Showing 63001 words to 66000 words out of 79955 words
Chapter 22 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
yayi
"Zaman me zakiyi a gida Madina? Da kinyi jamb din, result na fitowa a shekarar nan ma zaki iya
samun admission"
Shi yayi mata bayanin muhimmanci yin jamb din shekarar da ka zana jarabawa, amman yayi
mata bayani a kurarren lokaci tunda har an gama saidawa, ko da ba'a gama saidawa ba sai dai
tayi saboda shi bawai don ko daya a cikin bayanin ya gamsar da ita ba. Ta fi son bin komai a
hankali, kuma daki-daki. Yanzun kuwa dadin hutun ma take ji, daga islamiyya sai in tana da
wanda zatayi wa kunshi da kusan kullum ne, da dare tana da isasshen lokacin da zatayi karatu
tunda tasan zata koma bacci da safe in ta gama aikin ta.
Bambanci da yake cikin kowacce rana a wajen ta shine yawan mutanen da ta yiwa kun shi sai
kuma sabon abinda zata karanta. Banda wannan kullum iri daya ce, abu iri dayane. Sai kuma
Daada da take ganin kamar tana ramewa, kamar kuma akwai rashin kuzari a yanda take
gudanar da al'amuranta ba kamar da ba, kusan kullum sai ta kai hannu ta taba fuska ko wuyan
Daada dan taji idan akwai zazzabi sai taji lafiya kalau. Yau ma kuwa hakanne ya faru har ta sa
Daada yin murmushi
"Na ce miki lafiya ta kalau Madina"
Numfashi Madina ta sauke
"Kina ta ramewa Daada...ko dai in kira Daddy muje asibiti a kara duba ki"
Dariya Daada tayi
"Allah da gaske, ni gani nake kina ta ramewa"
Kafin Daada ta amsa sallamar Nawfal ta katse ta
"Hamma dan Allah ba Daada ta rame ba?"
Madina ta tambaya bayan ta amsa mishi gaisuwar shi, kallon Daada yayi sosai, yana kula da
yanda shekaru suka nuna a fuskarta, bai gani ba da, amman akwai rama a fuskarta, duk da ita
din ba mai jiki bace ba tunda can ma, amman fuskarta a cike take, yanzun kam har hancin ta da
yake dogo ya kara fitowa, kana ganin kwanciyar karan hancin daya fara tun da tsakiyar girar ta
"Baki da lafiya ne? Jikin ne?"
Kai ta girgiza musu
"Ku me yake damun ku ne?"
Saboda bata son damuwar da take kan fuskokin su
"Kuma bata yin komai da hanzari kamar da fa"
Madina ta fadi
"Yarinta nake karawa ne kullum? Jikin girma ne, kuyi addu'ar samun jiki me kyau irin nawa"
Dariya sukayi gabaki daya, duk da a kasan ta Nawfal akwai damuwa, waje ya samu gefen
Madina ya zauna har lokacin sai kallon Daada yakeyi, musamman yanda sai da ta dafa kujera
sannan ta iya mikewa dakyar kamar tana jin nauyin jikinta
"Bacci ma nake ji ni kam"
Shagwabe fuska Nawfal yayi
"Ko gaisawa ba muyi ba Daada shine zaki tashi? Ba zaki zauna muyi labari ba?"
Murmushi tayi
"Ai nasan kana nan har in tashin... Wacce gaisuwar? Ba gani ba ka ganni ina lafiya, kaima
kuma nagan ka kana lafiya"
Kai kawai Nawfal ya jinjina yana sauke numfashi, har ta shiga daki bai daina kallon in da ta bari
ba, haka kawai sai yake jin zuciyar shi tayi nauyi. Sai dai bai ce wani abu ba har akayi sallamar
da ta sa Madina mikewa tana fita tsakar gidan dan ta ga ko waye ya shigo, sanda ta dawo yaja
kafafuwan shi ya dora su kan kujerar
"Kunshi zanyi Hamma, in zuba maka abinci?"
