Showing 6001 words to 9000 words out of 53214 words

Chapter 3 - Hafsat Ilham Book Complete by Billy Galadanci .pdf

20 Mar 2025

3488

dan taba
hira se kace kana gaida momy kuma ta tabbatar ta sanar mata"
"Zayyan tayaya zanyi hira da Elham dan Allah, ni harga Allah kazantar Yarinyar nakeji Wlhy"

"Kaika sani ni kaga ina kan aiki se an jima" datse wayar yayi kan yace wani abin,shi kuwa yayi
sororro yana kallon wayar,ya dade yana nazarin maganga nun zayyan kan daga bisani yakira

Safeenah,lokacin ita da Elham ne zauna sunawa momy tausa,domin agunta Abdul ya gado
k'yank'yami sam bata huldarta da hadimai,shiya sanya Fulani Babba ke cewa dan bata gada
bane. Dagawa tayi cikeda girmamawa ta gaidashi sannan yace "ki sending mun Number din
Elham yanzunnan kinji ko?" D'an kallon momy tayi kasance war ita sam bata san meke faruwa
ba kuma dama tasu bazuwa tayi d'ai data Raihan ba sannan tace "To Yaya Yarima yanzu zan
turo" momy ce ta bude idonta dasuke a lumshe tun sanda suka fara mata tausar tace

"Me zaki tura masa kuma?"
"Number din Elham yake so wai" gaban Elham ne ya fadi yayinda zuciyar momy tamata sanyi
ganinta takusa cimma burinta....a d'aya bangaren kuwa Abdul ya baiwa Elham msd col har biyu
bata dauka ba kasancewar wayanta nacikin gidansu ita kamma bata gidan tana gun momy,se
bayan isha tashigo wanda bata mabi takan phone d'imba,tana gama wanka tabi lafiyar
gado,can acikin bacci taji wayarta na ringing janyota kurun tayi ta daga ta kara a kunne,a
tunaninta samra Ce tasani ita kadai ke mata Wannan iskancin,cikin muryan bacci tace

"Samrah wai meye haka ne,kina yawan san takura ni wlhy,bacci fa nake" dan gyaran kwanciyar
sa yayi sam be fahimceta ba yace

"Hafsat ya gida?" Zabura tayi jin muryar Abdul tace "yaa Abdul ina Kwana ya aiki?" Murmushi
rikicewar ta ha sakashi yace batare daya shirya zuwan furucinba "Hafsat ina Kwana fa? Sabida
kurun ke kina bacci seki ce dani ina kwana, Toni ban ma kwanta ba balanta na gari ya waye"
kasa sakewa tayi da dogon surutunsa tace "kuskure ne Kayi hakuri yaa Abdul" shiru dukkansu
sukayi sannan yace "seda safe,gobe Idan kinje wurin yarki kice ina gaidata" Murmushi tayi
itama tace "zan fada mata inshaa Allah nagode sosai"

"Kinyi Alkawarin zaki fad'a d'in?" Ita dai binshi tayi da to a ranta tana tunanin yanda za'ayi ta
sanar wa momy Wannan zancen, ahaka ta ajiye wayar tana nazarin dalilin kiran,ba wata
kwakwarar dalili neman magana ne kurun.

Da safe ya kasance asabar dan haka da wayarta ta tsala ado ta tafi part d'in momy,suna
gaisawa tafara gyaran d'akin momy ko ina yayi kalkal sannan ta dawo gyaran parlor tana
tsakiya da gyaran wayarta yafara ruri,dagawa tayi takara a kunne da sallamar ta,amsa ta yayi
cikeda isa yace "ki ajiye duk abinda kikeyi kije part d'in momy ki kaimata Waya zanyi magana
da ita" d'an wai gawa tayi ta kalli momy dake cin breakfast,tace masa tana me shigewa cikin
dakin "yaa Abdul inajin nauyi fa mezan ce da ita,dan Allah ka kira yanzu phone nata yana kusa
da ita" shiru yamata tayita hello hello,ba amsa can taji ya katse wayar,kiransa tayi back yaki
dagawa har kusan so biyu,Sekuma taji ba dadi ganin cewar sam yaqi daga wayar kuma ta
fahimceahi yana da saurin Fushi ta sani Fushi yayi,dawowa tayi parlor din taje dakyar tace
"Momy dama yaa Abdul ne jiya yace na gaidaki,yanzu kuma yace na baki wayar kanna zo nan
ya yanke ko zaki kirashi da wayanki dan Allah" momy gani tayi tamkar Abdul ya sanarwa Elham
bata daga kiransa,kuma seta kula tamkar Elham ta damu Wannan ya sanya ta,dauki wayarta
tayi kiranshi,jikin shi har rawa yake ganin ta kirashi ya daga,ko gaisawa basui ba yace

