Showing 15001 words to 18000 words out of 65850 words

Chapter 6 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf

Advertisement

02 Aug 2025

2681

tayi tana mai murmusawa,
Yana kokarin binta yaji muryan binyamin da ya tsinci duk abunda ya faru yana mai faɗin maike
faruwa anan,
Gyara mood ɗinsa yayi yace bro nothing kawai muna maganane,
Dan kallansa yayi kafun yace oh okay ,
Kafun yabar gurin yana mai tarayo abinda ya faru a kansa.

Babu wani fargaba deenah ta kutsa kanta gurin ,
Take waɗanda suka santa suka fara kus kus kus musamman da aka ganta da drinks ta fara
serving ,.

Attention"
Muryan widad ya karaɗe gurin ta mic ɗin dake gurin,
Kowa yamayar da hankalinsa gareta dan sunsan its something big,

Folding hannaye deenah tayi tana mai kallan widad,
Cigaba widad tayi tace inasan kuyi welcoming maid ɗinmu ta yau and trust me y'all gonna be
shocked cos I was too,
Meet deenah othman ali,
a maid and a daughter of a maid in the maikudi's mansion,
I know Lotta you are curious to know who she be"
So here I am telling y'all who she be so enjoy your party in the company of Deenah the maid,

A take gurin ya kaure da dariya kowa yana faɗan albarkacin bakinsa ,
Ita dai deenah bata ce komai ba illa murmushi da tayi ta cigaba da aikinta dan ko kaɗan bataji
zafin abun ba a zuciyarta,

A hankali kowa ya cigaba da al'amuran gabansa inda deenah kuma ta cigaba da kai kawo
wajen serving nasu,
Kiran sunanta widad tayi tana mai faɗin"maid deenah"
Dago kai tayi ta kalleta ,
Alamu widad ta mata da hannu kan tazo,
Mama kaltu ce da shigowanta kenan tace deenah oya maza je ki kamar widad ke kiranki inajin
tana san wani abu ne ,dan Allah maza kar muyi abunda hajiya zatayi complain ,bari naje na kai
wannan empty tray ɗin a Karo snacks ɗin nan,
Babu musu deenah tace to ta nufi gurin widad,

Kawo mun pizza ɗinchan,
Kallan pizza ɗin deenah tayi taganta tama fi kusa da widad ɗin ,danne zuciyarta tayi ta karasa ,
Tasa hannu ke nan zata ɗauko plate tasaka slice ɗin pizza ɗin akai widad ta sa mata kafa ta
faɗa kan table ɗin dake kunshe da snacks ɗin sai kuwa kanta ya shiga cikin bowl din ice cubes,
Dagowa tayi cikin fushi ,wani takaici na mata yawo a wuya musamman ganin yarda su hazal ke
mata dariya wadda na kusa da su ma suka dauka ,
A take zuciya ta kwashi deenah ta dauko glass cup dake dauke da grape juice ta watsa a jikin
milk gown din dake jikin widad bugu da kari kuma ta dauke ta da wani gigitaccen mari tace "
Wannan bashin da kike bina ne na biya ki na marin da kika taba mun and insan ki sani nan ba
makaranta bane ,
Duk abunda suke a idanun azad wanda hankalinsa rabi yana kan deenah inda daya bangaren
kuma abokanansa suka rikesa da wani abun daban ,
Bai aune ba sai gani yayi sun kaure da faɗa inda widad dake kuka ta hankaɗa deenah cikin
pool ɗin dake gefensu,

Wani irin ihu deenah tasa jinta tsundum cikin ruwan tana mai faɗin help me i can't swim"

Ai kamar me suka fara mata video dan kamar larurar su kenan a ga wallenka a dora ka a
media,har saida ta yi kasan ruwan babu wanda yayi kokarin kaimata dauki cikinsu dan su abun
dariya ma ya basu wai bata iya ruwa ba,

Gudu da karasowar azad zuwa gurin yayi daidai da faɗawar binyamin cikin ruwan ,
Dif gurin yayi lokacin da binyamin ya fito da ita dauke a hannunsa ,

widad ya bawa wani kallan banza kafun ya maida kallansa kan Azad wanda shima yake dauke
da fargaba har a lokaci yace "azad ka biyoni,
Babu musu azad ya mara masa baya inda shi kuma yake dauke da deenah a hannunsa .


