Showing 60001 words to 63000 words out of 65850 words

Chapter 21 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf

Advertisement

02 Aug 2025

2679

ammi da tafi kowa Baki Tayi tace"tanan kuka bullo kuma kenan,sai ku faɗa muji wake da
shi.

Cike da fusatar rainin wayan da Ammi ke masu uncle sultan yace Gashi nan ɗanku zaune
binyamin ku tambayesa.

Binyamin?

Baki ɗayansu suka haɗa Baki wajen faɗa.



CHUCHUJAY.

KALUBALENAH

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

37

Na
    CHUCHUJAY

....kuresa sukayi da idanu dan san jin abunda zaice karma ace amminsa da mahafinsa wanda
yake mutum Mai karancin magana.

Kasa yayi da kansa yace "bansan deenah nada ciki ba ,amma indai tana dashi tabbas nawane
and kamar yarda ta faɗa cikinta ba shege bane dan Halak ne ,haka yake ,deenah mata tace.

Wani irin duka ammi ta kaimasa tana Mai rafta Salati tace "ubanka ,ni zaka ma tonan silili .

"Ibrahim control your wife "grandpa ya faɗa .

Jin muryarsa ba wasa yasa Tayi shiru tana tafarfasa ta ciki.

So muna jinka"

Eh grandpa ,nida deenah munyi aure a gwagwalada gurin wani malamin su ammar babban
limamine Sannan da abokinsa Malam harisu shima shaidane ,ammar da ihsan ma shaidane ko
ihsan,

Kaɗa kai ihsan Tayi tace "eh anyi haka grandpa dani akaje sannan a gabana aka daura auren.

Mai yasa kayi haka binyamin?
Kana tunanin idan kace mun kana san deenah zan hanaka aurenta ne?

Bana kinta ,hakazalika kakarka deenah tana cikin mutane mafi soyuwa  a duniyarnan,mai yasa
kayi gaban kanka ka yanke wannan danyen hukunci?

Kara kasa yayi da kansa yace "Grandpa naso faɗa maka amma nakasa saboda ammi ta mun
katanga da hakan,
Ammi tasan ina san deenah amma ta dage akan ba haka ba ,karshe ma cemun tayi idan na
kuma maganar inasan deenah zata bata mun Sannan idan na kuskura na maku magana akai
zata tsinemun dole nayi shiru,
Nikuma grandpa Allah ya sani inasan deenah bazan kuma iya rabuwa da ita ba ,shiyasa da
mukayi magana da ammar yamun Suggesting auren wanda gudun aikata barna yasa mukayi
hakan amma ba dan cima ko daya daga cikin dangin mu mutunci ba.

A lokacin dana tafi Belgium dama mun gama magana ne akan idan na dawo zamu sanar
daku,to nasan abunda ya sa deenah bata faɗa maganan cikin nawane ba ,sannan nikuma
bamu getting in contact saboda i was sent to prison na 2 months for violating rule na garin
wanda ban sani ba, It was just two months shiyasa ban faɗawa kowa ba,
Ana sakina na dawo gida ,grandpa kuyi hakuri nasan ban kyauta maku ba amma bazan iya
hakura da deenah ba haka zalika bazan iya daukar tsinuwar ammi ba.

Shiru gurin Ya dauka,kowa a gurin da akwai abunda yake cikin zuciyarsa kar ma ace ammi da
aka hana magana alhalin akwai magana tsababa a bakinta,

Daddy ne yace "to kajifa Alhaji abunda ya faru ,ada nayi tunanin shima zai ce ba cikinsa bane
sai kowa ya kama gabansu mu murike abunda ta haifa mu nema mata saki ko yace babu aure
tsakaninsu,amma tunda abun yazo da haka to kaga Ai Alhamdulillahi kaga sai muje gurin shi
wancan liman ɗin mu tabbatar da eh ya daura wannan auren sai azo muyi musu addua ,koya
kace.

