Showing 27001 words to 30000 words out of 71253 words

Chapter 10 - YANCINA KO BUDURCINA COMPLET by Ummi Muhammad Usman.doc

keso nake kuma sangani irin na ganni acikin ahalina gani ga ummata amma kuma na kasa gayawa ya Aliyu ya taimakz ya kaini in ganta
Wunin yau duk a kasalance nayi shi kewar gida ke damuna da San jin halin da suke ciki dan abincin ranar da na girka kasa cinai sai masugadi na mik'awa na daren ma dana shirya kwata-kwata banji sha.awar cinsaba Ina kwance a kan kujera acikin falo Ina tunanin ta yadda zantun kareshi ya barni inje gida ta fad'o falon babu KO sallama na d'ago kai na kalleta ta watsan harara na kauda idona daga kanta batare da nace mata komai ba tai tsaki tare da shigewa d'aki nabi ba yanta da kallo sanye take da riga da wando wad'anda suka bayyana surar jikinta said'an yalolon mayafin data rufe tulin gashin dokin dake kanta na girgiza Kai cike da takaicin matar sunna tafita ahaka tunda nake bantab'a ganin haka ba sai a gidan nan


Tunanina ya tsaya sakamakon ganinta da nai akaina na dago Kai na kalleta tana tsaye rik'e da k'ugu ta ya tsina furka tana kallona tace ke kukun gidannan ki tashi ki shirya mana abinci a dinning dan my special yana hanya kuma kinsan yana dawowa abinda ze buk'ata kenan


Na tashi na nufi kicin batare dana ce mata komai ba danni ban d'auketa wata cikakkiyar me nutsuwa ba na shirya dukkan abinda nasan ze buk'ata na shige d'aki na kulle bandad'e da shiga ba naji tsayuwar motarsa a harabar gidan na d'an zuge labule kad'an na lek'a harabar gidan dedai lokacin daya gama parking ya fito shigar da yai tai mutuk'ar da cewa da jikinsa sanye yake da yankanti jar riga da bakin dugon wando hannunsa d'auke da farar rigar likitoce da jakar aiki tafiya yake cikin nutsuwa da kuzari na zuba mai ido ta tsakankanin labulan a gaskiya ya aliyu me kyaune tun ganin farko da nai mai na tabbatar da hakan gashi mutum me tsafta komai yai saiya burgeka na Saki ajiyar zuciya yayinda ya k'ulewa ganina na Saki labulen tare da jingina bayana da jikin tagar na runtse idona sakamakon jin danai wani Abu na yawo acikin jinin jikina


A hankali na furta ya ubangijina kada kad'oramin abinda bazan iya ba San mutumin dabesan Ina yiba be kuma damu daniba ya Allah ka....
Kiran sallah magariban da najine ya katseni na nufi banda'ki domin yin alwala subahanallah nace ganin jini ya biyo bayan fitsarin da nai kwata kwata na manta lokacin yin period d'ina yayi na d'auraye jikina na fito na nufi durowar da nake aje auduga domin in tsaftace jikina amma kaf na duba babu sai alokacin na tuna Ashe wancan watanma da tushu na k'arasa kwanakina dan haka na d'auki pant na koma band'akin sai kumame nan ma na tatda Ashe tushu d'inma itama ta k'are na zauna ajikin bathtub tare da dafe kaina da hannuna dan tunanina ya k'are bansan yadda zayi ba na tabbatar dai pant baze yimin komai ba koda zansa guda nawa bazasu dad'eba zasu b'aci ga dare yayi kuma bani da wani Abu dazanyi amfani dashi kuma bazan iya Aiken megadi ya suyominba koda dare beyiba tunanina ya tsaya akan inje insanar da ya Aliyu Ina San auduga nan ma naga Kai tsaye bazan iya zuwa insanar dashiba



Na fito daga band'akin bayan na sanya pant har hud'u na gyara jikina Ina tunanin yadda zanyi tunanina ya tsaya akan in rubuta mai a takadda in sanar dashi tunda bazan iya tunkararsaba na d'auki takadda da biro na zauna agefen gado na fara da rubuta.


