Showing 21001 words to 24000 words out of 79955 words

Chapter 8 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

har dariya yayi. Ko ba shiga da yanayin Madina ba, ita
din takan saka nishadi a tare da duk wanda zata ci karo da shi. Ko bata sanka ba kuka hada ido
zatayi maka murmushinta da zai wahala ka kasa mayar mata da shi.

"Muje kafin rana ta bude da yawa"

Madina ta ce tana wucewa da kara fadin

"Daada sai mun dawo"

Bin bayanta Salim yayi yana mamakin yanda take iya sauri da gajerun kafafuwanta, ko

"Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya"

Da Daada ta furta bataji ba balle ta amsa, a bakin mota ya sameta a tsaye. Da kadan kanta ya
wuce kugun shi, yar dariya ya sake tsintar kan shi dayi yana zagayawa ya sa mukulli ya bude
murfin motar ya shiga. Hannu ya mika ya bude mata itama tana shiga ta zauna hadi da jan
murfin motar.
"Wacce kasuwar zamu je?"

Salim ya tambaya yana yin baya da motar, dan jim Madina tayi sannan ta amsa shi

"Kasuwar cefane...in da ake saida su nama da kifi"

Kai Salim ya jinjina, ya kan kai Saratu lokaci zuwa lokaci.

"Hamma Khalid yace likita zaka zama ko?"

Kan dai ya sake daga mata, haka kawai saiya tsinci kan shi da son tambayarta

"Ajin ki nawa? Me kike son zama ke?"

Kallon shi tayi yana ganin girman gilashinta ta gefen idon shi

"Aji hudu uku zan shiga hudu yanzun..."

Kamar tasan gilashin yake tunani a ranshi ta kai hannu tana gyara zaman shi, ya kula takan yi
hakan ne saboda ta saba, ya zamar mata kamar habit, bata mintina bata kai hannu fuskarta ta
gyara zaman gilashin kamar wanda zai fado ba.

"Ina son zama yar jarida"

Kai Salim ya jinjina

"Glasses dinki..."

Ya soma kafin ya karasa ta amsa da

"Blurred vision...bana ganin abubuwa da kyau sai da shi"

Dan kallonta Salim yayi yana maida hankalin shi kan tukin da yakeyi. Baisan me yasa yake son
tambayar ta abubuwa haka ba, rayuwar mutane ba abinda ya shafe shi bace ba. Tauna bakin
shi yayi ta ciki don ya gujema wata tambayar kafin ta sake kubce mishi. Shirun ne yayi ma
Madina yawa, saboda ita mutum ce da Allah ya halitta da tambaya da kuma son hira, ko
bakunta bata iya ba, ko mun girmanka tasan kalar hirar da zatayi da kai da ba zaisa zaman ku
ya gundure ka ba.

"Baka jin kida kai a motar ka? Hamma Khalid da kida a motar shi, duk idan yazo zamu je waje
yana kunna mana"

Cikin sanyin murya Salim ya amsa da

"Bana son hayaniya"

Bayajin ya taba kunna ko da radio din cikin motar ne tunda Daddy ya bashi ita. Ko TV zai kalla
da yawan lokutta sautin gabaki daya a kashe yake, sai dai yayita kallon hotunan

"Ko kai ma kana da matsalar kunne ne kamar yanda nake da ta idanu?"

Murmushi Salim yayi

"Nace bana son hayaniya kina ta mun surutu"

Dariya Madina tayi

"Ni bana so idan ba karatu nakeyi ba inji nayi shiru...baya mun dadi"

Bata kuwa yi shirun ba har suka karasa kasuwa, sai dai a karo na farko a rayuwar shi da surutu
bai hau mishi kai ba, asalima ko bai amsa ta ba nishadi take saka shi. Bai fita daga mota ba,
anan ya jirata, da yake ta iya wahalar da kanta duk abinda ta siyo sai ta dawo ta kawo sannan
ta sake komawa. Da ta siyo kifi harda lemon roba na coke ta hado mishi
"Kana ta zama ko? Yanzun zan gama, saura abu guda biyu"

Ta fadi tana mika mishi lemon

"Ka sha wannan, ko kana jin yunwa in samo maka wani abin?"