Kai ya girgiza mata, bayajin yunwa, wayar shi ya ciro yana kwanciya kan kujerar sosai ya shiga
whatsapp yana sake kallon hotunan da Murjanatu ta turo mishi yana murmushi shi kadai, har
Madina ta shiga daki ta dauko kayan kunshin ta, ta sake ficewa bai ma kula ba. Bai san lokaci
na wucewa ba musamman da Murjanatu kamar ta duba zuciyar shi ta ga yanda yake kewar ta
ta zo online. Earpiece din shi da bai cika mantawa ba ya ciro a aljihu ya saka saboda ta kira shi
video call.
Sallar la'asar da aka kira ne ya sa shi yi ma Murjanatu sallama yana mikewa yaje ya dauro
alwala, batare da ya kalli matar ko yarinyar da ta gaishe shi ba ya amsa yana wucewa, dan
lokacin ma kokarin maida links din hannun rigar shi daya bude wajen alwala yake yi. Ita ma
sallar ta mike taje tayi, don sallah na daya daga cikin abinda bata wasa da shi. Sanda ta karasa
ma matar hudu kusan da rabi. Kudin da ta bata cikin wata jaka taje ta zuba, abinda take siye
bashi da yawa, Julde na bata kudin kashewa sosai, Salim ya sa taje ta bude account a banki,
shi ya dauketa sukaje tare. Yanzun ma idan kudin kushin sun kai dubu biyar ko fiye da haka sai
ta fada mishi yazo ya kaita taje ta saka a ciki.
"In sun taru da yawa zakiyi wani abu mai muhimmanci da su"
Salim din ya fadi, sai da ta fara tarawa tukunna zuciyarta ta raya mata tarin abubuwan da take
son tayi da kudin in har sun kai mata yawan da take fata.
"Kunshi kamar kina ma mutum goma, tun dazun"
Nawfal ya fadi bayan ta shiga falon ta samu waje ta zauna
"Kasan wahalar kunshi ne Hamma?"
Kallon ta Nawfal yayi
"Bawani wahala, ai na iya"
Dariya Madina tayi, sosai dariya ya bata
"Ka iya me? Bafa zanen kujeru ba Hamma, kunshi...kunshi irin wanda mata sukeyi"
Kai Nawfal yake jinjina mata tunda ta fara magana fuskar shi babu alamar wasa
"Ni nake yiwa Jaan, kuma kowa ya gani sai yace yayi kyau"
Duk da taji wani iri a zuciyarta bai hanata cigaba da dariya ba
"Baki yarda ba kenan? System dina dayan daya baci ne nake da hotunan da kin gani"
Dariyar dai Madina ta cigaba da yi mishi
"Ki dauko kayan kunshin ki kawo hannun ki kisha mamaki"
Mikewa tayi ta nufi dakin ta tana dauko jakar kayan kunshin, akwai saura da yawa a
kwarkwaron da tayi ma matar na bakin lalle ta kuwa mikawa Nawfal da ya sauko daga kan
kujera shima yana zama kan kafet suka fuskanci juna da Madina da ke kokarin gintse dariyar ta
tana son ganin iya ina Nawfal zai kai da maganar ya iya zanen lalle kafin ya fito ya fada mata
wasa yake. Fuskar shi babu alamar wasa ya ware mata tafin hannun shi na hagu yana daga
mata girar shi duka biyun. Wani irin tsalle zuciyar tayi kamar tana son bayyana kan fuskarta,
hakan ya sata saurin sadda kanta kasa tana jan siririn numfashi, hannun nata da taji yana zufa
ta goge jikin wandon ta sannan ta dora shi kan na Nawfal.
Salim ya sha rike hannunta, a rana sai ta rike hannun Daada babu adadi, tafin ta ne kawai kan
na Nawfal, amman ji takeyi kamar ta dora shi kan murfin tukunyar da aka sauke daga wuta,
dumin na gangarawa har cikin wani lungu a zuciyarta da sai yau ta san da zaman shi. Fuskar
shi ta ke kallo da yanda ya nutsu akan hannun ta kamar a duniya kaf bashida wani abu mai
muhimmanci da yafi zanen da yake mata, wannan karin duka jikinta taji ya dauki dumi sai kace
zazzabi na shirin kamata.
