Showing 18001 words to 21000 words out of 71253 words

Chapter 7 - YANCINA KO BUDURCINA COMPLET by Ummi Muhammad Usman.doc

hak'uri da abinda yai miki Fatima
Kici gaba dayi mai komai na kyautatawa da sannu wata rana komai ze wuce wata rana koda k'ud'i akace yai miki wani abin baze yiba
Kedai ki k'ara hak'uri domin shine maganin komai
Nace to ya umar na gode.
Yace babu komai Fatima ke kamar k'anwa ce agareni fatana dai ki k'ara jajircewa kada ki gajiya
Na daga Kai tare da cewa na gode yaimin sallama ya fita
Nabi bayanshi da kallo a raina Ina inama ya Aliyu yana da kirki kamar ya umar da banyi k'unci a rayuwar gidannan ba

Umar yana fitowa motarsa ya nufa ya shiga ya ja yafita daga harabar gidan ba tare da ya kalli inda Aliyu yake tsaye ya na jiransa ba
Aliyu ya bishi da kallo har ya fice hakan ya tabbatar masa umar fishi yai dan haka ya d'auki motarsa ya bishi a baya

Umar na zaune acikin k'ayatatcen office d'insa yana ta faman duba fayal fayal d'in marasa
Aliyu yai sallama ya shiga
ya amsa batare daya d'ago ya kalle shi ba

Yaja kujera ya zauna yana fuskantarsa yace wai umar meke faruwa lokaci d'aya akan wata can kad'auki fushi dani kada fa kamanta ba Santa nakeba k'ak'abamin ita akai ni kuma nake hak'urin zama da ita to akanme take k'ok'arin wuce iyakarta.

Umar ya dakata daga abinda yake ya kalleshi yace amma a gaskiya Aliyu kaban mamaki da bakinka kake fad'ar haka da kake cewa ba Santa kakeba ai itama ba sanka take ba ko ta tab'a cewa Aliyu Ina Sanka bata fad'aba
Dan haka yadda a Kai maka haka itama akai mata yanzu haka ma yadda akai mata tafika jin zafi da ciwo
Amma ta hak'ura ta jure take binka domin aljannarta ta kuma faran tawa iyayenta rai

Amma Kai kake wulak'antata kana tunanin duk randa Abba yasan irin zaman da kuke zaku kwashe ta dad'i ne da shi
ba Kai ba harni laifin saiya shafa
tobari kaji in fad'a maka gaskiya tun yanzu zanzare hannuna daga cikin al.a muranka tunda kai bakajin shawara tunkan Abu ya k'arasa lalacewa a..
Aliyu ya dakatar dashi dacewa wai duk akan yariyar canne kake fad'ar haka har kake tunanin janyewa daga gareni haba umar kasan abinda kake fad'a kuwa kada kamanta abotar mufa tun muna yara
mun k'ulla alk'awarurruka da dama a tsanin mu
Mun yarda da junanmu bamu tab'a samun sab'ani ba sai yanzu akan yarinyar nan
Umar ya da katar dashi da cewa da kata Aliyu yanzuma ba ita tasa ba
Kai ne
Me ye dalilin da bazaka kula da matarka ba ka sauke hak'k'ok'inta da ke kanka
Wallahi Allah babu ruwansa da rashin son da kake fad'ar ba kayi mutuk'ar kazalunceta saiya saka Mata dan ba kyaleka zeba muddin da aurenta a kanka

Aliyu yaja numfashi yace to shikenan in sha Allah zan gyara hakan baze kuma faruwa ba naima alk'awari shikenan ko

Umar yai murmushi yace ya wuce Allah ya baka iko idan ka gyara zanfi kowa farin ciki
Aliyu ya gyara zamansa yace Ina cikin matsala umar
Umar yace subahanallah matsala kuma abokina meya faru?
Babbar matsala ta itace Abba ya barni in auri Hindu tunda dai na auri zab'insa
Umar yace bangane abinda kake nufi ba?
Aliyu yace Ina nufin muje musami Abba a Karo na biyu da zancen auren Hindu
Umar yace haba Aliyu kaifa kace mata biyu basu daga cikin tsarinka?

Aliyu yace daba
amma yanzu dole inyi tunda haka Allah ya tsaramin kuma kada kamanta ina San Hindu akanta na fara soyayya sannan akwai alk'awarin aure tsakaninmu umar ya kyalkyale da dariya yace Aliyu kenan Ali haidara Ali jan zaki Ali gadanga k'usar yak'i Ali...
Aliyu ya d'aga mai hannu yace wai meye hakane umar ya ya Ina gaya maka matsalata kana shugoda wasa cikin lamarin.

