Showing 42001 words to 45000 words out of 71253 words

Chapter 15 - YANCINA KO BUDURCINA COMPLET by Ummi Muhammad Usman.doc

kiran megadi megadi da gudu megadi ya fito daga d'akinsa ya tareshi a hanya tare da tsugunawa yace yallab'ai barka da fitowa ai Ina ta amsawa baka ji bane ba tare daya saurari abinda yake cewa ba yace waye da waye ya shigo gidan nan koya fita bayan fitata
Megadi yace wallahi babu Wanda ya fita tun fitarka sai hajiya k'arama
Aliyu ya ya mutsa fuska yace wacece haka

Megadi yai murmushi yace HAJ me kirki baya goya marayu yarinya me halin manya wadda take bayarwa da dama batare da haggu ta sani ba ai nan ta fito da k'atuwar a kwati da k'yar take janta zata fita muka gaisa nai nai ta kawo a kwatin in d'aukar mata tak'i amma naga tana fita tasami taxi ta hau ai suna fita kana shig....

Kau Aliyu ya d'aukeshi da Mari tare da cewa uban waye ya baka umarnin ka bud'e mata k'ofa ta fita ko tunda take gidan nan katab'a ganin ta fita ita kad'ai
Megadi na dafe da kunci ya girgiza Kai kayi hakuri Alhaji wallahi nazata kasani ganin baka dad'e da fitaba saina d'auka bala guro zatai bansan baka saniba da bazan barta ba
Aliyu yaja dogon tsaki ransa a mutuk'ar b'ace yace wallahi kayi addu a inganta indawo da ita gidan nan inba hakaba wallahi kayi ta aikinka ya fad'a tare da juyawa a fusace
umar ya kalli megadin yace yi hak'uri musa ransane ya b'aci da abinda kayi shiyasa ya mareka kasani ba halinsa bane wulak'anci idan ya huce na sani da kansa ze baka hak'uri kodan gaba idan irin haka ta faru ka dinga sanar da shi a kan lokaci me gadi yace insha Allah nazan kumaba dan Allah ka bashi hak'uri kada yarabani da hanyar abincina wallahi Ina da iyalai
Umar yace kada kadamu za..
Dogon hon d'in da Aliyu ya sakine yasa umar juyawa yayinda megadi ya nufi get a guje dan ya bud'e masa

Umar ya bud'e gefen me zaman banza ya zauna Aliyu yaja motar a guje suka fita daga gidan umar ya kalleshi yace ka kwantar da hankalinka a bokina in sha Allah zamu ganta batayi nisa ba banasan ganin wannan tashin hankalin a idonka

Aliyu yace dole hankalina ya tashi umar yanzu ya ya zanyi idan ba aga yarinyar nan ba mezan cewa Abba da su mama ka sani komai zan fad'a bazasu yarda ba

Umar yace insha Allah za a ganta yanzu Ina muka nufa Aliyu yaja numfashi yace tashar mota zamu ko tana can umar yace to Allah ya tak'aita mana wahala ya amsa da ameen.



Tin k'arfe goma na safe suke yawan bin tashoshi amma har k'arfe biyu na yamma kome Kama da Fatima basu ganiba kuma a list d'in motocin da suka tashi anduba kome irin sunan ta babu Aliyu hankalinsa yatashi k'waloluwar tashi shi kansa umar a yanzu hankalinsa a tashe yake duk inda suka San Ana Lodi a cikin garin Abuja sai da sukaje wani wajenma da kwatance suke zuwa amma kome kalar fatima basu gani ba daga k'arshe gari suka shiga suka fara dubawa KO Allah zesa su ganta koda a hanyane



