Showing 33001 words to 36000 words out of 65850 words

Chapter 12 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf

Advertisement

02 Aug 2025

2671

doesn't matter who
you love ,love to your heart contain amma ki sani baki da miji da ya wuce azad"

Gyaran muryan da akayi ne ya hana Deenah maganan da take niyan yi,
Mubarak ne ya shigo ya buɗe fridge ya dauko sauran ruwan da azad ya rage ya shanye kafun
ya kalli deenah yace "deenah i want coffee "

"The fuck?
Kana hauka ne ?
Azad ya hayayyako masa ,

Taresa tayi ta hanyar faɗin"azad aiki nane don't get In between my work idan ni banyi ba Mami
zatayi and that's my reality,
Kan coffee machine ta nufa Dan haɗa ma mubarak coffee wanda ya fita already a kitchen ɗin,
Tana gamawa ta fice ta bar azad zaune wanda tana fita ya biyo bayanta yana faɗin "dan ubansa
ba zai iya zuwa ya haɗa da kansa ba ,
This should be the last time da zaka sake mata magana a haka ,idan ba haka ba wallahi sai na
ci maka mutunci
"What a rude boy".

Fuu ya wuce Ya bar gurin ,kallan mubarak tayi tace yi hakuri mubarak kar ka biyesa,
Sipping coffee ɗin mubarak yayi yace "kiyi hakuri deenah ,i don't mean to sound rude ,
Its okay kaji Kar ka damu so kana bukatan Wani abu?

Kaɗa kai yayi alamun a'a .
Dan haka tabar sashen ta tafi nasu Dan ta haɗa masu abun kari,

Koda taje ta tarar da Mami da mama kaltu zaune suna shan tea da soyayyan doya ,
Zama tayi tace la shine baku jirani ba"

Yar dariya mama kaltu tayi tace to "tsofaffi ina zasu Wani iya jiran ki mukam dai mun riga ki ga
naki chan,

Zama tayi ta jawo kulan da nata ke ciki kana ta hada tea,

Kasuwa Mami da mama kaltu suka tafi inda hakan yayi mata daɗi sosai,
Suna fita ta shiga tayi wanka ta danyi Yar karamar kwalliya ta dauko doguwar rigarta ta atampa
ta saka kana ta dauko jilbab ɗinta sky blue ta saka wanda sosai ya dauki fatar ta ,

Dan kamshi take mai sanyi wanda sai ka matso daf da ita zaka jishi,

Kiransa tayi a waya amma yaki dauka Dan dama saban sa kenan zai saka mata kati amma idan
ta kira bazai dauka ba ,

Yana kira tace masa ina zan ganka "
Regular place Dee Dan Allah kiyi sauri Dan ni already ina Gurin,
Murmushi tayi kamar yana ganinta kana tace "ka kwantar da hankalinka sarki na gani nan
zuwa,
Saurin kashe wayan tayi Dan abunda tace wanda ya barsa cikin jin dadi.

Zaune ta tarar dashi yana danne danne a wayansa,
Dayake ta bayansa ta biyo baiji zuwanta ba sai magananta inda take faɗin"Mai baby na yake ne
haka ya nutsu,
Jiyayi kamar Ya jawota ya rungumeta jikinsa ko zai ji sassaucin kaunarta wadda ke neman
zautashi,
Kashe Wayan yayi yace "babynki yana tunanin ki ne shiyasa ya nutsu haka,

Zama tayi a kujeran dake kallansa,
Ta Gaidasa cikin ladabi wanda Yana daya daga cikin abunda yake kara kwadaita masa alaqarsa
da Deenah,
Komai da ya danganceta Mai kyau da tsari ne.

Deenah a bari ya huce shi ke Kawo rabon wani ,ni kuma rabon nan bana so ya zama na wani
,rabon ki nawa ne,deenah result dinku yana nan fitowa and im positive zayyi kyau ,
And university zaki shiga after that ,so please deenah ina san na mallake ki kafun nan are you
ready?

Kasa tayi da kanta "
Licking lips ɗinsa yayi yace deenah "nasan kina jin tsoro but amincewar ki kawai nake nema ni
kuma i will fight for us ,Zan ma ammina magana sannan nayi ma Mami which i blv komai zai zo

da sauki,

Na amince "tafaɗa tana Mai sunar da kai cike da kunya,
Ji yayi kamar an sashi a aljanna ,
"Yes "yafaɗa "i love you so much deenah and na maki alkawarin i will be there for you in health
or in sickness ,in wealth and poorness .
Bazaki taɓa dana sanin zabina ba .

Kallansa tayi a karo na farko tace"
Ni marainiyace sannan kamar yarda na baka labari kwanaki yanzu bani da kowa sai mamina
Dan Allah kar kasa nayi abunda zan kuka da kaina,
Ni dai na yarda da kai fiye da kaina.

