Showing 9001 words to 12000 words out of 65850 words

Chapter 4 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf

Advertisement

02 Aug 2025

2670

kaltu kadai ta tarar a dakinsu tana bacci ,
Jakarta ta aje ta cire uniform dinta ta shiga domin watsa ruwa ,
A gurguje tayi shirin tafiya islamiyya wanda ke cikin tsohuwar bokonsu ,
Duk buruntun da take bai tashi mama kaltu ba ,kai tsaye sashen hajiya fattu ta wuce dan tasan
maminta na gurin indai bata dakinsu,
DA sallama bakinta ta shiga gidan inda ta tarar da hajiya fattu da azad suna lunch,
Cikeda ladabi tagaida ta inda ita kuma ta amsata cikin sake wa tana mai cewa"
Deenah yan makaranta inafatan dai makaranta yau tayi dadi,

Yar dariyar da azad yayi ne yasa ta dago kai ta kallesa inda itama hajiya fattu tayi hakan tana
mai cewa "lapia mene na dariya"
Goge mayonnaise din dake gefen bakinsa yayi yace im sorry mommy Kawai na tuna wani
abune,.

Oh ,Deenah don't mind him ,ina fatan dai zaki dage da karatu kiyi kokari sosai who knows sai
kiganki da scholarship na oxford university,do it for your mother Okay,
Murmushi deenah tayi tanajin wani dadi a ranta na wannan fata da hajiya fattu tayi mata duk da
tasan ko oxford din aka bata bazataje ba dan babu ma yarda Za'ayi ta tafi ta bar maminta a
wannan duniyar da basu da kowa sai kansu.
Tashi azad yayi yana mai faɗin sai dai scholarship din,
Oxford indeed,
Gudun kar hajiya fattu tamasa magana yasa kai tsaye ya bar gurin .
Babu wanda yace komai duk da duk sunjisa,
Katse shirun deenah tayi ta hanyar cewa hajiya mami fa,
"Eh maminki kam yau Ammin binyamin ta areta dan zata gyara part dinsa cos yanzu haka ina
tunanin anje daukosa a airport ,
Batace komai ba ta mike tana mai jin zafin kalmar wai an ari maminta sai kace wata kaya,
Kai tsaye part din tanufa,
Babu kowa a baban falon dake na kowa a gidan ,
Haurawa tayi sama tana mai sallama dan bata san inda zata fara neman maminta bama sef,
Abubakar ne yake sakkowa daga matatakalar inda sukayi Kiciɓis,
Baya cikin masu mata wulakanci amma kuma baya daga cikin masu mata magana wanda
hakan nature dinsa ne wanda deenah ke kira da halayyar yaran masu kudi ,wato wulakanci,
Kowannen su dan iskan kansane,ta gefenta ya rabe zai wuce,
Tsintar kanta tayi da fadin"abubakar dan Allah baka ga mamina ba ance min tana nan tana aiki,
Kamar bazai tanka ta ba ,"
Muje "shine kawai abunda ya faɗa kamar ana masa dole,
Fahimtar zai kaita ne yasa ta bisa .

Ta Babban falon suka bi ,
Wata kofa taga ya tura binsa tayi inda taga ya nufi wani dogon corridor,
Daki ya nuna mata yace tana ciki,
Har ya juya zai tafi taji muryarsa yana mai faɗin"
Welcome to ORCHID HIGH.
Murmushi tayi tace thank you wanda bama ta tunanin yajita cos yana kai ayar maganarsa yabar
gurin,
Koda ta bude kofar cikin falo taganta ganin maminta tayi ta dage tanata goge goge,
Shiga tayi bakinta dauke da sallama tace"mami ina baba asibe ne kike aikinta ,
Aje mopping stick din dake hannunta tayi tace"kin dawo kenan,wallahi asibe taje garinsu ne
mamanta bata da lapia shiyasa nake aikinta amma ai nama kusa gamawa maza je ki ci abinci
yana nan a kula ki wuce islamiyya,

"A'a mami bari na kama miki naga gurinfa yayi kura da yawa aikin ya maki yawa dama yau din
bawani abune muke dashi mai amfani a islamiyyar ba ina dai san najene kar nayita zaman
gidan,

Bata ce mata komai ba ta faa tayata aikin ,
Ya makaranta fa?

