Showing 27001 words to 30000 words out of 79955 words
Chapter 10 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
baya bukatar
amincewar kowa a kai, amman yana son goyon bayan Khalid, ko yaya ne yana son Khalid ya
kara mishi karfin gwiwa
"Ban san me zance ba ne ba"
Khalid ya furta cikin sanyin murya yana dorawa da
"Da gaske na rasa abinda zance, na san abune da zai faru wata rana, amman yanzun baiyi
sauri ba?"
Kafadu Nawfal ya dan daga mishi cikin rashin tabbas, mutane na tsoron abubuwa mabanbanta,
kananu da manya, duka biyun ne suka hade mishi waje daya, babban tsoron shi bai wuce
kasancewa shi kadai a filin duniyar shi duk kuwa da rashin girman ta, yana da su ya sani,
amman ba zai kira su nashi shi kadai ba, Nanna ta sha jaddada mishi ita da duka ahalinta ba
nashi bane ba, rabasun da takeyi da shi ba zabinta bane ba, dole akayi mata. Yana son ya
samu wani abu da zai kira nashi.
"Nawfal..."
Khalid ya kira yana saka shi sauke numfashi
"Ban sani ba Hamma, watakila yayi sauri, kawai ya faru ne..."
Baki Khalid ya bude zaiyi magana aka kwankwasa dakin
"Waye? Shigo?"
Cewar Khalid bayan an sake kwankwasa dakin a karo na biyu
"Nanna tace ka fita da motar ta a duba za'ayi abu da ita yau"
Kai Khalid ya jinjina
"Ka karbo mun mukullin..."
Sanin halin Lukman ya sa shi mikewa ya bude kofar yana kiran Lukman da har ya kusa kofar da
zata fitar dashi daga bangaren nasu
"Yanzun fa, ka dawo yanzun ka kawo mun"
Juyawa kawai Lukman yayi cikin sanyin yanayin shi da baisa tafiyar shi ta kasance ta malalata
ba. Yana da kazarniya sosai, kawai hayaniya ce bayayi, dan ta Lukman duniyar bata tashi ba,
babu wanda zaice ya taba ganin ran yaron a bace, ko a ranakun da babu makaranta ba kullum
kake ganin shi ba. Komawa cikin dakin yayi, kallon ledar kifin da yake ci yayi cikin wani yanayi
da yasa Nawfal fadin
"Ka sa a fridge mana, in ka dawo sai kaci a nutse..."
Dan jim Khalid yayi
"Bafa harshen kowa bane irin naka...zaiyi sanyi, bari dai in kai Kitchen kawai. Muyi magana idan
na dawo?"
Ya karasa yana tsugunna ya tattara ledar kifin
"Ni ma zanje wajen Daada, na so inga Adee, naga kaman akwai mutane da yawa a bangaren"
Kai Khalid yake girgiza mishi tunda ya kira sunan Adee din
"Bata gidan ma, ni na kaisu wajen gyaran gashi ne ko meye ita da kawayenta tun dazun, tace in
sun gama zata kira ni...ka shirya, bari in bi Lukman in karbo mukullin sai in sauke ka"
Khalid ya fadi yana fita daga dakin da ledar kifin shi a hannu. Shima tashi yayi yana hada duk
wani abu da yake son tafiya da shi gidan Daada din a jakar shi ta goyo, dan sai da Khalid ya
dan jira shi da ya dawo, ko rigar da yaso ya sake bai samu ya saken ba suka fita.
**
Daga bakin titi Khalid ya sauke shi saboda motar nata rirrikewa, da kafafuwan shi ya taka ya
karasa shiga, yana hango gidan yana jin zuciyar shi na tsalle har cikin tafukan kafafuwan shi,
dan duk wani taku da zaiyi sai ya kara gudun zuciyar shi. Bai san yayi kewar Daada har haka
ba sai da ya taka soron gidan yaji tsalle-tsalle da zuciyar shi takeyi, rabon da ya ji shi kamar
yaro dan shekara uku da yake dokin ganin wani nashi haka harya manta. Kamar ya karasa da
gudu ya shiga cikin gidan haka yake jin shi
"Daada...Daada Am..."
