Showing 27001 words to 30000 words out of 65850 words

Chapter 10 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf

Advertisement

02 Aug 2025

2677

kina 15 kika shiga orchid ihsan told me .

Murmushi tayi tace ina cikin karshen shekarana shabiyar time din and i will be 18 ,2 months
after na bar school,

Amazing "
So Kinga nama rike abunda ke raina sai kin zama adult .

.......ubanka ne yake ranka hala ."muryar ammi ta ziyarcesu ,karasowa tayi kamar ana ingizota ,
Deenah na ganinta tayi sauri ta mike dan tasan zata iya samata hannu,
Aikuwa kamar yarda tayi expecting din tayo kanta ta wawurota tana kaimata bugu tana zagi,
Da kyar binyamin ya kwaceta ya rike ammin yace ta gudu,Ai babu shari ta keta a guje ,
Hankaɗesa ammi tayi ta mara mata baya kamar wata mahaukaciya inda shima ya bita da nasa
gudun yana mai kiran sunanta,
Tashi zaune Mami tayi ganin yarda deenah ta shigo a zabure
"Lapia?
Bayanta ta koma da gudun jin miryar ammi na faman zaginta,
Kamar an watsota haka ta faɗo dakin tana mai faman danna wa deenah da maminta Ashar
kamar yar tasha,
Shiru mami tayi ranta cike da mamaki ganin tijararran zagi da take masu wanda bata san
dalilinsa ba ciki kuwa harda cema deenah shegiya wadda batasan asalinta ba,
Hannu ta fara kadawa Mami tana cewa "wallahi ki fadama Yarki ta fita shirgin dana kar ta
iskanta mun shi da mentality dinku na mitsiyata ,duk ranar kuma dana sake ganinta inda yake
wallahi abun bazai dadi ba ,
Dan ubanta ,
Binyamin ne dake bayanta cike da takaicin abunda take yace "Ammi please,nifa deenah ba ita
ke bina ba hasali ma nine ke kiranta tazo and ammi tayaya deenah zata iskanta ni when im very
old enough da nasan Mai kyau da kuma mara kyau,
And beside yarinyar nan is innocent bata taba miki wani harm ba so menene lapinta ?
Hasalima nine zaki ma kallan Mai laipi saboda Ammi i don't wanna hide it anymore,
I LOVE DEENAH ,
Yes Ina san deenah and bawai da wasa ba ammi inaso na maidata abokiyar rayuwata,i mean
ina son na aureta.

SO?
AURE?
Muryoyi uku suka tambaya cikin mamaki,
Mami ,ammi Sai azad wanda Ya garzayo Gurin Dan jin maike faruwa Dan Har sashensu ake jin
jarabar ammi,
Eh so da aure ammi i choose her Dan Allah stop all this.
Wata irin dariya ammi tasa tace aure Da soyayya indeed,

Yatsa ta nuna ma Mami tace "ke kuma kije ki faɗawa malaminki aikinsa ya karbu amma Ku Sani
zan karyasa  kuma zanyi maganin abun,
Tana kai karshen magananta ta fice a dakin fuuuu ko ganin azad da ta bangaza batayi ba ,
"Mami Dan Allah kiyi hakuri da abunda ammi na tayi dan Allah,
Bai jira abunda zatace masa ba ya fice a dakin dan marawa mahaifiyarsa baya,
Deenah wadda tayi mutuwar Tsaye a gun jin Wai binyamin ne ke fadin yana santa kuma zai
aureta ,
Maimakon taji haushin dukkan abunda ya faru da kuma wulakancin da akama mahaifiyarta Sai
ta tsinci kanta da jin wani irin arnen dadi da tasan yarda tayi ta boye ganin azad bakin dakin ga
kuma mami da mama kaltu wadda shigowanta kenan bama tasan Mai ke faruwa ba,
"Lapia dai ko?
Ta tambaya tana Mai Kallan Mami da kallo daya zaka mata kasan tana cikin halin bacin rai"
yar kwallar da ke gefen idanta ta goge tace mama kaltu ki tambayi deenah ,inajin ta chanza ni
matsayin uwa shiyasa yanzu bata jin maganata ,batasan Mu zauna lapia a gidannan Wai
soyayya fa take Da bilyaminu ,bakiji cin kashin da ammin sa tazo Har dakin nan ta mun ba ,
.wallahi ba soyayya fa muke ba mami,