"Momy dan manzan Allah kiyi hakuri, wlhy na gane kuskure na,na tuba momy wlhy zan auri
Elham din dan Allah kimun gafara" nisawa tayi sannan ta tashi tashige dayan sashen daba
kowa tace

"Zan gafarta maka Idan kamun alkawarin zaka rika kiranta so uku a rana,zaka mata yanda
kakewa Raihan sanda kake neman aurenta,zaka biya mata bukatunta Idan basufi karfin taba
kuma zaka shigo next month" nisawa yayi yace "zan yi momy,wlhy zanyi nanda sati biyu ma
Zanso inshaa Allah" sallama tamasa ta sauke qayataccen Murmushi cikeda nishadi ta koma
parlor......

Hankalin Fulani Babba sam baya jikinta ganin fa dagaske me martaba yake kuma kowa ya
goyo bayan hukuncin ta,ga faruk ya koma paris abinshi baya ma kiran Waya gida, gashi kuma
Raihan da Baba karami sun kara d'inkewa Yarinyar taqi bata hadin kai tai bori tace dole se
Abdul,duk tashige damuwa sosai.
Wanin ranar Rabin shi Elham a wurin momy ta yishi,se bayan la'asar tabar gidan zuwa
gidansu,Innah ta gaida inna ta ansata cikeda kauna tana kallonta ,ta yabawa yar yanda tayi
jarumtar cire faruk a ranta gaba d'aya, takuma sani badan bata sansa ba,kurun dai Hafsat ne
bata daukar wulakanci tasani wulakancin da Fulani Babba ta musu ne ya sanya ta fitar dashi
aranta.....wuraren shidan yamma yakirata,da sauri kuwa ta d'aga wayar

"Yaa Abdul Barka da yamma" seda yadanja fasali sannan yace "Lapia,karki karamun abinda
kikamun d'azu bana so" shagwabe wa tayi tamkar zatayi kuka,wanda ita bata dauka komai ba
tace "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri wlhy bazan kara ba" wani yarrrr yaji ajikinshi lokaci daya
abubuwan dake kai saqonni na fahimta acikin kwalwarsa suka dena aiki na na 1 mnt,dakyar ya
tattaro nutsuwar sa yace "Naji" a takaice,gani tayi tamkar be aminta ba tace cikin wata
shagwabar "Yaa Abdul plss mana,trust me bazan kara ba" kasala ce dabesan dalilin taba ta
saukar masa ya kasa koda motsi bale yayi magana takuma cewa "yaa Abdul Allah fa nace"
cikin muryar kuka,d'if ya kashe wayar yarasa dalilin dakesa kirjinsa ke dokawa dazaran tayi
magana,yace aranshi "nifa momy tabani aiki Wannan kazamar jakar zata rainani ko ubanwa
take wa shagwaba oho" ita kuwa tsaki taja tana share kwallar data sakko mata tace "Allah yaa
Abdul bazan taba sanka ba,na tsaneka Nakuma tsani halayenka na jiji dakai,zan aureka kurun
sabida iyaye nka".

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*A gaskiya kuna sakani farin ciki ba kadan ba,sena tattare dukkan nazari na da tunani,ababen
dake sarquwa a kwanyana dan gane da aika saqon fahimta duk se su tsaya cak,ni kanyi
mamaki matuka yanda kuke nuna kaunar ku ga rubutuna duk kuwa dayake nidin karamar su ce
acikin marubuta.....a wani bangaren mamakine kan kashe ni duk na tuna a shafin farko na book
nawa kuke fara comments,dan Allah ku yarda dani ina sanku har raina*

04
Wuraren karfe 9 na daren ranar ya kuma kiranta amma sabida hafsa tafishi zuciya ga kuma
rashin daukar raini ya sanya taki dagawa,msd col biyu ya bata,ranshi yaji ya sosu ba bad'an
ba, daba dan momy bace wlhy Wannan Yarinyar da tayi kadan yasani sarai tana ganin col nashi
tamasa banza,amma zata fahimci baya daukar raini Idan tashigo hannun shi....a bangaren
Elham kuwa ta kudiri niyyan bazata kara daukar wayar saba,tunda kullum burin shi ya bata
mata rai,ita banda munafurci ma batasan meye na kiran taba,washe gari kuwa bata ma tafi da
wayarta sashen momy ba haka taje saddan,ayyukanta tayi tazo ta zauna cin abinci tare da
momy da feenah,wayar feenah ya soma ringing, dagawa tayi ganin yaa Abdul ne