Shine abinda ya iya furtawa a madadin sallama, sunan na fitowa daga wani lungu na zuciyar shi
inda yake jin kewar Daada kamar yasa ihu
"Daada..."
Ya kara kira yana jin kafafuwan shi sun gaji, kamar dakin nata ya kara nisa. Daada da take daki
a zaune, hankalinta yana kan labaran da take kallo a talabijin dinta ta jiyo muryar shi a kiran
farko da yayi mata, kira na biyu ne yanayin yanda ya furta "Daada Am" din ya saka taji kamar
ruhinta ne yake shirin kubcewa daga gangar jikinta saboda yanda muryar ta dake ta
"Bukar..."
Ta furta da wani irin yanayi mai wahalar fassarawa tana dafa kujera ta mike dakyar, kira na ukku
ne ya mayar da ita ya zaunar tana wani irin maida numfashi, zuciya kenan, babu abinda ya
kaita wahala a kaf halitta ta tsarin jikin dan adam, da bata yaudare su haka ba. Kafin tunanin ta
ya tsawaita Nawfal ya karasa bakin kofar inda yayi tsaye kamar yana son daukar sababbin
hotunanta ne cikin kan shi ya adana a kusa da tsofaffin da yake da su
"Daada..."
Ya sake kira cike da tsantsar kaunar ta, ya manta yanda ita kadai take saka shi yaji abinda yake
ji haka, yanda matsayinta ba zai taba haduwa da na kowa ba a wajen shi
"Bajjo"
Ita ma ta kira shi, sai dai nata idanuwan ba kaunar jikan nata bane da kewar shi kawai, harda
hawaye taf a cikin su da wani yanayi a shimfide da ita kadai zata iya fassara shi. Ko takalma bai
cire ba ya karasa cikin dakin, itama mikewa tayi yana samunta a tsaye, batare da tunanin komai
ba ya zagaya hannuwan shi yana riketa a jikin shi
"Ina kaunar ki Daada, ban taba fada miki ba ko? Yau dai na fada, nayi kewar ki da yawa... Ba
kadan ba fa, da yawa sosai har bansan ya zanyi in fada ba"
Dariya tayi, hawayenta na samun damar zubowa, yayi girma saboda ba zaka kirata gajera kai
tsaye ba, amman kanta da kadan ya karasa kirjin Nawfal din, sake riketa yayi kamar zai cike
gurbin kewarta da yayi na shekaru biyu
"Kashin tsufa Bajjo, karka karyani"
Dariya sukayi a tare yana sakinta dakyar, dan har lokacin wata irin kewarta yakeyi kamar bata
tsaye a gaban shi
"Ina Madina?"
Ya tambaya yana kallon cikin dakin da bai canza mishi ba sam
"Tana dakin ta da littafi, in dai da littafi a hannun ta bata ji bata gani"
Dariya ya sake yi yana zame jakar shi daga kafada ya ajiye akan kujera, sai lokacin kuma ya
kula da takalman da suke kafar shi, dan murza goshin shi yayi, yana rankwafawa ya zare
takalman ya dauke su ya mayar bakin kofa, da hannu ya nuna inda yake tunanin dakin Madina
ne cikin alamar neman tabbaci, kai Daada ta daga mishi, kai tsaye ya nufi bakin kofar yana
kwankwasawa, jin shiru ya saka shi sake Kwankwasawa da karfin wannan karin, yanda ya kasa
kunnen shi yasa shi jin takun tafiyar ta, shekaru biyu kamar wasa.
