Showing 48001 words to 51000 words out of 71253 words

Chapter 17 - YANCINA KO BUDURCINA COMPLET by Ummi Muhammad Usman.doc

da Aliyu yaci gaba da ambata bayan ya lumshe idanunsa ya d'ora kansa a jikin kujerar motar a hankali yaji tiririn da zuciyarsa keyi na sauka nutsuwa na shigarsa

Cikin yan mintina motocin police har uku suka iso har cikin harabar gidan sai a lokacin yan unguwa suka an Kara da abinda ke faruwa Addu a suke Allah yasa k'arshen Kawu da ya'yansa ne yazo dan dama duk sun uzzira ma rayuwarsu ga lalata musu yara da suke da ire iren rashin tarbiyyarsu
Yan sandan na durowa Kawu fad'i yake gashi can maza Ku kamashi ya karairayamin yaro ze kasheshi har gida
Ko kulashi ba suyiba suka cacumi sadig a halin da yake ciki suka wulla a bayan mota suka had'a harda Kawu da mama ramatu sakamakon umarnin da a Kai musu tundaga sama Kawu sai kumfar baki yake yana fad'in me yai ga Wanda zasu Kama can zasu kamasu suda aka ketawa haddi aka shigo har gida aka da kar musu d'a dpo ne ya daka musa tsawa yace yai shiru in sunje police station saji yai umarnin a tafi dasu kamin su k'araso
Megadine yai musu jagora har zuwa sassan iya yana gaba Aliyu na bayansa su Abba ma na biye dasu a baya tun a bakin k'ofa ya fara karo da takalmin fatima yasa hannu ya kwashe su suka tin Kari d'akin iya tundaga bakin k'ofa suka Fara ganin jinin daya d'id'd'iga har zuwa cikin d'akin da sauri suka k'arasa inda iya ke yashe babu a lamar rai a tare da ita Aliyu ya durk'usa ya fara dubata umar na tayashi abba ya kallesu yace ya ya ta mutu Aliyu ya girgiza Kai yace bata mutuba suma tai insha Allah indai ta sami kulawar likitoci nan da d'an lokaci zata farfad'o
Abba yai umarnin yan sanda biyu mata su d'auketa zuwa mota a wuce da ita asibiti
Bayan fitarsu wasu kuma suka Fara bincike a d'akin band'aki har zuwa falo saida suka had'a duk wani Abu da suke buk'ata tukun suka tattara harsu Aliyu suka wuce police station.



Ahankali ta fara motsa k'afarta idanuwanta Nata rawa alamun tanasan bud'esu hasken d'akin na kashe mata ido a hankali ta bud'e idanun gaba d'aya tana bin d'akin da kallo tana tunanin a Ina take sannu kin farka taji muryar wata dattijuwa a gefenta ta juya ta kalli inda muryar ke fitowa wata kamilallar tsohuwa ce me cike da nagarta zaune agefenta tana kallonta tayun k'ura tana k'ok'arin tashi dattijuwar ta matso kusa da ita tana fad'in sannu kinji yi a hankali kada ki gotar da ruwan da aka samiki yanzu likita zezo yarona da ya kad'eki ya tafi kiransa ganin lokacin da aka bayar na farkawar taki ta wuce

Ta koma ta kwanta duk jikin ta nai mata wani irin ciwo
Cikin yan mintina likitan ya shigo bayansa wani matashine bak'i kyaukyawa k'ark'arfa tsakatsaki shiba dogoba shiba gajere ba ganin idanunta a bud'e yasa murmushi ya bayyana a fuskarsu tare suka furta Kalmar Alhamdulillah likitan ya cire mata ruwan da ya k'are ya k'ara au aunata domin k'ara tabbatar da lafiyarta ya kalli Wanda suke tare yace carften yanzu babu wata matsala ta dawo cikin hayyacinta dama razanace da firgici ya sata suma kumburin fuskar ta ma a hankali ze sab'e wannan kuma marin da tashane idan tai wanka zan bata maganin da zata shafa ze b'ace in sha allah babu wata matsala
Carften yace Alhamdulillah yan zu zuwa yaushe zaka sallame mu kasan zaman asibiti babu dad'i idan yaso saika dinga zuwa kana dubata a gida
Likitan yace wannan ba wata matsala bace ko yanzu za.a iya sallamarku yanzu zan turo sister lami ta d'an taimaka mata ta gyara jikinta ta d'anci abinci dan ta sami k'warin jikinta sai in sallame ku

