Showing 6001 words to 9000 words out of 65850 words
Chapter 3 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf
wanda baiyyi wanka ba fa ake ,
Nikam banasan amun wulakanci kan abunda nafi karfinsa gwanda kawai nayi wankana ko
mama kaltu,
Murmushi mama kaltu tayi tana mai jin san deena har ranta tace wannan haka yake deena kiyi
wankanki amma fa da ruwa mai zafi,
Haka zainaba ta shiga bayi tabarsu sunayi,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali a cikin gidan na maikudi,
Tunda deena ta fara makaranta yazama babu ma mai ganinta dan daga boko tana tashi abinci
kawai take dawowa taci ta wuce islamiyya,
Duk result din deenah da zai fito abun alfaharin zainaba ne ,
Tanajin dadi sosai a wani bangaren kuma tana ji aranta dama zata samu wadataccen kudin da
zata saka deenah a makarantar kudi koda ta karamin kudice ,
Ranar suna zaune suna hira da kaltu take tambayarta inda zata samu makaranta mai karamin
kudi,
Aji uku take na js yanzu ko?
Eh zainaba ta bata amsa tana jinjina wai yanzu sun kusa shekara biyu a gidan,
Dafata kaltu tayi tace ki kwantar da hankalinki,
Alhaji babba yana bawa yara hudu scholar a babbar makarantarsa dake cikin garin nan,
Makarantan datayi fice kuma ta kunshi shahararrun yaran masu hannu da shuni,
Amma akwai masu hannun jari cikin makarantar wadanda suma akwai yayansu a makarantan
cikin su kuwa harda abokan masu gidan ,
Makarantar ta wuce dukkanin tunanin mutum wajen haduwa sannan malaman dake kowayar
dasu jiga jigan masu jan kunne ne,
Nasan deena nada kokari to amma ta kara taci na farko a jnr exam dinsu insha Allahu nikuma
zan shiga nama hajjo magana deena zata samu shiga cikin wannan shararriyar makaranta ta"
ORCHID HIGH SCHOOL.
Where deenah's new life begin.
Orchid high school.
CHUCHUJAY.
KALUBALENAH
5
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
ORCHID HIGH SCHOOL.
Tsaye 15 years old deenah take a bakin gate ɗin tamfatsetsen gate din makarantar kirjinta na
dukan uku uku tana tunanin yarda zata shiga cikin makarantar tayi mu'amala da ahalin cikinta,
Tuna kalaman zainaba tayi inda take ce mata "deenah babu talaka sai wanda ya mayar da
kansa talaka a zuciya ,kidaina sawa kanki cewa ke talaka ce ,sannan ki cire tsoro a ranki na
wannan makaranta da kika samu ,
Dama ɗaya ce wadda idan ta wuce ki to da wuya ki sake samun irinta dan haka ki saki jikinki
kiyi amfani da wannan damar taki,ki kuma saka aranki karatu ne ya kaiki wannan makarantar
kuma Allah ne ya kaiki sannan yin Allah bana mutum ba ,dan haka tunda ya kaiki wannan
makarantar yana da manufa , Kiji ki ƙi ji ki gani ki ƙi gani,
Babu ruwanki da takalar faɗa kiyi kokari ki zauna da kowa lapia sai kiga kinci ribar rayuwa.
Gyara beret ɗin kanta tayi cikin ƙwarewa dan tunda ta fara mafarkin makarantar ta ke kokarin
taga ta kware wajen koyan abubuwa da dama,
Necktie ɗinta ta kara gyarawa zama sosai ,
Tayi tuck in na long sleeve white ɗin dake jikinta cikin dark and light brown skirt ɗin da ya wuce
gwiwa da kadan wanda da kyar maminta ta lamunce mata tasaka ,shima dan tasaka dogun skin
tight mai safa ne baki,
Sai armless brown top wadda take mahadin uniform ɗin,
tayi kyau sosai a cikin sabon uniform ɗin da makarantar ta bata,
Jakarta ta gefe da baƙin takalmin da mama kaltu ta siyo mata a gwanjo ta kuma kalla tana jin
baya ita kuma bazata bari wani ya faɗan mata otherwise ba.