Yanda take mishi maganar sai ka rantse yaron goye ne ta bari a mota, dariya ta bashi ba kadan
ba

"Wannan ma ya isa, nagode"

Ya fadi bayan ya karba. Ya kuma ji dadin lemon, da ta gama zasu koma hira ta dinga mishi tana
bashi labarin yanda sukayi da inda tayi siyayyar ta.

"Me yasa baka zuwa? Ka dinga zuwa dan Allah...kaga ni ban sanka ba sosai"

Madina tayi maganar cike da roko tana kallon shi ta cikin gilashin ta, sai ya tsinci kan shi da
daga mata kai, murmushin da tayi na saka shi jin wani bakon yanayi

"Dan Allah da gaske? Ko zaka dawo anjima? Miyar kifi zanyi, da dadi wallahi, Daada tace na iya
abinci, ko Hamma Khalid ma yana so inyi idan ya zo"

Kai ya girgiza mata

"Makaranta zanje Madina... Zan dawo ba yau ba dai"

Cike da fahimta tace

"To shikenan, Allah ya baka sa'a, Allah ya tsare ka ya taimake ka"

Addu'ar ta fito mata a saukake

"Amin"

Ya furta yana tsintar kan shi da dorawa da

"Nagode"

Kai ta jinjina tana mishi murmushi, tsaye tayi a kofar gidan kamar tana jiran ta ga tafiyar shi
tukunna, shisa yaja motar, ta mudubin shi yake hango tana daga mishi hannuwan ta duka
biyun, murmushi yayi, a hankali ya furta

"Madina..."

Batare da ya san girman rawar da madaukakiyar sunan zata taka a rayuwar shi ba.

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*RAI DA KADDARA 1*

07

Sake gyara zaman shi yayi a cikin mota a karo na ba adadi, bacci yake ji ba dan kadan ba,
saboda bai samu wadatacce ba da dare. Da ace babu hayaniya lafiya kalau zaiyi baccin shi.
Tunda motar a kashe take dole ya sauke gilashin kadan dan shige da ficen iska. Amman hakan
sai kwaso mishi surutan da baya bukata zuwa kunnuwan shi yakeyi. Harda yara da a lokacin ya
kamata ace suna islamiyya amman sun cika unguwa da hayaniya sun hana kowa sakat. Inda
unguwar su Daada yake yana da tabbacin da anyi gangami an tashe su ko da gidan nasu ne
sai an sa sun siyar sun tashi.

Yaran da zai jera ya zane ma jiki ya kirga sun fi goma sha daya cikin kan shi daga parking din
motar shi zuwa yanzun. Baya son hayaniya, baya son surutu gabaki daya, iya zaman da yayi ya
gama tsara kalar unguwar da yake son siyan gida in har ya samu wadatar hakan. Kwankwasa
gilashin motar yaji anyi ta gefen da yake, bude idanuwan shi yayi yana yatsina fuska saboda
kamar cikin kwakwalwar shi aka kwankwasa haka yaji. Juyawa yayi yana sauke idanuwan shi
kan fuskar Madina da take mai dariya da duka hakoran ta a bude

"Hamma..."

Ta fadi cike da fara'a tana saka shi kai hannu ya kara sauke gilashin motar kasa

"Yaushe ka zo?"

Ta tambaya tana dorawa da

"Me yasa baka shiga cikin gida ba?"