Haka yake wannan Alhaji"wato ina mutukar godewa Allah da ya zama aure sukayi ba aikata
alfasha ba saboda ina Mai tabbatar muku rabon nan dake jikinta dole ya fita koda basuyi aure
ba ,saboda shi rabo lokaci yake bi amma da yake Allah a tsarkake yake san wannan rabon sai
ya basu dabarar yin shi wannann auren,sannan ke mardiyya da kece mai babban kamaso a
cikin sa ,
Kafun kuma na manta inaso yanzu ba sai ajima ba ki nemi yafiyar ita maminta ,

Da zumbure zumbure ammi ta bama mami hakuri wanda grandpa yace baiyyi ba da sincerity
yake san tabata hakurin,
Haka nan tabata ta Tashi tabar dakin inda suka cigaba da tattaunawa akan abunda ya kamata
,ciki har da yanke shawarar zuwa sanarwa da ahalin gidan marna ,a cewar daddy ya hallata su
Sani.

A haka suka tafi deenah bata bari sun haɗu da binyamin ba Duk yarda kuwa yaso,

Bayan komawar su gida ne deenah ta nufi dakin Mami wadda tunda suka dawo bata fito ba,
Zaune ta sameta gefen Gado tana danna waya,
Zama tayi Gefe da ita tace "Mami dan Allah ki daina fushinnan dani ,idan ma kikace na rabu
dashi Allah zan rabu dashi indai baki so ,amma wannan fushin naki yana Sani cikin wani yanayi,

Aje wayan Mami Tayi ta kalleta da tsantsan kulawa tace"deenah ni bubu abunda nake so sama
da farin cikin ki ,ni ba Wai ina kin binyamin bane ,ada nayi tunanin zai amfani dake ne kawai
sanin halin masu arziki amma Na fahimci ba haka yake ba,
Kawai ni abunda ya dame Ni shine auren da kukaje kukayi a boye ,amma a ko yaushe mu gode
ma Allah,a yanzu ni na amince da aurenku kuma nasaka maku albarka .
Rungumeta deenah tayi tana Mai jin san maminta nakara shigarta ta ko ina,

Dakin farouk ta nufa Kai tsaye,bata samesa ba so ta wuce dakinta ta dan huta ,

Tana shiga ta ga missed calls nasa a wayanta har 13,
Jitayi kamar ta kirashi amma wata zuciyar ta haneta saboda bata shirya fuskantarsa ba .

Kamar yarda su daddy suka shirya suka dauka hanya Baki dayansu mazan dan zuwa
gwagwalada daga nan kuma su wuce kan tudu,

A lokacin da sukaje harda daddyn ammar da ammar kansa inda nan malamin ke kara tabbatar
masu da hakkun shine ya daura musu aure, sannan ya kira malam harisu wanda yake shine
shaida ta bangarensa,

Daga bisani suka wuce nassarawa ,gidan yana nan ya kara lalacewa amma hakan bai hana
daddy gane gidan ba dan babu ma yarda,za'ayi ya manta wannan gida,

Kishingiɗe suka tarar da kabiru wanda kallo ɗaya daddy ya ganesa,
A zabure ya Tashi Ganin arnan motocin da suka faka a kofar gidan ,cikin kankanin lokaci yara
suka fara taruwa kallan motan.

Sallama suka masa ,kalle kalle kabiru yafara yana san tabbatar dashi suke ko kuwa da wani a
bayansa ne,
Dashi din suke ,
Washe hakora yayi yana mai fadin"barkanku da zuwa saraki,ina fatan dai ba idirisa bane ya
kara jawo mun wata fitinan ake nema na ba.

Abban binyamin ne yace"A'a bawan Allah wannan zuwa namu zuwane na alheri ba sharri ba,

To to mushiga daga zaure,cikin gidan ya shiga yana mai kwalama idirisa kira ,Rabiatu ce
kanwar deenah wadda a yanzu ta zama budurwa ta fito da manyan tabarmi ta shimfida masu,
Yarinya Mai tarbiyya a gidan marna,da ladabi ta gaidasu inda suka zazzauna a babban soran
dake cikin gidan marna ,
A Dan gefe Kabiru ya zauna yana mai rarraba ido dan kwarjinin arzikin da suka masa ,

Kara gaidasu yayi yana Mai faɗin ina wuninku ,sai dai Har yanzu ban waye ku ba.

Grandpa ne yayi gyaran murya yace "t o munzo ne dai akan diyarka,

Da sauri yace "hala wannan tambadaddiyar Yarinyar salima ,"oh ni kabiru dan Ali marna wanne
irin balaine haka yake ta bibiyata shekara da shekaru naki samun sassauci,
Hala wani ta damfara cikinku.