Kai tsaye ta nufi wawakeken gate ɗin shiga makarantar da yake a wawake kamar yarda taga
sauran daliban nayi,
Bata kuma nutsewa cikin kallo ba sai da ta ganta cikin yalwataccen harabar makarantar da
dalibai ke kaikawo nazuwa ajujuwansu,takawa ta cigaba da yi dan nemo nata ajin wanda yake
ss1A,
Bayan ta gama zageye kasa bataga ajin bane ta nufi matattakalar benen da zata sada ka da
ajujuwan dake first floor,
Othman Deenah Ali,
Juyawa tayi jin an ambaci sunanta nervously ,
Wata kyakyawar malamace wadda kallo daya zaka mata kasan yar gayu ce gata very young ,
Kada kai deenah tayi tace "yes"
Follow me shine abunda malamar tafaɗa ta fara tafiya ,
Babu musu Deenah tabi bayanta da ɗari ɗari,
Wani office suka shiga bayan ta aika tace a kira mata class rep na ss1A,
Tsaye deenah tayi a gaban matar da ta zauna a mazauninta,
Cire glasses ɗin dake fuskar ta tayi tace"
You're welcome to orchid high deenah,and I hope you will abide by the rules ,
I am miss suraj Aafiyya ,ss1A class master ,
No fighting,no bullying ,cult,exam malpractice etc,
Girl you'll have to shun all the bad things because if you are caught in any of sort act, then its a
total withdraw,
And If you have any problem in the school I believe you know the door to my office ,
Once again you're welcome to orchid high.
Tsaf deenah ta fahimci abunda matar ke faɗi dan ihsan kanwar binyamin tana mata lesson na
English duba da sabon da sukayi wanda ihsan ɗince ta fara janta a jiki dan duk da girmewa
deenah da tayi tana jin santa a ranta ,
nacine da deenah sosai dan haka cikin lokuta da basu da yawa ta kile a yaren,
Sannan ihsan kan bata wayanta tayi research na vocabularies sannan ta yarda da bibiyar
dictionary ɗinta,
"Thank you aunty and i promise to abide by the school rules .
Miss suraj ,malamar ta faɗa cikin sigar gyara na aunty ɗin da deenah ta faɗa mata .
Murmushi deenah tayi cikin nauyi tace I am sorry ,"miss suraj .
Dan ita ta saba a bokon su ko wacce malama mace aunty ce.
Knocking Kofar akayi,izini miss suraj ta bawa mai knocking din da ya shigo,
Wani yaro ne ya shigo jikinsa sanye da uniform ,
Kallansa deenah tayi aranta tana mai furta "gaskiya yayan masu kudi daban suke,fatarsu kawai
abun kalla ce ,
Gaida malamar yayi cikin halshen turanci kafun ta amsa ta masa izini da ya zaga da deenah
makarantan sannan ta mika mata key din locker ɗinta wanda yake dauke da number 59 tace ya
rakata,
Babu musu deenah tabi bayan kyakyawan yaran da fuskarsa babu yabo babu fallasa,
Lockernta ya fara rakata ya nuna mata kafun suka fita dan yayi mata tour na guraren da ya
kamata ta sani a cikin makarantar,
Shiru suke zagaye filin sport ɗin dake makarantar kafun ya katse shirun ta hanyar kallan tag
ɗinta yace ,
Othman Deenah Ali.
Sunanki mai dadi,
Kallan tag ɗin nata da ta fahimci daga nan ya ga sunanta tayi tace nagode,
Sake sakin fuskarsa yayi fiye da da yace sunana umar izziddeen saraki"
But you can call me DEEN
And nini class rep na ss1A ,
Hannunsa ya mika mata for a handshake taki karba,
Sosa sumansa yayi yace ooopz you don't shake,?