Amincin Allah da rahamarsa ya tabbata agareka ya Aliyu ya aiki da fatan kadawo cikin k'oshin lafiya dan Allah ya Aliyu auduga ta mata nake so idan bazan takura makaba wadda nake amfani da itane ta k'are bansan yadda zanyiba kayi hak'uri idan nai kuskuren sanar dakai
Bissalam ka huta lafiya na karanta yafi so ak'irga sai naji uwa intashi inje in Kai masa saina fasa dan ganinake idan na kaimai tamkar zega rashin kunyata ne kiran sallhr danaji liman ya kwad'a na isha ne yasani zumbula dugon hijab d'ina na nufi falon dan gara in kai masa kada ya fita sallah ganinsa yaimin wuya


Na shiga falon da sallama suna zaune @kan carpet suna kallon labarai a tashar c n n Hindu na rumgume a gefensa sai faman shasshafashi take ya d'ago ya amsamin sallamar tare da zubomin manyan idanuwansa mas??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????u rikita duk wanda ya kalla dasu sai naji kunya ta kamani tamkar in koma da baya ko fahimtar hakan yai dan haka ya dakatar Dani da cewa

a a k'araso mana Fatima na k'arasa na tsuguna nesa dasu tare da sunkuyar da kaina
Jin nai shiru bance komai ba kuma ban d'ago k'wayar ido na ba yasashi janye ta daga jikinsa yace Fatima kina buk'atar wani abune na mik'amai ta kaddar hannuna tare da barin gurin da sauri yabini da kallo tare da jujjuya ta kaddar dana bashi ya juya ya kalli hindu dake faman cika tana batsewa yai murmushi batare da yace mata komai ba ya bud'e ta kaddar ya fara karantawa bayan ya gama yai murmushi me Kama da dariya a yanzu ya kuma tabbatar da yarintar ta idan banda yarinta meye abin jin kunya aciki
Sai kuma yaji ta burgeshi kunyarta na d'aya daga cikin abinda ke jan hankalinsa zuwa gareta


Yaji kunyar k'ansa mutuk'a daya kasa tuna abubuwan da ya dace yaimata Wanda har saida ya k'ure mata ta sanar dashi ya juya ya kalli hindu da ta zubamai ido yace my sweety kiramin Fatima!
Fatima tace cikin mamaki ya d'an daure fuska yace eh idan kinkirata ki wuce ki canza kayanki zamu fita shopping yanzu ta sake kallonsa kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta mik'e tanufi d'akin



Ina tsaye a tsakar d'akin na kasa zaune na kasa tsaye fargabace ta cikamin zuciya bansan yaya ze d'auki abinda na rubuta mai ba.
Naji an bubbuga k'ofa naje na bud'e tana tsaye a bakin k'ofar cikin tsananin b'acin rai nai d'an murmushi nace anty Hindu shigo mana

Ta watsomin harara tace bashi ya kawoni ba kije yana kiranki na amsa da to harta juya ta dawo tare da nunani da d'an yatsa tace ki kula da kanki ki kuma taka a sannu wallahi wallahi idan na kamaki da shiga gonata gamammu baze yimiki kyau ba ta juya ta tafi yayinda nabita da kallo har saida ta k'ule

Na Saki ajiyar zuciya cike da tunanin abinda take nufi na idan na shiga gonarta iya tunanina bangano abinda take nufi ba dan bamma fahimci gonar tataba
Na shiga falon da sallama ya amsa min har lokacin yana nan inda na barshi saidai yanzu ba kallo ya ke ba ya kashe TV d'in na nemi gu na tsuguna ya kalleni tare da kiran sunana Fatima
Na.am na amsa yace kije ki shirya zamu fita shopping kiyi lis d'in duk abinda baki dashi dan karki manta idan munje sai.a siyo na amsa da to zuciyata cike da mamakin wai yau har dani ya Aliyu ke fad'in in shirya muje shopping lallai ikon Allah da yawa yake babu abinda nai illah kalmina da nasako Mara tudu na kalli kaina a mirrow sanye nake da riga da skeet na popul d'in les na d'ora dogon hijab d'ina har k'asa saboda kayan su kamani sosai

Na fito na tatda shi a falo yana ganina ya mik'e yace je kikira hindu ku sameni a mota na amsa da to na nufi hanyar d'akinta ina k'wank'wasawa sai gata cikin shiri tana cewa ganinan my ganina ya katseta ta watsomin harara tare da cewa lafiya


Nace lafiya lau ya Aliyu ne yace mu sameshi gurin mota taja tsaki tare da bangajeni ta wuce nai murmushi na bita a baya har zuwa harabar gidan yana zaune a mazaunin direba muka taddashi ta bud'e gaba ta shiga yayinda na bude baya zuciyata cike da d'aukin yau zan fita Inga gari.