Daddy wanda Har a lokacin bai magana bane yace"nasan baka gane ni ba ko,

Inafa zan gane ka ranka shi dade ,ni banma taba ganinka ba ,inama nake da kimar da zan
shiga cikin masu kuɗi irinku,Ai mukam sai dai mu dinga share inda zaku taka,

Dan murmushi daddy yasa yana Mai tuna tsageranci irin na kabiru ,"Alhaji Ali marna fa daddy
ya tambaya.

Matsar kwalla kabiru Ya fara yace"kabari Kawai ,bari tuna min ,Ai baba Allah ya dauki abunsa
shekara biyu kenan,gani nan dai ya mutu ya barni cikin masifa,shegen cin bashi irin na baba
kuma shine silla,Dan duk wani abu da ya bari a biyan bashi yakare,Allah ma yasa imani ya
shigeni an biya din da tuni yana chan yana fama da malaikun kabari suna chudarsa ta ko ina, Yanzu kuna kallona aljihuna babu ko ƙarkarfana,ga jarabtar ƴaƴa ,nan Salima ciki biyar ta
zubar,nan idirisa kaninsu bashi aikin komai sai shaye shaye da daba,ga mahaukaciyar mata
tsinanniya itama ,rabi ce kawai yar zo in nuna.
Allah alhazai watarana jinake kamar na gudu,

Dan murmushi daddy yayi Yace "hakki kenan.
Kasan shi Alhaki dan kuikuyo ne ..duk inda yaje ya dawo zai sameka har inda kake,
Nasan baka tuna ni ba amma Ni bazan taba manta ka ba,sunana Alhaji NA'ABA,
Mahaifin matar dan uwanka marigayi OTHMAN ,Maimuna,
Nasan Yanzu kan tuna,

Take kabiru ya duburburce ,

Kwantar da hankalinka ba faɗa ya Kawo mu ba"uncle sultan yafaɗa.

Ba faɗa ya kawomu ba "Daddy ya kara maimaitawa,munzo ne akan baku hakkinku a
matsayinku na dangin mahaifin deenah.

Deenah?wacece deenah?kabiru ya sake tambaya a hargitse .

Deenah dai diyar maimuna wadda ta haifa ka mata kurciya ta barta gidannan a lokacin dama
bata san kanta ba,

Deenah dai diyar zainaba da kuka ma sharri kuka koresu daga gidanan ,ita nake maka magana,

Deenah ɗon nan da nazo nan inasan ku bani ita kuka shaida mun ta mutu alhalin bata mutu ba.
Tana nan hannun a halinta masu arziki da suka gaji arziki,

Nuna su grandpa yayi yace wannan Kuma sune dangin mijinta kagansu suma babu tsiya a tare
dasu,
Kalla nan, "ya nuna binyamin yace "wannan kuma shine mijinta Kagansa dai bashi da wata
makusa .
To munzo ne mu sauke nauyi mukuma shaida maku mun aurar da ita mu sauke nauyi,
Ga alewa chan da goro munzo dashi masu yawa ku raba ma kowa ku shaida masu DEENAH
Tayi gaba Har abada.

Kuka kabiru yasa wiwi yana ma faɗin"Allah na gode maka da kasa irin othman na nan a doran
kasan
,da ace deenah ta wulakanta inajin adadin balain danake ciki da yafi haka,
Allah sarki zainaba ,mutuniyar kirki,ina zan ganta ta yafe mun,
Wallahi alhaji komai ya faru ladi ce tana nan tana fama da hauka tuburan a daki ma aka kulleta
,a kullum idan abun ya Tashi zakaji tana tona ma kanta asiri na irin asirin da Tayi ma maimuna
da othman,wasu abun ma baka gane mai take cewa ,kullum maganar ta ita Yar wuta ce.

Waiyazubullahi"Suka hada Baki wajen faɗa,
Haka nan kabiru yake ta nema yafiya musamman ta deenah da zainaba da ya cinye musu gado
saboda san zuciya .
Koda zasu tafi saida suka haɗa masa kuɗi Baki dayansu dan baka rama mugunta da mugunta,

Kafin kace mene gari ya dauka DEENAH ta zama mai kuɗi

CHUCHUJAY ✍


KALUBALENAH.

