Showing 57001 words to 60000 words out of 65850 words
Chapter 20 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf
yarda da ita baki daya,
Tana kan bacci taji alamun ana kallanta ,bude idanunta tayi ta sauke su a kanta,mikewa tayi
tana mai gyarawa tace MRS MAIKANO?
wani iri taji a ranta,kamo hannunta tayi tace ,deenah bazan ce dole ki karbeni a matsayin uwa
ba sannan bazan taba kokarin kwace gurbin zainaba ba ,nice na haifeki amma zainaba ce uwa
a gareki dan nasan bazan kai ya ita ba,
Amma still bazan cire ran zaki kirani mahaifiyarki ba ,
Rashin ki wasn't easy and i know akwai wata alaka mai muhimmanci tsakanina dake a ranar da
na fara haduwa dake ,
Jikina ya bani ke wata barice ta jikina ,
Ki huta dan in Allah Ya kaimu gobe inasan na kaiki gidan daddy ki ga kakanninki.
Zansa adda ta Kawo maki abinci cos Nasan zaki fin jin dadin ci ke daya.
Tashi tayi tana mai goge kwallar dake shirin zubo mata ,
Tasa kafa zata fita kenan Muryar deenah ta hanata a yayin da tace "MIMI ".
Juyowa tayi dan kamar a mafarki taji abun,
Da gudu deenah tazo ya faɗa jikinta tana mai sheshekar kuka,rungumeta Tayi tana mai jin
deenah din har ranta .
Washe gari da safe deenah tafara Tashi a gidan ta fito dan kama Yan aikace aikace domin
baccin ma babu shi gaba daya a idanunta,
Ganin farouk tayi zaune yana video game da adda ,tayi mamaki saboda ko bakwai bata karasa
ba.
Farouk na ganinta Ya mata alama da hannu yana mai faɗin"sis come over here.
Sis?
Ta maimaita tana Mai Kallansa,
Kallanta yayi yace Uhum,you're my elder sister mimi told me that and i like you,
Ina San na samu sister dama i only have adda and she's my aunty and she's boring and
outdated amma ke naga alaman you will be fun,
Kunnensa adda ta kama tace boring and outdated ko its okay zaka zo har inda nake ka sameni,
Dariya suka saka tare inda adda ta kalli deenah tace kinji naughty kaninki ba ,
Its okay bari naje ja haɗa mana kalaci,
Bari Nazo muje deenah ta faɗa .
A'a deenah zauna Ke da farouk karki wani damu Im set,
Bata Kuma cewa komai ba ta zauna kusa da farouk da yace oya sis can you play a video game,
Murmushi tayi tunawa dan abokiyar yinta sabs da kwana biyu basuyi magana ba,
Daukan ps din Tayi tace "i use to play with my bestfrnd and trust me i always beat her up,
Dariya yasa yana Mai dafe goshi,
Yace sis ko elder cousin ɗina wid bragging ɗinta kenan and i always beats her up and inajin
dadin yarda nake defeating nata so i really miss her ,tana school .
Umm thats good so lets battle,tunda suka fara take bashi chance ya cinyeta wanda yana ganin
yayi winning zai wani ihun murna yana yeeehhh".
Suna kan yin game din mimi ta fito,zama tayi gefensu cike da sha'awan yarda taga ƴaƴan nata
suna nishadi,
A tare suka gaidata suka cigaba da game ɗinsu wanda suna hakan mami ma tafito,
Bayan sun kammala breakfast ne suka shirya domin zuwa gidan daddy ,mimi ta kirasu tace
zata kawo musu surprise dan haka yayanta ma yazo ,mahaifin nata da yasan surprise dinta
bana banzane yasa ya maida abun serious dan haka kafun kace menene ya kira yayan nata da
matarsa.
Mintuna marasa yawa ne suka kaisu gidan ,
Farouk ne ya fara buɗe kofan mota ya fita yana mai rugawa gidan da gudu yana mai faɗin "old
couples faroukuuu is here".