Gabanta ne ya fadi jin tambayar da tayi mata
Saurin danne takaicin da ta kwaso tayi tace ,mami makaranta daɗi kamar ba yau na fara
zuwaba ,sai kinga ma yarda yan ajinmu suka karbeni abun nikaina saida ya ban mamaki ,
Tana kokarin kara hada karyar da take sharara mata ne hannunta ya goce ta buge wani vessel
dake kan table a aje wanda karar faduwarsa da fashe warsa yayi daidai da sautin muryar da
mai ita ya danno kai falon ,

Holy fucking fudge..
That's my favorite vessel .


CHUCHUJAY.

KALUBALENAH.

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

7
A tare deenah da maminta suka ɗaga kai dan san ganin wanda ya shigo ɗakin,
Kallo ɗaya deenah ta masa ta ganesa dan takanga hotonsa a wayan ihsan,
Cike da fitinanniyar masifa ya karaso ɗakin yana mai faɗin,
"Who the hell are you guys"
And mene kuke mun a falo haka ,
Juyawa yayi ya fita yana mai kiran Ammi"cikin wata irin shagwababbiyar siga".
Da sauri mami ta tako inda deenah ɗin take ganin tana kokarin taɓa fasassun kwalaben dake
kasa a zuzzube,
"Mami wallahi bada sane na ne na fasaba.
Ganin yarda ta firgice da barnar da tayi yasa ta jawota jikinta ta rungume tana mai faɗin"
Ya isa ai kowa yasan tsautsayi sannan wannan abun da kikaga ya fashe to lokacinsa ne yayi
koshi mai abun idan da ace yana hannunsa zai fashe tunda wa'adinsa yayi bari yanzu zan
gyara gurin,
Rufe bakinta keda wuya ammi ta shigo tareda shi a bayanta yana wani kwaɓe fuska,

Maike faruwa anan ne zainaba?
Tsugunnawa mami tayi cikin biyayya tace wallahi hajiya tsautsayine deenah na tayani aiki
abunnan ya zame ya faɗi ,

Cikeda da wata kasalaliyar muryar wulakanci yace "
Tsautsayi ?
Ammi kinajin wani bullshit ba?
Beside wama ya basu izinin shigo mun part,ammi kinsan fa i hate kazaman mutanen nan they
are hungry wolfs abu kaɗan suke jira su kwashi na kwasa yanzun ma who knows Ko sun satan
mun wani abu cos talakawannan chance kaɗan suke jira basu iya talaucinsu ba,

Kayi hakuri ranka ya daɗe shine kawai abunda mami ke iya furta wa,bawai batajin zafin abinda
ke faruwa bane a'a tana danne wa ne a matsayinsu na masu nema a kasan su,
Wani irin bakin cikine yazo magogwaron deenah ya tsaya jin yarda yake musu diban albarka
har yana kiransu da barayi inda mahaifiyarsa kuma ke tsaye tana sauraransa,
Gyara tsayuwa amminsa tayi a karo na farko kuma tayi magana ,
BINYAMIN take it easy umm,laipinane dan asibe ne bata nan so na roka fattu ta bani mai aikinta
so kagani ba laipina bane cos bansan suna da barna ba amma an maka laipi kayi hakuri kaji
son,
Don't mind yan aikinnan kar ka bari su bata maka mood dinka oya maza kaje kashirya ka fito
kan alhaji babba ya fara nemanka,
Kara kwabe fuska yayi cikeda kyamarsu yace "No ammi sai kin fara dubasu ki tabbatar basu
mun sata ba cos nasan zaiyyi wuya talaka ya kasa sata a guri.
Cigaban hakurin da mami ke masa shine ya ke kara tunzura deenah,
Cikin murya kuka tace "_
Mu ba barayi bane sannan dan muna nema karkashinku bashine ya mayar da mu
wulakantatuba halak ɗinmu muke nema ,
Namaka barna cikin rashin sani amma bashine ya baka damar wulakantamu ba dan yarda kake
dan adam muma haka muke ,kake ta wani fama kwabe fuska kwazozan ƙato da kai ,koni bana
ma mami haka a shekaruna sai kai ƙaton banza.