Mmn beby nusy. A??]
{



WhatsApp number 07010238476
11/18/21, 11:00 PM - Fiddausi Yunus: WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200# ZAKU IYA BIYA TA 3048536089 ALIYU JIBRIN ALI FIRST BANK KO KUTURO CARD WAYA MTN KO AIRTEL TA 07010238476 IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA KEDA ALLAH



??.\??cLOVE STORY HOT ROMANTIC


YA Allah Kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka ka shirya mana zuri.a ameen??R0???_




PAGE4??_/Q7??_/QC?&
{4??_/Q8??_/Q
be tsaya ako Ina ba sai a wani shahararran stor yai parking ya bud'e motar ya fita tare da cewa Ku fito muje muka fito suna gaba Ina binsu a baya har zuwa cikin k'ayatatcan super market d'in ya juyo ya kallemu yace kowacce ta d'ebi dukkan abinda take buk'ata yai gaba ya barmu


Hindu ta bi bayansa zuwa b'angaren da yabi wato na turaruka na bisu da kallo kamin na fara duba abinda nasan Ina da buk'ata audugar kawai na d'auka sai tushu dana san Ina da buk'ata sai wata teddy danaga taimin kyau sosai taban sha awa sannan na fara duba turaruka na d'auki najiki saina kaya dana d'aki da toilet


Kamar daga sama naji ance wanake gani kamar Fatima Ahamad Uba jin muryar me maganar kamar muryar da nake ishin ji ya sani waigawa a k'agauce ganin Aisha ya sani sakin baki nace Aisha Usman kece ta tahu dagudu muka rumgume juna tace Fatima dama Zan kuma ganinki
Na k'ank'ameta yayinda hawayen farin ciki ya zubomun nace Aisha da gaske ke nakeji ajikina Alhamdulillah Allah na gode ma

Me ya kawoki nan garin ko dama kina zuwa garin Abuja
Ta d'an zame jikinta daga nawa tace a dalilinki muka dawo Fatima sai kuma ubangiji ya kuma kaddara had'uwarmu

Na kalleta nace ban gane ba waima yasu mom da ya kabir
Ta kalleni tai murmushi tace mom tanan lafiya k'alau ya kabir kuma ga shinan muna tare da shi dandai idanunki sun rufene

Na kalli inda take nunamin yana tsaye ya hard'e hannuwansa a k'irji yana kallona tamkar a yau ya fara ganina na kalleshi har yanzu yananan da kyau kamar yadda na sanshi ya k'ara haske saidai ya rame sosai na risina nace ya kabir Ina wuni

Yai murmushin yak'e yace lafiya lau Fatima ya me gidan naki na sunkau da Kai tare da cewa lafiya k'alau

Aisha tace banji dad'in ta wowarki babu KO sallama ba Fatima
Dan bayan bikin ki da sati biyu munje gidanki nida mom d'ina domin yi miki fatan alkairi sai akace mana mijinki ya daukeki kun koma gurin aikinsa da zama
ba mu masan kuna cikin garin nan ba dan bayan aurenki babu dad'ewa muma muka dawo nan garin da zama sakamakon matsalolin da ya kabir ya had'u dasu bayan aurenki

Nace matsaloli kuma Aisha ta d'an gyara tsayuwarta tace eh matsaloli Fatima bayan aurenki ya kabir yasha fama da cutuka kala-kala dalilin k'wallafa ki da yai a ransa baya iyaci baya iya sha sai ambaton sunanki babu abinda ke faranta mai rai har aga murmushinsa sai in yaji labarinki

Ya kabir na mutuk'ar sanki Fatima tunda nake ban tab'a ganin abinda ya kabir ya so ba irinki Fatima tunda har ya Kai en yanzu ya kasa fiddake daga ransa
A kullum sai yai mana zancen kyawawan halayyarki bansan sai zuwa yaushe ze dena tunaninki ba da ambaton sunanki