I'm sorry" ta furta"
No its okay yafada yana mai cewa nan cheerteam ke zama,i will introduce you to the leader
Idan kinasan joining,
cikin sauri tace"no nagode".
Murmushi yayi yace "as you wish,
And now the last place is the cafeteria,then sai muje aji kiga class mates ɗinki saboda we will be
having class by nine"
Ba musu ta bisa tana mai yaba kirkinsa .
Babu kowa a cafeteria ɗin haka suka gama tour ɗinsu suka nufi class ,
Tana lura da yarda mutane ke nuna ta musamman yan matan amma ta zabi da ta toshe
kunnuwanta ta rufe idanunta tunda dama tasan ai ita ba tsarar su bace.
Glass door din ajin deen ya tura ,kowanne dalibi acikin ajin saida ya juyo dan an riga an kawo
musu tsurkun scholarship student tazo tana tareda class rep ,
Tana shiga gabanta ya cigaba da duka ganin classy yaran dake cikin ajin wanda gasu dai cikin
school uniforms suke amma a jikinsu sai kaga fancy abu kar ma ace matan ,
Kamar ance ta ɗaga idanunta ta sauke su kan azad,
Duk da basu ga miciji amma at least taga wanda ta sani and tasan bazai mata wulakanci ba
cikin makarantar kilan ma wannan ya zama silar shakuwarsu tunda ajinsu ɗaya,
Tsintar kanta tayi da yi masa murmushi ,haɗe fuskarsa yayi ya mayar da headphone ɗinsa
kunnensa ya koma ya rufe idanu,
Azad na ɗaya daga cikin big boys din makarantar wanda ko wacce mace burinta ace saurayinta
ne saboda haka ne Allah ya ɗora masa girman kai bugu dakari kuma yana dan masu
makaranta shiyasa yaran ke masa fadanci,
Tsaye deenah take bakin board tare da deen wanda yake so su bashi attention ɗinsu kafun ya
fara introducing deenah wadda ya umarta ta faɗi sunan ta,
Cikin sakin fuska tace"hello class my name is Deenah Othman ali,
We saw that dummy ,
Ɗaya daga cikin yan matan ta faɗa wanda hakan yasa dukkansu suka kwashe da dariya,
Ba dai tayi kasa a gwiwa ba tana mai san sake magana wata acikin daliban mata tace "
Hey miss scholarship wanne designer company ne suka maki jaka da takalmi,
Ai kamar jira suke yan ajin suka sake kwashe wa da dariya suna faɗin "gucci .
Suna cikin wannan dariyar iskancin aka turo kofar,
Juyawa sukayi baki dayansu dan ganin wanene,
Karar takalmin ta mai tsini shi kaɗai kake ji sannan kamshin designer perfume ɗinta,
Beret ɗinnan a karkace sai expensive black human silk cut wig ɗin dake kwance luf a bayan ta
da gefen fuskarta ,
Shigowa tayi tana wani taunar chew gum ɗinta hannunta dauke da karamar hand fan pink,
Necktie ɗinta Kansa ba na makaranta bane something fancy ne"
QUEEN yan korarta suka faɗa inda ita kuma take jin kamar ana fasa mata kai ,
Chan gefen azad wanda idanunsa ke rufe kunnensa a toshe wata yarinya wadda taji ana cewa
benaxir ta nufa da saurinta ta jawowa gwanar da ta shigo seat,
Zama tayi tana mai harɗe kafafunta wanda sai a lokacin ta kula da deenah dake gefen deen a
tsaye,
Dan murmushin gefen fuska tayi kafun tace "ita kuma waccan sabuwar teacher ce mukayi ne,
Banazir dake gefenta ne tace scholarship student ce,
Yar dariya yarinyar tayi kafun tace ,kuce mun new fun toy"
Benaxir introduce me to the new toy"
Ganin abunnasu bana kare bane yasa deen wanda shima ba sauraransa suke ba saboda kowa
naji da Kansa yace "
Deenah use that empty seat ɗazu aka shigo dashi its yours and do not mind them,
Babu musu ta nufi seat din wanda yake daga gefen na deen ,
Tana kokarin zama tajita akasa benazir ta janye,
Tum ta faɗi a kasa wanda a take suka sake fashe mata da dariya,
Sosai taji zafin faɗuwar amma ta danne ta daddafa ta mike ta jawo seat ɗin ta zauna tana mai
kallan WIDAD wadda kallo daya ta mata ta gane ta duk da kuwa rabonta da ita tun zuwanta
abuja farkon zuwanta gidan,wanda ranar ta tsinci mahifiyar azad na faɗa masa widad suntafi
mexico na shekara biyu.