CHUCHUJAY

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA

11

Kai tsaye part ɗinsu yayi da ita azad na biye a bayan sa zuciyarsa babu daɗi,
Allah yasa ammi bata gidan dan haka ya ajeta a babban falon dake gidan ya maida kallansa
kan azad yace,je kira ihsan ta taimaka mata,
"Eh brother I guess tana bukatan mouth to mouth ne,
Rike kugu binyamin yayi yace ina shi yasa nace ka kira ihsan ta taimaka mata ,ko kuwa ni ko
kaine wani zai bata sai naji,
Bai kara wani musun ba ya nufi cikin main gidan dan kiran ihsan,
Abubakar ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ,
Kallo ɗaya yayi masu ya dauke kai zai wuce"

Kai zo nan"
Babu musu ya taka dan amsa kiran yayan nasa ,
Allah yayisa mutum mai ɗan banza miskilanci shiyasa baya shiga sabgar kowa dan magana ma
shi bawai ta damesa bane,

Mai ya haɗa yayinyar nan da waccan mai kama da mayun"

Licking lips ɗinsa yayi kana yace "bro how should I know,
Widad is always a bully ita nature nata ne so about deenah bansan mai ne tsakaninsu ba 
maybe you should ask azad shine dan ajinsu"
Yana rufe baki su ihsan na saukowa inda take faɗin yanzu shine babu wanda ya ko pressing
mata chest ta ne cos ta sha ruwa ne kuna so ta mutune ".

Dan tsaki binyamin yayi yace "da muna so ta mutu da baki ganta ba a nan and last i remember
she's not our muharamma so why should we touch her boob's ?
Spare us the doctor shit and tend to her  .

Karasowa tayi tana mai bata tamaiko ta hanyar pressing mata chest ɗinta kafun tace "
Last I remember bro bance kutaba boobs ɗinta ba,
Tsaki yayi yabar gurin yana mai cewa azad ya biyosa wanda ya rasa dalilin da yasa yayanasa
keta umartarsa da ya biyosa ,
Sai da sukaje compound ya kalli azad din da serious face yace "
What's going on"

Sniffing azad yayi yace brother idk how to put it amma deenah tana shan bullying hannun su
widad saboda status nata ,so yau ne widad ɗin tasan deenah suna aiki a gidannan ne so shine
da faɗa ya shiga tsakaninsu deenah din tayi backfiring which she never did".
Shiru binyamin yayi yana mai jin wani bakon lamari a cikin zuciyarsa dangane da abunda azad
din ya fada masa amma lokaci ɗaya ya danne abun ta hanyar faɗin ,idan da kwadayi ai da
wahala mai yasa bazasu zauna a matsayinsu da Allah ya sasu ba ,
Allah ya taimaketa i was fast da tuni ta mutu kaga karshen kwadayi kenan,
Imagine bata iya swimming ba,tsaki yayi yace "Allah ya kyauta kana ya bar gurin.

Binsa da kallo azad yayi yana mai jin rashin dadin abunda binyamin din ya faɗa,
Juyawa yayi dan komawa yaji halin da deenah ke ciki,
zaune ya tarar da ita jikinta lullube da abun rufa wanda ihsan ta dauko mata bayan ta bata dry
riga tasa,hannunta kuma dauke da coffee mug,
Zama yayi gefen ihsan dake faman mata sannu yace deenah sannu,

Kaɗa masa kai kawai tayi bata ce komai ba ta cigaba da sipping coffee din,
Ina big Bro din?
Ihsan ta tambaya tana mai kallan kofa,

Ya wuce.

