Showing 21001 words to 24000 words out of 65850 words
Chapter 8 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf
tace komai ba,
Tafiya Mai ɗan nisa sukayi a motan wanda babu wanda yace da kowa komai ,shi ya maida
hankalinsa kan tuki ita kuma tana Mai kallan window .
wani garden Mai kyau taga sun shiga,
Parking yayi a gefe ya kalleta yace oya bismillah,babu musu ta buɗe ta fita tana mai kallan
kyakyawar halittar nature da Allah yayi a gun,
Jagora yayi Mata gurin wani tsauni ,
Tsaye tayi ganin ya fara hawa ,
Juyowa yayi ya kalleta yace tsoro kikeji hala,
Come on ba abunda zai sameki im here with you,hannunsa ya miko mata babu musu ta kama
cos at that very moment haka nan ta tsinci kanta da yarda dashi,
Sama chan suka hau ,
Wow ta furta lokacin da ta hangi ruwan dake kasan tsaunin wanda yake tafiya gwanin sha'awa,
Zama yayi itama tayi yarda yayi ɗin tana Mai jin iskar gurin Mai daɗin gaske tana ratsa ta ,
Dutse karami ya dauka ya jefa cikin ruwa a lokaci ɗaya kuma yana satar kallanta yana ganin
yarda take kokarin danne bacin ran da ya dauko ta dashi .
"I use to come here duk lokacin da nake da damuwa sannan ni'imar dake Gurin takan san naji
kaina all cleared up so this is my secret place and yes nima Ina samun hard time saboda I'm
human kamar kowa ,maybe ma fiye da naki so let go of all your worries and idan kina san
magana akai i will listen daga nan har lokacin da zuciyarki zata huce i will do you that.
Karamun dutse ta dauka ta cilla cikin ruwan kana tace da kara"rich people stink and I hate them
,they are all sick,
I'm not going back to that God forsaken school again.
Kana ta kara sa wani ihun wanda ruwan ke amsawa,
Shiru tayi na wani lokacin kafun kuma tasa kuka.
Gyaran murya yayi lokacin da tayi Mai'isanta yace"deenah life without challenges is not a
life,dole a rayuwa ka samu kalubale masu dama wanda yana cikin jarabawarka ce ,a rayuwa
kuma sai kayi hakuri ne zaka ci riba sannan yarda kike da bad picture na Masu kuɗi nima inada
shi akan talaka cos ni a da ko hanyar da talaka ya taka bana takawa saboda kiyayya saboda i
was stabbed by one ,we are not here to talk about me but you so Ina so kiyi hakuri ki kara
jurewa cos Allahn da ya kawoki orchid da rayuwar mutanen cikinta dama garin nan baki ɗaya
shi ya san dalili sannan Ina da yakini babu sharri a cikinsa I blv you'll achieve abunda kika saka
gaba indai a ranki kin yarda zaki iya .
Cikin wani sabon kukan tace "yaya bilya wannan abun is beyond hakurina ,although nasan bani
bace but no one would blv bani bace saboda fuska nane a gurin ,wane irin tsana ne da zaisa
wai ni ayi Photoshop na video of me masturbating in the school toilet and video din yana
circulating cikin makaranta ,how do I face the world? We are talking about my nudity sannan babu Mai yarda wai bani bace cos my face was there
and same toilet din same day ɗin that same toilet I was there but wallahi bani bace ba haba this
is to much and a big reason for one to commit suicide God forbid .
Dafe bakinsa yayi jin abunda ta faɗa ,shi kansa da yake namiji baya tunanin Iya taking wannan
kalubalen da deenah ke fuskanta Yayi yawa wai ace yara da ko 18 Wasunsu basu gama cika ba
sun iya iskanci kusufa kusufa
Shiru yayi yana sauraran kukan ta dayake taba zuciyarsa haka nan ,
Har tayi Mai isanta baice mata komai ba saida tayi shiru kana ya kalleta yace ,how are you
feeling?
