Showing 72001 words to 75000 words out of 79955 words

Chapter 25 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

irin wannan sai kaga idanuwan shi duk sunyi zuru-zuru
ko idan aiki ya sha mishi kai, in tace ya rame baya cin abinci yanda ya kamata sai yace mata

"Mantawa nake yi Mug, bakya tuna mun, mantawa nakeyi idan abubuwa sun mun yawa"

Yanzun idan ta ganshi haka sai taita jin kamar harda lefinta, kamar in shi ya manta bai kamata
ita ta manta ba. Ko ba komai Salim ne, komai nata damuwar shine, shirme da hankali zai bata
nutsuwar shi kamar duk duniya babu wani abu mai muhimmanci kamar sauraren ta da abinda
yake damunta. Ya kamata shima tashi damuwar ta zama tata, ta kamanta mishi kalar karamcin
da yake nuna mata. Tun dazun ta manta basu yi magana ba, bata ma tuna da shi ba sai yanzun
da damuwar da take neman ya taimaka ya saukaka mata ta taso.

Tsintar kanta tayi da jin kunya har tana kasa kiran shi, ta dai dauki wayar ta sake komawa falon
ko da shi zai kirata. Daada ta samu a zaune ta fito itama, yanzun tafi zama cikin dakinta fiye da
yanda take zama a falon. Canjine Madina take gani bayyane a tare da Daadar da ya girmi tsufa
kamar yanda take yawan fada, kullum gani Madina takeyi tana kara ramewa kamar bata cin
abinci, da ba gida daya suke ba kuma ba ita take kula da cin safe, rana harma na daren Daadar
ba zatace ba'a kula da ita yanda ya kamata.

"Assalamu alaikum"

Muryar Nawfal ta daki kunnuwan Madina tana sakata saurin daga idanuwanta da zuciyarta da
tayi tsalle zuwa cikin su tana kallon Nawfal da ya sakko kafar shi cikin dakin fuskar shi dauke da
murmushi, manyan kayane a jikin shi, yadi kalar sararin samaniya sai hula mai kalar amman
mai duhu, kayan sun karbi jikin shi, rigar na nuna fadin kafadun shi da cikar halittar shi duk da
bata matse shi ba. Sai dai akwai banbanci a yanayin yanda muryar Nawfal ta sauka a
kunnuwan Madina da kuma na Daada. Muryar Bukar taji, muryar dan ta da rayuwa ta zabi ta
rabata da shi a karo daban-daban.

Da ta daga ido ma ta sauke akan Nawfal fuskar Bukar ta gani, murmushin shi mai sanyi kamar
halayen shi take gani, duk da ko kusa da sanyin halin Bukar din Nawfal bai kai ba, ita kam yau
Bukar take gani kamar yanda yanzun da karfin alaka ta jini tasa take ganin Yelwa a tattare da
Madina duk da kowa yasan Yelwa zaice bata kama da Madina, amman jini yafi karfin wasa. Da
duk wayewar gari da yanda nauyin kirjinta yake karuwa a tsayin shekarun nan, yanzun ya kai
inda take jin anya bashi zaiyi ajalin ta ba kuwa? Idan ta kwanta bata tunanin komai sai yanda
zata sauka daga gado da safe, yanda za tayi rayuwa a yinin ranar batare da ta kara ma Madina
damuwar da take gani cikin idanuwan ta ba.

A satikan nan tana bude bakin ta yafi a kirga sai ta kasa furta komai, me zata ce? Me zata
fadama Madina? Ta ina ma zata fara? Yarinyar bata taba tambayar ta komai ba, kamar sun
zauna sun hada baki da Nawfal suka zabi shirun da ya saukaka mata komai saboda bata da
kwarin gwiwar fuskantar su da labarin da ba zai amfane su da komai ba, bata son ko na minti
daya su raba nauyin da take ji tare, duk da tasan nauyin ba nata bane ita kadai, wata rana dole
ta raba shi tare da su, yanzun tana jin kusancin ranar fiye da kowanne lokaci. Girma sukeyi su
duka, shekaru na riskar su, rashin tabbas din yau da kullum na kara lullube Daadar.