Fatima kam tafiya ta kan kama alk'ur aninta ta d'auko a cikin jakarta tana karantawa yayinda direba yake ta bawa mota wuta cikin hukuncin ubangiji da yake babu wani tsaye tsaye sai gashi sun isa kano a lokacin da ya kintata
tunda yace sun shigo kano ta rufe alk'ur anin ta zubawa hanya ido tana kallo zuciyarta cike da farin ciki da d'aukin sanganin Umma da iya ya juya ya kalleta yace wacce unguwa zamu tace gwale yace kinsan bansan hanya ba saidai ki dinga yimin kwatance cike da zumud'i tace to
Cikin nutsuwa take yi mai kwatancen har k'ofar gidansu dake sani mainagge yai parking a k'ofar gidan

tana ganinta a k'ofar gidan tace Alhamdulillah bawan Allah na gode ta bud'e Jakarta datasa k'udin da Abba ya bata bandir d'ayane na 'yan dubu dubu ya bata ta d'auko ta k'irga mai kud'insa ta bashi ya karb'a yana godiya ta fito ta shak'i iskar unguwar ta fesar ta Saki murmushi tare da fad'in Allah mungode maka da ni imomin da kayiwa garinmu ita kanta iskar dad'inta na musammanne ya fito mata da kayan ta ya d'auka ya kai mata har bakin tamgame man get d'in gidan ya ajiye taimai godiya sukai sallama ya shiga mota ya tafi dan a yau yake son komawa


ta k'wank'wasa k'ofar me gadi yazo da sauri yana tambayar waye?
tace fatima ce
mlm isa ya bud'e k'ofar yana ganinta ya bud'e baki tare da kiran sunan da yake kiranta haj k'arama kece dama kina nan
Tai murmushi tare da jan akwatin tana k'ok'arin shiga tace kaji mlm isa da wata magana bagani ka ganniba

Ya karb'i a kwatin hannunta ya d'ora aka yana ta faman yi mata sannu ya nufi b'angarensu ta bishi abaya tana k'arewa gidan kallo ganin yadda aka kuma k'awa tashi idan ba idanunta ke mata gizau ba sai taga ma kamar har girma aka k'ara mai ga wasu zinduma zinduman motoci da suka cika harabar gidan

Harbakin sassansu megadi ya kawo mata kayanta sannan ya ajiye tai mai godiya ya juya ita kuma ta fara jan a kwatin tana k'walla kiran sunan Umma Umma amma har ta isa tamgameman falon bataji d'uriyar taba babuma motsin kowa tabi falon da kallo da yake kaca kaca datti da yana sun cika gurin irin an dad'e ba.ayi amfani da gurin ba

Cikin tashin hankali ta Saki a kwatin ta nufi d'akin Umma tana k'wala kiran sunanta amma batanan duk inda take tunanin ganinta ta duba bata gantaba acikin gidan da gudu ta nufi sassan iya ta cikin falonsu tana k'wala kiran sunan iya a bakin k'ofa sukaci Karo ta jawo gindi ta tahu saboda jin muryar fatima da tai duk ta rame ta k'arjale da gudu ta k'arasa ta zube a tsakar d'akin da yai datti sai futar da wani irin wari yake ta kamo iya ta rumgume a jikinta ta fashe da kuka tana fad'in innanallahi wa Inna ilaihir raji un iya me ya sameki haka wace irin mummunar kaddarace ta samemu haka

Iya ta k'ankame Fatima ajikinta hawaye na zuba a idanunta tace alhamdulillah Allah na gode maka da kasanya zan k'ara ganin ziri ar ahamadu kamin rasuwata Fatima kece nakeji a jikina Fatima na kuka me sauti tace nice iya me ya faru da Ke haka bayan tafiyata Ina Umma data barki cikin wannan halin ina Kawu mustapha da ya barki acikin irin wannan yanayin

Iya taja ajiyar zuciya tace rabi.a batanan Fatima kawunki ya koreta daga gidan nan
A rikice Fatima tace subahanallah bangane ba iya ya koreta zuwa Ina meke faruwane iya

Iya ta goge hawayen dake tsiyaya a idanunta tace kinsan komai dake faruwa a gidannan tundaga rasuwar mahaifinki har zuwa b'atan d'an uwanki da aurenki bayan aurenki rayuwa tai tsanani ga mahaifiyarki dan kawunki ko ruwan sha indai yasan a gidan nan zata sha to baze bariba abincin da zataci saida ya zamo sai tafita mak'ota tayi aikatau zata samu taci tasha harma ta bani duk dani mustapha kanbani sau biyu a rana safe da dare tai hak'uri ta jure daga duk wani wula k'anci da cin kashi da za suyi mata dan tana fatan randa zaki zo da kuma bayyanar d'an uwanki ta Kore duk wata damuwa amma saida yaron nan ya koreta daga gidannan tare da gargad'i me k'arfi a kan duk Randa ya kuma ganinta a a riyar gidan a bakacin rayuwarki dan zesa a kasheki har gidan aurenki