"Yaa Abdul ina Kwana" be amsata ba yace kije gidan su Elham ki kai mata Waya Kokuma kice
da ita nace lallai ta kirani yanzu" tana kokarin sanar masa Elham na kusa kurun ya datse wayar
tabe baki tayi ta kalli Elham tace

"Elly ina wayan kine?"" Kallonta sukayi har momy,sannan tace

"Tana sashen mu,agida na barta" dan yake tayi tace "Gwaramun me martaba ya kirani ban
dauka ba nasan ze fahimci bana kusa akan yaa Abdul ya bani ko half msd c ne Idan akwai,ya
tsani ya kira mutum yaqi d'agawa ko alama,yanzu kinga masifa yake wai na sanar dake ki
kirashi yanzunnan" batayi magana ba shiru kurun tayi momy ce tace "ki tashi kije ki kirashi
yanzu" mikewa tayi jiki ba kwari taje gidan msd col hudu ta tarar Nasa ,seta tsinci kanta da kasa
kiranshi tsoro me tsanani ya shige ta,ta sani bazata iya gaya mai bakar magana ba amma fa
batada juriyar wulakanci,tsaf zata kashe masa Waya Idan yanemi gaya mata ba daidai,daga
karshe dai phone nata ta kashe gaba d'aya.... Ba ita ta koma part d'in momy ba se bayan isha
sannan ta Shiga, suna wa momy tausa wayar feenah ta fara ringing tana dubawa taga Abdul
ne,tana daga wa yace "Idan Elham tana kusa ki bata yanzu" batare da tayi magana ba ta
mikawa Elham waya,tana karba tabar wurin seda tashiga d'akin momy sannan tace cikeda
faduwar gaba

"Assalamu Alaikum" cikin tsawa yafara masifa

"Ke Elham me kika dauki kanki ne? Tun yaushe kike ganin col dina bakya dagawa kuma bakya
kira back,kuma tsabar raini seki kashe wayar gaba daya,me kike tagama dashi kazama dake,ke
badan umarnin iyaye ba da kin isa na rab'i hanyar dakika bima,iyayena naso su miki gata amma
kina wulakanta musu yaro,ke bakisan halacci ba ko,dama mana tsinatacciyar mage ai bata
mage,kisani wlhy talaka irin ki nafi karfin wulakanci daga wurinta,alkawrine nayiwa momy zan
kiraki kullum so uku arana,dabadan uwa na uwa ba wlhy bazan kara kiran kiba,jaka kawai

dabata san girman na gaba da itaba,kuma Idan kin isa Nakuma kiranki kimun banza,zan miki
uzurin bakya kusa amma wlhy bazan miki uzurin rashin kirana back ba,idan katin wayane
bakida zan miki VTU yanzunnan" kukane ya kwace mata,jin tana sheshekar kuka yasanya ya
kashe wayar dak'yar ta iya saisaita kanta ta koma parlor d'in, momy ta zata wayar arziqi sukayi
se washe baki taki,a daddafe ta gama abinda take ta koma gidansu,wanka tayi sannan ta kunna
wayarta tayi adu'o in Kwanciya Sekuma ta kasa baccin ta soma kuka me tsuma zuciya,a haka
ranar ta Kwana kuka tana mejin zafin zagin wulakncin da yamata,a rayuwar ta ta tsani a Rena
mata iyaye da talaucinsu ko sabida kurun suna karkashin inuwarsu bashi ze basu damar
wulakan tasu ba,mijin da zaka yana maka zagin na tozarci tunkan ayi auren hmmm...washe gari
da ciwon kai ta tashi dama kuma sn fara final exam na kammala secondary skul,ranar ba skul
basuda Exam kasa yin komai tayi,Wuraren 9 wayanta yafara ruri janyo wa tayi a wahalce,ta
kara da kunne "Assalamu Alaikum" "Alaikissalama" ya fada cike sa isa

"Yaa Abdul ina Kwana?"

"Lapia kin tashi lapia?"