Yawu ta hadiye tana dan daga wuya da nufin hango abinda Nawfal din yake zana mata ya kuwa
sake yin sama da hannunta yana fadin
"Kibari in gama Malama"
Dariya tayi
"Karka bata mun hannu Hamma, ka tsaya inga me kake"
Kafada Nawfal ya makale mata yana saka idanuwan shi cikin nata
"Allah ki tsaya in gama"
Kai ta jinjina mishi haka kawai tana jin ba zata iya musu da shi ba. Duka bai kara minti goma ba
yayo kasa da hannunta dai-dai lokacin da zata hadiye yawu, ta kuwa sarke wajen kokarin yin
dariya, duk da haka ta kasa dainawa, taurari ne Nawfal ya zana mata, daya kwandalele a
tsakiyar bayan hannunta, sai yayi yan kanana daga gefe, haka jikin kowanne yatsa yayi karami
guda daya
"Inalillahi..."
Ta fadi tana cigaba da dariya, turo baki Nawfal yayi dan baiga abin dariya ba
"Kowa a makaranta yana tambaya wanda yayi mun kunshin nan"
Murjanatu tace mishi, tunda da a yatsunta kawai take saka ja idan ta siyo, shi yace ta kawo ya
zana mata, batayi musu ba kuma ta bashi, da kanshi yake kirkirar zane kala-kala, mai taurarin
shine yake ganin yafi kowanne kyau, ko kafin ya taho duka hannuwan Murjanatu biyu saida yayi
mata, da yan yatsun kafa ma
"Gidado ka kware da kunshin nan yanzun, kaga yanda na kafar yayi kyau"
Har sumba ya samu ta godiya. Sai Madina ce zata saka shi gaba da dariya
"Hamma... Hamma.. Meye wannan?"
Tayi tambayar a tsakanin dariyar da takeyi, kwarkwaron ta ya ajiye mata yana komawa kan
kujera ya kwanta
"Ai sai kiyi tayi tunda baki san abin arziqi ba"
Mikewa Madina tayi da sauri tana nufar dakin ta ta shiga bandakin da yake ciki ta bude famfo ta
saka hannun, sai dai ya riga ya fito, zai kuma yi aqalla kwana uku ko hudu bai gama fita gabaki
daya ba ko da tana yawan amfani da ruwa. Dariya kawai takeyi, tana fitowa daga bandakin taji
wayarta da ta bari cikin dakin tana ruri, da sauri ta karasa ta dauki wayar, muryar ta dauke da
dariya ta ce
"Hamma..."
Bayan ta kai wayar kunnen ta
"Ina kika je? Ina ta kiran ki. Ke da wa kike dariya?"
Dariyar ce ta sake kubce mata
"Ina nan fa, nabar wayar a dakine, na ma wata kunshi sai nima akayi mun..."
Sai dai kafin ta gama dariyar da ta sake kubce mata ta bashi labari harya katse ta
"Kunshi? Kikayi? Wayayi miki?"
Salim ya jera mata tambayoyin a numfashi daya
"Hamma Nawfal fa.. Wai ya iya, yana ma matar shi, kaga abinda ya zana mun a hannu?"
Ta karasa tana dariya, shirun da taji ya biyo bayan maganar ya sata fadin
"Hello..."
Har sau biyu tana sauke wayar daga kunnen ta dan tunaninta kiran ya katse sai taga sakanni
suna tafiya, sake mayarwa tayi
"Hamma... Bana jin ka fa. Ka kashe ka sake kira"
Numfashi taji ya sauke cikin kunnenta, muryar shi can kasan makoshi yace
"Ina zuwa"
Kafin ma ta amsa taji alamar ya katse kiran daga bangaren shi, cajarta ta karasa ta ciro tana
daukar wayar ta nufi falo, har lokacin da murmushi a fuskarta.