Dariya deenah tasa jin abunda ya kira kakannin nasa dashi,
Shiga sukayi a tare ,tunda suka shiga idanunsu ke ka deenah musamman da sukaga
kamanninta da Mahaifiyar maimuna kamar an tsaga kara,
Kallan su suka maida kan maimuna wadda bayan zamanta Ko gaisawa basuyi ba tace "daddy
,Ummi,yaya meet my daughter DEENAH, yarinyata da othman wadda Alhj Ali marna yace ta
mutu alhalin bata mutu ba ,wannan kuma matar othman ce wadda itace ta raini deenah all this
while .
A tare suka saka Salati wanda nan take idanun Ummi suka ciko da kwalla,
Daddy ne ya kalleta da kyau kana yace"zo nan jikata zo ,come here and feel your family ,
Wasu hawaye ne suka fara bin kuncin deenah wanda bama tasan lokacin da suka fara fitowa
ba,
Da sarsarfa ta Tashi ta nufesu tana mai jinta a wata duniya wadda ta kasa fassara wace iri ce ,
Jikin daddy ta faɗa,
A hankali yake shafa kanta kana ya kalli ummi yace "i told you da dadewa ummin muna,i told
you inajin a jikina abunda maimuna ta haifa na raye kuma ko ba dade ko bajima zaizo
garemu,yanzu gashi munyi hakuri sannan munyi addua".
Share hawaye Ummi tayi tace 'haka aka yi,Allah kuma da ya Tashi hukuncinsa sai ya dauke ta
gidan marasa mutuncin nan,
Babu abunda zamu ce maki zainaba sai dai Allah ya saka maki da aljanna,
Ke din ba kishiyar maimuna bace ,Ƴar muce kamar ita ,
Ke ɗin yanzu ahalin muce ba ahalin marna ba,kin zama mu mun zama ke ,daddy ka sake ta
nima naji duminta.
Yar Dariya daddy yayi yace "kina kishi kenan Allah ya bayyana amaryata ,
Gyaran muryar yayan maimuna ne ya jawo da hankali kowa inda yake faɗin"daddy nima dai a
barni na gana da diƴata ko.
To kinji deenah maza je ki gaida uncle Dinki da matansa,
Babu musu tayi gurin da suka zauna dan gaida su,
Mamaki ne ya kamata Ganin mutumin da bata taba zatan ta haɗa iri da shi ba ,
Shima da mamaki yake kallanta dan sarai ya ganeta ,fuskarta fuskace da bazai taba mantawa
ba,
Deenah OTHMAN Ali ba ,
Ba Ke ce Yarinyan nan da sukayi case da WIDAD ba?
Da mamaki ta kaɗa kai tace nice ,
Dafe goshi yayi yace OMG"what a small world,
Im sorry my daughter ,kiyi hakuri akan dukkan abunda ya faru a baya,na goyi bayan WIDAD
without knowing that yarana biyu ne a tare,i knew about how she constantly tortured you amma
nayi shiru sabida ita din ƴata ce which i know i shouldn't have done that.
Shiru dakin Ya dauka dan dukkansu suna da labarin Yarinyar da WIDAD ke bullying a school .
Share hawaye Mami tayi wadda bama ta da labarin wai deenah nashan wahala a hannun wasu
a makaranta,tasani kuma deenah tayi shiru ne gudun kar ta shiga damuwa amma still da ta
faɗa mata.
Karfin gwiwa deenah ta hada tace "uncle its okay ,ni komai ya wuce a gurina sannan ni ban
taɓa rike widad a raina ba ,ban taba jin na tsaneta ba duk da kuwa na tsani actions nata da
halayyarta amma yanzu i have a big reason not to hold grudges against her.
Haka kowa a gidan Ya dinga kokarin nunawa deenah da maminta soyayya ,
Kwana sukayi gidan Alhaji NA'ABBA daddyn maimuna wanda ya ɗinga bata labaran kuruciyar
Maimuna.
