Showing 3001 words to 6000 words out of 53214 words

Chapter 2 - Hafsat Ilham Book Complete by Billy Galadanci .pdf

20 Mar 2025

3489

me" kuka Raihan ta saka amma ba wanda ya kulata har sukaje gida,suna isa ta
tattare kayanta tabar motar a fusace,ba wanda yabi ta kanta suka kwasa sukayi part na
momy,acan Elham ta gayawa momy abinda yaa Abdul yaa basu kuma tamasa godiya da adu'a
me yawa ta bashi clips data siya masa,momy taji dadi sosai....

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awara Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                         02
Tana baro sashen momy Fulani taci karo da yaa faruk,hannayen shi yasa duka biyu ya daga ta
yace "Kingan ki ba nayi se tsawo" d'an bata fuskarta tayi kasancewar batasan irin Wannan
wasan daya ke mata hasalima batasan koda hannunta yake tab'awa gashi ta kula shi sam be
dauki abin wani abin ba,tana yunkurin sauka tana wuntsila kafa yaa Abdul yafito daga part
d'in,kallon mamaki yabisu dashi aranshi yana mamakin iskanci irinna Hafsat,sam bazakayi
tunanin koda yatsa ka saka mata abaki zata ciza ba,d'an tab'e bakinshi yayi ya wuce
Su,yayinda tana ganinshi taji wata irin kunya ta lullub'eta lokaci d'aya kuma ta dena yunkurin
sauka daga jikinshi,sauketa yayi ganin yaa Abdul, b'ata fuska sosai tayi tace "yaa faruk dan
manzan Allah kadena kokarin kai hannu jikina ko wane lokaci,nafa sanar maka banaso yanzu
sabida Allah me kake so yaa Abdul yace?" Dariya yayi yace "Nadena princes Ni nasaba
rayuwar turai wanna ba komai bane awurinmu"
"To ai nan ba turai bane so seka maintaining kanka gaskia nidai Banaso" takarashe maganar
cike da shagwaba,wanda ba karamin burgeshi tayi ba. yace yana kallonta "Elham bakice mun
komaiba I'm sure kinga message nawa since morning"  Murmushi tamasa tace "yaa faruk
kenan,kasani sarai bana bud'e phone nawa se 4 kullum,da yamma nagani trust me,and bansan
me zance maka ba" kwai kwayar maganar ta yayi "kice Nima ina sanka yaa faruk mana"
tufakan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta sannan tace "Yaa faruk dan Allah ka dena kana
bani kunya wlhy"
"Naji yanzu jeki u ttxt me plss,and make sure u do that before going to bed" dan Murmushi
tamasa tace

"I'm not even sleepy @ all let's chat" Murmushi shima yamata yace "Fine then ping me if ur free"
tafiya take tana Murmushi harga Allah tana kaunar yaa faruk,yafi kowa Santa agidannan me
maraba ne da Fulani kurun suke nuna mta kauna fiye da shi,sun d'auketa tamkar yar uwarsu
kuma jininsu kokuma Sune suka haifeta duk kuwa dayake itad'in ba kowa bace face 'ya awurin
hadiminsu,a hadiman ma me gadi......bayan tayi wanka ta shirya cikin rigar bacci fara k'al ta
tufke gashin kanta a tsakiya sannan ta saka hula a kanta ta kwanta,wayar ta ta dauka ta turawa
faruk message

"Sweetest I'm done" Murmushi ya turo mata yace "fine,that's good rose yanzu sanar dani
menene amsarki zaki aureni?" Murmushi ita ma ta aika masa,sannan ta tura masa da hoton
hrt,batai magana ba,hrt yakuma aika mata shima sannan yace "Rose mana sanar dani plss,I'm
telling Idan kin amince gobe zanje na sanar da me Martaba kina kammala Wannan makarantar
Abani matana muje gidana" Murmushi tayi tace

"Zan aureka mana yaa faruk koda gobene na shirya wlhy" tsallah ya daka tamkar yana ganinta

yace "I'm so much happy miss Rose,thanks a lot for loving me I really appreciate ur love"
"I thank you too,charming" murna ce ta kama faruk yata mata hira da wasanni......