Sam widad bata ganeta ba dan ita bama ta da time ɗin da zata tuna ta,
Benaxir ce ta nuna mata widad tace hey little poor kid,Idan kika bi widdy kin haye a orchid
saboda babu ya ita idan kuma kikace zakija da ita ki shirya shiga uku so kisan matsayinki na
mai mana running errand,
Suna kan maida dariya malamin dake daukar su English ya shigo,
Yar dariyar rainin hankali widad tayi lokacin da yace Good morning class,
A fili tace the oval head is here,
Yana jinta baice mata komai ba sai yayi choosing yayi ignoring nata dan yaran makarantar
kamar jira suka ka taɓasu kaji shamaci,
Deenah ya tasa ya ce tayi introducing kanta yana san sanin student dinsa ,babu musu ta tashi
ta fadi sunanta ,
Har zata zauna yace mata wane school ta Bari,
Ba tareda kyamar makarantar ta ba tace community school,
Ai take suka kara fashewa da dariya wanda har saida malamin ya daka musu tsawa sannan
wasu sukayi shiru amma banda rikakun yan iskan aji,
Ana gama basu karatun malamin ya fita,
Yana fita deenah taji an finciki hannunta an jata waje.
CHUCHUJAY.
KALUBALENAH
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.
6
Tunda ya fara janta bai tsaya ko ina ba sai a sketching room ,
Mayar da kofar yayi ya rufe batareda ya damu da bugun da widad ta fara ba lokacin da ya kulle
kofar,
Tsaye deenah tayi tana mai kallansa tana mai san ganin gudun ruwansa ,
Nunata yafara da yatsa yana mai faɗin,
Ki kiyayeni and you better stay on your lane saboda ni ba sa'anki bane naga take takenki
kamar kina san nuna wa makaranta kin sanni to just know that idan makaranta tasan kin sanni
kece a kasa because I will tell everyone that aiki kuke a gidanmu ,
I don't even know why the fuck you're here ,
I mean this place ain't for low life's like you so gwanda ma tun wuri kitattara kiyi gaba saboda it
won't be fun,
Poor ass kid*
Ya na gamawa ya juya zai fita,
Cikeda bacin rai tace ,All I know ban taba maka abunda zaka tsaneni ba but kasama kanka
tsanata and yakamata ka sani nima bani nasa ma kaina ba , Allah ne ya ke so ya gani haka
,kuma koyaya yayi dani ina gode masa a kullum,kuma ai da muke masu aiki yafi masu sata
tunda halak muke nema ,
So yanzu ma kaje ka faɗa musu muna aiki a gidanku kaga idan zan mutu ne,
Juyowa yayi yana wani murmushin rainin hankali yace "dama ai talakawa are always preachers
kuma babu ne ke sawa ,
Nidai kar kice ban maki warning ba,
Yana kai aya a maganarsa ya bude kofar wanda take widad ta faɗo,
Tsaki yayi ya raba ta gefenta ya wuce,
Kallanta ta maida kan deenah wadda takaici ya tsaya mata a wuya tace"
Ke dan ubanki mene ya hadaki da azad ,and mai yace maki da har da kulle kofa,?
Sai dai in ubanki,
deenah ta faɗa tana mai rabawa ta gefenta zata wuce,
Damko shukun dake kanta widad tayi ta jawota baya da karaji tace "did you just said ubana?
How fucking dare you?