Umar ya gyara zamansa yace Aliyu kenan ai dole in shugo da wasa kadafa kamanta dududu watanni uku rak dayin aurenka sannan yanzu mu kuma zuwa da wani batun auren ai kaima kasan Abba baze amince ba

Aliyu yace haba umar saboda me kake tunanin Abba baze amince ba bayan ba yau nai auren ba ba kuma jiya ba kai da bakinka kace watanni uku har da wasu kwanakima dan haka ni Ina tunanin Abba ze amince musamman ma da yake ya San da maganar dama tuni

Umar ya d'anja numfashi yace to shikenan mu gwada mu gani sai musa ranar zuwa ko Allah ya bamu sa.a
Aliyu ya amsa da ameen summa ameen ai sai musa rana weekend d'innan ya kamata mu tafi ze fi ko
Umar yace to Allah ya kaimu a ranar zamu dawo ko kuwa acan zamu kwana yace a.a aranar zamu dawo kodan yarinyar nan dan ba da ita zamu tafiba
umar yai murmushi yace Allah ya kaimu.A??]
{



Please
Comments
Share



Mmn beby nusyA??]
{A??]
{A??]
{A??]
{



Ayimin afuwa za.a ganshi kad'an wani uzirine ya kamani in sha Allah daga yau kullum zaku dunga ganin posting d'ina



WhatsApp number 07010238476
11/18/21, 11:00 PM - Fiddausi Yunus: ??c??c"YANCINA KO BUDURCINA??c??c



WRITING BY



UMME MUHAMMAD HASSAN



(Mrs Aliyu jibrin Ali)



WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200 NAIRA ZAKU IYA BIYA TA 3048536089 KO KATIN WAYA AIRTEL KO MTN DAN ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTAMIN BOOK KO BANCE ALLAH YA ISA BA KUNSAN HAK'K'IN WANI ABIN TAMBAYANE




???a??.\LOVE STORY HOT ROMANTIC



Please matan aure kad'ai???i



Ya Allah kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka ka shirya mana zuri.a ameen??R0???_

3??_/Q3??_/QC?&
{3??_/Q4??_/Q
Aliyu da umar zaune agaban Abba bayan sun gama gaya masa abinda ke tafe dasu
Abba yai shuru na d'an lokaci sannan ya kallesu bayan yaja numfashi yace haider bazan hanaka k'arin aure ba domin nasan Allah ne da kansa ya halatta maka auren macce fiye da d'aya sannan yace idan bazakai adalci ba ka auri d'aya dan haka nake baka shawara idan kasan bazakai adalci ba to kabar matarka d'aya ta isheka rayuwa domin samun dacewa ranar alk'iyama
Idan kuma kanasan zaka k'ara aurene domin zab'in da nai maka be maka ba
zaka k'ara domin ka wulak'antata to ka sanar dani tun wuri kada ka munafinceni ko ka yaudareni abinda nake so kasani shine fatima marainiyace
Idan kasan zakai aurene domin ka musguna mata ka kuntatawa rayuwarta to ka sakomin ita
Domin amanace ita a hannuna naiwa mahaifiyarta alk'awarin rik'eta tsakani da Allah
Ina horarka da ka rik'e matarka da muhimmanci kada kazalinceta koka musguna Mata
Wallahi Aliyu idan nasameka da laifin zalintar yarinyar nan zanyi mummunan sab'a maka ya juya ya kalli umar yace
umar ya amasa na.am abba yace inaso kazamo shaida atsakanina da abokinka bana amince da auren shiba muddin na sameshi da laifin wulak'anta yarinyar nan ko musguna mata zan d'auki mummunan mataki akanshi

Umar yai k'asa da kansa cikin ladabi yace in Allah ya yarda Abba baza kasameshi da wani laifi ba zasu zauna lafiya
Abba yace to Allah yasa haka suka amsa da ameen
Abba yace maganar turawa gidansu yarinyar da kakesan kuwa zan tura aminai na ayi magana da mahaifinta idan ya amince zanyi shirye-shiryena da ya kamata kaima saikai shirinka dan ba wani lokaci za.aja ba nan da sati uku zuwa hud'u za ai komai a gama kaidai ka sanarwa med'akinka sannan kuma ka rarrasheta kayi mata komai na kyautatawa