Jin dakin ya yi jum kamar an dauke wutane yasa deenah tayi realizing abunda take faɗa da
kuma inda take,
Dagudu ta rabe ta fice a dakin zuciyarta na dukan uku uku,
Mami da gaba daya ta kidime ce ta cigaba da basu hakuri dan ita kanta batayi tsammanin
deenah zata fadi haka garesu ba.
Rike kugu biyamin yayi cike da mamaki yace ,
Ammi naji da kyau kuwa?
Ni poor a** little begging bitch dinchan ke kira katan banza,
Ammi katan banza fa.
Wata dariyan yayi irin ta mamakin nan yace katon banza fa ammi,
Kallansa ya maida kan mami da kanta ke kasa yace "hey old woman Ki shirya barin gidannan
keda yarinyan ki mara tarbiya ,mumuna yar kyauyen chan saboda ta ja maki balai.
Fuuu ya wuce bedroom har yana kokarin bige mami da tayi saurin kauce masa.

Tashi ki bace mun and make sure kun hada jakanku kamar yarda yafada maki,
Idan ance kubama yaranku tarbiyya sai ku ki alhalin kunfi kowa sanin talauci sai da tarbiyya .

Sum sum Mami ta taso dan barin sashen ranta fal takaicin abunda ya faru,
Chan ta Tarar da deenah tana kuka,
Kotakanta bata biba ta koma chan karshen gadonsu ta zauna tana mai dafe kai,
Ganin haka yasa baba kaltu cewa ,"ai ke kya faɗan abunda ya faru tundaita ta gagara sai kuka
da ta zauna tana mun,
Cike da bakin ciki ta fada mata abunda ya faru tana mai karawa da cewa, "ai na gode sosai da
kika jawo aka zageni har ana kokwanto akan tarbiyar dana baki,
Yau ko duka ya rufeni dashi ba zakice masa katon banza ba ballantana zagine kawai kuma ni
banga inda yake fitowa a jiki ba,ai shikenan sai ki fara hada mana kaya kanki kika yiwa .
Kuka sosai deenah ta sake fashewa dashi na bakin ciki bana dana sani ba ,dan jin abunda
maminta ke faɗa na kan ta hada musu kayansu sai taji dama zazzaginsa tayi ta rama abunda
ya faɗa musu sai a koresu da hujja.

Bangaren binyamin kuwa koda ya shiga bathroom tunanin abunda ya faru kawai yake ,wai shi
yar wannan yarinyar sa'ar kaninsa zata kira da katon banza,
Saurin tsane jikinsa yayi bayan ya fito kana ya shafa mai yana mai Allah Allah ya ida yaje ya
samu Alhaji babba tunda ko kai ka dauki mai aiki saida yardarsa za'a koresa shima kuma sai da
dalili babba wanda dalilinsa baza a kirasa da karami ba,
Knocking ya ji a bakin kofarsa ,cikeda masifa wadda a zahiri idan ka kalleta bazaka kirata
masifa ba yace who is that*
Daga bakin kofar ihsan tace bro nice ,
Bai sake cewa komai ba wanda alamune na ta shigo so ta sa kai ta shiga ,
Zama tayi kan stool din dake gefen mirror while shikuma ya cigaba da taje gashinsa ba tareda
ya damu da san sanin menene ya kawota ta ba dan muradinsa kawai nasan ganin su deenah
sun bar gidan shine a gabansa ,
Ganin bazai kulata bane yasa ta katse shirun ta hanyar cewa"
Bro nasan you dont wanna listen but it's about deenah, dazu naji ammi na maida maganan ,
Dan Allah brother kayi mata hakuri ,deenah yarinyane mai kirki sannan nasan ta faɗi abunda
tace ne bisa kuskure shes a nice girl when you get to know her dan Allah brother MiN give her
another chance"

Wani kallan banza yayi mata a lokacin da ta kare zancenta kana ya rike kugu yana mai facing
dinta "why should i get to know her ,
Ni sa'anta ne ,
Beside ni kinga nayi maki kama da class na talaka ?
Dukkansu barayine and to hell with her being nice "shit,
All I fucking care about shine a yau sai ta bar gidannan.
Get out".