Tana jin ina ma ace ta san sauran kwanakin da suka rage mata, da tafi tsara yanda komai zai
kasance

"Daada Am"

Muryar Nawfal ta kutsa cikin tunanin ta

"Soyayyar tawa ce ta motsa haka kike ta kallo na harma bakyajin me nake cewa?"

Murmushi tayi tana jin wani abu ya rabe a cikin kirjinta

"Ko bata bakina ma ba zanyi ba"

Dariya yayi yana karasawa ya tsugunna a gabanta

"Bana son ramar nan dake cikin idanuwan ki Daada... Duka kwana nawa ne ban ganki ba yau
amman kin kara ramewa"

Kai Daada ta girgiza tana sauke idanuwan ta daga cikin na shi saboda bata son yanda yake
kallon ta kamar yana neman tono dukkan sirrikan da take boyewa

"Wai ba zaku kyaleni ba ne? Idan ma bana ramewa yanzun surutun da kuke mun zai sa in fara"

Ta karasa maganar tana kokarin mikewa, Nawfal na tayata cikin hanzari, yana tuna mata
lokuttan da ta taimaka mishi ya mike haka, ta ma daga shi gabaki daya tana mikarwa. Sai da ya
tabbatar ta tsaya da kafafuwan ta tukunna ya saketa a hankali yana nazarin ta bayan ta juya,
yanda take cira kafafuwan ta dakyar yasa zuciyar shi yin nauyi. Ko lafiyar ta kalau akwai abinda
ta saka a ranta, shisa take boye mishi haka, daya shigo gidan suka gaisa take tashi tabar falon,
idan dakin ta ya bita sai ta kwanta kamar bacci ya dauketa, wata rana ya dauki filo ya kwanta
anan kasa, ko ya dora kan shi akan gadon har saiya gaji da zama.

Yanzun da yake kallon ta babu komai cikin kanshi sai rokon da yake ma Allah na ya ara mishi
lokaci mai tsayi tare da Daada saboda itace cikon komai na rayuwar shi, ko Murjanatu bata gani
ba sai dai a waya, akwai tarin abubuwan da yake bukatar aron lokaci ya gudanar da su tare da
Daada a cikin rayuwar shi. Itama tana jin idanuwan Nawfal din, tasan kallon ta yakeyi, kanta
take ji yayi nauyi fiye da misali, kamar babu iska a cikin shi duk da bata san ko akwai yiwuwar
cewa iska zata kasance cikin kai ba, kawai hakan zata iya amfani da shi wajen misalta yanayin
da take ji.

Hasken daya gilma cikin idanuwan ta na sakata runtsa su ta bude, sai taga duhu, ba duhu irin
na gabatowar magriba ba, duhu fiye da na tsakar dare saboda bata iya ganin kyallin komai,
sake runtsa idanuwan nata tayi wannan karin duhun na karasawa har cikin kanta

"Daada..."

Taji an kirata kamar daga wata duniya saboda nisan da kwakwalwar ta tayi da kanta duk kuwa
da suna hade waje daya, hakan na sa wani abu cikewa a kirjinta kafin komai ya tsaya mata cak.

*

Kamar shirin film haka komai yake dawo ma Madina da Nawfal, da murmushi a fuskokin su,
komai na tafiya lafiya kafin ya birkice a kasa da minti daya. Kowa ka tambaya zaice shi ya fara
ganin alamar Daada zata fadi, amman babu lokacin wannan musun tunda babu wanda ya iya
karasawa ya tare ta a cikin su sai bayan da ta kai kasa tana faduwa tare da wani bamgare na
zuciyoyin su. Sai sakanni suka dinga wuce ma Nawfal da nisan awanni, komai baya sauri har
shi kan shi, haka yaji daga daukar Daada daga cikin gidan zuwa motar shi haka shigowar su
asibiti, haka dorata akan gadon da ya kama aka gungura har zuwa dakin da wani likita ya kai
hannu yana turo shi baya kafin su maido kofar su rufe.