Nai d'an murmushi me ciwo nace ze denane Aisha na d'an kalleshi nace
Kayi hak'uri ya kabir kacireni daga zuciyarka kamanta dani kamanta da katab'a sanin wata Fatima a rayuwarka kaci gaba da rayuwarka tamkar yadda kake da kamin muhad'u ka kaddara dama ubangiji be nufi aure a tsakanin muba shiyasa ya kawo kaddarar data rabamu
Kariga kasan dukkan abinda ya kubce maka dama ubangiji ya rubuta ba rabanka bane abinda kuwa kasama dama Allah ya hukunta babu yadda za ai yatsere maka I nai maka addu a ubangiji Allah ya baka mata ta gari wadda ta fini komai wadda zaka so fiye da yadda ka soni


Ya girgiza Kai yayinda hawaye ya ciko idanunsa yace bazan samuba Fatima bazan tab'a samun macen da zan so ba ko da rabin son da nake miki ba domin ke sanki daban Allah ya halicceshi a zuciya ta harga Allah nasan nayi rashin da har abada bazan iy....


Idan kin gama zancen kya iya wucewa mutafi dare yanayi na d'an juya na kalli me maganar ya Aliyune tsaye a bayana fuskar nan kamar be tab'a dariya ba gabana yayanke ya fad'i innanallahi kawai nake fad'a a raina
Aisha ta kalleni ta kalleshi tace Fatima KO shine mijin naki na d'aga mata kai batare da na iya cewa komai ba Aisha ta risina hade da cewa Ina wuni
Lafiya ya amsa a tak'aice fuskar nan ko annuri babu ya kabir ya mik'a mai hannu had'e da cewa Assalamu alaika ya Aliyu ya maida hannunsa aljihu ya amsa wa alaikassalam ya juya ya tafi cikin sauri nad'ebi kayan tare da cewa to Aisha mun tafi Ku gaidamin mom sai wata rana ta biyoni tare da mik'omin wani d'an card tace to Fatima mun gode ga address d'in gidanmu dan Allah idan kin sami dama number tace ajiki card d'in ki kirani na k'arb'a tare da cewa in sha Allah Zan Kira nabi bayansa da sauri zuwa inda yai parking d'in motar dan tuni ya tsufa aciki na bud'e bayan motar na shiga na zauna tun kamin in gama rufe murfin ya figi motar da gudu muka fita daga harabar super market d'in


Gaba d'aya motar babu Wanda ke cewa kowa komai in ka d'auke hindu da ke bin wak'ar dake tashi a cikin wayarta yai parking a farfajiyar gidan ya kashe motar ya fice batare da ya gyara parking dinba kuma be cewa kowa komai ba na fito nabi bayansa da ledar siyayyata ya yinda hindu ta kuma gyara zama tana amsa wayar da aka kirata

A tsorace na tura k'ofar falon na shiga da sallama yana tsaye a tsakiyar falon sai kaiwa yake yana dawowa na d'an rab'e Zan wuce d'akina kamar daga sama naji yace meye alak'arki da wannan d'an iskan da na ganku tare


Na juyo na fuskan ceshi cikin sanyin murya nace bafa d'an iska bane ya ka...
Kau naji saukar Mari a fuskata tun kan in k'arasa na dafe inda ya maran da hannuna yayinda hawaye ya fara sintiri a fuskata

Yaci gaba da fad'a cikin b'acin rai dankin rai namin hankali kin maidani sakarai daga jeki zab'i abinda kike buk'ata shikenan na baki lasisin yin zance da ko wanne k'ato duk abinda kuke fad'a a kunnena nafi 30 minutes Ina tsaye Ina sauraranku amma kwata kwata Baku kula dani ba saboda idanunku sun rufe to dukkan kalaman da kuke inajinku Ku gaku tsofaffin masoya KO hummmmm



Yaja numfashi to idan ban kirashi d'an iska ba da wanne suna kikeso na kirashi tunda besan darajar aure ba besan mutumcin matar aure ba yaja tsaki tare da cewa nayi da na sanin fita dake da nasan zan had'u da wannan bacin ran wallahi da ban bari kin fita ba da aurena a kanki kike kula wani wallahi da ba....