Kallansa ihsan tayi da fuskar damuwa tace "brother MIN nasan kanada bad experience akan
talaka amma that doesn't mean dukkansu barayyine beside an mafi samun barayi cikin masu
kudin cos a koda yaushe burin mai kudi daya shine yaya zai kara arziki,
Brother Deenah is not any talaka give her another chance,

Are you done?

Ganin bashi da alamun wasa ne yasa tace "yes"
Kamo hannunta yayi kiii yayi waje da ita ya watsa bakin kofa ya mayar ya rufe..

1 hour later.

Shiru deenah da maminta zaune suna jiran tsammani ,
Sallama  kaltu tayi tace zainaba ana nemanku sashen Alhaji babba and ki kwantar da hankalinki
shidin mutum ne mai adalci ni na tabbata bazai biyewa binyamin ya kore ku ba akan dan
abunda bai taka kara ya karya ba ,
Deenah yarinyane and nasan ta fadi duk abunda ta fadane a matsayinta na wadda bata iya jure
acima mahaifiyarta mutunci kuma ta wannan ina tare da ita saboda babu maiso acima
mahaifiyarsa mutunci yayi shiru.
Maza kuzo muje ,
Babu musu suka tashi jiki a sabule karma ace zainaba,
A babban falon da suka zama baki daya suka tarar da su,
Jiki a sabule suka karasa ciki bakinsu dauke da sallama bisa jagorancin kaltu,
Umarni Alhaji babba mutum mai kwarjini ya basu su zauna,

Nifa granny im not here Dan mu maida abunda ya faru kawai inasan a kori matarnan da
yarinyanta daga gidannana cos I wont stand them ko kadan saboda yar wannan yarinyan idan
ina ganinta gidan nan zan iya maketa ko wane lokaci,

Sai da ya kai aya Alhaji babba ya kallesa cike da nutsuwa yace ka gama?
Bai basa amsa ba ,sanin bazai basa dinne ba yasa ya maida dubansa kan su deenah yace "ke
deenah ko maza taso a bayan umminki ki dawo nan gabana ina ganinki,
Da fargaba deena ta tashi ta karasa tana jin kamar ta gudu musamman irin yarda biyamin ke
mata wani banzan kallo ga kuma idanun hajiya fattu a gefe da ammin binyamin dana hajiya
Babba wadda tunda ta amsa gaisuwarsu batace komai ba dan In Alhaji babba na guri shi keda
magana,
Durkusawa deenah tayi tace Alhaji gani,
Tambayarta yayi abunda ya faru,zanzan ta zayyana masa komai ba tareda ta boye nata
kuskurenba,

Kallan binyamin yayi yace kai kana da laipi binyamin,
Bance ita bata da laipi ba duka kuna dashi,
Bude baki yayi zaiyyi musu ya dakatar dashi.
Nuna mami yayi yace ita mahaifiyar deenah ai zata haifeka mai yasa zaka ci mata mutunci haka
kuma kayi tunanin yarinyarta zata yi shiru,
Ai baka dau hanyar mutunci ba saboda ko kaine ba za kayi standing a cima ita amminka

mutunci ba har ana kiranta barauniya ,
Yanzu I won't make this long,
Deeanah da mahaifiyarta bazasu bar gidannan ba ,ina nufin zasu cigaba da aikinsu saboda ni
banga abunda sukayi wandaya cancanci kora ba,
sannan inaso kai ka fara bawa maifiyarta hakuri bisa rashin ɗa'ar da kayi mata sai ita ma ta
baka hakuri and case close,sannan babu talaka sai bawa mafi munin aiki gaban ubangiji,ka
kiyaye,

Zainaba ce ta ɗan gyara zama tace alhaji amin afuwa zan tsoma baki,ni ina ganin ba sai ya bani
hakuri ba wallahi ban dauka da komai ba..
"A'a mami ya baki kawai dan nima bazan bashiba idan bai baki ba ,

Jawota maminata tayi inda shikuma ya zabura yana mai faɗin kana dai ji ko grand pa,
Yar dariya alhaji babba yayi yace naji ai ba akan bata take ba ,

But..
No buts binyamin kawai ka bada hakuri .