Karya yake dayace yana sanki kuma zai aureki kenan,
To wallahi this is not going to happen deenah not when im alive bazai iyu ba,
azad Ya fada yana Mai kokarin goge tasa kwallar kafun shima ya bar Gurin.

Kalanta Mami da mama kaltu sukayi a tare ,mamice ta fice a dakin inda mama kaltu ta rufa
mata wanda hakan ya nunawa deenah ta taro match bata da players amma a zahiri kuma sai
tsintar kanta tayi da murmusawa da ta tuna kalaman binyamin.

CHUCHUJAY.

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

KALUBALENAH

19.

A wani irin yanayi azad Ya nufi part ɗinsu yana kuka ,
Mahaifiyarsa ce dake saukowa daga sama ta gansa ,
Saurin saukowa tayi tana rafka salati ganin hawaye na bi masa kunci wiwiwwi,
Rikesa tayi ta jijjigasa tana Mai faɗin kai Lapia".
"Ba Lapia ba mommy im sick and i think im dying "
Mutuwa kuma azad na shiga uku Mai ya faru ,
Kaninsa mubarak da suka shigo tareda kanwarsu farhana ne ya fara kuka jin abunda
mahaifiyarsu ke faɗin na Wai Mutuwa,
Mommy whats going on".
Nima abunda nake san Sani kenan mubarak ,azad ina sauraranka waya mutu,

cikin kukan yace ,mommy babu wanda ya mutu amma ni zan mutu idan na rasa deenah ,
Wallahi mommy ina santa and i want to marry her".

Wait !wacece deenah ,who's deenah .
Dan tsaki mubarak yayi yana mai rabawa ta gefensu Dan wucewa kafun yace "mommy duk
gidannan wacece deenah idan ba so called best friend ɗinsa ba kuma yarinyan mai aikinki,
farhana abeg muje na koya miki assignment ɗinchan Bro Abubakar na jirana zamu danyi
football match,
"Inajin Mai aikin ma mutum ce and wallahi abubakar let this be the last time da zan maka
warning akan kiran deenah mai aiki.

Uhmm lallai brother wai deenah sha shes beautiful .

Wani banzan kallo ya bawa farhana wadda tayi saurin tsallakawa ɗan bin bayan Mubarak.

Ajiyar zuciya mahaifiyarsu tayi wadda bama tasan uban da zata ce masa ba,
Dafa kafaɗansa tayi ta kama hannunsa ta kaisa falo ta zaunar kan kujera ,
Sai da yayi sheshekansa Mai isansa sannan yayi Shiru yana aajiyan zuciya duk tana kallansa ,
Matsowa kusa dashi tayi tayi gyaran murya ta nemo wananan motherly baiwan da Allah yayi
mata tace "azad look here,kana kuka ne over nothing,mene wani kana san deenah zaka aureta
yarinyan da take kusan tsararka ,kaifa yanzu sa'ar aurenka habiban Uncle mamman ce kaga
she's just five itane dai dai aurenka,amma deenah, Oh come on my kid don't get distracted,
Mu kashe maganan daga ni Sai kai azad please banasan kowa yaji maganan wata deena Dan
Allah azad.
Shiru yayi baice mata komai ba amma deep cikin zuciyansa ya gama kudirar niyyar hakan ba
abune Mai iyuwaba bazai taba yarda ba koza'a mutu a dawo bazai taba yarda ba shine wanda
zai mallaki deenah ba binyamin ba .