Dattijuwar dake zaune tana sauraransu tace a a k'yaleta zamuje gida zan gasata da kaina Kai dai bamu sallama likita yace to carften zo muje ka karb'a sai Ku wuce ya amsa da to ya bishi yana satar kallon Fatima

Bayan sun karb'i sallama sun fito tana rik'e a jikin dattijuwar suna gaba carften na binsu a baya yadda haj kewa bak'uwar wata kulawa ta musamman shine ke burgeshi yana ganin yadda take tarayrayarta har saida ta kawo ta mota ta bud'e baya ta zaunar da ita tana fad'in sannu kwanta ki huta kinji 'yata bari muje gida ki samu kiyi wanka ki huta ahankali ta furta na gode umm@ Allah ya saka da alkairi
Kul hajiyar tace kada in kumajin Kalmar godiya a tsakaninmu ta kalli carften dake faman kallonsu yana murmushi tace to mlm kallamu shiga mota ka kaimu gida
Ya d'anyi murmushi yana shafa kansa yace Kai haj nine kuma kallamun yau ta bud'e gaba ta shiga tana fad'in shugoni ka kaimu idan ba kallamunba da menene Kai tun d'azu Ina kallonka ka dami 'yata da kallo ka hanata sakewa ya shiga ma zaunin direba ya zauna yayiwa motar key yana murmushi tare da fad'in haj kenan.



Cikin'yan mintina suka isa wani katafaren gida me mutuk'ar kyau yayi hon megadi ya bud'e musu ya shiga yai parking a parking lot da temakon haj fatima ta fito daga motar ba kuma ta saketa ba har saida ta kaita had'ad'd'an d"akinta me mutuk'ar tsaruwa ta zaunar da ita akan gado ta nufi band'aki tana fad'in Bari in had'a miki ruwa kisamu ki gasa jikin ki k'yaji dad'i ta amsa da to cikin d'an k'ank'anin lokaci ta fito tazo ta Kama Fatima ta mik'ar tana fad'in zo muje in daddanna miki jikin

Cike da kunya Fatima tace zan iya Umma haj tace kin tabbata ta d'aga Kai cike da jin kunya
Duk da haka saida ta kaita har ban d'akin sannan ta fito ta nufi kicin domin ta bawa jimmala me aikinta umarnin ta shirya abincin da mara lfy ze iya ci amma saita tatda tayi nisa ma da aikin dattijuwar tace sannu jimmala da aiki kamar kinsan abinda zance kiyi har kinyi nisa
Jimmala tai murmushi tace haj ai sojane yaiyo waya yace a girka haj tai murmushi tace Ina ruwan carften to in kin kammala sai ki shirya mana a falo ba lallai ta iya hawa dinning ba jimmala ta amsa da to haj
Ita kuma ta juya ta nufi falo a tsakiyar falon ta tatda carften a tsaye da alama shigowarsa kenan tace a a soja ya naganka a tsaye
Yace ai shugowata kenan haj kayane na siyowa yarinyar nan kada tayi wanka tarasa na sawa nasan naki baza suyi mata ba!
Haj tace aikuwa ka kyauta d'an albarka kamar kasan abinda ya fito dani kenan to bari na Kai mata ko ta fito sai ta shirya ta fito taci abinci ya amsa dato, ta nufi d'akinta shima ya nufi d'akin sa dan ya d'an watsa ruwa