"Better than before "
"That's good yanzu it's to 11,
Let's go back to that school and koda zamu Kai darene i will make sure that babu Mai copy na
wannan vid ɗin a wayansa and trust me indai na gane Mai laipin sai ya bar orchid this I promise
you.
and mark you,binyamin not bilya please.
CHUCHUJAY.
KALUBALENAH
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
15
Koda suka koma makaranta lokaci daya yasa ayi masa assembly wanda dukkan makarantar ta
hallarta dan ko babu komai suna shakkar sabon basket ball coach din nasu musamman idan
suna tuna dukkan da Yayima widad,
Warning Mai girma ya bawa makarantar baki daya wanda yawancin su suke clueless akan
abunda yake magana tunda vid din a iya set dinsu deenah ya tsaya ,
Sallamar kowa yayi kana ya umarci duk wani Mai waya yazo ya aje,
Babu musu kowannen su yayi hakan inda in yabi layi layi kowa ya dau wayarsa ya goge ciki
kuwa harda su widad da take ta sassama da idanu wai ita gwana,
Haka ya gama da basu warning Mai kyau akan duk wanda yake behind wannan case ɗin ya
tabbata ya fara shirin barin makarantan,.
Ta ɗaya bangaren principal ɗin ba karamun haushin binyamin yake ji ba dan gani yake gaba
gaba za'ace an bama binyamin matsayinsa tunda sune masu abun.
Tsaye widad tayi bayan binyamin ya sallamesu tana mai zagaye cike da fargaba tana jiran
ukasha,
Kamar an jefosa yazo gurin yana wani fito,
Dukansa tayi a kirji tace" just know that I wont get caught,I mean I refuse to be caught Kai
kasan brother ɗin azad ɗinnan bashi da mutunchi muddin ya gane we are involve mun shiga
uku i don't wanna mess with him again,not ever,
Jawota yayi ya haɗeta da jikinsa yace "come on baby girl ukasha ne fa hala kin manta ,
We would never be caught and koda an kama mu there is always plan b and we will use it so
chill and make out with me ,
Hankaɗe sa tayi ta nuna kansa da yatsanta tace "you must be sick somewhere here ,so karma
ka taɓa tunanin abu kamar haka zai faru tsakanina da Kai im off limit and we are only partners
in crime so fuck up.
Tana Kai karshen zancenta ta wucesa ta bar gurin inda shi kuma ya bita da kallo yana Mai sidar
leɓe.
************
Rasa bakin godia deenah tayi ga binyamin cos yayi Mata babban alfarma wadda har ta mutu
bazata manta da ita ba kuma ita tasan babu abunda zata masa ta biya sa ,
Tare suka tafi gida a motansa bayan ya gama abunda yake,
Babu wanda yace da kowa komai har suka isa gida ,
Kallansa tayi a yayin da yayi parking motansa idanunta nasan kawo ƙwalla tace "nagode maka
,bansan da wane baki zan iya gode maka ba bisa abunda kayi mun ,nasan bazan iya biyanka
ba amma bazan gaji ba wajen maka addua a agurin Allah Ya biya maka dukkan bukkatunka na
alheri ,wanda kuma basu da alheri Allah Ya musanya maka da abunda yafi alheri . Tana Kai karshe ta bude motan ta fice wanda Yayi daidai fitowar ammin binyamin ,
Gaisheta deenah tayi ta raɓa ta gefe zata wuce Dan tasan ko ta tsaya ɗin ba amsata zatayi ba ,
Jawota ammi tayi baya tana mai faɗin "ke Dan ubanki bazaki rabu mun da yaro ba ko ?