Ya san kafin ya amsa tambayoyin biyu in dai Madina ce ta kara jero mishi wasu, shisa yayi shiru
yana jiran ta gama. A cikin watanni biyu baya jin akwai wata halayya ta Madina da bai sani ba,
don tana cikin mutanen nan da ake ma rayuwar su lakabi da budadden littafi, ba su da wahalar
fahimta. Haka kawai idan gari ya waye a tsayin rana bai ganta ba bayajin dadi, tunda ya san
makarantar da take wasu lokuttan yakan dai-daici lokacin tashin su sai yaje. Ba zai manta ranar
farko daya fara zuwa ba, yana tsaye ya jingina da motar shi ya hango ta.

Duk yaran da suka fito zaka gansu su biyu har fiye da hakan ma, Madina ita kadai ya hango, ba
gilashin fuskarta yasa ya fara gane ta ba, uniform din jikinta da yake tunanin zai wahala bai iya
shigar da jikin shi cikin kafar wandonta daya ba, bai taba ganin wando irin na jikin Madina ba,
har rigarta tasha bamban da ta sauran, hijabinta ce kawai bata ma kai ta wasu tsayi ba, idan
iska me karfi akeyi zata iya yawo a samanta saboda girman kayan da suke jikinta, tana hango
shi ta washe mishi baki tana kara saurin tafiyar ta, sanda ta karaso kasa rike dariyar shi yayi

"Madina..."

Ya iya kira, bata san dalilin dariyar shi ba ta fara taya shi

"Wanne irin kaya ne wannan?"

Dan juyawa tayi har lokacin dariya takeyi

"Bana so inji kaya sun matseni"

Kallon ta Salim yakeyi, komai nata daban yake, ba zai kirga yawan matan da ya sani ba,
amman ko mai shigen muryar Madina bai taba cin karo da ita ba. Bambanci da take da shi da
sauran mutane ne abinda yaja shi. Ko yanzun da take mishi murmushi da dukkan hakoranta a
waje bambanci yake sake gani
"Yau baki dawo da wuri ba..."

Ya soma a gajiye, kafin ya karasa ta katse shi

"A'a mun tashi fa, ai kullum-kullum karfe biyar da rabi ake tashin mu, akwai wa'anda suke zuwa
daga unguwa mai nisa, ni ce na tsaya na siya awara, akwai layi kuma. Ban san ka zo ba da na
taho"

Numfashi Salim ya sauke yana nuna mata alama da hannun shi da ta zagaya ta shigo motar.

Sai da ya dakuna fuska dan karta fadi a gudun da tayi tana bude murfin motar, ledar awarar da
sai lokacin ya ganta ta ajiye akan kujerar motar tana fadin

"Bari in kai jakata ciki in fada ma Daada na dawo kar ta dauka na tsaya wani waje"

Bata ma jira amsar shi ba, ko murfin motar bata rufe mishi ba ta juya. Numfashin dai ya sake
saukewa da murmushi a fuskar shi. Hannun ta da ta dauke ledar awarar ya fara gani dan yanda
ta shigo motar kamar an jehota sai da ya sake yin dariya, duk idan yana tare da Madina sai ya
dinga jin tamkar yana biyan bashin duka lokuttan daya kamata ace wani abu ya saka shi nishadi
bai ji nishadin ba, da wahala kaga fuskar shi babu murmushi duk idan suna tare, ko ita din ya
gani kafin ta bude bakinta ta ce wani abu shigar jikinta ta bashi dariya.

"Ga ruwa na dauko maka"

Ta fadi tana sauke numfashi hadi da mika mishi ledar ruwan da ya karba ba dan yana jin kishi
ba, ya siyi ruwa har roba biyu a hanya, tsintar kan shi yayi da fasa ledar ya dan sha ruwan yana
rike ledar a hannun shi

"Daada tace tana gaishe ka"

Kai ya jinjina mata yana kallo tana bude ledar awarar da tayi mishi kyau a ido, harda albasa da
kabeji yankakku a ciki sai yaji kulle a farar leda ta bude tana ajiyewa daga gefe a cikin ledar
awarar.