Na katseshi cikin kuka nace dan Allah kayi hak'uri ka saurateni kada kayimin mummunan fahimta wallahi da..

Dan Allah yimin shiru me zaki cemin bayan abinda naji da wanda naji koba tsohun saurayin ki bane Wanda yak'ici ya k'i sha saboda tunanin yayi rashinki

Cikin kuka nace dan Allah kayi hak'uri idan maganar da nai dashi ta b'ata maka rai nasan duk abinda kaji na fad'....

Yasake ka tseni da cewa ya isheni banasan kuma jin maganar shi kuma muryarki da yaji Allah ya isa ban yafe masa ba ki kuma gaugauta tashi daga gabana tun kan ranki yab'aci abinda kikai bawai ya b'atamin rai bane dan abinda kakeso shikake kishi ni kuma babu sanki a raina duk abinda zanyi inayi ne dan martabar aure na da yake kanki badan so ba kuma ki b'acemin da gani ya fad'a cikin tsawa da gudu na shige d'akina na fad'a kan gado tare da k'ara fashewa da kukan daya tuk'emin zuciya...








Mmn beby nusyA??]
{





WhatsApp number 07010238476
11/18/21, 11:00 PM - Fiddausi Yunus: WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200# ZA KU IYA BIYA TA 3048536089 ALIYU JIBRIN ALI FIRST BANK KO KUTURO CARD WAYA MTN KO AIRTEL TA 07010238476 IDAN KIKA KARANTA MIN BAKI BIYA BA KEDA ALLAH DUK WANDA YA FIDDA MIN BOOK SHIDA ALLAH.



??.\??cLOVE STORY HOT ROMANTIC




Ya Allah kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka ka shirya mana zuri.a ameen??R0???_




PAGE4??_/Q9??_/QC?&
{5??_/Q0??_/Q
Kuka nake me cin rai babu me lallashina ko tausayina naji tausayin kaina mutuk'a na irin wannan rayuwar da nake ciki mara yanci danasan abinda ze faru kenan da tun farko na hak'ura da audigar gashi dalilinta yaimin mumunan zato ya kuma k'i fahimtata

Nayi kuka sosai har saida naji kaina yana sarawa tsigar jikina natashi zazzab'i na Neman rufeni da k'yar na iya tashi na lallab'a na shiga band'aki na watsa ruwa na tsaftace jikina na fito na sanya kayan barci na kwanta har lokacin hawaye bebar sintiri a fuskata ba
Kalamansa sun tsayamin a rai

Abinda kikai bawai ya b'atamin rai bane dan abinda kake so shi kake kishi ni kuma kinsan babu sanki a zuciyata
Hawaye ya kuma wanke min fuska ga zazzab'i daya rufeni sai rawar d'ari nake
Na janyo bargo na lullub'e jikina maganganunsa na tab'amin zuciya


Tunda ya kwanta tunaninta ya cikamai zuciya kwata kwata ya kasa samun sukuni gani yake abinda yai kwata kwata be kyautaba shi kansa ya rasa dalilin da yai abinda yai d'in kishi wani b'angaran zuciyarshi yace da shi tuni ya kauda da wannan da sauri kishi taya ya zeyi kishinta bayan yasan baya sonta kukanta ya tsaya mai a zuciya ji yake tamkar alokacin take yinsa

Ya tashi daga kwancen ya zauna agefen gadon zuciyarsa tai rauni mutuk'a tausayinta ya cika mai zuciya yai ajiyar numfashi tare da sanya hannu ya dafe goshinsa shikansa ya rasa abinda yake damunsa a yan kwanakin nan duk lokacin da tunanin ta ya ziyarceshi sai tausayinta ya tsirga mai ya kanji wani Abu na daban nai mai yawo acikin jininsa duk da matsayinsa na k'wararran likita ya kasa gane me yake damunsa
Gashi a yanzu ya rasa abinda yasa yake yawan tunaninta a gida ko office da tausayinta da begen sanyata acikin idanunsa a koda yaushe yarasa meye dalili

Ba dai hakan shine son ba cikin sauri ya girgiza kansa yace Kai ba Santa nake ba illah Ina yawan tunatane dan kyautatawar ta gareni da biyayyarta da yawan hak'urinta
Wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login