........jaraba kawai ammi take tana kumfar baki,ta inda take shiga ba tanan take fita ba almost
hours nawa da faruwar Abun amma a yanzu ma dasuke cin abincin dare bata hakura tayi shiru
ba,
Aje spoon Abba yayi da karfi yace "wai nikam madam menene damuwar kine kike ta magana
guda ɗaya wadda babu wanda yasan tushenta.

Abba kaima dai ka faɗa wanda take faɗannan ma dominshi yaki zuwa yaci abinci and Bai
masan tana yi ba ,
"Cike da masifa ammi tace "oya Tashi kibar Gurin nan ,maza dauki abincinki kije chan dakin
yayan naki ki karata dama halinku ɗaya ai ,
Dan murmushin ihsan tayi ta dauki plate din abincinta Dan ammi dama ta gargadesu akan kar
su kuskura abbansu yaji maganan amma hakan Bai hanata mita ba duk da a faɗan bata fito
takamaimai tace ga akan abunda take ba ,

"Alhamdulilah cewan Abubakar,
Tashi yayi tsan badan ya koshiba amma Sai rashin san hayaniyarsa ga ya ga alama
mahaifiyartasu yau hayaniya take ji ,
Tashi shima Abba yayi yana Mai faɗin bari Nima na tashi Tunda duka kin koremu dama ina
saurine,
Batace masu komai ba ta cigaba da cin abincinta Tana Mai ayyana abubuwa da dama akanta .

Bangaren deenah kuwa bata samu daman magana da mahaifiyarta ba sai da dare bayan sun
gama cin abinci wanda yake kamar al'ada suke haduwa su uku suka ci,
zama gefen Mami tayi tace "mamina dan Allah ki yi hakuri kar kiyi fushi dani ,
Wallahi Mami ni bani nasa Yaya bilya faɗan abunda ya faɗa ba hasalima ni bansan abunda
yasa ya faɗi hakan ba,

"Kina tunanin ban lura da irin farincikin da kike ba saboda ya faɗi hakan ba deenah ?
Kinaso kijefa Mu cikin matsala ko?
Kin rantse da Allah Sai kin jefa Mu cikin tarkon matar nan ko ?
Mama kaltu gatanan kilan zatafi jin magananki kifada mata wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa ,
Baki mama kaltu ta shiga bama Mami inda take mai kara tunatar da Deenah akan da kiyaye ,
Da kyar suka samu suka shawo kan Mami wadda tsakaninta da Allah take tsoran duk wani abu
da zai haɗa ta da ammi...

"Meet me outside the compound "shine message ɗin da ya shigowa deenah cikin wayanta
lokacin da ta gama shirinta na zuwa makaranta ,
Dan murmushin jin dadi tayi ganin binyamin ne ya tura mata sakon,amma tuna faɗan maminta
yasa ta ma kanta fada ta tura masa sakon
"No ka wuce zan biyo su azad.

"I'm still waiting kiyi sauri"
Ganin reply ɗinsa yasa ta tabbatar da bazai tafi ɗinba,
Harzata fita maminta ta kirata tace "ga kudin mota a hakura da bin su azad dinnan,at least zan
iya baki kudi since Alhamdulillah akwai daidai mu,
Bata mata musu ba ta karba Dan ta fahimci Mami daga jiya zuwa yau kiris take jira tace wani
abu,

Su azad basu fito ba Dan haka tayi sum sum kamar wata munafuka ta fita a gidan dan zuwa ga
binyamin,
Chan nesa da gida ta hango motansa,

Sum sum kamar munafuka takarasa ta buɗe tana waige waige ,
Dariya yasa lokacin da ta shiga motan,
Ɗan kallansa tayi ta haɗe rai tace "
Mene kuma Allah Sai na tafi dama Ai Mami taban kuɗin mota,

Haɗe hannayensa yayi yana mai gumtse dariyarsa yace tuba nake Dee.