**
Baiyi tunanin kafafuwan shi zasu dauke shi daga dakin su zuwa na Salim ba saboda rawar da
sukeyi, tashin hankalin da yake ciki bai barshi ya tuna cewa ana neman izini kafin a kwankwasa
daki ba, turawa kawai yayi yana samun Salim a tsaye da alama wanka ya fito ya sake kaya
"Bajjo..."
Salim ya kira ganin tashin hankalin da yake shimfide a fuskar Nawfal din
"Hamma..."
Nawfal ya kira yanajin zuciyar shi akan harshe
"Meye? Menene?"
Numfashi Nawfal ya sauke
"Hamma Khalid..."
Kokawa yake da sauran kalaman
"Hatsari sukayi...ya kirani....banaji sosai... Hamma ina ta kira ba'a dagawa...ba'a daga wayar"
Mukullin motar da yake kan gado Salim ya dauka, Nawfal baya bukatar Salim yace mishi ya
wuce, gaba yayi yana bin shi a baya har suka fita daga gidan. A wajen ajiye motoci suka ci karo
da Julde da zai fita, tashin hankali bai hana su duka biyun jin kamshin da yakeyi ba. Ganin
Salim bashi da ko takalmi yasa shi tambayar
"Lafiya? Ina zaku? Me ya faru?"
Salim ne ya iya amsa shi da
"Khalid ne yayi hatsari"
Wani irin rugugi Julde yaji cikin kirjin shi har hanjin cikin shi na taya zuciyar shi amsawa. Su
duka ukun motar Salim suka shiga, dan Julde baya ya bude yana zama. Sai da suka hau titi
sannan Salim yayi tunanin bai ma san inda zasu nufa ba
"Yana ina? Ina akace maka yake?"
Kafada Nawfal ya dan daga
"Nima ban sani ba, mu bi hanyar wajen aikin shi kawai"
Kallon shi Salim yayi
"Baka da hankali ne? Kasan hanyoyi nawa ne zaka iya bi zuwa Asad?"
Kamar Nawfal zaiyi kuka yace
"Dan Allah ka zabi daya kawai kabi Hamma, kayi sauri"
Dayar kuwa ya zaba yana karanta duk wata addu'a da zata zai iya tunawa, tashin hankali bakon
abu ne a wajen shi. Ya sha ganin mutane a asibiti suna faduwa suna tashi akan tashin hankali
idan sun kawo yan uwan su, ko kuma ya fada musu rasuwar wani makusancin su, sai dai ya
kalle su kawai saboda ko da wasa ma baya son ya hasaso me suke ji, don hakan na nufin ya
saka kan shi a takalmin su, ya kwatanta da wani na shi, ba zai iya ba, baya so ya ma iya. Sai
gashi yau yana zaune tashin hankalin ya same shi har cikin gida. Daman zuciyar shi a jagule
take tun wayar da yayi da Madina. Kai ya girgiza dan ba wannan bane abu mai muhimmanci
yanzun.
Suna hawa titin Kawaji kuwa suna ganin cunkoson da aka hada a wajen, gurin ya cika, ko gefen
hanya Salim bai samu ya sauke motar ba, a tsakiyar titi ya tsaya suna fita daga ciki gabaki
dayan su. Sai da yaji shigar kwalta a tafin kafafuwan shi tukunna yagane cewar bai saka takalmi
ba. Runtsa idanuwan shi kawai yayi yana fitar da numfashi, ta tsakanin mutane suke kutsawa.
Nawfal najin kafafuwan shi na kara yin sanyi da duk takun da zatayi
"Trailer ce akace ta kwace duk ta bi takan motocin nan"
Ya tsinto muryar wani yana fada a cikin mutanen yana sa makoshin shi bushewa kamar an zuba
yashi. Julde ya fara hango Khalid a tsugunne ya hade kan shi da gwiwar shi, har tuntube yakeyi
wajen kokarin ya karasa wajen shi, Nawfal kam jinin da yake gani ya kara daga mishi hankali
"Khalid..."