Ubanafa "
Hey eye"
Ubana ?ni widdy a fucking charity student ni kike faɗawa ubana,
You're dead! bitch,
Mari widad ta kaiwa deenah a fuska wanda tana kokarin ramawa saboda yarda ya gigitata taji
an ririketa,
Kokarin kwacewa take amma ta kasa sakamakon mutum uku da suka riketa,yan koran widad
,benazir,walida,hazal.
Duk inda zakaga widad zaka gansu,
Yaran masu kuɗine wanda still bazasu haɗa kansu da widad ba dan kudin mahaifinta bawai
kananan kuɗi bane shiyasa suke like da ita musamman da suka gane tana san attention.
Rike deenah sukayi gam gam widad ta fito da scissors ɗan karami a jankata ta kallesu tace
remove her beret tana bukatan warm welcome so Zan aske gashin kanta duka,
Dariya suka saka baki dayansu inda walida ta janye beret din tana mai fadin "what a waste
yanzu wannan uban gashin za a yanke,
Wani side smirk widad tayi tace "idan mai saurin fitowar gashice ai babu dadewa wani zai tofo
amma for now wannan sunansa waste "
Wani ihu deenah tasa lokacin da widad ta rike jelar shukun dake kanta zata aske"
"The hell is going on here?
Muryar mss suraj ta karaɗe sketching room din,
Licking lips widad tayi ta rufe almakashin tana mai faɗin "
What a bad timing,
Sakinta sukayi baki dayansu inda widad ta rungumeta Tana mai shafa bayanta tana cewa"ke
kam bakisan wasa ba ,it was only a joke and a funny one ,
A tare dukkaninsu suka sa dariya inda suka marawa widad baya wadda ta rigasu fita cikin wata
takama,
Takowa ciki mss suraj tayi ta duka ta dauko beret din deenah tace "
Indeed the joke was a funny one I see "shiru deenah tayi batace mata komai ba illa hulanta da
ta karba ta dora akai tana mai faɗin. "Thank you ma".
Rike kafadunta biyu tayi tace "what i said earlier in the office still counts ,
You talk and I listen okay".
Kada kai deenah tayi tace "thank you ma,
Dafata tayi sannan ta juya tafara tafiya inda deenah ta rufa mata baya tana tunanin yanzu da
sun yanke mata gashi fa,
Dafa kuncinta tayi tana tunanin marin da widad din ta mata ,
Dafata taji anyi ta baya ,juyawa tayi dan ganin wanene,
Wata kyakyawar yarinya ce cikin uniform ,
Murmushi tamata kana ta mika mata hannu tace i'm sabreena ja'afar ,ss1B
I saw you in mss suraj 's office earlier ,the new student right?
Mika mata hannu deenah tayi tace yea"
I'm Deenah Othman ali.
Murmushi mai kyau sabreena tayi tace"bamu class daya but i like you and inasan ki zama friend
ɗina,
Nervously deenah tace "to "dan bama tayi tunanin taji hausa ba,fahimtar rashin sakewar da tayi
ne yasa sabreena ta rike mata hannu tace "its not like me nace inasan wani da ƙwance but I just
like you and nasan you will make a good frnd and i need one ,so let's take it slow and we will get
to know each other ,but first let's exchange digits, Wayanta ta ciro cikin yar karamar golden fancy bag din dake sakale jikinta,
"
I don't have a phone"
Deenah ta fada ba tareda taji wani abu ko kunya ba wajen faɗan hakan,
Maima zatayi da waya a shekarunta tasan mami bazata taba bata waya ba in har ba makaranta
ta gama ba,
Dan kallanta sabreena tayi tace its okay ,
Sai a wannan karan ne deenah tayi mata murmishi,
Tare suka taka da deenah har ta rakata bakin class dinsu sannan ta wuce nasu,
Duka ranar haka nan dai tayita tana tunanin yarda zata yi rayuwa a haka dan a yau kadai ta
gane abun ba karami bane ,yakin babba ne .
A gajiye ta koma gida da yan transport din da maminta ta bata ,
Mama