Zuciyar shi bata doka ba sai da yaga ta murza kofar alamun budewa zatayi, idan yace yanayin
da yake ciki yana da fassara zaiyi karya. Numfashin shi ne ya dan tsaya na dakika kafin yaja
iskar da itama baiji inda ta tafi ba bayan Madina ta bude kofar, wandone a jikinta ta nannade shi
har kusan gwiwarta, sai rigar sanyi marar nauyi, mai hade da hula da ake kira da hoodie a
turance, dogon hannu ne shima ta ja shi kadan, hular nada zaren da ta kama ta kulle shi dan
hular ta zauna mata a kai sosai, sai gilashin ta da ya rufe rabin fuskarta.
Ko ya hasaso yanda Madina ta koma a shekaru biyu rak yanzun daya ganta tsaye a gaban shi
komai ya goge, su duka kallon juna suke, ita tana mamakin yanda akayi ta gan shi a kofar
dakinta, karatu take na wani littafin kimiyya da Salim ya siyo mata, da highlighter a hannunta
tana shaida a duk wajajen da take da tarin tambayoyin da idan yazo zata tsare shi ya amsa
mata taji an kwankwasa dakin, zaton ta Daada ce zata tambayeta wani abin da ta ajiye ta rasa
inda ta kai shi. A nisantaccen mafarki bata hango kasancewar Nawfal cikin gidan ba, shisa
ganin shi ya zama kamar an kwada mata guduma a tsakiyar fuska.
"Madina"
Ya kira, muryar shi na dira cikin kunnuwan ta, tana nan yanda take, muryar shi, sam bata canza
ba duk da ta dade bata jita ba, shi dinma banda tsayi bata jin ya canza
"Madina..."
Ya sake kira ganin kamar ta kasa yarda shi dinne a tsaye, dariya yayi mai sauti yana kai hannun
shi ya taba goshin ta da tayi kokarin karewa tana murmushi
"Kin canza"
Ya furta saboda ya kasa rikewa a cikin shi, ta canza ba kadan ba, wani irin canji da bai taba
tunani ba
"Hamma... Da gaske kaine?"
Tace tana kasa daina murmushi, kai Nawfal ya daga mata shima ya kasa daina murmushi,
ganin yana kara takowa cikin kokarin hade space din da yake tsakanin su yasa ta daga hannun
ta tana matsawa, kai take girgiza mishi, duka alamu sun nuna rungumarta yake sonyi, shi din
dan uwanta ne, duk da na rana daya Daada bata taba mata bayanin dangantar da take tsakanin
su ba. Ta san shi din baya cikin jerin mazan da suka halarta su rungumeta, tana zuwa
islamiyya, tana kuma iya kokarin ta na ganin bata tsallake wasu layuka da zasu iya wasa da
lahirarta ba.
Babban abinda take tsoro bai wuce kwanciyar kabari ba, lahira na ba Madina tsoro fiye da zaton
mai zato, ko mutuwa taji anyi duk yinin ranar bata da sukuni, musamman idan a cikin unguwar
sune, sai ta kasa cire tunanin yanda mala'ikan mutuwa ya kasance unguwa daya da ita, amman
ba wajenta yazo ba, tuni dai yayi mata na zuwan shi babu sanarwa.
"Madina..."
Nawfal ya kira wannan karin yana jan sunan nata, dariya tayi, mamaki yake ba kadan ba, har
tayi girma haka, girman da take kokarin jan layi a tsakanin su. Hango ranar daya bar kasar
yakeyi, yanda dakyar ya bambare Madina daga jikin shi, dakyar ma ta bar shi ya tafi, amman
yanzun har tayi girman da take ganin ta wuce ya rungumeta, shekaru biyu suna da nisa ne har
haka? Yayi tambayar cikin kan shi yana neman amsa duk a waje daya.