Batace komai ba illa murmushin da tayi Dan wannan sabon sunan na Dee da yake faɗa mata
dadi yake mata ,
Tada motan yayi yace bari mubar unguwanmu tunda naga alaman tsoro kike,
Badai tace masa komai ba ya ma mota key suka dauka hanya ,

Mintuna kalilan suka kaisu cikin makarantan,
Parking yayi a inda ya ke parking kana ya kalleta ganin tana Mai kokarin bude murfin motan,
Murmushi yayi yace hajjaju Ai ban buɗeba tukunna and i blv bakiyi latti na zuwa makaranta ba
so magana zamuyi,
Gyara zamanta tayi duk da tasan maganan mene itama tanaso a yita din,
Gyara zamansa yayi yana Mai facing dinta yace "deenah duk wani abu da na faɗa a gaban
Mami da ammi i mean it,ina sanki deenah ,bansan yaushe hakan ya fara ba but all i know shine
na kamu da sanki mai tsanani sannan ni bandamu da duk wani abu da mutane zasuce ba
saboda ba Dan mutane nake sanki ba dan Allah nake sanki kuma shi shaida nane ,bani da
komai bani da kowa a gabana face ke ,
Banso Abun Ya kasance a haka ba hasalima Banso faɗan abunda yake zuciyana ba Har Sai kin
gama orchid but i guess muna namu ne shikuma Allah na nashi ,
Sannan soyayyar da nake maki bawai ta wucin gadi bace deenah i want to marry you,
Just look at me am not getting any younger ,i have everything da ɗan adam zai nema a rayuwa
but ni ban cika ba idan har ban mallake ki ba deenah,
I will take care of you da dukkan rayuwata ,i will give you a good life ,bazaki taɓa kuka dani ba
insha Allahu ,sannan ina mai daɗa tabbatar maki zaki sameni a duk yarda kikeso and ni idan da
so nane na aureki kina gama orchid ,but that doesn't mean zan tsayar maki da karatunki ,"NO"
Zan baki duk wani ilimi da kikeso a duniya duk wani qualifications da kikeso kisamu akan ilimi
zan tsaya maki ,i will support you and be with you in the journey daga nan har china idan ma
chan kikesan zuwa zan biki, yardarki kawai nake nema,
And yes im not forcing you into this idan kinji baki sona ki faɗa mun ,i want to know saboda na
sake kara dage damtse wajen zana soyayyata a zuciyarki saboda na gama gamsuwa cewa ni
dake are meant for each other so i will never back up ,
Kije ki bama Abun thought and ki dauka dukkan lokacin da zai isheki zan jira.

Wani irin yanayi deenah ta tsinci kanta ,
Kallansa tayi tana Mai jin wata irin kwalla na bimata kunci ,
Bakinta na rawa tace yaya bilya Mai yasa zaka soni?
Baka sanni ba fa ballantana asalina sannan ni ba yar kowa bace ba kuma ni mairaniyace bani
da kowa daga ni Sai Mami na wadda itace uwata kuma itace ubana sannan yaya bilya ammi
bata sona kuma nasan bazata taɓa sona ba sannan Mami na ma tace nabi a hankali nidai tsoro
nakeji.
Kallanta yayi da kyau sannan shi yasani niyarsa game da deenah mai kyauce ,

Dan murmushi yayi yace deenah kina sona ?
Shiru tayi batace komai ba illa kasa da tayi da kanta saboda kunya,
Licking lips ɗinsa yayi na kasa yana Mai rike karan hancinsa cos yanajin kamar He's trying to
force her"

Deenah look bazan maki dole ba like i said earlier amma kije kiyi shawara da zuciyarki indai
kikaji kina sona ni duk wani abu da kike kira matsala a gurina ba matsala bace,
"Wai ko Dan ammi bata sanki ,ni bai damuna cos ni ina sanki kuma nine zan zauna dake ba
ammi ba and I'm very sure she will come around saboda babu wanda zai zauna dake yaji bai
sanki,
Sannan about ban sanki ba shima ki ciresa a ranki cos cikin lokacin da na kwashe tare dake
nagama sanin wacece ke kuma ke na zaba ,sannan sanin labarinki kece kike da ikon sanar
dani ni kuma na saurara sannan duk muninsa babu abunda zai chanza a cikin sanda nake maki
,and duk wani tsoro da kikeji ki daina saboda nidai banida matsala ta wannan fanin tunda ni
naganki nace inasanki and nothing will change that.