*Bayan sati biyu*

      Fushi sosai Elham ta dauka da faruk sabida yayi kokarin tab'a jikinta kota karfin tuwo,ko
hanya basa hadawa domin kuwa dasun hadu take sake hanya,Abdul kuwa wani abu ya tsare
shi a Niger be koma ba sam satinnan dai yake shirin komawa,faruk ya damu ganin ko wayarshi
bata d'agawa,yauma kamar da damuwar rashin faruk d'inta tashigo pool na gidan,harga Allah
tana missing na faruk,kurun tana sone ta nuna masa kuskurensa Shiyasa take ta faman azabtar
da har kanta ma,kamar daga sama taganshi akanta hannunta ya finciko ya juyota ta fuskance
sa a bango yaje ya mannata ya daga hannayenta duka biyu ya manna a bangon ya riqe gagam
yace "Tell me miss Rose? Why are punishing me like?" What the fuch did I do to you?" Kasa
magana tayi kuma bata wani yi yunkurin kwace kanta ba,zuba masa manya manyan fararen
Idan uwan ta tayi cike da tsoro,wanda shima din ita yake kallo....a haka yaa Abdul ya shigo ya
samesu mamaki suke bashi shikam sam ba kunya a idonsu,ita ce ta ganshi kasan cewar shi
faruk ya baiwa kofar shigowa baya,daga nan tafara cuku cukun kwace kanta

"Yaa faruk plss let go of me" be sake taba illah ma ya kare riketa tamau ya zuba mata ido, a
tunanin yaa Abdul sabida sun ganshi ne take kokarin basarwa ,tana hango sanda ya girgiza kai
ya juya kurun, a fusace tace "Wannan mugun halin yasa kake kara nisanta kanka dani,na sanar
maka haramunne abinda kake,niba muharra marka bace,ban riga na zama mallakinnka ba
mene na tabamun jikina" a fusace ya saketa yafara banbami

"Idan sabida wanna kike mun ihu zaki zama mallakina Hafsat,kullum magana d'aya bakida
zance sena jikinki sekace kece kikafi kowa a duniya,wlhy nasan maganin ki,yanzunnan zanje na
fadawa me martaba ina sone ya daura mun aure dake faqat shikenan?" Ya kura mata yana jira
yaji cewarta,cikeda warning tace
"Hakane bazan hanaka aikata Wannan ba,sedai fa ka sani karka kuskura na kuma ganin
hannunka a saman jikina harsai ranar da aka daura auren namu,baka majin tausayina yaa faruk
baka ganin yanda na rame duk sabida ina missing naka,simple abu ya gagareka" sassauta
murya yayi "kiyi hauri miss Rose bazan karaba" daganan dai suka shirya Kansu yamata
alkawarin baze kara tab'a taba.

Zabura Umma tayi dajin zancen faruk tace "Au Wato dama faruku duk gargad'in nan danake
maka baka saurara ta? Ina kataba ganin Sarki me jiran gado ya auri yar talakawa ,yar talawan
ma yar me gadi! Wlhy faruk kobana numfashi kan auri Elham ban yafe maka ba" gigicewa yayi
ya Hau ban baki da ban hakuri amma sam Umma bata sakko ba kara hawa ma takeyi tamkar
wata farashi,wasa wasa fa kusan Kwana uku yana rokarta taki aminta,dolece ta sanya yaje
wurin momy, ba karamin dadi momy tajiba mamanta zatayi auren Hutu dajin dad'i ,tace "Karka
damu umarul faruk zanje da kaina gunta na mata magana da yardar Allah zata a mince,kaga
dama na yayanka da Raihan muna jirane nan da watanni shida Su kammala skul inyaso se a

hada gaba daya" godiya yayi yatashi yabar wurin cikeda murna,washe gari kuwan momy ta
shirya zuwa bangaren Umma,gaisawa sukayi cikeda girmama juna tamkar ba komai a kasan
rayukansu game da juna sannan ,gyaran zama Fulani tayi tace

"Fulani Babba dama nazone in roki Alfarma awurinki akan zancen faruk da Mamana,dan Allah
ki janye furu cinki ki barsu suyi auren Su,tunda addini da al'ada duk basu hana ba" wani mugun
kallo ta wurga mata sannan tace