"Fito to... Nayi kewar ki"
Dariya tayi sosai
"Ni ma haka, baka kira sai nayi bacci"
Kallon ta yayi
"Ke kuma ba zaki jira ni ba"
Dariyar dai ta sake yi, har lokacin ta kasa yarda shine a gabanta, wani irin yanayi take ji har
jikinta na daukar dumi saboda murna. Tare suka jera zuwa falon, sam ya kasa daina kallon ta,
sosai ta canza mishi kamar ba Madinar da ya sani ba, dariyar ta ce kawai bata canza ba, har
yanzun idan tayi dariya duka idanuwanta sai sun rufe, sai su kansu idanuwan, basu kara girma
ba. Kallon ta kawai na saka shi jin lallai yazo gida. Wani numfashi da baisan yana rike da shi ba
ya sauke bayan ya zauna
"Daada baki ce mun zai zo ba"
Kallon shi Daada tayi
"Nima ban san zai zo ba Madina, yanda kika gan shi haka nagan shi"
Kai Madina ta jinjina tana murmushi
"In kawo maka ruwa?"
Ta tambaya saboda ta ma rasa abinda ya kamata tayi, kai Nawfal ya daga mata badon yana jin
kishin ruwa ba, shima zuciyar shi ta cika taf da farin ciki. Yana son ganin Adee da Daddy,
amman anya kuwa zai iya barin gidan Daada a yau? So yake ya kwana suna labari, in sun gaji
suyi shiru su zauna tare da juna kawai, wannan yanayin na yau yana son ya adana shi a wajaje
fiye da zuciyar shi yanda in ya tafi zai dinga ziyartar wajajen suna saka shi nishadi. Ruwan
kuwa ta kawo mishi a kofi ya karba
"Abinci fa?"
Kai ya girgiza mata yana saka dayan hannun shi ya bubbuga gefen shi kan kujera
"Ki zauna muyi labari... Nayi kewar ku da yawa..."
Zaman kuwa tayi, Daada na bin su da kallo zuciyar ta cike da farin cikin, tsoron da take kwana
da shi tana tashi yana barinta da ganin Nawfal din. Idanuwanta ne kawai akan su, tunaninta
yayi nisa, ba zatace ga abinda suke fada ba, amman dariya sukeyi, sosai dariya suke kamar
basu da wata damuwa a fadin duniya
Haka take son ganin su
Tare da juna
Cikin farin ciki
Haka take fatan rayuwar su ta kasance
Sai dai kaddara ta riga fata.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*RAI DA KADDARA 1*
09
"Adee..."
Nawfal ya furta bayan sun shigo dakin ita da Khalid suna gaisawa da Daada,wata irin kewar ta
na tsirga mishi, dariyar da takeyi bai hanata hararar shi ba
"Bawani nan..."
Murmushi yakeyi yana mika mata hannun shi daga inda yake zaune, karasawa tayi ta kama
tana zama gefen shi kafin ta zare hannun nata tana daka mishi duka.
"Ouchhh... Adeee"
Ya fadi yana murza wajen dan yaji zafi sosai
"Ka zo ba zaka iya kirana ba Nawfal, ba sai kazo inda nake ba in ganka..."
Har lokacin murza wajen yakeyi
"Saboda ke fa na zo, yanzun nake so in kira inji ko kin dawo..."
Tabe baki Adee tayi, Nawfal na gyara zaman shi kan kujerar yanda zai fuskance ta, fuskarta
fayau take babu kwalliya, amman sai yaga har wani kyalli-kyalli takeyi mishi
"Kinyi kyau sosai"
Murmushi tayi, kowa haka yake ce mata tun bayan sati daya da fara mata gyaran jikin da bata
san nawa Nanna ta kashe a kai ba. Kuma itama tana jin santsin da fatarta tayi, daman fuskarta
tunda can babu kurji ko daya, tana dai gani a fuskokin mutane, ita wannan zumuncin ne bai
taba tsallakowa kanta ba.
"Nagode"
Ta fadi, kai ya jinjina mata yana sata girgiza mishi nata, ita ba dan yace tayi kyau take mishi
godiya ba
"Ina nufin nagode da kazo..."
Wani sauti Khalid ya fito dashi daga kasan makoshin shi yana dorawa da
"Karku fara dan Allah..."
Cikin yanayin da yasa su yin dariya
"Daada ina Madina?"