A lokacin da ta sanar da sabs dangantakar ta da WIDAD bakaramun mamaki sabs tasha ba ,so
deenah is her cousin's ,cousin , already dama deenah yar uwa ta dauketa,
Koda sabs ta sanar da widad batace komai ba dangane da abun amma a cikin zuciyarta sai
take jin kunyar komawa Nigeria tayi facing auntynta mafi soyuwa a gareta gaskiyar ta jitane
wani iri and she's getting hard to digest it.
CHuCHUJAY.
KALUBALENAH.
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
36.
Kwanci Tashi babu wuya, deenah da maminta sun kwashe wata guda a gidan mimi wanda
deenah ta saki jikinta sosai da sabbabin dangin nata,
Babu wanda Ya ƙara mata maganan cikinta wanda a yanzu yake wata uku da satika,
A lokacin da laulayin Ya tashi mata sosai Mami da mimi sun nuna damuwarsu mutuka amma sai
suka danne ,
Mimi Da kanta ta kaita Ganin likita ya duba ta ya bata magunguna dan mami cewa tayi bazata
je ba saboda tana fushi da ita.
Bayan sun dawo ne mimi ta rakata Har ɗakinta ta kalleta da kyau tace "deenah nasan baki san
magana akan cikin nan sannan nima bana san na maki magana akansa but atleast ko dan
maminki yakamata ki buɗe baki sannan kinsan dole zaki faɗi wanene uban cikin so why are you
doing all this to us , Maminki tana cikin Baƙin ciki sosai akan wannan al'amarin musamman idan tana tuna marin da
aka mata sabida Ke sau da dama takan yi tunanin ko tafaɗi ne wajan maki tarbiyya,
Kallanta tayi cikin sassanyan yanayi tace "deenah ina zargin wani abu wanda nake tunanin
zargina ba kuskure bane amma inaso ne ki faɗa mun da bakin ki and i will fight the world for
you,so ki faɗa mun koda kuwa a matsayin stranger ne ba a matsayin uwa ba.
Kuka deena tasa tana Mai faɗin"Mami i was wrong,ban ma kaina kuma ban ma mami adalci ba
amma mimi kamar yarda na faɗa cikina wallahi dan halak ne ba shege ba,
Shiru mimi tayi tana nazari kafun tace "kina nufin a da aure kika samu.
Kaɗa Kai deenah tayi alamun eh.
Abun ya daki mimi cos a iya saninta babu wanda yasan deenah nada aure hasalima shine yasa
ake faɗin tayi cikin shege.
Gyara zama Mami tayi tace "okay stop crying deenah na ,now tell mimi "what happened".
Cikin fargaba ta fara bama Mimi labarin abunda Ya faru daga farko Har Tafiyar binyamin da
Kuma rasa contact da tayi dashi.
Shiru mimi tayi tana nazari, ga wani Mamaki da ya cikata ,ta sani soyayya ce ta saka deenah
tafka wannan wautar dan wauta ce karara.
Cikin sheshekan kuka da tsoro deenah tace "mimi dan Allah kar ki faɗa ma Mami sabida bazata
iya dauka ba sannan nasan bazata taba yafe mun ba sabida bata taba amincewa da alaka ta da
biyamin ba,
Murmushi mimi tayi tana tunanin ta yarda zata bullowa wannan babban al'amarin,
Gyara mata pillow tayi tace "oya kwanta ki huta zamu yi magana saboda wannan maganan
babbane and i won't tell your Mami amma ki sani dole zata sani saboda tafi kowa chanchantar
ta sani ɗin,amma ba zan faɗa mata yanzu ba sai na gano bakin zaren.
Bayan kwana uku da maganan mimi da deenah tana kwance taga message dinsa kamar a
mafarki"Dee where on earth are you?
Ta karanta message ɗin yafi sau ba adadi,
Bayan message ɗin kuma sai kiransa ya fara shigowa kamar bazai dai na ba,
Take wani irin haushinsa da kuma sabon fushin da take dashi ya harzuko mata,.