"Kinga Fulani wlhy ko ubanwa zaki gayawa bazan sauya Wannan maganar ba,ke gani kike
kamar bansan tuggun dakike kullawa ba? Kome nawa Kinbi kin kwace mun yatashi daga nawa
ya dawo naki,bayan kin hade kai da mijinki kun kashe nawa mijin sabida ya Hau sarauta,yanzu
kinzo kinaso ku daura Abdurrahman har dan munafurci wasu na kiranshi Yarima ,shine zaki zo
sabida ki kara batawa faruk suna zaki hada shi da wata shegiyar talaka wai ya aura,a zatonki
bansan me nake ba kokuma banida hankaline,duk muna funcinku ina kalonshi wlhy, kuma da
yardar Allah bazakuci nasaraba faruk shine ze gaji sarautar ubansa,ko Raihan sabida banaso
tashiga damuwa ne kasancewar ta mace kurun ya sanya na yarje mata auren Abdul" kura mata
ido kurun momy tayi sanda ta kai aya sannan tace

"Kinga Yaya habiba ba zwa nayi Kici mun mutunci ba,zancen kashe margayi me martaba
dakike kuma kije mun barki da hukuncin Allah,zancen kuma sarauta dakike keta Shafa ni kina
sane yarona bata shafeshi ba,Idan kuma har Allah ya zabeshi keda iyayi nki baku isa ku hana
ba,auren Raihan da Abdul dakike magana ita Elham malama ba 'ya bace daki kece Raihan
macece ai itama macence bakya duba damuwar dazata Shiga? Tsabar sonkai musulunci da
kanshi yamana nuni a sassa daban daban,kuma hadisin ya inganta cewa imanin dayanku baya
taba Cika Harse Idan ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa,kekuwa taki yar kawai kika
sani,wlhy kiji tsoron Allah" mikewa tayi a fusace

"Kinga Nana barmun sashen na,borin kunya kikeyi Allah ya Toni asirin ku da wuri Wannan
karon,wlhy inhar muddin ina numfashi bazaki taba cin nasaraba,nakara fada ko bayan raina
faruk ya auri Elham dashi wayanda suka daure masa gindi Allah ya isa ban yafe ba,Idan
gaskiyane ba mugunta kike shirin masaba ki baiwa Abdul Elham d'in ya aura mana" mikewa
itama tayi

"Naji Yaya habiba Abu daya nakeso ki rubuta ki ajiye wlhy Nima ko bayan raina ban yarjewa
Abdul auren Raihan ba,dukkanin Su suyi asarar ababen kaunar Su,zan kuma tabbatar miki
cewar ba mugun nufi araina domin kuwa aure ne Elham da Abdul anyishi an gama,ke kuwa
Idan kin isa ki hada auren faruk da Raihan kema din kiyi auren huce haushi" zage juna sukayi
tatas wanda da faruk da Raihan duk suna jiyosu, aikam hankalin dukkaninsu ya tashi,bayan
Fulani ta wuce suka yita baiwa ummansu hakuri amma bata hakura ba....

"Koda momy takira Abdul dake birnin London tafada masa kasa yi mata musu yayi kasancewar
sa me tsananin biyayya....gashi kuma bashida wacce ya tsana arayuwa sama da Elham" kuka
sosai ya saka shikadai tamkar wani karamin yaro a ranshi yace "Ina zankai Wannan kazamar?

Ina zan iya da yarinyar da faruk ya gama lalatawa gaba daya,kai wlhy gobe dolene nakira
momy na bata hakuri,idan ta rabani da Raihan mutuwa zanyi".....


Kasancewar yau weekends yasanya Elham ke kitchen tana girki asaman risho,taba tsakiya da
aikin tajuyo sallamr su Raihan itada uwarta,mahaifiyarta inna ma fitowa tayi dauke da mamaki
a fuskarta tana musu Barka da zuwa , sheqeqe Umma ta kallesu tace

" ke Asabe gunki nazo,wato sabida kinaso yarki dole setayi kud'i shine kiketa faman qaqa bawa
faruk itako,kuma kunga bakuci nasaraba bazan taba bari me jiran gado ya auri yar matsi yataba
shine kuka zago kuka koma gun Abdul mijin da kowa yasani Raihan dina ze aura,kuka asirce
uwarsa tace yanzu Elham ze aura? To ban hana kuba amma wlhy ku kuka da kanku da abinda
zan muku Idan kuka wa y'ata kwacen miji,faruk kuma baze taba auren yar masu Kwana a kofar
gida bba".....ba karamin ,baci ran innah yayi ba da Wannan cin kashin bayan sun wuce tayita
yowa Elham fada akan shishigin ta da samarin,amma ba ruwanta da zancen aurenta da Abdul
domin kuwa uwarshibce ta nemi alfarma, ita kanma bataji Wannan labarin ba se yanzu,ga shi
Innah tace ko wayar faruk ta kuma dagawa Allah ya isa,wunin ranar a daki tayishi tana
kuka,bazata taba musawa momy ba kodan halaccinta agareta,kazalika bazata taba kaunar
Abdul ba kamar yanda bazata taba iya dena san faruk ba.