Dadi yaji da yaji ta bakinta "
Kar ki damu deenah bilya will always be there,
Kasa tayi da kai tana dariya jin bilyan da yace dan haka ita ma cikin sigar tsokana tace
,shikenan yaya bilyana ɗan mai karfi.

CHUCHUJAY✍

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

23.

Kai tsaye sashen amminsa ya shiga bayan rabuwarsa da deenah,
A zaune ya tarar da ita tana waya da wata ƙawarta ,
Zama yayi dan jira ta gama ,yana kula da irin kallan da take masa na mamaki ɗan tunda abun
faɗan ta da deenah ya chanza sosai a gidan ,

Hanging wayan tayi ta kallesa ,
Gaida ta yayi cikin ladabin sa na ko yaushe ,

Amsawa tayi kana tace "hope I'm safe '.
Yes "ya bata amsa kafun yace "ammi na yarda ni ɗanki ne sannan na yarda kina da dukkan
right a kaina amma at times i need to choose what i want sannan nasan ke me san abunda
nake so ne so please ammi yau ma nazo maki nan ne akan abun da nake so which is Deenah".
Ammi ina san deenah ,ina mutukar santa har ila adadin da nake ji idan har na rasata zan rasa
rayuwa ta ,tsugunnu yayi gabanta yana mai rike hannunta yace "ammi i want this girl in my life
dan Allah ammi ki yarda na aureta and ina mai tabbatar maki zaki sota fiye da yarda kike
tunanin ,na yarda da hakan sabida nasan wacece deenah , Dan Allah ammi kar kice mun a'a saboda ni yanzu amincewar ki kawai Nake nema kafun na

sanar ma Abba ,

Kallansa tayi da kyau kana tace kana san deenah ?
Daga mata kai yayi alamu Eh"

Itama tana sanka ne?

Dan murmushi yayi cikin tuna yanayin tata soyayyar ta kunya kana Yace "fiye da tunanin ki
ammi ,im positive idan aka raba deenah dani halin da zan shiga zata shige sa ,

Mikewa tayi tace aikuwa zata mutu saboda ban haifeka ba domin na mika ma ɗiyar masu
aiki,mitsiyata wadanda ke cin arziki kasan mu ,wallahi babu wanda ya isa ,
Kuma inaso ka Sani muddin abbanka Ko kakanninka sukaji zancen nan na kana wani San aure
ta kasa aranka saina tsine maka .

A'ah Ammi "cewan ihsan dake shigowa jin hayaniyan ammin,

Karasa shigowa tayi tace"haba ammi mana abun Ai bai kai nan ba dan Allah,sannan menene
aibun deenah ne nikan being a maid is not a crime fa and yaranki ya nuna yana santa why not
give them your blessings,

Bazan bayarba "tafaɗa a hasale ,bazan bayar ba dan ubanki ,bari kiji kema duk ranar da kika
kawo mun ɗan matsiyata to wallahi haka ne zai faru dake and itama shegiyar yarinyar bari naje
na sameta na cimata ita da uwarta kila ta sa ta cire karyar san da take ikirarin tana maka ,

Riko hannunta yayi yana hawaye wanda ya basu mamaki yace "ammi kiyi hakuri kar kije ki cima
su deenah mutunci,
Badai maganan ne baki san ji ba naji bazan sake maki ba sannan su abba ma bazasu ji ba .

Tashi ya fice a sashen nata yana Mai ganin wani dumm,
ɗakinsa Ya wuce kai tsaye yaɗan kwanta yana Mai jin damuwa fal ransa
Rumtse idanunsa yayi yana Mai jin kansa na ɗan sara masa ,
Ihsan Che ta shigo kasa cewar bai ma kofar key ba,
Zama tayi a gefensa tace brother kayi hakuri da maganan ammi dan Allah kar kaje ka sama
kanka damuwa, buɗe idanunsa yayi ya kalleta Yace sis i love deenah wallahi tsakani da
Allah,bansan mai nene damuwan ammi ba ,i want this girl and this girl want me so menene
aibun haka? I choose this girl to spend the rest of my life with" so who's problem is that?

Mai yasa ammi take san kasheni da raina ?
Kwallan da baisan ta ina ma yake fito masa bane yayi tsalle zuwa kan kuncinsa wanda hakan
ya mutukar tsorata ihsan and ta yarda da cewa tabbas binyamin yana san deenah.

Lallashinsa tayi sosai kafun ta bar dakin.