Fitowarta kenan haj ta shigo tana ganinta ta Saki murmushi tace Masha Allah sannu yarinyata harkin fito toga kaya kisa saiki fito kici abinci Ina falo Ina jiranki ta amsa dato ita kuma ta fita
ta shirya acikin doguwar rigar da aka bata tayi kyau sosai saidai ta d'an rame kasancewar halin data shiga na rashin lfy a falon ta tatda haj ta durk'usa ta kuma gaisheta haj tace Masha Allah dama haka kike da kyau tayi murmushi tare dayin kasa dakai cike da kunya haj tayi murmushi har zuciyarta take jin k'aunar yarinyar da ko sunan ta bata saniva da kanta ta zuzzuba mata abincin ta mik'a mata tare da fad'in maza kici idan ba hakaba in baki da kaina Danni ba a fulako a gidan nan ta karb'a duk da bakinta babu dad'i haka ta rink'a ci kad'an kad'an gudun kada haj taji babu dad'i idan bata Ciba a jikinta taji Ana kallonta ko bata juyaba taji kaifin idanuwansa a kanta tasake jan mayafin kanta ta kuma rufe jikinta tare da ture abincin daga gabanta tace Umma na k'oshi
Umma ta d'an harareshi saboda ta fahimci ganinsane ya hanata ci tace a a yarinyata Idan kin fisan kici ke kad'ai to tashi ki koma d'aki,
ta sake yin k'asa da Kai tare dayin d'an murmushi tace a a wlh Umma k'oshi nai kinsan har yanzu nakin nawa babu dad'i, haj tace sannu haka nefa
Ya zauna a kusa da haj yana cewa wato yau haj kinyi'ya ko nemana ma bakyayi ko haj tai murmushi tace daga yau na dena yayinka ga'yatanan ta zo yaja plet d'in da haj ta gama zuba abincin yace ai shikenan ni n gudu Adamawa gurin innaye dama wannan zuwan da k'yar ta barni na dawo,
Haj tai murmushi tare da fad'in da yafima
Har suka kammala cin a bincin kanta yana k'asa tanajin hirar dasuke amma bata tanka ba idanma sun sata saidai tai murmushi bayan sun gama jimmala ta kwashe kayan ta gyara wajen haj ta gyara zamanta tace kiyi hak'uri yarinyata muna ta mu amala bamusan sunan juna ba ni sunana haj ruk'ayya mu 'yan asalin jahar Adamawa ne aikine ya dawo da megida na jahar nan wannan shine Wanda tsautsayi yasa ya bigeki yaronane sunansa ishak munasan ki fad'a mana sunan ki da inda kika fito domin mukira iyayenki dan yau kimanin kwanaki biyu kenan da samun hatsarin da kikai kinga duk inda'yan uwanki da iyayanki suke suna cikin tashin hankali da fargaba rashin sanin halin da kike ciki


Fatima ta d'an gyara zamanta tace da farko Ina mik'a godiyata ga Allah mad'aukakin sarki sannan Ina godiya da irin taimakon da kuka yimin ni sunana Fatima ahamad uba.







Mmn baby nusy 07010238476
11/19/21, 7:58 PM - Ummi Tandama???i: WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200# ZAKU IYA BIYA TA 3048536089 KO KUTURO CARD WAYA MTN TA 07010238476 DUK WANDA YA KARANTA BE BIYABA SHIDA ALLAH.






Ya Allah kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka kashirya mana zuri a ameen??R0???_





6??_/Q9??_/QC?&
{7??_/Q0??_/Q
FATIMA AHAMAD UBA shine cikakken sunana
Alh Ahamad mutumin cikin garin kanone an haifeshi a unguwar sani mainagge su biyu iyayensu suka haifa da shi da k'aninsa mustapha sai mahaifiyarsu me suna Fatima wadda suke Kira iya
Iya macece mai kirki da San jama a ga yawan ibada haka kuma abin hannunta be rufe mata idoba.
Mahaifinsu Alh.uba Allah yai mai rasuwa tun suna yara k'anana sun taso cikin maraici. Iya taci gaba da kula dasu da'yar Sana'ar data keyi,domin mahaifinsu ya mutu bebar musu komai ba sai gidan da suke ciki.
A haka iya taci gaba da kulawa da su har Allah ya raya matasu suka kammala secondary school kasan cewar halin rayuwar da suke ciki bebar babana yaci gaba da karatu ba dan dama tuni Kawu mustapha yak'i makaranta saiya kama'yar buga buga domin tallafawa iya da rage mata d'awainiya.


Ahaka cikin ikon Allah, Allah ya had'a mahaifina da Alh salisu mutumin garin katsina yana zaune a kano cikin unguwar d'isu
Dalilin had'uwar tasu kuwa wata rana Abba na ya dawo daga kasuwar kwari,inda yake zuwa sana'ar dako idan ya samu yana tafe,a hanyarsa ta komawa gida ya tsinci wata jaka a gefen hanya harya gotata sai ya dawo ya d'auka batare daya bud'eba ya nufi gida da ita ya shiga da sallama iya dake zaune a tsakar gida tana k'ulla bushasshin kayan miyan da take siyarwa ta amsa tana cewa "sannu da zuwa baban gida, da yake haka take kiransa sunan uban miji gareshi ka dawo?
Ya amsa, yauwa iya na dawo, sannu da gida ta amsa da yauwa ga tuwanka can a gindin murhu d'auko kaci yanzu haka tunda ka fita baka sanya komai a cikin kaba ya d'auko yazo gefen tabarmar da take zaune ya zauna yana cewa wlh kuwa iya kamar kinsani
Iya ta d'ago ta kalleshi cike da tausayawa ganin jakar da tai agefensa tace a a wannan jakarfa babangida
Ya d'auko jakar yana cewa wlh iya a hanya na tsinceta can gefen hanya bamma duba ba na d'auko ko zamuji me cigiya sai a bashi