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awara Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                           03

Washe momy na tsakiya da breakfast Abdul ya kirata,k'aidane Awurinta idan tana cin abinci
bata magana,Wannan yasanya sam bata d'aga ba,se bayan data kammala sannan tayi kiransa
back....gaisawa sukayi cikeda girmama wa,sannan cikin sanyin murya yace

"Momy dama akan zancen Elham ne damukayi jiya,dan Allah momy ki yi hakuri,wlhy narigada
na gama tsara rayuwata zanyine tane da Raihan,Idan akaimun haka ba'a mun adalciba" gyrana
zaman ta tayi ta daura kafarta daya kan d'aya sannan tace

"Babana Ashe kam kacika me hikima,kuma zuwanka a kasar turawa yayi matukar tasiri
akanka,Ashe dai mutum da kanshi shine yake tsarawa kanshi rayuwar dayake so yakuma ga ta
dace dashi banida Wannan karatun kuma agidan mu ba'a koyar dani irin shiba,wanda na sani
shine Allah wanda ya halicci komai da kowa shine yake karawa bayinsa rayuwar data dace

dasu ba wai Su bane suke tsarawa kansu,amma nagode daka sanar dani yanzu....zancen
Mamana kuma Idan baka manta ba aiba tilastaka nayi ba,rokarka kurun nayi nace ka fitar dani
kunya dacin zarafin da akamun,amma tunda tsarin rayuwar ka a hannunka yake,nagode maka
kaje ka ci gaba da tsarin yanda kaso....abu na gaba kuma kaje na janye maka auren Elham
sedai fa ko bayan raina ban yarje maka auren Raihan ba,seka shirya tsara wata rayuwar da
wata ba itaba me tsari" kit ta kashe wayar gaba d'aya,jikinshi ne ya mace koda yakuma kiranta
ta kashe wayarta.....Faruk duk ya gama kad'uwa shida Raihan yayinda Fulani Babba ta dauki
k'iyayya me tsanani ta d'aura wa Elham da iyayenta,bata tsammanin zata iya bari faruk ya tab'a
auren Elham,kazalika bazata taba iya barin rayuwar Raihan ya tagayyara ba beside koda faruk
ze rasa sarauta ai Idan Raihan ta auri Abdul sarauta tamkar a hannunsu take,zasu Shiga
malamai su mallakeshi kuma jikokinta su gaji sarautar daga baya,shirya wa tayi taje fadar me
martaba....

    Durkusa wa tayi har kasa ta kwashi gaisuwa,me matarba ya bukaci a basu wuri,bayan kowa
ya fashe tayi gyaran zaman tamatelarta tace "Ranka ya dade me martaba dama nazone akan
wata muhimmiyar magana,dangane da,zancen auren Abdul da Raihan, Haj Nana ce tace wai
bazata tab'a bari Yaronta ya auri Raihan sabida wani dalili nata da ban sanshi ba,nikuwa a
ganina da Abdul da Raihan duk abu d'aya ne abin beyi zafi har haka ba" jin tayi shiru ya sanya
yafara magana
Da daddaya tamkar baya sanyi