She was very touched to the extent that ta kasa magana illa kallan window da tayi tana Mai san
tare kwallar dake shirin fito mata tace "ni na kusa latti,
Babu musu ya bude lock din motan inda itakuma ta bude ta fice da sauri hartana hada hanya.

DEENAH taji an ambaci sunanta.



CHUCHUJAY.


ƘALUBALENAH.

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

20
Juyawa tayi dan ganin mai kiranta ,hannunta ya kama ya fara janta wanda hakan ya faru a kan
idanun binyamin da yafito a mota .

bai tsaya ba sai da yakai inda yayi masa kafun ya tsaya ya sakar mata hannu, bata rai tayi tace
"ko menene hakan kuma yanzu azad ?
mene damuwanka ,
Snipping yayi yace ke,kece damuwata deenah ,For GOD sake i thought we have talk about this,
Amma bakiji ba ko ,kin fi gane tashin hankali ba ,
nafaɗan maki bazan yarda ba kima tunanin wasa nakeyi ,to ba wasa nake ba ,stay away from
him idan ba haka ba duk abinda ya faru kece sila,
Juyawa yayi zai bar gurin ta tsinci kanta da cewa "i dont love you as a man azad ,amma shi

yayanka i love him as a man ,shi nake so ba kai ba and ina tunanin this is my life and my
decision so please azad let me write my own destiny,ka daina waɗannan abubuwan i really
don't wanna lose a friend ,

yarda tace tana san binyamin ji yayi kamar ta dauki masho ta soka masa a ƙahon zuciya,
Wata irin dariyan baƙin ciki yasa kana yace "yau lastly kinyi confessing shi kikeso a gabana
right,get this straight into your thick skull deenah baza ki auri binyamin ba ni zaki aura sannan i
dont wanna be your friend i want to be more than a friend ,i want to be your everything and i will
be .
"Wai kai ana so dolene ?
nafaɗa maka yayanka nake so just rest and stop pushing those threats at me,you ain't gonna do
nothing and this is the last time we will talk about this,
Dariya yasa ya juya ya bar gurin batareda yace mata komai ba .

dukan Abunda ya faru a idanun binyamin ne wanda ya biyosu ganin irin fizgar da azad yayi
mata ,bai fito daga inda ya boye ba har sai da deenah ta bar gurin,
Babu abunda ke masa yawo a ƙwanyarsa illa furucin deenah na cewa shi take so wanda hakan
ya basa kuzari da ƙara ƙyaimi wajen ganin ya mallaketa dan dama shi yardarta yake nema,

Yana zaune a office ɗinsa yaji an buɗe an danno kai babu ko knocking ,dago kai yayi da
mamaki dan san ganin wanene,tsaye azad yayi a gabansa yana kallansa ,shima kallan nasa
yake dan ya yarda yaran nan bashida hankali,
ganin bai magana bane yasa ya maida hankalinsa kan laptop dinsa ya cigaba da abunda yake"

"brother im here to talk to you.
daga fingers dinsa yayi yace no"binyamin,call me binyamin azad saboda da ace brother ka
ɗaukeni kamar yarda ka faɗa bazaka faɗo mun nan ba babu ixinina so get to the point and get
out.

Gyara tsayuwa azad yayi yace okay"
Stay away from deenah saboda ina santa kuma na yarda itama tana sona so please stop
confusing her,ina santa kuma auranta zanyi.

Tsayar da typing din da yake yayi ya kallesa da kyau kana ya kaɗa kai yayi ɗan murmushi yace
idan ka gama zaka iya fita ,

ganin babu alamun wasa a fuskansa yasa ya fita a bakin kofa ya hadu da abubakar wanda duk
abunda suke yana jinsu,
Ta gefensa ya raba Ya wuce ,riko hannunsa Abubakar yayi yace ,Azad this is not necessary ,bai
kamata ace kana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login