Iya ta kalleshi ta kalli jakar tace kaima baban gida da rigima kake kawai daga ganin jaka a hanya saika d'auko ba kasani ba ko abin cutarwane a ciki

Yayi murmushi yace babu komai in Allah ya yarda sai alkairi iya
Ya janyo jakar yana cewa bari muga menene aciki iya ta dakata da abinda take ta zubamai ido tana sauraranshi.
Ganin abinda yake cikine yasa ya matsa baya da sauri tare da fad'in subahanallah iya ai kud'ine a ciki!
Iya tace kud'i kuma d'annan! Ta fad'a tana lek'awa. Aikuwa kud'ine da gaske ta fad'a tare da komawa ta zauna tana cewa, kuma kace a hanya katsinta."
Yace wlh iya
Ta d'anyi Jim na d'an lokaci sannan tace Allah sarki duk wanda ya yarda wannan dukiyar yana can cikin tashin hankali."
Yace wlh kuwa duk Wanda ya yarda wannan dukiya bashi da kwanciyar hankali."
Iya tace sosai ma Ku....
Karar da sukaji a cikin jakarne ya katse su suka zubawa jakar ido cike da tsoro har abin ya dena basu motsa ba ba kuma sucewa juna komai ba bayan d'an lokaci abin ya kuma d'aukar k'ara a tsorace ya zura hannu a cikin jakar ya d'auko abinda ke k'arar wata 'yar k'aramar wayar hannuce me kyau ya latsa inda yake ganin Ana latsawa idan an Kira waya a tsorace yake komai kamar Wanda za a Kama jin Ana masa sallama yasa ya d'an sami nutsuwa ya amsa, Wanda yaiyo wayar yai mai bayanin shine ya yadda jakar da kuma inda yake tunanin ya yar
A bayanin da yaimai yasa ya fahimci tasa ce yai mai kwatancen gidansu domin ya zo ya k'arbi kayarsa basu dad'e da gama wayar ba yana yiwa iya bayani, yaji wani kiran ya shigo yake sanar masa ya iso
Iya ta ce ya je ya shigo dashi bayan ya fita sun gaisa da mutumin yai mai ba yanin kansa yaji dad'i yace yaimai sallama da mahaifinsa ya gaya mai ya rasu saidai mahaifiyarsa yai masa iso har zuwa cikin gidan iya ta shin fid'a masa tabarma ya zauna suka gaisa cikin girmama juna ya fara bayani
Ni dai sunana Alh salisu ni mutumin unguwar d'isune Ina harkar kasuwanci to a d'azune munyi cinikayya da wasu munrabu Ashe bansa kud'in a motaba sai da naje gida tukun naga babu na koma wajen bangani ba har na fidda rai sai na tuna akwai wayar da nasa aciki shine na Kira duk da banyi tunanin za.a d'agaba sai gashi an d'aga harda yimin kwatance inzo in karb'a na gode sosai.

Iya tace menene na godiya ai duk yiwa Kaine
Yayi murmushi yace ai dole inyi godiya wlh bantab'a tunanin ganin kud'in nan ba saboda yanzu duniya babu gaskiya abinda ake zuwa har gida a sata balle kayar ai idan babe tsananin gaskiya da tsoran Allah ba babu me bayarwa bare kud'i masu yawa haka.

Iya tace to Allah ya k'ara tsarewa sai a dinga kulawa!ya amsa da insha allahu ya d'auko kud'i ya bata tak'i karb'a yace dan Allah iya ki karb'a kisa albarka bawai na bakine da wata manufa ba, a,a saidan Ina ganinki tamkar ma haifiyata ne kamar yadda Ahmad ya rasa mahaifi haka nima na rasa mahaifiya.