Julde da Salim suka kira lokaci daya suna sa Nawfal kallon inda suke, dagowa Khalid din yayi,
har idanuwan shi sun zurma ciki saboda tashin hankali. Shi da yamma ma ya kamata yabar
wajen aikin, sai abokin aikin shi ya kira cewar yar shi bata da lafiya suna asibiti, shine ya karbe
shi har daren, cunkoso ya samu akan hanya, tsaye motar shi take kamar ta sauran mutane da
dama, da kuma babura, ba zaice ga abinda ya faru ba, ihu da kara kawai yaji sai motar shi da
yaga tana gaba da kanta, ashe trailer din data kwace sai ta danne motocin da suke can bayan
su, da tafiya ake kilan sai hatsarin yafi haka muni.
Sanda wani ya bude motar shi ya fisgo shi ya juya bayan shi ya dora idanuwan shi kan wani
mutum da kafar shi ta fita kasa motsawa yayi, tsaye yayi yana kallon yanda ake zaro mutane
musamman masu mashina daga karkashin motoci, tunda yake bai taba ganin tashin hankali irin
wannan ba. Nan take zazzabi mai zafi ya rufe shi, tunanin ya kira Nawfal ne ya zo mishi, sai da
ya ma rasa abinda zaice mishi, bai san ya kiran ya kare ba ko ya akayi ya samu waje ya
tsugunna, kawai yasan ko kifta idanuwan shi yayi sai ya dinga ganin mutane da jini na gifta
mishi
"Khalid..."
Salim ya sake kira yana kama hannun shi ya mikar da shi tsaye
"Kaji ciwo? Ina kaji ciwo?"
Yake tambaya yana bin jikin Khalid din da kallo
"Daddy..."
Khalid ya kira da dukkan zuciyar shi yana jin yanda babu wani girma da zaiyi a duniya da za'ace
baya bukatar lallashin iyayen shi. Karasawa Julde yayi da sauri
"Kaganni nan Khalid, baka ji ciwo ba dai ko?"
Kai Khalid din ya daga mishi yana jin wasu hawaye masu zafi da suka cika mishi ido, da
shikenan fa, karshen ganin da zai musu yau da safe kenan, dan Adam da gaske ba abakin
komai yake ba, kana tafiya ajali yana bibiyar ka, ko tsautsayi, duka tarin mutanen da tsautsayin
ya fadama sun bar gidane batare da sanin ba zasu koma ba, iyalai da yan uwa suna can suna
dubar hanyar komawar su, wasu sai dai suji ana sallamar su matsa za'a shiga da gawa, ko suzo
asibiti kaza su dauka. Ko ina jikin shi bari yakeyi, wani irin tsoro na shigar shi.
Bashi da rabon wahala, amman bayan motar shi gabaki daya ya molaqe, ba dabarar shi ba, ba
komai ba, ko addu'ar fita daga gida bai tuna yayi ba yau din. Allah ne kawai ya kubutar da shi
"Baka ji ciwo ba?"
Julde ya sake tambaya, kai Khalid ya daga mishi, kamar haka Nawfal yake jira ya tsugunna
saboda kafafuwan shi da yaji shima sunyi sanyi. Fuskar shi ya saka cikin hannuwan shi yana
jero duk wata kalar godiya da zai iya wa Ubangiji da ya tseratar da Khalid din
"Meye kai kuma? Ka tashi Bajjo, baka gan shi ba? Lafiyar shi kalau babu abinda ya same shi"
Kai kawai Nawfal yake dagawa Salim din amman shi kadai yasan yanda zuciyar shi ta girgiza,
baka isa ka hana kaddara yin aikinta akan makusancin ka ba, amman in zaka iya bayajin shi
kam zai bar ko tsinke ya soki Khalid. Sai da Salim ya kamashi shima ya mikar
"Ku taho ku koma mota..."
Cewar Salim yana jan rigar Nawfal din, Julde ya kama hannun Khalid, bayan suka shiga su
biyun. Julde ya rufe bangaren Khalid yana daga kan shi yayi nasarar saukewa akan Mero da
hasken fitilar wata mota ya haska mishi fuskarta dai-dai lokacin da ta shiga gaban wata mota
tana rufe murfin tare da bude wani abu a cikin kirjin Julde da