Oh kajifa yayi saving nata yakuma tafi big bro nada moods kaman wata mai ciki,
Shiru deenah tayi tanasan fahimtar abunda suke faɗa wanda zuciyarta ke san karyata mata ba
binyamin ne ya taimaketa ba,
Sallamar ammi ce ta katse musu maganar da suke,
Turus tayi ganin su zaune sunsa deenah gaba,

Lapia mai mai'akin nan mara ɗa'a take yi a falona kan kujeru na ,tashi maza tashi tafaɗa tana
mai takowa cikeda ƙyama ,
And uban wa ya bata cup ɗin binyamin take shan abu a ciki,
Fizge blanket ɗin tayi ,baki ta saki ganin rigar ihsan jikinta,
Gabansu ihsan ta shiga tace "
Ammi please tafada pool ne shine big bro yayi saving nata ya kawota gurina  and ta jikine so na
bata rigana ta cire jiƙaƙƙun,.

Cikeda balai ammi tace aikuwa sai ta cire a kona dan wallahi bazata jawo maki talauci ba dan

saka rigarki da tayi tsiya zata iya raɓarki,
Kama rigar tayi tana kici niyar yagawa inda ihsan da azad suka hau kiran sunanta akan tayi
hakuri,
Kuka deenah tasa ganin ammin na neman mata tsirara,

Hankaɗqata ammi tayi bakin kofa da karfi wanda ta faɗa daidai kafar binyamin da shigowarsa
kenan,
Dago kai deenah tayi cikin kuka ta kallesa Tana mai rike gaban rigan da ammi ta fara yagawa,
Hannunsa sanye cikin aljihun wando ,cikin nutsuwa ya kalli amminasa kafun ya maida kallan
kan deenah yace"
Ke tashi ki bace mun a gurin nan,
A kidime ta kallesa ,
Wata tsawa ya buga mata akan ta tashi ta fice a gurin,
da gudu ta tashi ta fice a gidan tana kuka,

Kallan amminsa yayi yana mai takawa gareta,
"Ammi please maine kikeyi haka ma yarinyanan salan ta rainaki cos kinsan yaran talakawan
nan da rainin tsiya ,
"Nayi din ka dakeni kaji ubana"
Munafiki kana zaginsu kana taimakonsu ,
Natsani yarinyannan ,wallahi da ace a karkashina take da tuni abicinta ya kare a gidannan
,shegu irin maita,tana kai ayar zanceta ta wuce sama tana mai jin zafi a ranta dan a wuya take
dasu deenah tun abunda ya faru .

Barin gurin binyamin yayi ya nufi sashensu inda azad ma ya fita agida while ihsan Ta bi bayan
amminsu .

Bangaren deenah kuwa tana fita kai tsaye bangaren su ta nufa,
Tsaye tayi bakin kofar ɗakinsu tana mai saisaita kanta gudun kar maminta ta fahimci tana da
damuwa,taji dadi da ta tarar mamin na bacci dan haka kai tsayee ta bude wardrobe ɗinsu ta ciro
doguwan rigarta ta material tasaka ta cire ta ihsan ta tura can kasan kaya.

Washe gari bayan ta gama tattara musu ɗakinsu ta kalli maminta wadda taji sauki tace mami
bari naje sashen hajiya kaka,
"To sai kin dawo nima bari na tashi naje na dan kakkama aikin da ya rage".

"Mami Ki bari na dawo sai na yi ai tunda jikinki ba wani dadi.