"Ka iya cin awara? Ka san awara?"

Yar dariya yayi mai sauti

"Lallai yarinyar nan..."

Cewar Salim yana sata yin dariya

"Nasan unguwar ku ta yan gayu ce, ba masu sai da awara shisa"

Tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, tana daukar awara daya ta saka cikin bakinta.

"Adee tana mana a gida ai"

Tauna awararta Madina takeyi tana mika mishi ledar da ya saka yatsu ya dauki guda daya ya
dangwala yajin ya saka a bakin shi

"Hamma Nawfal baya son yaji shi"

Maganar ta kwace mata batare da tasan dalilin da yasa tayi ba, numfashi Salim ya sauke,
Nawfal din da ta kira na saka shi jin wani yanayi da bai da fassarar shi. Wani irin shiru ne ya
ratsa cikin motar saboda. Ita kanta Madina ji takeyi kamar anyi wasu shekaru ne masu yawan
gaske da tafiyar Nawfal din, ba zata ce tunanin shi baya fado mata ba, ko agogon shi da yake
ajiye akan gadon ta yana tuna mata shi, da tana sakawa, sai ta cire ta ajiye, ko karatu takeyi
wani lokacin zaka ganshi a hannunta tana ta jujjuya shi. Idan zatayi bacci ma lokutta da yawa
agogon na hannunta ko da ba tunanin Nawfal takeyi ba ta riga da ta saba dauka.

Daina saka agogon ya zama hanyar ta guda daya ta nuna fushin ta da karya alkawarin shi da
Nawfal yayi na cewar shekara daya kawai zaiyi ya dawo. Amman yanzun kam anya akwai
wannan fushin?

"Kullum kike siyan awarar?"

Salim ya tambaya saboda yau ne karo na farko da shiru yayi mishi yawa, baisan ko dan in dai
tana waje ya saba da hayaniyar ta bane ba

"Um um fa, ni kadai nake ci. Daada wai mai yayi yawa yana saka mata heart burn"

Shima kwara hudu yaci ya kara shan ruwan da yake hannun shi. Yana kallo ta kulle sauran da
alama itama ta isheta

"Zan tafi, yanzun za'a kira sallah"

Salim yayi maganar yana mika hannun shi bayan motar ya dauko wata bakar leda yana dorawa
akan jikinta

"Komai kika ce kina karantawa, bana karanta duk wani abu da bai shafi karatuna ba, sune suka
mun kyau a ido"

Bude ledar Madina tayi tana lekawa, sai da ta gyara zaman gilashinta sannan ta kalle shi da
wani yanayi a fuskarta da ya saka zuciyar shi daukar dumi, idan litatttafai zasu bayyana wannan
yanayin a fuskarta duk zuwan da zaiyi zai kawo mata ko dan ya gani

"Nagode Hamma, kasan duk na karanta na dakina, maimaita wasu nakeyi. Daddy yace zai
kawo mun amman bai zo ba jiya... Nagode sosai sosai"

Murmushi kawai ya iya mata yana kallo ta sa hannu ta zaro littafi daya tana shafa shi a gefen
fuskarta kamar akwai wani abu a tare da littafin da ita kadai ce take gani, dayan hannunta ta sa
tana bude murfin motar ta fita, harta kai kofar gida ta dawo tana daukar ledar awarar ta hadi da
fadin
"Sai anjima...Allah ya tsare maka hanya"

Bata jira amsar shi ba ta sake juyawa, murfin motar ma sai shi ya rufe abin shi, hankalinta
gabaki daya yayi kan litattafan. Da murmushi a fuskar shi ya kunna motar da yayi dai-dai da
kiran sallar Magriba da akayi. Yana hanya ana tayi a masallatan da yake wucewa, banda sallar
asuba da itama dan Khalid na tashin shi baya kowacce sallah a cikin jam'i. Baisan lokacin da
hakan ya fara ba, rana daya ya wayi gari za'a kira sallah yana kwance bai mike ba duk da wani
duhu da yake ji yana karuwa a zuciyar shi. Wata rana yana aji haka zaiga mutane na fita dan
gabatar da sallar su, ko ya fita yana komawa mota ya zauna har sai an idar.