Aliyu ya amsa da in sha allahu za ayi hakan na gode sosai Allah ya k'ara girma ya amsa da ameen ku tashi kuje allah yai muku albarka ya sawa abin albarka gaba d'aya suka amsa da ameen sukai mai sallama suka tashi suka fito Dan ayau suke San komawa abuja

Suna fitowa Aliyu ya rumgume umar tare da fad'in Alhamdulillah umar naji dad'in amincewar Abba Ashe burina ze cika
Umar yace masha Allah na tayaka farin ciki Allah ya tabbatar da alkairi saidai abinda nakesan in tuna ma shine ka kula da maganar Abba akan Fatima Dan Allah ka tsaida adalci atsakaninsu
Aliyu yad'an sake shi ya kalleshi yace wallahi umar addu.ar danake yi kenan ubangiji ya bani ikon yin adalci a tsakaninsu
Saidai kasan matsalar d'ayace
Itace duk adalcin da zanyi atsakaninsu zanyi saidai bazan iya kusantar yarinyar nan ba saboda ta yimin k'ank'anta idan naje mata a yanda nake ai sai inji mata ciwo kuma ma sai ta rainani

umar dake kallonshi yace sannu me k'arfin doki
amma a gaskiya furucinka yaban mamaki a matsayinka na me ilimi sannan cikakken likitan mata
Dan Allah ka gayamin ayar kur. ani kota hadisi da yace ba za.a kusanci yarinyar mace matar sunna dan kawai shekarunta sun kasance kad'an
Aliyu yaja numfashi tare da girgiza kai yace babu amm...
Umar ya dakatar dashi da cewa babu wata amma auren yarinya k'arama koyine kuma sunnane me k'arfi manzanmu fiyayyan ha litta (s a w)ya auri matarsa nana Aisha shekarunta basu gaza tara ba wasuma sukace shida kaga auren yarinya k'arama sunnane kenan kuma da kake cewa bazaka iya kusantartaba saboda kada ta rainaka kenan duk masu auren k'ananan yaran rainine yake shiga tsakaninsu
Yai murmushi yaci gaba kaga malam babu wani raini illah girmama juna da k'ara dan k'on so da k'auna abinda nakesan kasani wlh auren irin su Fatima yafi kawo farin ciki da kwanciyar hankali ga samin nutsuwa fiye da auren babbar mace wayayya mace me shekaru da ilimi a kullum gani zata dingayi tayi karatun boko ishashshe bazaka juya taba dan kallon kanku d'aya take ma bazata bikaba baka isa kuma ka bata umarni tabiba saboda tana ganin zurfin iliminku d'aya shekarunku d'aya wayonku da basirarku sai tai tunanin zezamo d'aya ko ta dunga tunanin tafika
Umar yai d'an tattaki tare da matsowa ta dafa Aliyu yace
Aliyu kai likitane cikakke likitanma na mata kasani ka kuma tabbatar babu irin namijin da kamar Fatima bazata iya d'aukaba dan shekarunta sunkai kuma jikinta ya nuna hakan dan ta mallaki abubuwan cikakkiyar mace wanda acikin manyan matan ba kowace ta kai taba

Shawarar da nake baka ka tsaida hankalinka guri d'aya ka kula da matarka da daraja kabata hak'k'inta dake kanka tun kamin lokaci ya k'ure maka ba wai ina kushe manyan mata bane a.a kasan ni in gaskiya tazo saina fad'a

Aliyu yai murmushi yaja hannun umar suka tafi yana cewa Allah ya bani ikon yin komai bisa adalci umar yace Ameen ya Allah

Mama da ummi kuwa kwata-kwata zuciyoyinsu basu so k'arin auren a yanzu ba sun amencene badan ransu ya soba saidan ganin abba ya amence masa saidai sun tausayawa Fatima mutuk'a domin a ganinsu shekarunta sunyi kad'an da fara d'aukar matsalar kishiya musamman da basu gamsu da tarbiyyar da nagartar wadda ze auro d'inba
Mama bata so auren ba kwata-kwata tayi takaicin da maganar ta fara zuwa gurin abba dan dabeje ba da ta dak'atar dashi to yariga yaje dole babu yadda ta iya tanaji ta na gani haka tasawa abin albarka tayiwa Aliyu gargad'i sosai akan kula da Fatima dan sosai take jin soyayyar yarinyar acikin zuciyarta

Suma su faiza basu so k'arin auren ya haider d'inba amma hakannan suka hak'ura sun so zuwa wajanta mutuk'a amma hakan be yuhuba dole suka hakura

Shirye shirya yakankama ab'angaren ango da amarya dan duk wata gayyata da baiyiba a aurensa na farko yanzu kam yayi dan wannan auren shine auren da yake so ko da yaushe acikin zirga zirga suke shida umar dan ganin komai yayi mai yadda ya ke so

A b'angaren amarya kuwa suma shirin bikin sukeyi sosai da sosai sun gayyaci jama. a iri daban daban haka uwar amarya Momy ta dage da gyara yarta da kayan gyara na mata sosai da sosai dan San ganin yarta ta dawo cikakkiyar budurruwa wadda bata tab'a sanin d'a namiji baA???