Washe gari bai kasa a gwiwa ba ya nufi Gurin Mami dan neman tata yardar amma ga
maminkinsa nata fushin ma yafi na ammi dan ita tunaninta kawai zai yaudarar mata yarinyane,
Tunda ya bar gidan a ranar yake walagi a titi yana Mai tuno hawayen da ya gani a kuncin
deenah lokacin da mami ke faɗin bata yarda ba ,

Wayansa ya ciro Ya kira best friends ɗinsa da tun yarinta suka Tashi haka zalika har girmansu a
states ,
Number sa na states yayi ta gwada wa bai shiga ba so sai ya danna na sister ɗinsa aina dan
san jin ko ya sake layine dan tunda ya baro states they hardly get in touch wanda yafi maida sa 
laipinsa,

Ringing ɗaya aina ta dauka jikinta na rawa dan tana balain san binyamin wanda yake nuna
mata Ko in kula ,
Da wata irin murya ta ce hello cike da rawar kai"

Ammar fa bana samun layinsa na states  "
Ya tambayeta briefly dan Ya washi rawar kan aina musamman idan yana Guri ,

Cikin wata siga tace la brother meen Ai yaya ammar yau kwanan sa uku a nigeria yanzun nan
ma ya tashi a falo muna kallo tare ,brother ihsan fa?

Kashe Wayan yayi ba tareda ya bata amsan tambayar da tayi masa ba dan bashine abunda
yasa shi kiranta ba ,

Kallan mamman su tayi bayan ta kashe wayan tace mamma guess who called me ,
Kallanta hamshakiyar mahaifiyarta tayi tace i guess ba sai Nayi guessing ba cos naji kin ambaci
sunan binyamin ,
Binyamin ?
Ammar da Ya shigo ya faɗa yana Mai karasowa da saurinsa yace hope baki ce masa ina naija
ba cos trust me yana chan yana cika ban kirasa ba da Zan dawo cos that's the first thing i
always do,
Dan taɓe baki aina tayi tace " to brother kasani dai i cant control my self gabansa ni kam na riga
na faɗa masa ,
Cije lebensa na kasa yayi yace shit "
Aina oh no,
Mamma i have to go ,see you later bye ,
Yana kai karshen zancen sa ya fita yana Mai dialing layin binyamin ɗin wanda take ta ringing
yaki dauka ,
Yasan halin abokin nasa Da fushi indai akan alakarsu ne ,

Tashi aina tayi tana Mai faɗin mamma bari na bishi dan dama na daɗe rabo na da ihsan,

Kallanta mamman tayi tace a dai ja aji aina yanzu kina zuwa yasan danshi kika zo,
Dan zama tayi tace Allah Ko mamma?

Ehen ki bari zamuje zuwa na musamman zan kira mahaifiyar tasu nasan she would be more
than glad ,
Aje wayanta tayi tace wallahi mamma har fa nafara hakura da shi kiran nan nawa da yayi ya
dawo mun da sabon tsumi,
Dariya mahaifiyar tasu tayi tace ,kar ki damu ɗiyata a wannan karan zaki samesa indai kika
kwantar da hankalinki kikayi duk yarda nace .

Asalinsu ,
Ammar Buhari asalin yan garin bauchi ne wanda aka haifesu a nan cikin garin abuja ,
Iyayensa dana binyamin abokai ne wanda saboda iyayan ne yayansu suka kulla tasu aminan
takar ,
A da ihsan bata da kawar da ta wuce aina amma daga baya gabanin girma sai suka fara baya
baya da juna musamman da ihsan ta kula zubin tarbiyar aina ba irin tata bace sannan ga aina
yarinyace wadda bata san shawara ,
Mahaifiyarsu hajia Balaraba shuwa arab ce wadda ita kaɗai take a wurin mahaifinsu Alhaji
Buhari farouk ,
Yaransu biyu a duniya ammar da aina ,
Basu da tsarin tara iyali da yawa wanda hakan ya faro ne daga ita maihaifiyar su ammar ,
Hajiya balaraba irin iyayen nan ne da idan yayansu nasan abu she will go to any extent dan ta
sama musu farin cikinsu ,
A lokacin da aina ta nuna tana San binyamin taso tayi mata fighting akan abun amma daga
baya da taga aina ta zama very busy da career ɗinta na modeling yasa ita ma ta watsar da
batun ,amma a yau kuwa ta kula soyayyar binyamin ta dawo sabuwa a cikin xuciyar ainanta ,
Kuma ta sa aranta zata sama mata shi a duk yarda take san sa.

.....kamar yarda ammar yayi expecting kuwa binyamin fushi yayi dashi dan yana jin wai ammar
na naija Ya juya kan motarsa ya koma gida ,
Dakinsa ya wuce kai tsaye ya kwanta dan Ko cin abinci baya so in fact yunwar ma shi baya ji,
Yana kallan kiran deenah na ta shigo masa waya yaki ɗagawa dan bashi da kwarin gwiwar
mata magana a yanzu dan shi kansa bai san ta ina zai fara ba,

Karatun Quran yasa Ko zai ji dan sassauci ,
Aikuwa a hankali ya fara jin zuciyarsa da hankalin sa sun fara kwanciya,
Cikin mintun kalilan kuwa bacci barawo yayi awan Gaba dashi.