Tashi mamin tayi tana mai faɗin"bari kiga je abunki ni da kike gani haka kwana daya nayi ban
aikinnan ba ji na nayi duka ba dadi yanzu kuma Allah ya bani lapia ai sai na koma kan aiki ba,

A tare suka fita ,

Tun a bakin sashen hajiya kakan take jiyo dariyar ihsan tana mai faɗin "wallahi grandma da
sake ban yarda ba .
Sallama tayi bayan ta nemi izini ta shiga falon,
Zaune hajiya kaka take a kujera ta mimmike kafafunta ihsan na kasa tana matsa mata inda
binyamin ke zaune yana mai daddana wayarsa kamar ma baya jin hirar da suke

Gaidasu deenah tayi inda hajiya kaka tace ma ihsan"
Tashi dama ba wani iyawa kikayi ba gaba daya yaran gidannan baku wani iya tausa ba amma
deenah kuwa hannunta Allah ya sa masa albarka"

Oh grandma ma Deenah zata school ne zakiga mai danna maki tsohuwar kafar nan taki .

Ita dai deenah babu abunda take sai murmushi inda rabin hankalinta na kan binyamin wanda
still hankalinsa na kan wayansa ,
'Yaya bilya ina kwana,
Ta tsinci kanta da faɗa,

A hankali ya dago idanunsa ya dora akanta da mamaki,
Dariya deenah da hajiya kaka suka saka,
Aje wayan yayi a cinyansa yace ke zo nan.
Matsawa tayi gefen hajja dan ita tama saba da bilya din
nan and batasan lokacin da ta faɗa ba,

Ganin ta makale ma hajiya kaka ne yasa yace "
Hajja ki jama yarinyar nan kunne Allah ta fita harkana,
Kar kuma ta sake cemun bilya ko wani yaya cos we are not related Zan zaneta wallahi,

Kallansa hajiya kaka tayi tace yo wai ni da kike ta kumfar baki ne akan wannan bilya din nace
sunanka ne ,mene na damuwa kuma yaya ai girmane aka baka,

Daga chan bayan deenah tace yo ni hajiya idan ma baisan yayan sai na bari na koma yallabai
bilya ai ,kuma ni dama godiya zan masa akan taimakon da yayi mun jiya,
Wani tukukin takaici yaji jin ta kara dagula masa suna wai yallabai bilya ,
Bai bi ta kanta ba ya tashi ya fita dan muddin ya tsaya zai iya sabama hajja ma ba deenah ba
cos yana balain jin haushin bilya ɗinnan da take kiransa dashi ,in general ma shi baya san tana
shiga masa harka saboda dalilai da dama.

CHUCHUJAY.

ƘALUBALENAH.....

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA

12

✏CHUCHUJAY

kallan kallan da kananun maganganun da ake binsu dashi wanda a yanzu ya daina damunta
shine a yanzun ma ake a cikin babban cafe ɗin dake cikin makarantar ta orchid ,
Gyara zama deenah tayi tana mai kallan azad wanda da naci saida ya samu guri a gunta,
azad your a** girlfrnd is coming this side control her,
ɗaga kai yayi ya hango widad wadda ke takowa garesu cikin wata irin isa da takama ita a dole
isassa gefenta kuma babban abokin azad ukasha wanda ba ajinsu daya ba amma lokaci guda
ya zama kamar ɗan ajinsu saboda deenah daya darsa idanunsa akanta,
Sabreena ce dake zaune kusa da deenah tana sipping coffee tace i don't like this ukash,

Rufe bakin sabs ke da wuya suka karaso gurin inda widad ta ja kujeran dake kusa da azad ta
zauna tana mai rike hannunsa tare da faɗin baby kana tare da maid ɗin gidanku tana serving
naka kenan"
Its a good thing ke tashi ki karbo mana two sandwich da two milkshake,
"Widdy don't start this rubbish please ke baki gajiya da abu ɗayane,
So what idan suna aiki gidansu azad ba sata suke ba and beside the dude doesn't mind calling
her his friend you bitch"
Sabs ta faɗa tana mai buga container ɗin da take shan coffee ɗin aciki.

