Showing 51001 words to 54000 words out of 65850 words
Chapter 18 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf
ya kara birkitota,
Lallami babu irin wanda BINYAMIN baya yima deenah ,sai da ya tabbatar da ya gama cike
kowanne gurbi na cikin zuciyarta kana yayi kokari wajen tafiyar da ranakun nasa da yarage
masu ma'ana waɗanda suka chanchanci tunawa dan so yake idan tayi kewansa ta samu
memories ɗin daza suna kwantar da hankalinta,
*"A ranar da zai wuce sabon tashin hankali deenah ta tsinci kanta dan ji takeyi kamar bazai
dawo gareta ba muddin ya daga kafarsa ya bar kasar,
Amma Sanin cewa shiɗin nata ne yasa ta mika ma ubangiji lamuranta ta duku fa da yimasa
adduan samun nasara addukan wani lamari nasa na alheri da yasa gaba,
Da kyar suka rabu da juna shima sai da ya ga idan har ya tsaya to tabbas jirgi zai tafi ya barsa ,
Yagama mata arranging komai da zata bukata sannan ya samata kuɗi issasu a account ɗinta da
ya bude mata sannan ga sabuwar macbook da ya siyan mata cos tace idan ya kirata a waya
video call ya mata karami wanda ita kuma tana san ta gansa babba a screen ,yasha dariya
sosai kafun ya siyan mata macbook wadda dama yana da niyyan siyan mata saboda school.
A ranar da Ya tafi ji tayi gaba ɗaya duniyar ta mata zafi ,wani rashin lapia da bata san ta inama
yake dosowa ba taji ya rufeta wanda ta danganta da Rashin nasa ,
Haka ta koma sukuku school dan batajin daɗin yarda basu yi magana ba .
Bayan ta koma gida Kamar wasa ya kira ta ,saida ta buga wani tsalle kafun ta dauka wayan
tasa a kunneta cos tasan shine duk da kuwa number ne, tsaf ta haddace code din kasar na
waya saboda tana expecting kiransa which bata san missing,
Langwaɓewa tayi kamar tana gabansa lokacin da ta tsinkayi muryarsa cikin sanyi,
Ajiyan zuciya Ya sauke a lokacin da yaji muryanta yace"a kwanaki kalillan ɗinnan babyna nayi
missing naki kamar na gudo haka kawai nake ji.
Kwaɓe baki tayi tace "uhum shiyasa naga ai 5 days baka neme ni ba sai yau,
Gyara kwancciyansa yayi yana Mai lumshe idanu yace "Dee kinsan na kwana a lagos ne then
the next day i took another flight na chan ,
8hours tukunna na Sauka a Brussels,
I was exhausted ,and guess hutun ba wani yawa i was running here and there and yea i need a
new line and i had to settle down,amma kina maƙale a raina dan ban isa na cire kiba,
im sorry.
Dan murmushi tayi jin yarda yake jero mata bayani,
Licking lips ɗinta tayi tace naji zan hakura but only idan kamun wakar sangaya"
Dariya yasa sosai yace what?
Dee sangaya fa ?
And kinsan fa ban iya ba.
Da shagwabanta tace ni dai Allah inbaka mun ba Zan kashe wayana kuma bazan kara daukan
wayanka ba ,so just do it anyhow amma sangaya ya fito cikin wakan.
Lallashinta ya fara yace" okay drama queen ɗina ya isa haka indai wakan sangaya kike so
yanzu honey ɗinki zai maki and trust me kin daina jin wakan kowa sai nawa dan nafi m shareef
zakin murya da iya waka,
Yauwa babyna ina sauraranka ".
Babu musu ya fara rera mata jagwans din wadda ta sata cikin nishaɗi wanda dalilinta take
dukkan wani tunanin nata mara kyau ya kawar .
Hakan sai Ya zama al'adarsa a duk lokacin da ya kirata ko voice call ko video call sai ya san
yarda zaiyyi ya faranta mata duk da basu kusa inda itama a nata Bangaren take iya kokarinta
na ganin tayi masa reciprocating .