"Habiba dukkanin abinda kika zomin dashi yanzu ina sane dashi,ki sani shi Allah ba'a masa
wayo,ko kad'an abinda kikayi be kyau tuba,ai kodan darajar mahaifiyata kya duba ki bar faruk
ya auri Elham,nine me yanke wa yarana hukunci akan wayanda zasu aura amma fa ki sani wlhy
muddin kika hana faruk ya auri Mamana bazan bari Abdul ya auri Raihan ba,sabida Elham tafita
bukatar taimako,kisani wanna umarnine na mahaifiyata akan inganta rayuwar Elham ko bayan
Ranta,nasani cewar Idan na kuskura na had'a su kishi bazaki tab'a bari Elham ta zauna lapiya
ba Wannan dalilin yasanya na ce shi Abdul ko yana so ko baya so ya auri Elham,Raihan kuma
Baba karami na zab'a mata,Idan baki manta ba tun farkon dashi suka shirya Kansu kece kika
hana kike turawa Abdul,nasani tunaninki Abdul shine ze gaji sarauta Shiyasa kikeso ki Aura wa
Raihan shi toki sani ba sankai alamurana kazalika Abdul baya san sarauta sabida haka bazaki
b'ata mana zumuncinmu ba sam,ko Nana,na sanar mata tuni bawai dan yanzu zancen faruk ya
taso ba,na dade da sanar mata bazan bari akan Raihan zumuncin Baba karami da Abdul ya
lalace ba labari yazo min cewar basa koda gaisawa kuma Abdul bashida gaskia tun farko
yasani sun daidaita kansu,abin haushin ma har mu iyaye mun Shiga ciki daga zuwan shi ya
b'ata komai kekuma habiba kika zuge yarki akan kwadayin mulkin da dukkaninmu a duniya
zamu mutu mu barshi,ki sani wlhy Wannan karon bazan saurara miki ba,karna kuma jin zancen
Abdul da Raihan,kuma lallai ne ta auri Baba karami,kusan shekaru 4 tana bashi wahala baku
isaba" jin yayi shiru ya sanya tayi godiya kurun ta wuce abinta, rayuwarta ta baci,tsakani da
Allah bataji dadin Wannan abin ba,dama kuma Raihan ba itace take san Abdul ba kwad'ai ta
mata san duniya uwar tayi....jiki a sanyaye tashige part d'inta abin haushi kuma seta taradda
Baba karami da Raihan suna zance ga dukkan alamu kiran dame martaba ya musu dukkansu
yayi tasiri akan su,dama ga soyayya.

     Abdul na zaune yana mamakin dalilin daya sanya momy ta dauki zafi har haka kusan
kwanaki biyar bata daga wayar sa,ga d'ayan bangaren Raihan ma bata daga wayarsa,kullum
cikin kiran Feenah yake,akan ta bashi momy amma sam momy bata karbar wayar,jin karar 
shigowar message yayi a wayarshi koda ya duba Raihan ce
"Salam yaa Abdul plss Kayi hakuri dani kamar yanda Nima na hakura dakai arayuwa,abubuwa
ne iri iri daba kasan dasu ba,banajin dadin rashin daga wayarka amma nasani hakan shine
daidai,ban guje ka sabida bana sankaba,wlhy ko kadan ba haka bane na dai gane kuskure
na,sam ban kyautawa Baba karami ba,ina fata zaka fahimceni kuma Wannan baze taba mana
zumun cin muba.Nagode Raihan." Nisawa yayi bayan ha karasa karanta message din yace a
sarari..."Bazan taba dena sanki ba Raihan abu daya na sani tunda kika iya jin zaki rabu dani
cikin lokaci kankani haka tofawa Nima zan hakura dake, Elham kuwa bazan taba Santa
ba,zande aureta kurun sabida biyayya....

  Yau Kusan kwanaki goma sha d'aya fa momy bata d'aukar wayar Abdul,ya damu
matuka,Wannan dalilin yasanya ya kira friend d'inshi zayyan ya sanar masa komai,gyaran
murya zayyan yayi yace

"Zancen gaskia moris maganar iyaye ba abin wasa bane,nifa iya gaskiya Na nake gaya maka
ka daure wa kanka ka aure yarinyar,kasani Kaima momy tafisan ka fiye da kowa a yaranta
mesa d'an wannan abin ze gagareka,macece fa a hankali zaka koyi santa insha Allah" dan
nisawa yayi yace "Zandai aureta zayyan amma sam bazan tab'a Santa ba wlhy,kuma yazanyi
da san Raihan ? Wlhy ina kaunarta" dan guntun tsaki zayyan yayi yace

"Kaga nifa moris bana sanka da rigima,kaida kanka fa kace dani tajuya wa first love d'inta
beside haka zaka bari ran momy yata b'aci mahaifiya uwa fa ? Kasani wlhy ka gyara tunanin ka
tawa shawarar kenan" nisawa Abdul yayi yace

"Yanzu ya zanyi zayyan?"

"Zuwa zakayi ka fara  kiran Yarinyar a Waya,kuma ka daure kace ta hadaka da mahaifiyarka ka
bata hakuri,ka sani fushin mahaifa wlhy Masifa ne moris"

"Tayaya zan kirata ince tabani momy zayyan?, girmana ze fadi a gunta fa" tsaki zayyan yayi
"kaje wurin tariyar girma ka b'atawa mahaifiyar ka rai,bawai nace ne kace ta baka momy kai
tsaye ba,kurun kamata dabara,misali bayan kun gaisa ya skul,waye waye Idan kun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login