sabida haka kije can da taurin kanki,ina
watannin mu biyu a haka baki damu ba,kinfi damuwa da karatunki,kinfi mayar da hankalinki
akan neman ilimi to kije na dena hanaki karatun aikin kuma kije kiyi tayi ba ruwana dake da
rayuwar ki gaba d'aya wlhy,ke har yanzu girman kanki kikeji da ganin Kud'in watace,so please
kiyi sha'aninki" daga nan ya wuce ya barta gun a tsaye tana famar rusa uban kuka,gashi ta kasa
nunawa kowa damuwarta.
*Nigeria*
Tunda suka isa momy ta hadasu da Princess suzo da ita,Abdul idan ba cikin mutane ba ba
ruwanshi da Elham,ko abincinta baya ci,kallo daya me hankali ze mata ya gano sam bata cikin
kwanciyar hankali,ko mahaifiyarta ta fahimci hakan kuma data tambayeta setace da ita stress
din karatu ne ke damunta,dukda bata yarda ba amma haka tayita hakuri ta qyaleta, tafito daga
gidan mahaifiyar ta zuwa sashen momy ga had'u da raihan haka kawai taji gabanta na faduwa
cikin dakiya ta tsaya Su gaisa,bayan sun gaisa kamar abun arziqi sekuma Raihan ta kalleta
tace
"Elham sekuma mukaji zance mara dad'i Ashe yaa Abdul aure ze qara? Ni wlhy se yanzu ma
nakeji biki saura sati uku,da har inajin haushi zai auro miki yar talaka wa sekuma na tuna duk
k'anwar ja ce,Allah ya sanya alkhairi acikin bikin" haka Elham taji wannan zancen tamkar saukar
aradu aranta tace "Aure kuma? Nashiga ukuna,dama akan wannan yaa Abdul ke wulakanta ni ?
A fili kuma se tace tana me tattaro nutsuwarsa da kokarin wanzar da yalwar murmushin yaqe a
fuskarta " Hakane Wlhy kinji dai abin alkhairi, nima kuma Senayi godiyar Allah sabida Sa'a
had'aka kishi da 'ya'yan masu kisan kai wlhy gwara maka yan uwanka talakawa da basu san
tashin hankali da hadama akan mulki ba" sumsum Raihan ta wuce batare da ta koma magana
ba,anan tabar princess ta wuce gidansu a rikice,tana tuqi tana kuka duk tabi ta rud'e ta gigice, a
d'akinshi ta wuce ta sameshi yana waya,zama tayi kusa dashi tana sharar k'wallah harya
idar,kallonta yayi yace
"Ke lapiya meye haka?" Tana sheshekar kuka tace " Yaa Abdul waida gaske zaka k'ara aure?
Da gaske nanda sati uku aurenka ban saniba" tsaki yaja irin dama akan wannan kike mana
kuka,gincirawa yayi yace yana Murmushi "Ea Hakane aure zanyi kuma nan da sati
ukun,Meyene aciki to?" Zare ido tayi tace tana me riqe masa kafa "yaa Abdul mena maka
zakamun hakan dan Allah Kayi hakuri,wlhy idan kamun haka mutuwa zanyi bana san kishiya
tsoron ta nakeyi bazan iya had'a ka da wata ba" miqewa yayi a fusace "ke meye haka? Sabida
wannan borin zaki zauna kinamun kukan raini,ubanwa ye yace ki aika tamun abinda kikemun
tsabar mugunta, to dolene na auro uwa ta gari wa y'ay'ana wadda Zata kulamun da princess
kuma ta haifa mun da yara masu tarbiya kuma na gari kekuma meye nawa na miki yanda
kikeso karatu kikeso da gayu da bariki nikuma haqiqanin sunna nakeso na raya ta usuli bawai
shirmen kiba" wani razanannen qara ta saka da kuka me ban tausayi......
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: ☀️Hafsat Elham☀️
HASKE WRITER'S ASSO.
Wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa GA qawata Hafsat Abubuakar qaya.
30
Ethan abun duniya ya isheta,ta Kasa gane inda zancen Abdul ya nufa kome Tamasa ai bata
cancanci wannan d'anyen hukuncin ba, shin Anya Kuwa Abdul Yasan Abinda yake shirin
aikatawa? Da sauri ta miqe ta zari key na motar ta ta nufi fada tuqin takeyi Kawai amma Sam
hankalinta baya Kan abinda takeyi se uban Kuka takeyi bata tab'a Zata cewar haka azabar kishi
yakeyiba ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito wani tafarfasa da d'aci zuciyarta ke
Mata ikon Allah ne kadai yakaita fada lapiya, Ko lucking car batayiba ta afka cikin gidan Kai
tsaye part din mommy ta nufa, a parlo ta Sameta itada Abdul Suna hira Kai tsaye Saman
cinyoyin mommy ta d'are ta soma Kuka da sambatu
"mommy Dan Allah Kiwa yaa Abdul magana yamun rai idan wani abun namasa yayi hakuri wlhy
banason kishiya banso ya had'ani da kowa, karatun Kuma da bayaso shima na dena bazan ma
koma qasar ba" kukan takeyita baji ba Gani,d'agota mommy tayi " Elham Karki Zamo cikin
mataye Marasa yarda da k'haddara ina tunkafin kuzo me gidanki ya sanarmun Kinsan komai,
shine kuma Yanzu zaki biyewa mutane su rikitar dake a karin banza,ina nan ina faman saka
Miki albarka akan yarda da khaddarar dakikayi Ashe ba haka bane zaki biyewa mutanen banza
su kaiki su Baro,to ki Sani zamu b'ata dake kishiya ba abun gudu bace 'yar uwace kuma
abarso,karna kuma ganin kin Tashi hankalinki Akan zancen kishiya tunda mijinki Yana
qaunarki, Maza tashi ki koma dakinki yanma nayi" mamakin Jinwai tun Kan Suzo ta Sani
takeyi amma batace da mommy komai ba Tamata godiya jiki ba k'wari ta Kama Hanyar waje
tun a Hanya kafin taje gun mota take ganin Jiri ya soma kwasarta har Abdul yafito tana nan bata
qarasa gun Mota ba tana tafiya tana bin bango tana layi ,ta bayanta ya tsaya Yana nazarinta
Harga Allah badasan ranshi zeyi aurennan ba amma yana mamakin sanda Elham tayi wayewar
aikata abinda ta aikata ba wannan kadai zeyi ya rage jin zafinta aranshi, da k'yar ta isa mota
koda tashiga ma sam batasan me yakeyiba, Allah shiyake halittar mata da mishi amma Elham
tana daga cikin mataye Masu azababben kishin tsiya, da k'yar ta iya yin rivers ta harbawa
motar wuta ,mahaifinta ma dayaqi yarda ya dena aikin gadin binta yayi da Kallo harta bacewa
ganinsa ganin yanda batako tsaya sunyi sallamaba kuma yaga ta sharara da wani uban gudu
na Allah ya kiyaye....... Ganin haka ya sanya Abdul juyawa ciki aranshi yana Mata aduar sauka
lapiya.