Ganin kiran nasa Yaki karewa ne yasa ta dauki wayan a kiran da ya kuma na yafi a kirga,
Bata jira abunda zaice Ba Cike da fushi tace "don't you ever try calling me again,
Let me be,idan Kuma ka sake kirana zan maka abunda zamuyi dana sani baki daya ,and set my
divorce letter and send it via message sai ka koma gida amminka ta aura maka yarinyar da taga
ta dace da kai.
"Dif ta kashe wayanta tasaka wani kuka,
"Da Baki masa haka ba you should have talk,
Daga kai tayi ta sauke cikin na mimi,
Shigowa mimi Tayi tace if i guess right binyamin ne ba?
Kuka ne yakwace mata cikin kuka tace "shine mimi,he used me and dumped me mimi and
mamansa have the guts to slapped mami .
Zama mimi Tayi ta jawo kanta ta dora kan kafadarta tace"shush everything is going to be
okay,yanzu ki tashi muje mu sanar da maminki abun da ya faru and i will talk to daddy zamuje
chan gidan he will have to divorce you indai kinji you're convinced and I'm not saying that what
you did was okay, deenah abunda kikayi baiyyi ba kuma baki kyauta Ba, Kin zaɓi daɗin Bakin ɗa namiji akan maminki wanda kinsan ke kanki Baki kyauta mata ba,and
yanzu Gashi you're pregnant kina tunanin idan yace Ba aure tsakaninku sannan shaidunsa ma
suka faɗi haka kece a ruwa fa,
This is your mistake so learn from it.
So?
Sniffing tayi tace"im ready mimi ,na shirya faɗa ma mami da su daddy ,cikina na binyamin ne
sannan we got married ,ammar da ihsan Da kuma malamin sune shaidata ,
I want to see yarda amminsa zatayi da wannan gaskiyann.
Shafa kanta mimi Tayi tace oya share hawayenki ,as far as sun sani it dosent matter your mami
is here ,im here and your grandparents are here,your whole family as a team so ki kwantar da
hankalinki, ko sunki mu zamu rike kuma mu kula da abunda kika haifa ai namune.
...koda Mami taji maganan auren deenah ba karamun razanata abun yayi ba cos bata taba
tunanin young deenah ɗinta zata iya bin wani namiji ta aurensa Ba batare da ta sanar da ita ba,
Kuka sosai deenah ta saka a lokacin da Mami ke faɗin bata kyauta mata ba sannan bata kyauta
ma kanta ba,
Hakuri ta ɗinga bata akan hakan da ta aikata amma mami tace ta rabu da ita dan abun ba
karamun dukanta yayi ba ,
Haka zalika koda aka sanar da su daddy abun ya mutukar girgizasu dan Har karamun faɗa sai
da daddy yayi mata amma kuma da yayi wani tunani sai ya bama zuciyyarsa hakuri dan abunda
tayi yafi da ace ta aikata barna.
Daddy ne ya kira grandpa dan Ya sansa sosai shiyasa koda yaji binyamin ɗan wanene yace
abun zaizo masu da sauki.
A ranar suka duguntsuma suka nufi MAI KUƊI mansion,
Kasan cewar Mai gadin yasan da zuwansu yasa ya buɗe masu a lokacin da sukayi horn ,
Babu abunda kirjin deenah yake illa dukan tara tara a lokacin da suka shiga gidan ,
Iso aka masu zuwa babban guest room ,
Tunda suka shiga deenah bata ga idan da ta Sani ba wanda hakan yayi mata daɗi,
Basu dauka lokaci Mai girma Ba grandpa ya shigo yana mai dogara sandarsa,.
Guri ya samu yana mai faɗaɗa fara'arsa amma a lokaci ɗaya he was confused da yaga falon
dauke da ahalin Alhaji NA'Abba ciki kuwa harda mami da deenah wanda bai san Mai ya Kawo
su ba ko ya haɗasu.
Bayan sun gaisa ne daddy yace"Alhaji Ai maganan nan ta dangi da dangi ce,Dan abunda ya
Kawo mu ya shafi mutane da dama a gidan ka ,kagan na farko ya shafi jikanka Binyamin shi
yamafi shafa ,sai iyayensa da duk wani babba ma a gidannan dan maganar bata mu da kai
bane kaɗai.