NA
CHUCHUJAY✍

SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

38&39.

Bayan dawowarsu daga gidan marna aka sake zama inda iyayen suka bukaci Deenah da
Biyamin su zo,

Tunda tazo bata bari sun haɗa ido ba,
Bayan sun zazzauna ne daddy ya kalli Deenah yace "Gdota ina san na tambayeki,
A lokacin da kika auri binyamin ina fata ba dole yayi maki ba,

Kasa tayi da kanta tace,ba dole yayi mun ba Daddy da amincewa ta,

Alhamdulilah".

To Yanzu kina san shi kenan zaki zauna dashi ko kuma a raba auren,

Shiru tayi na wani lokaci wanda hakan yasa zuciyar binyamin tsinkewa dan tsoransa ɗaya tace
a raba aurensu ,yana jin zai mutu ne,

Dago idanunta tayi ta sauke cikin nasa ,wani marairaice mata yayi ,
Dauke idanunta tayi tace "daddy ina san shi ,

Alhamdulilah suka haɗa Baki wajen faɗa.

Hajjo ce tace to Yanzu dai kamata yayi azo Ayi shagalin biki a hade da baby shower sannan
kuzo ku danne kirjina dan dama na daɗe da sanin munafukar yarinyar nan zata mun haka.

Dariya suka Saka Baki ɗaya,
Bayan sun sallameta ne ya Tashi zai bita Abbansa yace "maza zauna ai bamu gama magana
da kai ba.

Koda ya fito already Yaji sun tafi ita da miminta daga Bakin hajiya fattu dan mimi gunta ta sauka.
Sanin ko ya kirata bazata dauka bane yasa ya shiga sashensu dan dauko key ɗin motansa ya
bita dan yau ko me za'ayi sai yayi magana da ita dan yaga alamun tana san haukatashi ne.

Yana shiga yaga ammi zaune wadda tayi zurfi cikin tunani,sanin zata iya zuwa bata musu daɗi
bane yasa ya wuce ta ya shiga ɗakin sa ya dauko car key ɗinsa,
Yazo fita kenan muryarta ta katsesa inda take faɗin"
Binyamin ni bani da matsala da DEENAH da talaucinta nake da matsala ,amma yanzu inajin
zuciyata zata sauya saboda naga ita ɗin irin masu arzikine ,kakanta fa Har net worth gare
shi,mahaifiyarta kuwa a cikin matan manya ma ba'a gasa da ita ,kai a gunta na fara ganin latest
channel xx bag ,a lokacin ni saida na yakice na iya siya wadda bata kaita tsada ba,Dan haka ni
bani da matsala a Yanzu.

Rintse idanunsa yayi dan Ya fahimci babu abunda zai faɗa ma ammi taji,
Dawowa yayi Ya zauna yace" ammina da mai kuɗi da talaka duk na Allah ne,kinga sai kiga kai
da kake da tarin dukiya ka shiga wuta wanda yake talakan futik ma kigansa a gidan Aljanna
mafi girma ,ammi Allah fa badan baya san bayinsa bane yasa yayi wasu masu arziki wasu
marashi, Wani arzikinsa silar halakarsa ne ma wani kuma talaucinsa ne silar kubutarsa,

Ammi dukkanmu mutuwa zamuyi ,sannan cikin kasa za'a buɗe a samu ,daga mu sai wannan
farin kyallen ,babu kuɗi ,babu gida,babu mota,babu gado,
Ammi imaninka ne kawai da aikinka zai kwaceka dan Allah ammi ki daina irin wannan halayyar .

Shiru tayi batace komai ba dan tasan koma Mai zatace ba fahimtar ta zai ba.

Na tafi ammi.

Sai ka dawo "shine abunda Kawai tace masa,

Kasan cewar a lokacin da zasuje gwagwalada su sukaje gidan daddy yasa yasan gidan,
Koda Isar sa gidan a waje yayi parking motansa,
Ya dade a waje yana Tunanin shiga ,

Brother in law?

Juyawa yayi jin muryar farouk a gefensa ,
Takowa farouk yayi da fara'arsa yace brother in law mai kake yi anan?
Ba shiga ciki zakayi Ba?

Durkusawa yayi dai dai tsayinsa yace"big boy how are you ?

Im fine brother in law.