Iya ta fashe da kuka tare da cewa tundaga ranar da mahaifiyarki tabar gidan nan tsawan watanni takwas bata kuma zuwa ba tun daga lokacin ni kuma na kwanta cuta amma babu kulawa babu magani fata suke in mutu su sami yadda sukeso ni kuma addu a nake Allah ya bani lafiya da tsawan kwana in sake ganinku


Tunda iya tafara magana Fatima take wani irin kuka me ban tausayi kamar numfashinta ze d'auke ta sake k'ank'ame iya suka ci gaba da kukan tausayin Kansu

Ganin iya na wani irin Abu ne yasa dole Fatima ta lallashi kanta taje ta d'ebo ruwa ta bata tasha sosai takama ta ta kaita band'aki ta wanke mata jikinta daya b'aci



Aliyu kam ya shiga tashin hankalin da be tab'a shigaba wuni guda suna yawan neman Fatima babu wani Abu dake tsaidasu face sallah ko abinci baya iyaci umar yai lallashi yai nasiha akan ya kwantar da hankalinsa amma Ina ya kasa k'arfe bakwai dedai Abba ya Kira wayarshi ya lokacin suna zaune acikin wani masallaci da sallah t riskesu a wajen Aliyu ya d'aga ya amsa sallamar da yai masa Abba yace gamu a airport mun sauka Aliyu ya mik'e tsaye cikin tashin hankali yace Abba tare kuke dama Abba yace eh tare muke kasa hak'uri nai nace gwara inzo Inga yar amana da kaina kasan ita amana nauyi ne da ita
Aliyu yace to Abba gamunan zuwa nida umar ya kashe wayar tare da fad'in innanallahi wa Inna ilaihir raji un







Mmn beby nusy 07010238476
11/19/21, 11:29 AM - Ummi Tandama???i: WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200# ZAKU IYA BIYA TA 3048536089 KO KUTURO CARD WAYA MTN TA 07010238476 DUK WANDA YA KARANTA BEBIYA BA SHIDA ALLAH




Ya Allah kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka ka shirya mana zuri.a ameen??R0???_






6??_/Q5??_/QC?&
{6??_/Q6??_/Q
Umar ya mik'e tsaye ya dafashi yace lafiya Aliyu me yake faruwa yanaga hankalinka ya k'ara tashi

Aliyu yaja numfashi me zafi ya fesar yace Su ummi sun iso tare da Abba suke komai ya kuma lalacewa um@r
Umar ya dafashi yace ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zezo da sauk'i yanzu muje mu d'aukosu yace to suka fece daga masallacin


A harabar airport d'in suka taddasu sun kammala komai su kawai suke jira Abba ne da ummi sai faiza da maryam ganin fitowarsu daga motar faiza d maryam da sauri suka nufeshi suka rumgumeshi tare da fad'in yaya munyi kewarka yayi d'an murmushi tare d'an bubbuga kafad'unsu ya janyesu daga jikinsa ya k'arasa gurin su Abba ya risina ya fara gaishesu Abba ya amsa ya d'agoshi ya d'an rab'ashi a jikinsa yace lafiyarka kuwa haider me ya sameka naga ka zabge ko baka da lafiyane Aliyu yayi d'an murmushin yak'e yace lafiyata k'alau Abba
Abba yace to Alhamdulillah suka gaisa da umar sannan suka rankaya mota

Umar ne ke jan motar yayinda Aliyu ke gefensa su kuma suna baya suna tafe suna hira tare da tambayar bayan rabuwa har suka iso lokacin Ana kiraye kirayen sallah issha su ummi suka shiga ciki yayinda su kuma sukai alwala a harabar gidan suka wuce masallaci bayan sunyi sallah sun dawo a harabar gidan suka tatda su ummi da mamaki suke kallonsu Abba ne ya fara magana lafiya kuka fito waje da alama ko sallah ba kuyi ba