Yana nan zaune wayar mommy ya soma ringing,d'agawa tayi ganin baquwar lamba ya sanya
ta ajiye bata d'agaba ta mayarda dubanta Zuwa gareshi tace
"Babana lapiya dai ka tafi kuma ka dawo? " Sosa kanshi yayi yace " Kawai Naji bazan iya zuwa
gidan Yanzu ba" kan tace wani abu wayar yafara ruri a Karo na biyu,ganin Sunan Elham NE,
da Sauri ta d'aga
"Mamana ya akayi? " muryan namiji tajiyo "Haj bame wayar bace tayi accident Anan kan
Hanyar government house kuma gata a kwance sedai ace Allah ya sauwaqa, Yanzu zamu
wuce da ita babbar asibitin kwararru ta jiha shine muka Kira ganin Kamar number dinkine a
sama kuma munma Kira wacce Muke tsammanin ta mijintane amma be d'aga ba" miqewa
momyn tayi da salati d'auke abakinta
"Malam injin dai Tana da rai? " ta wurgo masa wannan tambayar "Haj bazan iya cewa komai ba,
Sabida banida masaniya,kurun dai na kula she's unconscious" a gigice ta ajiye wayar ta Kalli
Abdul
"Babana tashi muje ba lapiya, Elham tayi accident a Hanyar government house" haukace mata
ne kurun beyiba amma Kam ya kusan zaucewa, Kasa tuqin yayi kurun yafito ya tsaya yana
tunanin wane Hali Illy take cikin, seda driver yazo yajasu,suna zuwa wurin da akayi accident
d'in Abdul ya dakatar dasu Kallo daya Abdul yayiwa motocin guda biyu zufa ta keto masa Sam
dazaran kaga Motan Elham Kasan akwai Marsala, fitowa yayi yaje wurin mutanen dake
tsatsaye a wurin " Malam Dan Allah meya faru? " ya tambaya bayan ya musu sallama "AI
malam wlhy wani mummunan hatsarine ya afku, wata yar matashiyar budurwace tazo dagudu
k'addara ta afka mata Kasan wani lokaci idan ajalin mutun yazo bayan Sanin me yakeyi kurun
baiwar Allah nan tayi maja da waccen motar ta ibar yashi kaga yanda motar ta ta dawo wlhy
malam bakaga yarinyar ba gwanin ban tausayi ni inaga wlhy ko aure batayiba amma mutuwa
tazo mata a bazata" wara idonshi yayi ya dafe k'irjinshi dake masa zafi yajuya zuwa mota
maganganun da mutumin ya fad'a suna masa yawo aka, ya Kasa gaskata zancen
mutumin,koda yashiga motar suna masa maganr kasa amsasu yayi kukan ma ya gagareshi a
haka har suka k'arasa asibitin, shine ya fara fitowa daga cikin motar ya nufi cikin asibitin.....
Kallon nutsuwa likitan yayiwa Abdul kan yace " Yarima tun kafin faruwar wannan accident d'in
binciken mu ya nuna mana cewar matarka na cikin matsanancin damuwa, Zama mu iya cewa
shine yayi sanadin wannan accident data Samu Sabida Tana d'auke da matsanancin ciwon
zuciya Wanda akalla zefi shrkaru goma acikinta faruwar wannan abun ya sanya gaba d'aya ya
taso mata lokaci d'aya had'uwar sa kuma da wannan accident yasanya kuma lokaci d'aya
zuciyarta ta buga!!!" cike da razani Abdul ya d'ago ya kalleshi "Bugawar zuciya fa kace doctor?
Mekenan Kake shirin sanarmun? Kuma ni iyakar sanina matana batada ciwon zuciya mema ze
haifar mata da ciwon zuciya??" tasowa likitan yayi ya zago ya dafa kafad'arsa yace
"Abdulrahman ko bansankaba bazan make k'aryaba balantana muntaso Dakai tun Muna Tara
atare, ba dalilin maka haka,abu na gaba kuma ka sani matarka wannan ciwon ya jima ajikinta
Danma