Shegiya gayyar tsiya to wallahi ke da kazamiyar uwarki Ku kiyayeni Kar na xamar muku
damuwa,
Da sauri binyamin Ya zagayo Ya rike hannun amminsa yana Mai raba ta da jikin deenah kana
yace "deenah oya wuce ,
Babu musu ta wuce ta shige cikin gidan ,
Wani mugun kallo ammi ta basa tace "binyamin wallahi kaji na rantse maka idan baka fita
hanyar yar aikin nan ba zan ci maka sosai da sosai bana San iya shege ,
Bata jira Ya kuma cewa komai ba ta figi hannunta ta nufi motanta ranta a bace.
Kallan hanyan da deenah tabi yayi yana Mai jin Wani iri a tattare da ita karma ace adduan da
tayi masa wadda ta tabasa sosai,
Kada kansa yayi yana Mai murmushi Ya nufi nasu bangaren yana Mai Kaɗa keys ɗinsa .
Walwala deenah ta ɗinga yi gudun Kar maminta ta gane tana da damuwa wanda sarai mamin
nata ta gane Amma da ta fahimci deena bata san tasan tana da damuwa yasa ta basar tana
mai Dan tsoma bakinta cikin hirar da suke da mama kaltu,
Wuraren karfe huɗu ta shirya dan zuwa daukar karatun qura'ani ,
Tana jin muryar azad yana kiran sunanta ta masa banza Dan bata san magana dashi ko kaɗan ,
Saurinsa Ya kara Ya riko gefen hijab dinta ,tsayawa tayi bata juyoba ,
Cikin wani irin yanayi na dana Sani Ya zagayo ,marairaice idanu yayi kamar zai kuka"deenah
please I'm sorry ,nasan abunda nayi bai dace ba i should have been the first person to stand by
you amma sai Ya zama nine mutum na farko da Ya fara questioning naki Dan Allah kimun
afuwa i was just angry and i couldn't help it.
Kallansa tayi cikin daurewa fuska tace "kagama ko najira da Saura?
Nagama"yabata amsa yana Mai sake jin ba daɗin yarda yanayinta Ya kasance ,fisgar gefen
hijab ɗinta tayi ta wucesa without wani tunani ko yunkuri na juyowa .
Duk yarda azad yaso deenah ta sauraresa abun Ya ci tura dole Ya hakura Ya bata space,
Washe gari sabs na zauwa makaranta kai tsaye office din binyamin ta nufa Dan ta gane culprit
ɗin kan video ɗin ,zaune ta tarar dashi yana duba wasu files ,
Umarni yayi mata data shigo,
Narrating masa investigation ɗin datayi akan real person nakan vid ɗin kafun ta bashi tace "real
culprit ɗin dake vid ɗin sunanta sammy bello and a class ɗinmu take and I'm
Very sure ba ita kadai bace akwai wani behind it which I'm sure idan akayi interrogating nata
zata fito da ko su wane ne,
Real video ɗin yana cikin flash ɗin.
Daukan flash ɗin yayi ya juya kana yace "kowa yana bukatan friend irinki,you're indeed a good
frnd and i really do admire the bond between you too,you can go and the school will take a big
step,
Godia tayi masa ta fita tana murna wanda Kai tsaye ta nufi library wanda ta tabbatar nan zataga
deenah,
Ille kuwa tana bi usual place na zaman deenah ta ganta zaune tana rubutu ,
Dafa ta tayi kafun ta zauna"guess what girl .
Kallanta deenah tayi tace"kinsan I'm not good at guessing just tell me,
Ganin yanayin fuskarta yasa tayi cutting to the chase tace "sammy was the girl behind your real
video kafun ayi editing a saka ki ,
Dan zabura tayi tace "i can't remember how i offend sammy ,ba girl dinnan ta class dinku ba?