Cewar Adee
"Sallah ta shiga daki tayi. Na san yanzun zaki ga ta fito"
Ai kam Daada na rufe bakinta Madina tana fitowa daga daki
"Adda..."
Ta kira tana karasowa ta zauna daga gefen Adee
"Hamma ina wuni"
Ta gaishe da Khalid da yake daddana wayar shi
"Lafiya kalau Madina... Kwana biyu"
Kallon shi tayi
"Ina cewa Hamma ya gaishe ka fa"
Shima nashi idon ya raba da waya yana kallon ta cike da alamar tambaya
"Wanne Hamman?"
Murmushi tayi
"Hamma Salim, ko shekaranjiya na ce ya gaishe ka, kullum ma idan mun hadu ina cewa ta
gaishe ka"
Wannan karin Adee ta kama Madina tana juyo da ita dan su fuskanci juna
"Hamma Salim naji kince Madina... Hamman mu... Salim na mu wanda duka muka sani?"
Yanayin da yake fuskokin su ne ya ba Madina dariya, yi suke kamar abune da ko a mafarki
basu hango zai faru ba, kai ta jinjina
"Hamma Salim kike gani? Kina magana da shi, shima yayi magana da ke?"
Kai ta sake jinjina ma Adee, Khalid da ya ajiye wayar shi kan hannun kujera fuskar shi dauke da
tsantsar mamaki yace
"Ya sunan bokon ki Madina?"
Har Daada sai da tayi dariya
"Da gaske nakeyi... Tafdin... Hamma fa... Bajjo kana jin ikon Allah"
Kai Nawfal ya jinjina musu, dan shi ya gama nashi mamakin tun kafin su zo
"Har daga makaranta yana dauko ta ya dawo da ita gida wasu ranakun..."
Sai da yaga hankulan Adee da Khalid sun koma kan shi tukunna ya dora da
"Suna labari da juna har suzo gida... More like Madina tana labari da shi kuma bai taba sauke ta
a hanya ba"
Baki Adee ta rike
"Ashe zanyi tsahon ran da zan ga ranar nan... Madina anya ke mutum ce?"
Dariya suke bata sosai ma
"Yanzun idan ya shigo fa?"
Daada ta fadi tana saka wani shiru ya ratsa dakin, Khalid na daukar wayar shi daya ajiye,
Nawfal ya koma cikin kujera ya zauna. Adee ma gyara nata zaman tayi tana kallon Madina
"Maganar kunshin, gobe idan Allah ya kaimu ne fa..."
Kai Madina ta jinjina mata
"Ban manta ba, wajen karfa tara In shaa Allah zan taho sai in fara ma wanda suke nan kafin
sauran su zo..."
Ganin sabuwar hira zasu dasa yasa Daada cewa
"Abinci fa?"
Adee ta fara amsawa
"Ni dai ina ci, sau daya naci abinci duk yau wallahi, cikina sai kullewa yake tun dazun"
Abincin kuwa Madina ta tashi ta zuba musu banda Nawfal da ya shiga kitchen din da kan shi
yana dafa ruwan zafi ya hada shayi, kankara ya dauka a fridge ya fasa ya zuba cikin kofin yana
karasa cika shi taf ya dauko ya fito. Banda Daada babu wanda yayi mishi magana tunda duk ba
bakon abu bane a wajen su. Musamman Khalid da ba zaice ga rana daya da yaga Nawfal
yasha shayi mai zafi ba. Sam baya so, suna nan suna hira Julde ya shigo ya same su, shima
abincin aka zubo mishi suna dasa sabuwar hira kamar lokacin gari ya waye musu ba dare bane
ba.
Shikam Julde hankalin shi yana kan Adee da su Khalid suka saka a gaba da tsokana. Haka
yake son ganin su kullum, yaran shi, farin cikin shi. Yanda maganar auren ta ya tafar mishi
batare da wata matsala ba abune da zai jima yana nutsar da shi duk idan ya tuna. Akan ce
mutane na daya daga cikin Rahmar da Allah zai maka, bai kara yarda ba sai akan bikin nan na