"Alhamdulillah" tabashi amsa a takaice "meyake damunki Elham,muryanki wani iri?" haushi ne
ya tarnake ta tace "Ba komai qalau nake" shiru yayi itama hakan kusan minti biyu,daga bisani
ya datse call din, tsaki taja tace aranta kadaiji da rainin wayonka d'an masu kud'i.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya sam Elham batajin dad'in rayuwar ta, ta tsani Abdul ta tsani
kalar wulakancin shi,ta tsani jin koda muryar sane,ta tsani tunawa da zancen auren sa gaba
daya,duk sanda ta tuna cewar sun kammala exams gaba d'aya gashi taji ance me martaba ya
saka bikin nanda watanni biyu setaji tamkar ta daura hannunta asaman kai ta zunduma ihu,ba
karamin dad'i tajiba sanda akace zezo kuma ya fasa zuwa sabida aiki yamasa yawa sabida
bata bukatar ganinsa....

Tafe take cikin doguwar bakar jallabiya me adon yellow stones, ga rigar tasha shape,d'an
karamin cikinta daya lafe tamkar ba'a saka masa ko loma d'aya aciki,ga wadaccen kugunta
daya ke kad'awa batare da tasaka shiba,tafiya takeyi tamkar tanajin tausayin kasa,fuskarta tayi
fayau ba komai a cikinta se powder da lipbalm, kallo d'aya zaka mata ka gano sam bata cikin
walwala,dadana wayarta take tana faking murmushin.....shi d'inma wayarsa yake dannawa
hankalin shi yana wurin abinda yake se karo sukayi da juna take wayarta ta sub'uce a hannunta
tafad'i a kasan interlock dake shinfide a wurin tare sukabi wayar har suna gwara kai,hannun
tane yariga nashi kaiwa yayinda nashi ya sauka akan nata,lokaci d'aya wani shock ya sauka
musu dukkansu atare suka d'ago suka kalli juna,a haka suka k'urawa juna ido tamkar wasu
statues,itane tafara dauke kanta,yayinda shi kuwa da sauri ya dauke hannunshi daga nata,atare
suka mik'e batare da kowa ya dauko wayar ba,Kawar da kanta tayi akaro na biyu tace "yaa
Abdul Kayi hakuri ban kula kana zuwa ba" dukawa yayi ya dauko wayar ya mata kallon tsafta
yace cikin gadara

"Duk lokacin da kuke tafiya kuna maida hankalinku akan hanya kina jina?" Kai kurun ta gyad'a

masa tana tunanin what on earth was he doing dabe mayarda hankalinshi akan hanyar ba
shima,tana tsakiya da tunanin ta tsinkayi murya sa yana cewa

"Wayar kinnan kai tsaye ta lashe screen Elham,ki shirya karfe 8 daidai ki sameni mota zamu
fita" batare daya jiyo cewarta ba ya wuce abinshi kazalika be bata wayar taba dashi ya wuce,
tab'e baki tayi itama ta wuce part din momy,a ranta tana mejin zafin lashewar wayar ta,harga
Allah bataji dadi ba....feenah ce tace da ita "D'an bani aron wayarki Elham inaso nakira Ashraf
ntwrk nawa ya dauke d'if MTN basuyi ba Allah" dan rausayar da kanta tayi tace "Yanzunnan
nayi karo da yaa Abdul wayar ta cinye screen wlhy,tanama hannunshi"

"Subhanallah wayar nan ko 9 month tayi kuwa? Amma banji miki dadi ba sam,yanzu me yace?"