SLM
Ina sanar da "yan uwa way'anda basu biya kud'in book d'in suba da suyi k'ok'arin biya idan Allah ya kaimu ranar Sunday zamu rufe group d'inmu na "YANCINA KO BUDURCINA zamu bud'e wani duk wad'anda suka biya kud'ad'ansu zamuyi addin d'insu zuwa sabon group d'in da zamu bud'e dan bazamu kuma sakin book a ko wanne group ba sai wanda mutane suka biya
NA GODE




Mmn beby nusyA??]
{A??]
{A??]
{A??]
{A??]
{




WhatsApp number 07010238476
11/18/21, 11:00 PM - Fiddausi Yunus: ??c??c"YANCINA KO BUDURCINA??c??c



WRITING BY


UMME MUHAMMAD HASSAN


(Mrs Aliyu jibrin Ali)


WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200 NAIRA ZAKU IYA BIYA TA 3048536089 KO KATIN WAYA AIRTEL KO MTN DAN ALLAH IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTAMIN BOOK KO BANCE ALLAH YA ISA BA KUNSAN HAK'K'IN WANI ABIN TAMBAYANE.




??.\???aLOVE STORY HOT ROMANTIC




Please matan aure kad'ai banda yan mata???i



Ya Allah ka jik'an iyayenmu kaiwa rayuwar mu albarka ka shirya mana zuri.a ameen??R0???_




3??_/Q5??_/QC?&
{3??_/Q6??_/Q
Ni kuwa bansan wainar da ake toyawa ba a lokacin domin kuwa bai sanar daniba haka zalika bansan da wani batun auren Saba tunda har na kwashe tsawon watanni shidda a gidansa maganar minti biyar bata tab'a had'a muba haka murmushinsa tsada gareshi a gareni dan sai ince tunda nake ni da shi bantab'a ganin murmushin sa ba duk da dai yanzu yad'an canza daga yawan d'aure min fuskar da yake yi dan yanzu bayan mun gaisa da safe yakan tambayeni da ko Ina buk'atar wani abun
Na kance a.a
Sai yace idan Ina da buk'atar wani abun ki dinga sanar dani na fannin kicin ko buk'atun kanki
Ni kuwa kullum amsar itace babu dan komai Ina da shi babu abinda na nema narasa a cikin gidansa daya wuce kulawa daga gareshi bansan kuma sai yaushe zan samuba.

Aliyu da umar zaune acikin mota yayinda umar ke Jan motar Aliyu na gefensa umar ya saki doguwar hamma akaro na uku tare da kallon Aliyu yace Kai abokina agaskiya na gaji da yawan nan kasan Allah yunwa nakeji mutuk'a kwata-kwata wunin yau banci wani abin kirkiba
A gaskiya zirga zirgar sha.anin biki a kwai wahala
Aliyu ya kalli agogon hannunsa yace wlh ni kaina bakaji yunwar danake jiba dan rabona dana sanya wani Abu acikina tun goman safe gashi yanzu k'arfe tara da kwata na dare
Umar yace to yanzu ya'ya za.ai
Yace kawai muje gidan abinci mafi kusa muyi maganin matsalar mu
Umar ya kalleshi cikin harara yace haba ya za.ai da mutum cinmu da aurenka muje wani gidan abinci ai wannan ma abin kunyane
Aliyu yace to yanzu yaya za.ayi
Umar yace gidanka zamu matarka ta sammana muci ko ma rage yunwar dake addabarmu
Aliyu yace haba dai yama za,ai muci abincin yarinyar nan kaima kasan ba dad'i zeba
Umar ya harareshi yace idanma ni kakewa rowa to yau shi zamuci haka kawai ga Abu agida sai muje dawa
Ya karya kan motar zuwa layin gidan Aliyu yana cewa barima ka gani muk'arasa
Aliyu ya amsa da to badan ransa ya soba saidan kada umar ya fahimci har yanzu babu wata alak'a me k'arfi a tsakaninsa da yarinyar