Ummi tace Ina fa lafiya ALH tunda muka shiga mukejin Ana ta bugun k'ofa da zage zage tsoro ya kamamu shine muka fito waje mujira zuwanku Abba ya kalli Aliyu yace meke faruwane haidar

Aliyu yad'an shafo sumar kansa tare da fad'in babu komai Abba Ku shugo yai gaba suka bishi a baya tunda suka shiga falon suke jin yadda hindu ke dukan k'ofa kamar zata b'alla tana fad'in bazaka bud'eniba ko haidar me kukeyi wallahi idan ka mu amalanci yarinyar nan saina kasheta duk duniya babu Wanda ya isa ya mallaki abinda yake mallakina wallahi bazan yadda ba ni zakaiwa cin amana wallahi sai na d'au mataki tunda ka gayamin baka Santa wallahi baka isa ka dawo kace zaka had''ani da ita a zuciyar kaba
Abba ya kalli haidar yace meke faruwane haidar Aliyu yai k'asa da Kai yace Abba wal
Abba ya tsaidashi da cewa kaga bud'e yar mutane tukun kamin inji komai a bakinka

Ya amsa da to ya nufi k'ofar sukuma suka zazzauna akan kujerun falon yana bud'ewa taiyo waje da gudu duk tai firgai firgai wuni guda a d'aki dan gaba d'aya yamanta da ya kulleta ta kalleshi tana huce bata kula da mutanan dake falonba tace ni zakaiwa haka ko haidar ni zakaiwa halin munafukan maza akan yarinyar da kaf duniya tasani baka Santa yarinyar da kace me zakai da ita yarinyar da kace auren dole akai ma da ita taima k'ank'anta taja numfashi tace wallahi kayi ta banza kullenin da kai dan bazan fasa ai watar da abinda nace ba wallahi idan ban kashe taba saina tabbatar na nakasata

Abba ya mik'e tsaye yace subahanallah me ke faruwane haider wacece ita wannan d'in wa kuma za.a kashe?
Hindu ta juyo ta kalli cikin falon sai lokacin ta kula da mutanan dake ciki duk da bata tab'a ganin mahaifin haidar ido da ido ba amma ganin farko da taiwa mutumin na tsaye ta gane mahaifinsane saboda tsananin kama data gani.

Aliyu ya k'arasa gaban Abba ya tsuguna muryarsa cike da rauni ya fara magana Abba dan Allah dan annabi kayi hak'uri wallahi ba laifina bane ka tambayi umar asalima bansan ta fita daga gidan ba dan Allah kayi hak'uri kada kayi fushi dani na tuba ya k'arasa muryarsa na rawa tamkar ze kuka
Abba yace banfa gane maganar da kake ba ka fito fili kayimin bayani kasani banasan k'umbiya k'umbiya

Aliyu ya gyara tsugunansa yace amm dama Fatima ce ta fita tabar gida tunda safe sabida jin irin maganganun da hindu take na saita kasheta lokacin natafi d'auko umar kamin in dawo ta tafi wallahi tun safe muke yawan nemanta nida umar amma bamu ganta ba ko umar ya fad'a tare da kallon umar

Abba yace Inna nallahi wainna ilaihir raji.un Aliyu kana nufin baka rik'e amanar dana bakaba yanzu dama kalaman da matarka ke furtawa akan 'yar da aka damk'a amanarta a hannu nane

Ya juya ya kalli ummi yace Ku tashi kud'auki kayanku mutafi ya dubi Aliyu da kansa ke k'asa fuskarsa cike da tashin hankali yace na baka nan da gobe duk inda yar mutane take ka nemota kabani kamar yadda na baka daka ga yamin tun wuri baka Santa da ban bari ka tawo musu da yarinya kana wulak'anta ba kaci amana ta haidar amma bani kaiwa ba kanka kaiwa Kaine ka rasa na gartattar mace me ilimi da tarbiyya ka tabbata gobe idan Allah ya kaimu ka dawomin da ita kamar yadda na baka kuma ka had'omin da takaddar sakinta dan aure a tsakaninku ya k'are zan zab'a mata wanda ze sota ba Wanda ze gayawa duniya a dole ya karb'etaba