************************************
Wasa wasa deenah har ta cinye semester na farko a orchid uni,
A daddafe take haɗa kayanta da zata wuce gida hutu ,wani irin zazzabine yake damunta wanda
ta dangan tasa da damuwa da ta sawa kanta na rashin ji daga binyamin,
Sati biyu kenan an shiga na uku rabon da taji daga garesa,
Takira layinsa yafi sau babu adadi amma bata samunsa wanda hakan ba karamun sata yayi a
tashin hankali Ba,
Babu wanda ya faɗo mata illa ihsan wadda koda ta kira nata layin itama bata sameta ba dan
haka ta kosa kawai ta ganta a gida tasan koma menene zataji bakin ihsan ko hajja idan ta dan
bigi cikinta,
Wuraren karfe biyu na rana ta isa gida ,
Duk da bata jin dadi hakan bai hanata Nuna farin cikin ganin maminta ba ,faɗawa tayi jikinta
tana Mai ambatan mamina.
Rungumeta sosai Mami tayi tana Mai yin Yar karamar dariyar farin cikin saka deenah a idanunta
dan tabbas a kullum tunaninta da hankalinta da adduarta suna ga deenah ,
Ɗan raba jikinta tayi da nata tace Deenah ni nagama kamar makarantan tafi karbanki fiye da
gida ,
Kafun deenah tace wani abu mama kaltu ta shigo da sallama tana mai ambaton sunan deenah
wadda ta faɗa jikinta tana Mai rugumeta cike da farin ciki,
Hakika su ɗin ahalinta ne mafi soyuwa a gareta.
Bayan sun gama yan mirnarsu bandaki deenah ta faɗa dan watsa ruwa kana ta dauro alwala
tayi sallah sannan ta zauna dan cin favorite alalenta da mami ta yi mata ,tana ci tana ma su
hirar makaranta ciki kuwa harda mrs MAIKANO da irin kirkin da take mata dan a yanzu sun riga
sun saba ma, Kamar wasa tana kan ci taji zuciyarta na dan Tashi mata,a Tunaninta yunwar da ta kwaso ne
dan haka ta cigaba da tura alalen duk da a yanzu ya daina mata daɗi kuma ,dan gaba daya
kamshinsa ma hautsina mata ciki yake .
Kamar an tsakureta ta Tashi a guje ta faɗa bayi dan wani amai da taji zai ƙwace mata,
A tare Mami da mama kaltu suka kalli juna da mamakin abunda yasa deenah amai ɗin,
Fitowa tayi Bayan ta amayar da dukkan alalen da taci ta samu Guri gefen mami ta zauna tana
Mai yatsine fuska tace "wallahi Mami banda lapia,
Kallanta Mami tayi da kyau tace maike damunki haka harda su amai deenah?
"Wallahi Mami zazzabine dama fa nake yi sati daya kenan ya tafi ya dawo kamar me .
To Allah Kara sauki Bari na baki maganin zazzaɓi da na karba gun hajiya bansha Ba in yaso
idan har zuwa gobe jikin ba dadi sai muje kiga likita.
To kawai tace ma mamin ta mike tace mami Bari naje na gaida su hajja dan ban shiga Ba,
A hakan kuma bakijin dadi deenah ?
Kizo kiyi kwanciyanki ki huta inyaso anjima sai kije ,
Mama kaltu ta faɗa tana Mai binta da wani irin Kallan tuhuma .
Taje ɗin dai indai zata iya ,
Mami ta fada tana Mai dan murmusawa,
Kamar kuwa jira deenah take ta mike ta yi sashen hajja,
Da murna hajja da ake ma tausa a shahararren falon nata ta tarbi deenah inda ta umarci
sabuwar Mai mata tausan akan ta tashi ta tafi,
Budeme deenah hannu tayi tace maza deenah zo zo hajja taji duminki amma fa kibi a hankali
kar ki ma mijina asara,
Dariya deenah tasa ta isa gareta ta rungumeta tana Mai faɗin dama hajja Ai karashe ne .