Beside we don't talk so why would she do that to me ,
"I don't know deenah but I'm very sure zata faɗa soon cos the flash is with mr binyamin,
Deena na tsaka da mamakin abun wayanta dake silent Ya fara vib ,daga wa tayi ,
Come to my office shine kawai abunda yace Ya kashe wayan,
Babu musu ta tashi tana Mai cewa sabs tazo suje,
Zaune suka tarar da sammy tanata faman kuka,
Umarani Ya musu da su zauna kafun ya kalli sammy dake kan kuka yace oya Ina sauraranki
Mai yasa kikayi framing deenah and trust me you wont like me idan kika min karya,
Cikin sheshekan kuka tace"i was intimidated sir"
Yar dariya deenah tayi daga gefe tace that video doesn't shows that you were intimidated rather
you were enjoying every bit so fuck up and start talking ,
You heard her "binyamin ya kara yana Mai juya pen a hannunsa ,
Kuka ta Saka tana Mai faɗin "sir it was ukasha ,shi ya biyani kuɗi nayi video ɗin sabida ina
facing financial problem but wallah sir bansan zasu cire fuska na bane su Saka na deenah ,i
promise I'm not lying ,wallahi i just did abunda nayi sabida sunce zasu bani 50 dollars and i
needed the money .
Dan shiru binyamin yayi yana San Ya tabbatar da gaskiyarta ,ganin da gaske ba karya din take
ba yasa YaCe ta tashi ta tafi zai nemeta,
Wasa wasa magana ta zama babban case wanda karshen ta sai da akayi expelling ukasha
bayan zaman da akayi akansu inda sammy kuma aka bata last warning.
Lokacin da maganan korar ukasha ta karade makarantan ba karamun tsorata widad tayi ba Dan
tagama sadakar da cewa ukasha zai faɗi sunanta amma ga mamakinta sai taji sunanta bai fito
ba,tana tafe Dan zuwa motanta da driver yazo daukanta taji an kira sunanta ,juyawa tayi Dan
ganin Mai kirannata , Dan murmushi sabs tayi ganin yarda ta haɗe girar Sama da ta kasa,
Dafa kafadarta tayi tace "widdy kenan i will vouch For this "wallahi kinada sa hannun a al'amarin
nan,i know you best widdy ,halinki bashi da kyau ko kaɗan halin banzanki yana da yawa amma
kisani lies always end and I'm very sure wata rana zakizo kina danasani na duk wani abu da
kike aikatawa just know that you're ruining your future .
Bata jira amsan da widad zata Bata ba tabar gurin,
Cije lebe widad tayi tana Mai jin wani irin frustration Yana taso mata,
"Don't worry about what your sister said ,Kar kiji kin wani damu ,school is not my own cup of tea
amma iyayena sun dage sai nayi ,ni a rayuwa bani da buri da ya wuce na zama mawaki and
kinga wannan is a golden opportunity ,but inaso ki sani widad ni ukasha bana aikin banza you'll
have to pay the price na rufa mini asiri da nayi and that mean i want something in return which
is a sex with you*
A mutukar hargitse ta hankade sa gudun Kar wani yaji sa kana tace"you will always be a jerk"
useless boy go and have sex with your mama rather,
I hate you"
Dariya yayi lokacin da ta karasa gun motansu ta shige "
"We will meet again widdy i promise.
BARKANKU DA SALLAH FATAN KOWA YAYI SALLAH LAPIA?
ALLAH YA KARBI IBADUNMU AMEEN.
CHUCHUJAY.
KALUBALENAH.
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
16.
Kamar anyi ruwa an dauke haka maganar video ɗin deenah ta dauke a makarantar dip Dan
kowa ya shiga taitayinsa tunda aka kora ukasha ,
Rumors suke da kus kus kan biyamin yana having affair da deenah ne wanda kowa yake tsoran
aji a bakinsa amma ko wannen su ya yarda deenah tanada wata boyayyiyar alaka dashi,
Haka rayuwar Deena ta cigaba da gudana cikin kwanciyan hankali dan ta gama bawa binyamin
matsayin shield ɗinta ,
Ko ina hankalinta ya kwanta ,a gidan, matsalar ammi kawai take fuskanta wadda karara take
nuna bata santa musamman idan tana ganin yanayin yarda shakuwa ke wanzuwa tsakaninta da
ɗanta,
Da kyar da sa bakin sabreena ta yafewa azad wanda yayi realizing mistake ɗinsa So no hard
feelings attached .