Sai ya hada azahar da la'asar yayi su a lokaci daya. Ko yanzun daya karasa gida ya ajiye motar
shi ya nufi bangaren su ya bude ya shiga a falo ya zauna yana sauke numfashin gajiya, saida
ya huta ya mike ya shiga kitchen tunda Adee tana nan yasan abincin shi an kawo ba sai yaje ya
zubo ba. Ai kam an kawo din, shinkafa da wake da miyar kifi. Daga Magriba har isha'i sai karfe
tara na dare ya hada yayi su, ya sake yin wanka yana shirya jikin shi cikin kananun kayan da
sukai matukar karbar shi sannan ya sake ficewa daga gidan.

*

Adee da take tsaye a gaban shi ta daga kai cikin alamun son ganin fuskar shi sosai yake kallo

"Dan Allah Hamma, kaji, dan Allah ka danyi fara'a idan zaku gaisa, a tsorace yake wallahi"

Murmushin da zuwa yanzun zaice Madina tafi kowa gani yayi mata

"Good...gara da yake a tsorace"

Kallon shi Adee tayi kamar zatayi kuka. Sau wajen hudu Salim din yana wuce ta tare da Ahmad,
cikon na biyar ne tana komawa ta ganshi zaune a falon Nanna, sai da zuciyarta ta buga

"Waye shi? Ban taba haduwa da yan ajin ku fiye da sau biyu a cikin wata daya ba"

Bawai bata so ta fada musu bane ba, ta rasa ta inda zata fara tun satin daya fita da Ahmad din
ya matsa mata da yana son ya gaisa da Julde, ko kuma tayi magana da shi a saka musu rana
yana son ko gaisuwa ce azo ayi, shine namiji babba a gidan su, kuma kamar yanda Hajiyar shi
take cewa babu wani abu da yake jira yayi aure sai lokaci, yana da muhalli, dan kasuwa ne da
yake harkokin shi a tsakanin Dubai da kuma nan Kano, suna da shaguna a cikin kantin kwari,
inda yake mallakin shine, bai kuma boye mata matakin karatun shi daya tsaya a diploma ba
tunda gabaki daya harkar karuwanci ce abinda suka saka a gaba. Diploma din ma yayine kawai
dan ra'ayin dan samun karatun boko da abokin shi ya kwadaita mishi.

Da ta fadawa Nanna ta samu Julde da maganar saiya wakilta Salim da yayi bincike kafin a sati
dayan da ya sakama su Ahmad na turo manyan shi. A tsorace Adee take dan har ranta tana
son Ahmad, irin soyayyar da bata hango kanta a ciki ba, yana da duk wata nagarta da cikar

halittar da kowacce mace zata yaba da ita. Sai dai a irin bincike na aure haka ake binciko
halayen mutum da wasu kan toshe kunnuwan su tare da rufe idanuwa wajen kin yarda, sai
binciken yayi hannun riga da halayen da kai aka nuna maka.

Ga Salim din yace mata

"Ina son magana da Ahmad, ki kira mun shi"

Batare da yayi mata wani karin bayani ba, tsoron ta shiya kara tsorata Ahmad din. Da yazo din
ma ya kirata ya sanar da ita yazo tana jin yanda muryar shi take rawa

"Tunda azahar nake addu'a Adee, idan Yayan ki yace ban mishi ba fa? Ya zan da tarin soyayyar
da nake miki?"

Kasa bashi wani kwarin gwiwa tayi saboda itama a tsoracen take. Dariya Salim yake sonyi
amman ya danne yana kama hannunta ya janyeta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login