Da mamaki grandpa ya Kalli daddy kana yace okay Babu damuwa bari na umarci kowa ya
hallara Allah ma kuwa yasa shi binyamin din jiyan nan da dare ya sauka gidannan.
Cikin kankanin lokaci kowa ya hallacci gurin ciki kuwa harda auntyn binyamin dake states da
suka zo tareda ihsan da taje hutu gunta.
Tunda ya shigo yake kallan deenah,
Itama ɗin shi take kalla Ganin yarda ya wani lalace Baki ɗaya ,
Mamakin abunda ya haɗata da MRS MAIKANO yafara,
Koda ya dawo gidansu Ya fara sauka ,yayi mamakin da yaga gidan a kulle ,koda ya bude ya
shiga take yaga alamun gidan ya kwana biyu babu kowa a ciki so kai tsaye ya wuce gidansu
dan yasan definitely tana chan ,
Amma nan ma ga mamakinsa bata nan ,koda ya tambayi mama kaltu sai ce masa tayi sun bar
gidan ita da maminta amma sai bata faɗa masa dalili ba ,shima gudun kar tayi tunanin wani abu
,yasan babu wanda ya isa ya tambaya ,hajjo ce kaɗai ita kuma tunda ya dawo bata gidan taje
unguwa ,a lokacin da ta dawo kuma dare yayi ga a daren yana ta gwada layinta amma baya
shiga,
Sai da safe ne ya tura mata message sannan ya fara kiranta amma taki dauka ,
Yaji mamaki a lokacin da ta dauka tana faɗa masa maganganun da yaji Kamar an soka masa
takobi a zuciyansa,a magananta ya tabbatar masa akwai damuwa amma ya rasa wazai
tambaya damuwar.
Guri ya samu Ya zauna yana jiran yaji mai ke faruwa,
daddy ne yayi gyaran murya yace Alhaji abu biyu zuwa uku suka kawo mu gidanann ,
Da fari dai ,meet my grand daughter DEENAH,
Yarinyar ɗiya ta Maimuna gata nan zaune ,
Da mamaki kowannensu ya kalli deenah,
Cike da ruɗani ammi tace "tayaya tazama jikarka ?
Hala da aka koresu daga gidannan gun wani malamin sukaje ya jefa masu fatsarsu kan babban
kifi amma idan ba haka ba wanne magana ne wannan,dukkan mu babu wanda baisan
matsiyata bane jinin karuwai.
Kala nan hajiya mardiyya "deenah ɗiya tace ni nahaifeta da cikina sannan a iya saninki dani
baki taba jin inda aka kamani ina karuwanci ba haka zalika maminta da kika daga wa hannu
kika mara wanda muna nan zuwa kan batun sabida ba tsoranki ne ake ba ,ai talauchi ba hauka
bane sananan da kika tsinci deenah cikin talauci bashine ya maida ta less human ba sannan a
yanzu ina Mai tabbatar maki da ita ɗin irin arzikice sabida last dana tuna baki fini dukiya ba.
Mimi ta faɗa ranta a mutukar Bace dan a harzuke take da ammi.
Mari ?
Grand pa ya Maimaita dan bai san Anyi ba,.
Daddy ne ya katsesa ta hanyar faɗin "muje kan babban abunda ya kawo mu Alhaji wannan duk
Ai maganan daga baya,
Yanzu maganar da ta Kawo mu magana ce akan cikin dake jikin deenah wanda sanadinsa ya
Kawo fitarsu gidannan wanda Allah ya jefa su cikin ahalinsu.
Ciki? binyamin ya faɗa da mamaki.
Eh ciki mimi ta maimaita tana Mai jin haushinsa.
Gyaran murya daddy yayi Ya cigaba yace "eh kamar yarda kuka sani muka sani deenah na
dauke da ciki sannan kafun ta bar gidannan sai da ta shaida maku cikinta ba shege bane da
ubansa ,sannan da aure aka samesa ,sannan shi wannan cikin jinin gidan nan ne.
Dariya