Tsaye yake amman ya rasa inda zai sa kan shi yaji sanyi, numfashi ma kokawa yake da shi a
wannan lokacin

"Ka zauna Hamma..."

Madina ta fadi cikin sanyin murya tana saka shi juyawa ya kalleta, nutsuwar ta na bashi
mamaki, akwai damuwa shimfide saman fuskarta amman a nutse take

"Tashin hankali baya taimakon marar lafiya, nutsuwa yake bukata fiye da komai. Nutsuwar ki ita
ce taimakon farko, ki rufe idanuwan ki kiyi numfashi mai nauyi ki fitar har sai kin tabbata kin
samu nutsuwar da kike bukata..."

Shine abinda Salim ya fada mata, ya maimaita mata har saida ya tabbatar ta fahimta bayan ta
haddace kowacce kalma. Shisa yanzun ita ta fada ma likitan sunan Daada, shekarun ta da
kuma lambar katinta da ta haddace ko da zasu taho asibiti a hargitse bata dauko ba za'a iya
amfani da lambobin a binciko file din ta kamar yanda tasan anyi yanzun din, ko ana kanyi
"Ina wayar ka?"

Ta bukata ganin gardamar da take cike da idanuwan Nawfal din akan tayin zaman da tayi mishi,
ta masa uzuri, wannan ne rashin lafiyar farko da Daada tayi yana nan. Aljihun shi Nawfal ya
laluba yana dauko karamar wayar da yaji a jikin shi ya mika mata. Lambar Salim da ta haddace
ta saka tana kiran shi, sai da ta kira sau uku ana hudun ya daga da fadin
"Yanzun na shigo na dauki wayar Bajjo, menene?"

Numfashi taja tana fitarwa

"Hamma ni ce"

Da mamaki a muryar Salim yace

"Madina?"

Cike da alamar tambaya kafin ya dora da

"Lafiya? Me ya faru? Ina Bajjon?"

Sai da ta kalli Nawfal sannan ta amsa

"Gashi nan, yana lafiya. Muna asibitin ku... Daada ce ta fadi"

Ta karasa tana jin yanda bugun zuciyar ta yake karuwa cike da tsoro, girman abin da ya faru a
gabanta yana danne ta

"Ki tashi ki duba saiki fadamun inda kuke?"

Mikewar tayi kuwa, ya nuna mata yanda zata karanta sunan kowanne ward a asibitin ta kuma
gane in da take, dubawar tayi tana fada mishi

"Gani nan zuwa yanzun... Daddy ya sani?"

Kai Madina ta girgiza

"Kai na fara kira..."

Ta fadi cikin sanyin murya

"Karki kira kowa tukunna, gani nan"

Wayar ta sauke daga kunnenta tana kashe kiran. Riga da wando ne a jikinta, ta dora ta sanyi
doguwa akan tshirt din da takai mata har gwiwar ta, akwai maballai a jikin rigar daga farko har
karshe, an yi kwalliya da wasu har a gefe, sai hula da ta dan tura baya batare da gashin ta ya
bayyana ba, haka take zaune sanda Nawfal ya zo, haka kuma ta fito batare da ta saka komai
ba sai takalmin da daman akwai shi a kafarta na yawo cikin daki. Tsaye take har Salim ya
karaso yana kai hannu ya tura mata gilashin dake fuskarta ganin ya dan sakko ita kuma bata
mayar da shi ba.

Tayi mishi kyau kamar ya dauketa ya boye, zuciyar shi ta yamutsa lokacin da ya yawata da
idanuwan shi akan fuskarta

"Wanne daki suka shiga da ita?"

Da hannu ta nuna mishi saboda idanuwanta da taji sun cika da hawaye, tana yin magana
zubowa zasuyi, kai ya jinjina yana kama hannun nata ya jata ya karasa da ita inda ta tashi a
waiting area din yana zaunar da ita. Nawfal ya kalla da yake tsaye

"Bajjo..."