Cike da murna da kewar juna suke hira da juna inda cikin hirar deenah ke dan bugan cikin hajja
akan binyamin wanda tace mata Ai itama rabon da taji daga garesa an kwana biyu amma ya
tabbatar masu aiki ne kawai yamasa yawa .
Tayi mamaki sosai a ranta sai ta fara tunanin dama da aikin da zaisa yayi sati biyu bai kirata ba
amma kuma ya sanar da gida kalau yake.
Wata zuciyar kuma sai ta taushe ta akan yana da babban daliline amma tasan zai kirata dan
haka sai ta masa uziri tana mai zuba ma kiransa idanu,
Nan take ji Wai ihsan Taje gun aunty dinsu a states wadda ta rike binyamin.
A haka deenah tacigaba da cin hutunta da tunaninsa fal ranta ga kuma damuwa da ta sama
kanta sannan uwa uba wannan kananun ciwan da take yi.
CHUCHUJAY..
KALUBALENAH
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA .
33.
Wai ni mamin deenah Baki kula da deenah kuwa gaba ki ɗaya ta chanza jikinta Yayi wani kyau
ya buɗe wanda ni kallo ɗaya nayi mata na fahimci akwai wata a kasa,sannan ga yan kananan
ciwokan nan da take ga amai ba fa laipa ba ,duk da nasan deenah yarinya ce mai hankali da
nutsuwa da kuma kamewa amma tabbas ɗan yau ba abun a shaidesa bane .
Da kallon Rashin fahimta Mami ta kalli mama kaltu inda a lokaci guda zuciyarta tayi mata wani
irin lugudan masu ,idan ta fahimci inda maganan mama kaltu ta dosa fa kenan deenah na
dauke da ciki kenan?
Da sauri takawar da wannan tunanin tana maiji aranta da ace ba kaltu ce ta faɗi maganan nan
ba da babu abunda zai hana tayi mata mutukar rashin mutunci na jifan deenah da take kokarin
yi da munanan alkaba'i amma a zahiri kuma sai ta danne tace"
Bana tunanin abunda kike tunani shine ,kai bama shi bane kawai dai larurane.
Dafata mama kaltu tayi tana Mai ɗan murmushinta irin na manya tace "na tabbata idan naga
mai ciki ina gane ta wannan wata baiwace da Allah yayi mun ,kana ban taba kuskure ba ,ba
kuma zan fara kan deenah ba ,
Zainaba deenah yaron ciki gareta dan jikinta da idanunta sun nuna ,idan kuma baki yarda ba ai
abunnan na Zamani yawa gareshi ayi gwaji dan shi abunan abun tsoro ne .
Shiru Mami tayi tana tunani tabbas itama ta kula da chanjin deenah amma ko da wasa tunanin
deenah nada ciki bai faɗo mata ba dan ta yarda da irin tarbiyyar da ta bama deenah tasan
bazata taba mata haka ba koda wasa.
Zan Kawo PT mamin deenah a gwada sai mu tabbatar amma dai tabbas bani tantama,
To kawai Mami ta iya cewa wanda kamar an jefo deenah din haka ta shigo cikin dakin,
Da kallo Mami ta bita daga sama har kasa wanda a lokacinne take kara ganin ƙibar da kuma
budewan da deenah din tayi, amma kam indai ciki deenah tayi ta kashe ta,
Zama deenah tazo tayi gefenta tace mamina hirar Mai kuke keda mama ne dan naga yarda
kuka ci serious haka akwai magana'
"Eh akwai deenah "
Mami tafada zuciyarta Cike da fargaba kana tace yaushe kika ga jininki na karshe?
Batareda wata damuwa ko tunanin wani abu ba ta ɗanyi shiru kana tace wannan watan ne na
biyu amma mami nafi tunanin circle ɗina ne zai chanza shi yasa last month banyi ba dan wani
lokacin naji ance yakanyi haka,
Wata kwalla ce ta ziraro ma Mami a gefen kuncin ta tace "deenah ina fatan ba abunda nake
tunani bane ,ina fatan kamar yarda kaltu ke hasashe ba ciki gare ki ba ,ko da yake ina zakiyi ciki
Bayan baki kula kowa,
CIKI?