Ya juya ze futa cikin fushi yayinda su ummi duk suke tsai tsaye Aliyu ya fashe da kuka yace dan Allah Abba kada kayi fushi dani idan Kai fushi Ina zansa rayuwata wallahi inasan Fatima dan Allah kada karabani da matata wallahi Ina mutuk'ar Santa ban fahimci haka ba sai yanzu dan Allah dan annabi kayi hak'uri wallahi zan nemota a duk inda ta ke amma dan Allah kada karabamu ya k'arasa cikin shasshek'ar kuka tamkar wani k'aramin yaro k'annan sama suka zube a gaban Abba suna kuka ganin d'an uwansu nayi suka shiga bashi hak'uri umar na tayasu

Ummi ta dubi Abba tace dan Allah ALH kayi hak'uri tunda ya gane kuskuransa kuma yanzu ba lokacin wata magana bane a fara neman yarinyar mutane tukun idan aka ganta komai me sauk'ine amma dan Allah kayi hak'uri ka zauna a samo mafita Allah ya huci zuciyarka

Ya koma ya zauna ya dubi Aliyu yace yanzu ya ake ciki da b'atan yar mutane kun sanar da hukuma Aliyu ya zauna daga durk'usan da yai yace a a bamu sanar da suba nan dai duk mun dudduba cikin gari harma da gefe amma ko Wanda ya ganta bamu ganiba to dama umar ya kawo shawarar gobe da sassafe zamu tafi kano ko can taje shiyasa bamuyi gaggawar sanarda hukuma ba

Abba yaja numfashi ya fesar yace hakan yayi Allah ya kaimu goben sai muje can gidan nasu gaba d'ayan mu Allah isa dai tanacan gaba d'aya suka amsa da ameen ya kalli umar yace a nema mana jirgin safe dan dai nasan yanzu bazamu sa muba da yanzu zamu juya ya amsa da to abba insha Allah
Aliyu ya mik'e tare da kallon umar yace key yana hannunka ko bani inje in samo musu abinda zasuci umar ya mik'e tare da fad'in muje Abba ya dakatar da su da cewa a a ku kaimu masauki maci acan
umar yace Abba ba a nan zaku kwana ba ya mik'e tare da fad'in eh ya kalli su ummi yace kutashi muje suka mik'e tare da d'aukar jakar kayansu Aliyu zeyi magana ummi ta d'aga masa hannu alamar yai shiru cikin k'asa da murya tace kada kace komai be gama hucewa bane ka bishi da yadda yake so
ya amsa da to ya d'auki jakar kayan nasu suka fice
Saida suka ne ma musu ma sauki suka gama komai sannan sukai sallama akan gobe za suzo da sassafe su d'ebesu zuwa airport


Fatima kam saida ta wanke iya tas ta canza mata kayan jikinta da suke ta faman d'oyi ta gyara d'akin ta kwashe bolar da ta cikashi tafita da katifar dake wari tai mata shimfid'a ta kwantar da ita ta d'auki ja karta ta d'ebi kud'i dubu biyar ta fita megadi na zaune ya najin redio tai mai sallama ya kashe redio ya kalleta yace HAJ wani Abu kike buk'atane Fatima tayi murmushi tace baba megadi na fad'a maka banasan hajiyar nan yai murmushi yace yi hak'uri bazan kumaba a kwai abinda kike buk'ata
Tace eh dama abinci nakeso ka siyomin dan Allah me d'an ruwa ruwa irin Wanda Mara lafiya ze ci ya karb'i kud'in yace to bari naje na dawo ya karb'a ya fita ita kuma ta koma ciki kamin ya dawo ta kammala gyaren b'angaren iya tayi wanka ta sake kaya doguwar riga ta saka yar kanti tayi Rollin da mayafin duk da ba kwalliya tai ba tayi kyau mutuk'a fuskarta sai shek'i take tana futar da wani annurin kyau tana idar da sallolin dake kanta megadi ya kawo mata sak'on ta karb'a tayi godiya ta bashi Leda d'aya daga cikin ledojin da ya kawo ya tafi yana ta godiya
A nitse ta dunga ba iya abinci a baki taci kuwa sosai bayan ta kammala bata itama taci iya ta dinga shi mata albarka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login