Wasa wasa wata irin shakuwace ke wanzuwa tsakanin deenah da binyamin wanda yake balain
ciwa Amminsa da ke lura da hakan tuwo a kwarya,
Kamar kullum yauma tana zaune tana aikin gyarawa maminta ƙumba wayanta ya dauki ruri,
Dagawa tayi tana Mai kallan idanun maminta kafun tace "okay ina zuwa,
Kallanta tayi tace "Mami yaya bilya ne yake kirana.
Kiyi masa me?
Wallahi Mami bansani ba yace nazo ne dai,
Dan shiru mamin tayi kafun tace"ki dai Sani mituncinki ya fi komai kuma shine darajarki kuma
shine ainayinki dan haka ki kiyayesa sannan inasan kar ki manta matsayinki cikin gidan
nan,mudin ma'aikatane da muke aiki a biyamu dan haka ki kula,
Dan sakalo tayi kana ta mike lokacin da mamin tace tashi kije,
Babu musu ta mike ta ɗauko hijab dinta tasaka ta fita dan amsa kiran binyamin wanda take jin
kamar tayi tsuntsuwa taganta gabansa,
"Yan Mata sai ina haka ,
Juyowa tayi tana Mai kallan azad wanda yake sanye da jersey da basket ball a hannunsa.
Ya bilya ke kirana wassup"?
Dan murmushin yaƙe yayi yace baza dai ki daina kiransa bilya ba kenan and whats the
occasion ni nakasa gane wannan sabuwar alaƙa taki da brother fa,
"Come on its nothing fa kai kanada wani irin negative tunanin see you later,
Tana kai karshen zancenta ta wucesa ,
Jiyayi wani irin tukuki ya tsaya masa a wuya dan har ga Allah bayasan alakar deenah da
yayansa ,bin bayanta yayi kasan cewar babban field ɗin da suke basket ball yana harabar gurin
da zata wanda yake haɗe da garden,
Zaune ta tarar dashi yana danne danne cikin wayansa,sallama tayi masa ta samu chan gefe
dashi ta zauna ,"ina wuni tafaɗa tana mai sunkuyar da kanta .
Licking lips dinsa yayi slightly wanda Ya zama sabonsa Ya amsata yana Mai murmushi kafun
yace "sannu da zuwa, i was bored and ina bukatan hira so i call on you cos these days dake
kadai nake hira naji daɗi,
Yanayin yarda suke hirar da nishaɗi ba karamin kwazira azad dake chan yana jefa kwallo cikin
raga yayi ba ,jiyake kamar yaje ya rufe dan uwan nasa da duka cos shi ya gama tabbatar wa da
kansa deenah matarsa ce ko ana muzuru ana shawo saboda ya gama yarda da amincewa
zuciyarsa soyayyarta duk da kuwa tazarar dake tsakaninsu ba Mai yawa bace amma ya yarda
da cewa shi din zai iya aureta tunda shi namiji baya kadan,
Yana wannan fusatar yaga tashinsu agurin suna masu cigaba da hira cikin wani irin nishadi
wanda su kansu basu san ya akayi ya ke ziyartasu ba musamman idan suna tare da juna.
Kakarewa deenah tayi lokacin da suka bar ta wuraren da azad yake sakamakon abunda
binyamin ya faɗa wanda yayi mutukar razanata wato"ZAKI IYA AURENA DEENAH?
Kwarewa tayi da yawonta lokaci guda kuma ta saita kanta kafun tace"yaya bilya aure kuma?
Yar Dariya yayi ganin yarda duk tawani rikice kafun yace oya matsoraciya wasa nake maki ,Kalli
yarda duk kika bi kika wani firgice