Ya kira a hankali, tun yarinta zaka iya cewa Nawfal na da juriya, tunda kafin kaji kukan shi zai
wahala komin dukan da Saratu zatayi mishi kuwa, sai ta mare shi ya fadi ya tashi yayi tsaye
kamar yana son ganin iya abinda zata iya yi. Kowa zai ce yana da karfin hali, abinda zai taba
shi mai girma ne. Shi ne zai karyata, Nawfal ne yaro mafi rauni daya taba cin karo da shi, ko
idanuwan shi ka kalla zaka ga wannan raunin, yana da babbar zuciyar da yake yawo da ita rike
cikin hannuwan shi yana jiran mai rabo ya gifta dan ya karbe shi cike da karamci.

Akwai vulnerability a tare da Nawfal din da baisan yanda zai misalta ba. Kullum ya gan shi sai
yaga kamar akwai abinda yake bukata da su duka suka kasa ba shi, ya dauka zai ga abin ya
kau bayan yayi aure, yana nan, matar shi ma bata bashi wannan abin da yake nema ba, har
yanzun bai cika ba, akwai rami mai girma a tare da shi. Wannan raunin kuwa shine a bayyane
yanzun, karasawa Salim yayi yana kamo hannun Nawfal din da yake kokarin kwacewa, sai dai
ba girman su bane kadai bambancin, harma da karfin su, jan shi yayi yana amfani da karfi
wajen zaunar da shi gefen Madina.

"Har yanzun ba su fito ba Hamma? Bata numfashi sanda muka zo...bata numfashi... Daada
bata numfashi Hamma..."

Kai Salim ya daga mishi kamar a gaban shi akayi, saboda fahimta Nawfal yake bukata, so yake
wani ya fahimci abinda yake ji ko zai samu sauki. Kirjin shi kamar zai tsage gida biyu, da gaske
labarin tashin hankali yake ji, bai taba fahimtar ya yake ba sai yau, wancen karin abinda yaji
wasan yara ne, ya dauka idan yazo yaga Daada, ana komai a gaban idanuwan shi sai yafi
samun sauki. Ashe ba haka abin yake ba, ashe nisan da yayi sauki ne, bai ganta ba, bai ga
kamar ya rasa ta ba.

Tare da wani bangare a zuciyar shi suka fadi, ko Daada ta tashi bayajin wannan bangaren zai
mike, faduwar da yayi ba wadda zai mike bace ba.

"Breath..."

Salim ya furta cikin umarni

"Yanzun Bajjo, in... Out.... In... Out"

Numfashin kuwa yake ja, yana fitarwa, muryar Salim na mishi jagora, har sai da ya dan fara
samun nutsuwa tukunna

"Ka zauna nan, ku duka ku zauna nan"

Ya fadi yana kallon Madina da ta kai hannu tana share hawayen da ya zubo mata. Bayajin ta
kamar Nawfal, tana da karfin hali duk da kankantar ta. Idan ta kama ya san zata ture damuwar
ta a gefe ta kula da Nawfal din. Yana shirin karasawa dakin likitan na fitowa. Daga inda su
Nawfal suke basa iya juyo abinda su Salim din suke fadi, ta gaban su dai suka wuce, sun fi
mintina sha biyar kuma kafin Salim ya dawo shi kadai.

"Me yace? Ta tashi? Me yace ya same ta?"

Nawfal ya jera ma Salim tambayoyin da kafin ya zabi wadda zai fara amsawa ya kara da

"Zamu iya shiga mu ganta? In shiga in gan ta Hamma?"

Kai Salim ya girgiza mishi a hankali

"Sai ta kara hutawa...za'a kara mata wasu tests din tukunna..."

So yake ya basu tabbacin da yaga suna nema akan fuskar shi kamar duk wani wanda zai kawo
marar lafiya, amman a yanzun ya ture batun cewa su din na shi ne, likita ne shi a yanzun, su
kuma yan uwan mai jinya.