Murya biyu ta faɗa a tare ,
Deenah da kuma ammi da ta zo gurin dan neman mama kaltu kan zata tantance mata sabbin
yan aikin da zata dauka a sashenta,
A tare Mami da mama kaltu suka juya dan kallanta,
Karasowa ciki tayi tace "biri yayi kama da mutum,ni dama nasan za'ayi haka tabbas ,Allah ya
rufamun sannan ya rufama binyamin asiri ,aikuwa wa'adin zamanki gidannan ina mai tabbatar
maku da yayi.
Fuu ta juya ta koma inda ta fito,
Wani irin kuka mami tasaka tana Mai faɗin ,shikenan deenah kin gama damu,
Duk irin tarbiyyar da na baki ?shekara nawa ina gina ta sannan a kullum nuna maki nake illar
alaka da maza wanda gashi kinyi kunnan uwar shegu da hakan kin jawo mun abun kunya ,
Cikin shege fa deenah.
Wani kukan ta sake fashe wa dashi inda mama kaltu ke faɗin"mamin deenah bafa a tabbatar ba
da gaske ki kwantar da hankalin ki ,insha Allahu ma mune mukayi kuskure .
Gashi kina kalla kaltu batace komai ba ,kina kallan idanunta kinsan bata da gaskiya Ai da tana
da gaskiya zata kare kanta,
Kasa deenah Tayi da kanta inda kirjinta keta dukan tara tara ga wani hawaye da taji yana mata
zarya wanda ita kanta baza tace Gashi na menene ba ,gaba daya harshenta yayi mata nauyi,
Tashi Mami tayi tana Mai hada hanya tabar dakin.
Kallan deenah mama kaltu tayi tace "deenah kiyi magana ,kina dai kallan halin da kika saka
mahaifiyarki a ciki ,ki koda karyata maganan damuke zargi ne ko maji dadi amma wannan
shirun naki yana nuna akwai damuwa fa ,cikin shegefa.
Ba tare da ta dago kanta ba tace "mama kaltu ni ban sani ban ko ciki ne dani amma kuma koda
shine ni cikina ba shege bane .
Da mamaki mama kaltu ta kalleta ,tace cikin ki ba shege bane?
Kenan a zahiri kinaso ki faɗa mun Tunanin mu na kinsan ɗa namiji ba kuskure bane.
Shiru deenah tayi batace komai ba,
Salati kawai mama kaltu take har tabar dakin tabar deenah wadda sai a lokacinne ta rusa wani
irin kuka Mai daci,
Tabbas idan cikine gareta ta kade dan mai cikin ma bata san halin da yake ciki ba sannan ta
kudira a ranta bazata taba ambatar sunansa ba koda za a kasheta indai bashine yazo ya fada
matsayinta garesa ba,tasani koda tace cikinsa ne babu wanda ma zai yarda da ita dama ace
ihsan na nan ne.
Ta dade tana kuka ita kadai a dakin kana ta Tashi ta shiga bayi ta dauro alwala dan yin sallar
la'asar.
Gaba ɗaya Mami ta fita hanyarta ,tana kalla mamin na haɗa kayanta da dare,
Ba tare da Mami ta kalleta ba tace ki tashi ki hada kayanki tunda kinyi sanadin da zai tona mana
asiri wanda nasan zamanmu gidan nan ya kare sannan inaso kisa a ranki zuwa safiya ki shirya
nemo uban shegen cikin da ke jikin ki idan ba haka ba zan baki mamaki.