Iya ta tausaya masa k'warai da gaske dan mutuwar mahaifa abune me mutuk'ar ciwo Wanda baka warke wa har sai sanda taka tazo tayi mai ta aziya tare da yi musu addu.a
Yaci gaba da cewa idan babu damuwa Ina so in tafi da Ahmad inda nake ya gani dan inaso mufara harkar kasuwanci tare tunda yace babu abinda yake siyarwa."
Iya tayi murmushi tace babu komai kuje ya gani mun gode Allah yasa ka da alkairi."ya amsa da amin
Ya mik'e suka fita suna k'arawa juna godiya."
Har soro iya ta rakosu saida taga tashin motarsu sannan ta koma gida. Bata dad'e da komawa ba mustapha ya shigo ya nemi guri ya zauna yana cewa, iya nifa yunwa nakeji.iya ta kalleshi tace Anya kuwa mustapha sai yanzune yakamata ka nemeni tun safe da kasa k'afa kabar gidan nan baka sake waiwayata ba sai yanzu da yunwar cikinka ta ciyoka.yanzu kayi dedai kenan muatapha yanzu ace duk abinda ze farantamin rai baza kayi shiba kana ganin yadda d'an uwanka yake k'ok'ari da fad'i tashi a kanmu amma nazakayi koyi da halayyarsa ba
Ya zumb'ura baki batare da yace komai ba can kuma ya hango kud'i sun lek'o a gefen ta barma da saurin baki yace iya wad'annan kud'a d'an fa?
Tai mai banza ta cigaba da safgarta
Ya sanyaya murya yace kiyi hak'uri iya in Allah ya yarda zanyi k'ok'arin koyi da halayyarsa"
Iya tayi murmushi ko kaifa ai fad'an da kaga Ina yi ma ba wai bana Sanka bane ba,a'a Ina yine domin inga ka zama mutumin kirki."yace to iya na dena ya sake tambayarta k'ud'in da ya gani ta yi mai; bayanin komai.

Alh salisu ya cika alk'awari ya d'ora salisu akan Sana ar dayafi k'arfi wato sana'ar saro shanu daga garuruwa yazo nan ya siyar ya kuma komawa ya saro wasu.Alhamdudullahi kamar yadda iya ta bani labari mahaifina ya fara Sana'ar da hannun dama,domin kuwa cikin ikon Allah be dad'e da fara sana'ar ba Allah yasa masa albarka daga yasaro zasu k'are ze koma ya kuma saro wasu ganin haka sai Alh salisu ya dinga ware masa ribarsa yana tara masa har zuwa wani d'an lokaci da dan k'a masa yace yaje yaci gashin kansa.
Dan haka mahaifina ya cika ba da bin garuruwa irinsu Adamawa gombe da dai sauransu
A irin hakane Allah ya had'a mahaifina da mahaifiyata a cikin garin Adamawa yaje saro shanu tunda ya d'ora ido a kanta yaji duk duniya babu macen da yake so sama da ita
Da yake Allah yayi aure a tsakaninsu mahaifina ya gabatarwa da baffanta San auren ta da k'yar baffanta ya amence saboda su biyu Allah ya bashi ya'yan saboda haka bayaso yai nisa da su amma ganin itama ta aminta da shi yasa ya bashi ita, don haka mahaifina ya dawo gida domin tafiya da waliyyansa.






Mmn beby nusy 07010238476
11/20/21, 10:11 PM - Ummi Tandama???i: OYOYO???b???bBASY FABRICS COLLECTIONS???aWAJEN SAIDA KAYAN ADO DA K'AWA NA ISASSUN MATA INA MATAN DA SUKEJI DA KANSU MATAN DA SUKA SAN SIRRIN ADO DA KWALLIYA INA'YAR LELEN MIJINTA INA WADDA TA KE SO TA BURGE MEGIDANTA A KODA YAUSHE TAURARANTA YA DINGA HASKAWA,INA"YAN MATAN DA SUKA SAN SIRRIN ADO MASU RIK'E ZUKATAN SAMARINSU DA IYA SA SITTIRA BASY FABRICS COLLECTIONS SUN KAWO MUKU INGATTATTUN KAYAN ADO ABAYAS & LACES AKAN FARASHI ME SAUK'I SUNA KANO ZOO ROAD NUMBER 08032682096 MUNA KASUWANCI CIKIN AMINCI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login