Yana tsaka da bacci wanda ya fara masa nauyi yaji kamar mutum na kansa yana kallansa,
Sharewa yayi ya kara gyara kwanciyarsa Ya cigaba da baccin sa ,

1 hour later .

Da salati a bakinsa ya farka duba da sallar magreeb da yaji ana kira ga kuma yunwa da ke
nanukar yayan cikinsa,
"Wayyo Allah Ya faɗa a razane ganin mutum zaune a kan couch ɗinsa yana video game,
Tsaki yayi da ya gane ammar ne yace "kai fa ɗan iskane ,
Wama ya baka izinin shigo mun ɗaki nane sannan zaka zo ka zauna mun kasan yarda wannan
jar fatar taka keda tsoratar da mutum sannan ace mutum ya Tashi daga bacci mai tsayi yayi
arba da ita .

Yar dariya ammar yayi dan ya riga ya saba da irin wannan iskancin da binyamin ke masa akan
haskensa wanda shida aina duk na mahaifiyarsu suka ɗauko,
Maido da kallansa yayi garesa yace at least da kaɗan na fika,

A"haba malam f*ck u*.
Kai kasan haskena bai yawa haka ba, yanzu bama wannan ba uban menene ya kawoka i
thought kai yanzu baka da mutunci tunda wai har kayi kwana uku a garin nan baka ne me ni ba,

Look here man we are all at fault fa ,kai tunda kazo garin nan ka nemeni ne,?
Ni jikina Ya bani ma kayi wata beb ne da ta ɗauke maka hankali daga kan kowa dan aunty ma
tace mun tunda kazo sau uku kawai kuka yi waya,

Hannunsa ya tura kan sumarsa da ta fara Tashi yace man share lemme just have a hot shower
na fito muje muyi sallah muje favorite eatery dinmu cos on God im famished .

No"cewan ammar ,inasan naci delicious pasta ɗin baby ihsan,

Dariya binyamin yasa yace "kai fita" ihsan yanzu ta wuce baby sai dai lady i guess rabonka da
ka ganta kama manta ,Anya ma zata tuna ka ,dauka dai wayana ka kirata ka faɗa mata in bata
komai ta shirya mana garden dining cos eating there would be fun hirar ma zaifi dadi,

Wayan binyamin Ya dauka bayan shi kuma ya shiga bayinsa domin wankan.



CHUCHUJAY

Share fisabilillah.
KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

24

Duk yarda ammar ke tunanin ihsan zata yi rawar kai da murna da ganinsa sai yaga batayi ba illa

dai tana yar fara'arta as usual bayan ta gaidasa ta kuma tambayi aina "
After that kuma ta bar musu table ɗin da ta haɗa musu dinner a garden cos bata ga Mai zata
zaunawa ba ,

Kallan binyamin yayi bayan tafiyan ta yace "guy ihsan just ignored me".

Dan sipping ruwan dake gabasa yayi ya kallesa kana yace "what were you expecting?
Kana expecting ta faɗa kanka ne tana murnar ganin sweet heart ɗinta na childhood?
Then you must be sick .

Did you just said that to me?
As in the great bloody hot ammar?

Whatchu bloody gonna do?
Just court the girl if you truly do love her like you said and stop expecting my sister to chase
you, she aint that low class girl and mind you we aint in the fucking states.
Binyamin yafaɗa yana Mai bruising ego ɗin ammar wanda ko da suna states baya bun mace sai
dai ta bisa ,ya daɗe yana san ihsan amma da yake a lokacin da bata da wayau ta kance ammar
take so wanda shi kuma a yanzu yake tunanin zai sameta tana running and dancing to his tone
, "Yes yasan ammar na San ihsan but dole he will have to do something about it bawai yana
tunanin zata zo Tana bibiyarsa kamar wata mara aji ba .

Its okay guy chill "i will win over her"
But mind you kamar yarda ka kankara mun kasani aina ma baza tana binka up and down ba
you will have to man up and face the reality.

Taɓe baki binyamin yayi yace "reality?
Last i remember ban taba ce maka ina san aina as a woman ba, yes talking about love i need
your advice on something ,

Jawo warmer ɗin pasta ɗin ammar yayi yana Mai Dan jin zafin abunda binyamin ya faɗa wanda
Gaskiya ne ,binyamin bai taba ji yana san aina ba hasalima ita kawai take haukanta akansa ,
Zubawa yayi yana Mai auno daɗin da pasta ɗin zai masa kafun yace who is the lucky girl?

She lives with us ."ya basa amsa ba tare da ya kallesa ba amma a zahiri yana tuna deenah ne
wanda hakan yasa shi kaɗai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login