Cike da bacin rai widad tace sabs please this is not the first time da kike mun haka akan low life
ɗinnan as if ba ni dake ne yan uwa ba ,
Bana so and ina tabbatar maki akwai lokacin da zata ɗasa maki dafinta lokacinne zaki gane
batayi worthing time naki ba,

Widdy im here remember and kinsan yarda nake ji kan deenah so please stop insulting her"

Kasan cewar tasan mai suka kulla da ukasha yasa bata sake magana ba ta juya ga azad
wanda har a lokacin baice komai ba,
Hannunsa ta rike a karo na biyu ,
Bai kwace ba kuma baice komai ba amma gaba daya hankalinsa yana kan  ukasha wanda yake
ta faman kallan deenah yana wani irin smirking while ita kuma hankalinta ma gaba daya yana
ga kan littafin da azad ya gama mata tutor,
Saukar hannun ukasha a waist ɗinta shine abunda ya dago da idanunta da hankalinta daga kan
littafin,
Marin da ta dauke sa dashi sai da ya jawo hankalin daliban dake gurin,

Tashi tayi tace"next time kaji sha'awan kara tabani kayi tunani,
Sabs let's go,
Azad sai mun hadu class nagan kana da bakuwa,
Gaba tayi sabs na biye da ita ,

Suna fita sabs ta kece da dariyan da ke cinta tana mai faɗi"
Girl that was fast ,kinga idanun shege kuwa,
I just love you more Dama inajin haushin yaranan bana kaɗan ba shege mayen mata,

Dariyar deenah ma tasa "
Daina sani dariya sabrina na tsani yaran nan tun tuni dama and tunda na gansa da widad nasan
ba alkhairi bane and i promise my self bazan kara bari wani ya takani ba a cikin makarantar nan
and it started tun a lokacin da na mari widad a party ɗin azad kuma wallahi dai dai nake dasu,

"Haka yake ta gurina na tsaya maki and a wani side din ga oga kwata kwata azad like abun
kamar jazz this boy just fall over hills,.

Eh ehn fall from wey bari mana we are just friends so run to your class Kafun mr long nose ya
hana ki shiga,

Duba agogon hannunta tayi tace God namanta fa shi ne last period omoh God is so kind da ya
bani bestfrnd like deenah ,kissesss muah muah take care,tana kai karshe ta ruga da gudu .

Kaɗa kai deenah tayi tace sabs and her issues ,
Tana kokarin bin hanyan nasu class ɗin tajiyo muryan azad yana kiran sunanta ,
Tsayawa tayi har saida ya karaso kafun tace "
Ya naganka kai kaɗai ya kamata ka tsaya gf ɗinka ko ka goyota tunda its a common thing a
gurinku rich kids,
Dan murmushi yayi yace you shouldn't have slapped ukash,

Bata rai tayi tace oh dama ai nasan you're with them and you're just pretending to be my friend
so karama masa mana since he is your best frnd,
Tana kare zancenta ta wuce ta barsa ba tareda ta saurari kiran da yake mata ba.
Fingers Ɗinsa yasa cikin sumansa yace "oh deenah that was not what I meant,
Bin bayanta yayi dan shiga ajin wanda already malami ya shiga,

AFTER AZAD'S PARTY.

Ranar monday da ta shiga makaranta bayan partyn azad abun babu daɗi cos duk inda ta juya
sai ta samu masu tsokanarta ko masu toshe hanci wai tana wari,
Tun kafun ta shiga class taga desk and chair ɗinta a babbale a bakin stairs,

Baga maza ba baga mata ba kowa da abunda yake cewa akanta karma ace yan koran widad,
Locker ɗinta na changing room ma haka ta gansa a balle kayanta na ciki ansa scissors an
yayyankasu ,gaba daya ta shiga confusion shin mene tayi haka na zunubi da suke treating nata
haka

A ranar ba karamun faɗa akayi ba tsakanin azad da wani classmate dinsu victor wanda yafara

bude mata ruwan flour tun daga ka akan wai shine aikinsu ,
Sosai azad ya fusata wanda baisan lokacin da dambe ya kaure tsakaninsu ba,
Yana wannan faɗan da victor a babban harabar makaranta benazir ta jefe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login