"Zamu san komai idan aka karasa sauran tests din...banda abinda zan fada muku yanzun da ya
wuce tana samun dukkan taimakon da take bukata"

Hannuwa Nawfal ya saka yana dafe kan shi da su, likita ne a gaban shi ba Salim ba, ya gani, ya
kuma ji a muryar shi, numfashi yake ja yana fitarwa a hankali sannan ya dago ya kalli Salim din

"Hamma..."

Ya kira amman Salim yaki kallon cikin idanuwan shi

"Hamma ka cire rigar nan kayi mun magana, dan Allah kayi mun magana"

Nawfal ya karasa cikin roko, muryar shi na fitowa cike da rauni.

"Ka fadamun... Kaji"

Yayi maganar cikin karfin hali yana son Salim ya fahimci zai iya daukar koma menene akace
yana damun Daadar, so yake yaga ba yaro bane shi karami da yake bukatar kariya. Dan
murmushi Salim din yayi mishi

"Sai an gama running tests Bajjo..."

Gardama zai karayi Madina ta katse shi

"Zaka zauna damu ko zaka kara dawowa?"

Numfashi Salim ya sauke yana godema Madina, idanuwan shi ya sauke cikin nata yana fatan
taga godiyar shi

"Zan sake dawowa...da sun gama abinda sukeyi zasu sake mata daki, sai ku zauna da ita"

Madina ce kawai ta iya daga mishi kai

"Idan kuna bukatar wani abin sai ki kirani"

Kan dai ta sake daga mishi, ya kalli Nawfal daya kauda na shi kan gefe da alamar fushi yakeyi
saboda yaki gaya mishi me ya samu Daada, numfashi kawai ya sauke yana wucewa yabar su a
wajen. Office din shi ya koma ya zauna yana sauke wani dogon numfashi hadi da kai hannu ya
murza kan shi daya fara alamar ciwo, ya gama round din shi sai kuma nan da awa daya, idan
ba an shigo da marar lafiyar da yake bukatar agajin gaggawa ba. Ya kira Julde bayan sun gama
magana da likitan yana kuma jira ne ya karaso asibitin.

Da gaske ne da yace ma su Nawfal sai an gama gwaje-gwaje tukunna, amman yana da abinda
zai fada musu, zuciyar da zaiyi amfani da ita ya fada musun ne bashi da ita. Da Madina ce ita
kadai zai san yanda zai gaya mata yayi mata bayanin da zata fahimta, Madina ce zai ma iya
neman wasu takardu akan matsalar ya bata ta karanta, zai sha tarin tambayoyin da yasan ba
zai iya amsa mata ba tunda shi ba likitan zuciya bane ba, amman ya san likitan zuciyar, ya
kuma san zaiyi farin cikin amsa ma Madina dukkan tambayoyin ta.

Nawfal yake ji, yanda yake a hargitsen nan yana ce mishi akwai yiwuwar sai an ma Daada aiki,
akwai yiwuwar ba toshewar jini bane da rashin kai kawon shi yanda ya kamata a tsakanin
jijiyoyin ta da kuma zuciyar ta kamar wancen karin, matsala ce da ta girmi a dora ta akan
magunguna, zai iya yiwuwa sashe ne kacokan a jikin zuciyar tata ya gaza yake kuma bukatar a
sake shi cikin gaggawa kafin ya haifar da wata sabuwar matsalar, duka hasashe ne yanzun,
babu abinda aka tabbatar sai likitan da aka kira ya zo. Bashi da karfin halin da zai sake daga
ma Nawfal din hankali akan hasashe, sai an tabbatar da komai tukunna.

Ya godema Allah da bai fada ma su Nawfal komai ba ganin yanda Julde ya hargitse bayan ya
zo asibitin ya karasa Office din Salim din ya kuma yi mishi bayanin hasashen da likitan yayi

"Dan Allah Daddy, kar su Bajjo su ganka haka su dauka wani babban abin ne,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login