Washe gari kamar yarda sukayi zato kuwa wuraren karfe tara na safe aka aiko kiransu a fadar
grand pa,
Tunda suka shiga kan Mami da deenah ke kasa karma ace na Mami dan ji take kamar kasar ta
tsage ta shige ciki ta huta,
Daga chan gefe suka rakuɓe musamman ganin yarda bacin rai ya bayayyana karara a fuskar
grandpa domin koda suka gaidasu hajja ce ta amsa amma shi kam Ko kala baice ba,
Mahaifiyar azad ce ta shigo daga karshe wadda itama maganar ta dake ta sosai sannan Gashi
a karkashinta suke dole tana ciki tsamo tsamo,
Likitan gidan ne Ya shigo wanda Bayan sun gaisa da grandpa yace masa "yauwa maza Dr
maina inaso amata pregnancy tests ne kamar yarda na maka bayani a waya sanann inasan
result din ASAP and na jini nake so bana fitsari ba sabida inasan idan na yanke hukunci ya
zamana ban shiga hakkin kowa Ba.
Babu musu Ya diba jinin Deenah wadda gaba daya zuciyarta ta kekashe dan ta riga da tasan
dole ne ma subar gidan ,dauke idanunta tayi lokacin da suka sauka cikin na ammi wadda ita ta
kawo karar a cewanta Deenah zata zama bad influence ga yaransu muddin ta cigaba da zama
gidan.
Ba a dauki Lokaci Mai yawaba Dr maina Ya dawo da result din test ,
Cike da hope hajja tace "ahap ni nasan duk maganar nan da kuke shirme ce deenah bata da
wani ciki,
Kai maina fada masu da bakinka.
Cike da sagewar gwiwa maina ya mikama grandpa result din yace the result is positive sir,
Deenah nada ciki na wata daya da sati uku,
Kasa Mami tayi da kanta tana Mai jin hawaye suna bin kuncinta daya bayan daya,
Ahap dama Ai na faɗa, ni fa tun farkon haduwa ta da yarinyarnan nasan karuwa ce Allah ne
yasa yaranmu sunfi karfinta ,kana kallan idanunta kaga jarababbiya.
Wani kukan Mami ta sake fashewa da shi jin kalmar da ammi ke jifan deenah da su.
Im very disappointed in you deenah"
Hajja ta fada tana Mai matsar kwalla ,
Hajiya fattu kuwa neman abun fada tayi ta rasa ,amma a ranta kuwa ji take babu dadi sosai,
Gyaran murya grandpa yayi Ya kalla Dr maina yace zaka iya tafiya Dr ,
Babu musu Dr Ya wuce inda ya rage daga grandpa sai su mamin da hajiya fattu da ammi.
A gaskiya kin mutukar bani mamaki Deenah, na dauka ke din yarinya ce mai nutsuwa ,koda
kuwa wani ya faɗa mun abu maka mancin wannan akanki banni yarda,
Amma wani hanzari ba gudu Ba kamar yarda na faɗa da farko ina san yanke hukunci ne ban
zalinci kowa Ba,
Kinsan wani Lokacin mata kan facing rape case so i will ask you this once sannan bana san kiyi
mun karya ,
Ki faɗa mun gaskiya were you raped?
Kasa deenah tayi da kanta kafun tace "Grandpa im sorry dana baka bad impression akaina
sannan i was not raped cikina dan halak ne ba shege ba.
Wani irin tsaki Ammi tasa tace "ban tuna lokacin da mukaji labarin aurenki ba ,ko kuwa
mitsiyatan danginki ne suka Maki aure daga kyauyenku mijin ke bin dare ?
Wazaki raina ma wayau a nan Ko kin ga munyi kama da jahilai?
Dakata ammin BINYAMIN ,this is getting somewhere Bari muji ta bakinta,
Kikace cikinki na halak ne Mai hakan ke nufi, sannan ya akayi yazama halali?
Grandpa ya tambaya .
Cikin kuka tace "ka yafe mun grandpa bazan iya fadan komai ba amma cikina ba shege bane,
Tsam hajja ta Tashi dan barin gurin dan ta lura deenah nasan wasa da hankalin kowa ne, ina
mutum ya taba samun ciki sama taka,
Kallan da Deenah taga hajja tamata ba karamun tabata yayi ba saboda ya nuna yarda Deenah
tayi breaking mata zuciyarta.