That's cool big man
Sistern ka fa tana gida?

Dan sosa gefan Baki farouk yayi yace well"a lokacin da farouuukuuu ya fita tana girki ne to ban
sani ba ko tana gida,i dont even think tafita cos big sis is a home girl,zo muje ciki.

A tare suka shiga ciki ,mamaki Biyamin yayi daya ga sun bi back yard,
Bai dai ce mata komai ba yabi bayan farouuuukuu dan yaran doesn't fail to amaze him ,he likes
him.

Kofar kitchen ya buɗe ta baya ya shiga ,tsayawa binyamin yayi,
Juyowa farouk yayi yayi masa alamu da hannu kamar irin barayin nan sunzo gida sata basu san
akama su,

Tsaye yayi yana kallansa da mamaki da kuma san yin dariya,

Hannunsa farouk ya kamo yace "brother trust farouuukuuu you gotta thank me later,
Ka biyoni Kawai.

Babu musu binyamin yafara bin mysterious farouk,
Wani corridor yaga sun shiga,

Farouk where are you?
Muryar Adda ta karaɗe,

Jawo binyamin yayi suka laɓe bayan labule har adda ta wuce bata gansu ba ,
Tana wucewa ya fito da sanda yayi masa alamu da hannu akan ya biyosa,

Babu musu binyamin ya bisa kamar jela ,

Kofar daki suka tsaya,
Hannu farouuk yasa ya bude handle din ya hankada binyamin yana mai fadin take care
partner,you're safe here,

Kamar An kama barawo haka yayi a lokacin da suka haɗa idanu da ita ,
Buɗe baki tayi zata saka ihu Sakamakon towel ɗinta daya kunce amma kafun ta kai ga hakan
yayi wani super ya rufe mata baki yakaita bango,

Zazzare idanu tafara idanunta Cikin nashi,
Kasa dauke idanunta tayi inda suka zubama junan su idanu ,

Jin Ana kwala mata kira daga waje ne yasa Tayi saurin buɗe wardrobe ɗinta na kasa ta tura shi

ta mayar kana da gudu ta dauki towel ɗinta ,tana ida daurawa Mami na shigowa,

Kallanta Mami tayi tace Hala sai Yanzu kike fitowa a wankan.

A duburburce tace "um 'a'a.

Dago haɓarta Mami Tayi tace "lapiarki kuwa?

Kalau Mami "Mai kika gani .
Kalau nake Yanzu zan fito Shiryawa Kawai nake karasawa ,

To sai kin gama bari naje dama miminkice ta Kawo kayan da zaki saka na taron da za'ayi wani
satin shine nace bari nazo nakira ki ki gwada,

Zabura tayi sakamakon kafarta daya taɓa ,

Juyowa mami da ke shirin fita tayi tace "lapia?

Cockroach ne mami ya wuce ta ƙafata,
Dan kallanta Mami Tayi kana ta ce Allah kyauta maki wannan yawan tsoran naki na tsiya ,

Mami na fita ta karasa da saurinta tasaka key,kafun ta cire taji hannunsa a ƙugunta,
Hannu tasa ta bambare Hannunsa ta taka gun dressing mirror,
Tsayawa yayi a bakin kofar Ya harɗe kafaffunsa yana kallanta ,
Gaba ɗaya ta chanza tayi wani irin kyau ,ga hips ɗinta da suka kara buɗewa ,ga boobs ɗinta da
sukayi wani fum fum,

Daure fuska tayi ta Fara shafa Mai ajikinta,ganin ya kura mata idanu ne yasa tace "shin mai ya
shigo da kai ɗakina dan ga dukkan alamu ta barauniyar hanya ka shigo.

Ɗan murmushi yayi jin abunda tace ,karasawa yayi a hankali gareta yace"barawone ni wanda
ya shigo ta barauniyar hanya zai sace ki,
Juyota yayi ya kama hannayenta Ya matseta jikinsa har sai da Tayi gasping,

Kafun tace wani abu ya kama lips ɗinta da take kokarin buɗewa Tayi magana,
Butts ɗinta da suka kara girma ya kama wanda bata san lokacin da ta ɗane jikinsa ba Tayi
crossing kafafunta a waist ɗinsa ,
She really miss this man,
Sai a lokacin take dana sanin words din data faɗa masa a waya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login