"Bafa abinda yace,kurun yace na shirya mu tafi wani gu anjima" dan Murmushi tayi tace "Allah
sanya wata wayar ze siya miki,nasan shi da kyauta inba hakaba aike da irinta har abada" sarai
ta gano abinda take nufi cewar iyayenta bazasu iyaba,bayaga laifin taba kasancewar tasani
komai momy ce ke mata.......gidansu ta koma ta tsala wanka ta saka hadaddiyar atamfarta
dinkin riga da skirt ja ya amsheta sosai,sosai ta murza dauri yasha steps ta feshe jikinta da
turaruka masu sanyin kamshin,light makeup tayi ta yafa dan mitsitsin mayafinta a kafada,ta
dauko yar cloche bag dinta da uban takalmi me tsini tafito cikeda yanga,karfe 7:56 tana wurin
motar tsaye yayinda Shikuwa 8 dinnan ya karaso shi d'inma se tashin kamshi
yakeyi,turarukansu suka hade suka bada wani kamshi me sanyin dad'i, dukkan ninsu sun
shagala da kallon junansu,itane tayi saurin sadda kanta kasa tace "Yaa Abdul Barka fa fitowa"
kallon ta ya d'anyi yace "yauwa" motar dayake komai nata is computerized kirar 508 ya bude da
remote key nata suka shige,hanyar Hamdan phones ya dauka da ita suna isa yace ta fito,a
yangace take tafi yarta ta catwalk ,shi harga Allah mamakinta yake yanda ta dauki kanta,kalli
shigar datayi sekace wata yar Sarki,se yauk'i takeyi tamkar zata karye,d'an guntun tsaki yaja
yabi bayanta,suna isa suka hadu da samrah da mijin dazata aura kamal,d'an gudu tayi wanda
ya qayatar da dashi ta daka tsallah ta rungume samrah, "saam dazu muna chat wayana ya
sub'uce mun ya lashe screen nayi bakin cikin baki kara samun hirarba" dariya sukayi tace
"akwai gobe zan shigo gidanku saam dolene naji kanun labarai" yana daga nesa kusa da wasu
samari yaji dayan cikinsu yace "Baba kalli inda Allah yayi yalwar kugu agun chic dincan me jar
atamfa, tsinanniyar yanzu zamu zamuce munasan mud'an latsa ta nuna ita ta manya ce"
rayuwar shi ce yaji ta masifar baci,barin wurin yayi yazo ya gasa da kamal da samrah yace
"Elham akwai wanda ke jirana muje muyi abinda ya kawo mu,mutafi" sallama tawa qawar
tata,sukaje wurin phones ya zaro mata iPhone 7 kurun yace muje" biyan kudin yayi,suka bar
shop d'in, duk daba hira sukayi ba sanda zasu zo seta kula ya sauya fuskar sa zuwa bacin
rai,gyaran zama tayi tace "yaa Abdul dan Allah ruwa nakeso" ko Kallonta beyiba har suka isa
gida,kallonshi tayi tace " yaa Abdul nagode sosai Allah ya kar'a girma da budi" Binta kawai yayi
da ido ya zaro wayarta ta dazu,yaciro sim card nata ya bata,karb'a kurun tayi tabar cikin
motar,da sauri yafito yace " zonan Hafsat" zuwa tayi kusa dashi ta tsaya yace "Ba'a sanar miki
anbiya sadak'in ki bane" shiru tayi rai abace yakuma cewa "Daga yau duk inda zakiji Sekin nemi
izinina kuma Wannan guntun mayafin bana sanshi,lallai kiyi Shiga ta mutunci koda bazaki saka
hijabi ba" batace komaiba ta juya,hannun ta ya damko ya juya da ita gaba daya ya daura dayan

hannunshi asaman kugunta yace "Bakiji abinda nace bane zaki juya kiyi tafi yarki sekace ina
magana da iska" numfashin tane taji yana zarya yana barazanar daukewa dakyar ta iya cewa
"yaa Abdul dan Allah ka sakeni ba kyau fa wlhy" sakinta yayi ya riko hannunta gagam ya matso
daf da ita har suna jiyo bugun zuciyar juna yace "Ohh Wato sabida niba faruk bane ko? Shi daidai ne ya murza ya kuma shade dukkanin jikinki
yanda yaso, kisani wlhy badan najin komai na taba kiba,ke kinmun kazanta na yi Wannan dake
,kisani Kinyi gangan cin shigowa rayuwa ta,kazama kawai" ya sake hannun da karfi anan ta
sake kwalin wayar da sim card din ta juya gida da gudu tana kuka.... [1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

06

Kara matsawa yayi kusa da ita yace cikin sanyin murya "Hafsat dan Allah ki tashi muje,koso
kikeyi kowa seya fahimci halin damuke ciki" dakyar ya iya furta kalaman ban hakurinnan,tunawa
yayi da maganar momy datace karya kuskura ya b'ata ran mamanta,Shiyasa kurun yake
rarrashinta kuma sarai ya sani feena seta gayawa momy cewar ga abinda ya faru,banza ta
masa ya sanya hannun sa ya dagota,da sauri ta kwace hannun nata ta kara matsawa cikeda
fusata,beta ba ganin ta harzuqa irin haka ba,d'an tattaro hakurin daya rage masa wuri daya yayi
yace cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login