A harabar gidan umar yai parking d'in motar suka fito suka shiga falon Kai tsaye da sallama a bakunansu suka nemi guri suka zauna babu kowa acikin falon sai sansanyan k'amshine yake tashi
Umar ya k'arewa falon kallo ko Ina a share a goge tayals d'in tad'al tad'al tamkar ba.a takawa ya maida kallonsa kan Aliyu yace agaskiya kayi sa.ar mata dan kuwa akwaita da tsafta duk lokacin da kashigo gidan nan zaka sameshi a tsaftace a gyare ga wani k'amshi na musamman yana tashi ka godewa Allah da ya baka mace me tsafta

Aliyu ya bi falon da kallo sauda yawa shima yakan yaba mata a zuciyarsa idan yai la.akari da duk girman gidan take iya tsafta ce shi ita kad'ai

Na kammala komai nawa na hidimar gida na fito daga kicin zan koma d'aki sanye nake da dogon hijab d'ina me duhu har k'asa
Ganunsu da nai atare da umar a zaune a cikin falon adedai wannan lokacin nayi mamaki dan basu tab'a yin hakan ba sannan banji shugowarsu ba na k'arasa cikin falon da sallama na durk'usa nace sannu da zuwa ya Aliyu
Ya amsa da yauwa ya gidan
Na amsa da alhamdulillah
Nace Ina wuni ya umar
Amsa lafiya lau k'anwata ya zaman shuru babu abikin hira
Nai d'an murmushi tare da cewa alhamdulillah
Na mik'e da niyyar shiga d'aki
Umar ya kalli Aliyu batare da yace mishi komai ba har na Kai bakin k'ofa naji muryarshi ya kirani kamar yadda yasaba yace KE
na jiyo tare da fad'in na.am dan nariga na Saba haka yake kirana tunda nake ban tab'a jin ya Kira cikakken sunana ba saidai ya cemin KE

Yace ki d'an kawo mana d'an abinda zamusa aciki na dawo cikin nutsuwa na tsuguna cikin sanyin murya nace saidai tuwan semonvita nai miyar d'anyar kub'ewa amma bari in dafa muku wani abin dan kada kuga na d'ad'e

Umar yai murmushi yace kinga kawo tuwan shima ya wadatar dama mun kwana biyu ba muci ba kuma zamufi jin dad'in cinsa a yanzu

Na mik'e na nufi kicin d'in tuwan semonvita ne miyar d'anyar kub'ewa wadda taji naman kasuwa sai kunun aya wanda yaji had'i na musamman na ciroshi daga firige yayi sanyi dan yanzu shina mayar ruwan Shana bana rabo dahad'ashi na had'a musu da farfesun naman kaza da ruwan roba naje nakai kan dinning table na shirya
Na koma falon na durk'usa na sanar musu na kammala shirya abincin
Umar ne yace sannu da k'ok'ari Fatima shi kuwa KO k'ala baiceba na tashi na wuce d'akina

Shiru ya d'an ziyarci falon Aliyu ya katse shirun da kallon umar yace to katashi mana ga abincin can yana jiranka
Umar yace ai nazata kadena maganane da naji Kai shuru kanaji ana magana sai faman zazzare idanu kake

Aliyu yai maumushi ya mike yace kaifa kafiya sharri towa zan harara
umar ma ya mik'e yane cewa kaji dashi dai ni muje kabani abinci inci ko na samu inje gida in kwanta in huta
Suka k'arasa dinning d'in sukaja kujera suka zauna umar ya kalli Aliyu yace to bisimillah zuba mana mana
Aliyu ya harareshi yace abincin ma ni zan zuba maka Ashe bazaka Ciba agidanka waye ya ke zuba ma
Kaidai ba mataba bare ince matarka
Umar ya d'auki plet hade da bud'e kular yana cewa kaida kake da matar banga banbancin muba
Aliyu yai murmushi tare da d'aukar plet ya saka malmala d'aya yar k'arama
Umar ya kalle shi yace wai duk fad'ar yunwar iya d'an abinda zaka kaci kenan
Aliyu ya d'age gira d'aya batare da yace komai ba
Umar ya tab'e baki tare da bud'e miyar zezuba wani daddad'an k'amshi ya bugeshi ya lumshe ido tare da had'iye wani yawu da ya tahumai bashiri ya zuba miyar tare da Jan plet d'in gabansa dan jiyai gaba d'aya yunwar da yake ji tatashi
Aliyu ma ya zuba tunda suka fara cin abincin babu me cewa kowa komai sunyi shiru tamkar babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login