Kasa yayi da Kansa cikin takaici yace kiyi hakuri i was wrong,
Dan murmushi deenah tayi tana mai fadin "shege kaya a ranta inda a fili kuma tace nima kayi
hakuri na kiranka katon banza ,bazan karaba but idan ka kuma ma mamina rashin kunya zan
kuma.
Wani kallo yamata na tsana kafun ya tashi fuu ya fice a dakin ,
Bayansa amminsa ta rufa bayan ta musu sallama,
Yar dariya kakan nasa yayi ya kalli deenah yace "deenah just be avoiding him and banda
fitsara,
Kasa tayi da kanta tace insha Allahu,ayi hakuri.

"Nikuwa ina san yarinyar ,ko za tana zuwa tana dan mun tausa da hira in bata komai,
A Karo na farko hajiya kaka tayi magana.
Babu komai fattu ta faɗi tana mai murmusawa a zuciyarta kuma tana mai san ta kebe da
zainaba da diyarta.


CHUCHUJAY.✍
8
KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU

Tunda hajiya fattu ta fara musu faɗa bata tsagaitaba dan acewarta abun ba karamun bata mata
rai yayi ba domin tsakaninta da mahaifiyar binyamin akwai wannan babban fachalancin shiyasa
kowa baya san dan uwasa yaga wallensa ,

Bana san abu makamancin wannan ya kara faruwa a gidan nan shine maganar ta na karshe
bayan ta musu izini da su tashi su tafi.

Haka tsakanin zainaba da ɗiyartata yakasance babu wani muamala mai daɗi da suka saba dan
sosai mahaifiyar tata tayi fushi da ita,
Kwana uku kenan suna cikin wannan yanayi ,
Bata amsa gaisuwarta ko ta mata, sosai deenah taji rayuwar ba dadi dan hakan bata taba shiga
tsakaninta da mamin nata ba ,
Ita tayarda ta dauki cin kashin koma wanene akanta amma a shirye take ta kuma daura
damara, bazata taba bari acima mahaifiyarta mutunci ba indai tana raye ,
Haka a kwanakin takanje sashen hajiya babba mace mai mutunci wadda tasan darajar mutum
kuma sosai take jan deenah ɗin a jiki duk da har a lokacin deenah ta kasa sakin jikinta,

kaltu ce ta shiga tsakanin mami da deenah wanda deenah ta dau alkawarin bazata kuma rashin
da'a ba ammafa a zuciyarta ta kudiri idan ba a kuma wulakanta mata uwaba kenan dan zataje
to any extent Akan maminta .

Tunda sabani ya shiga tsakaninta da binyamin bata kuma haduwa dashi ba sai a yau monday
data shirya dan zuwa makaranta,
Alhaji babba ya umarci su azad da su ringa tafiya da ita makaranta tunda gida daya suke amma
koda sau daya hakan bai taba faruwaba dan kafun ta fito ma sun umarci driver ɗinsu da ya tafi
ya kaisu makarantan karma ace azad ,
Bata taba damuwa ba dan maminta na bata kuɗin mota so bata taba laruwa da wani,

Tana cikin sauri dan gudun kar tayi late, kwatsam sukayi kicibis a babbar harabar gidan,
Idanun sune suka sarke guri daya,
Har zata wuce ta dakata tareda dawowa baya ta tsugunna har kasa tace yaya bilya ina kwana ,
Tashi tayi kamar kuma ba ita ta gaidasa ba ta taka dan barin gurin,
Zafin nama yasa ya fincikota dan wuya yake da ita ,
Dangwarar da ita yayi gabansa yace ke "wanene yaya bilya ?
Ni tsaran wasankine ko?
Idan kika sake bude kazamin bakinkinan na miyan kuka kika kara ce mun yaya bilya sai na
karyaki wallahi ,
Useless girl get out of my sight.
Tashi tayi ta fara takawa ko a jikinta daman ta gaidasane gudun kar ya nemi wani abun ya
manna mata sannan menene idan ta kirasa bilya taga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login