Showing 60001 words to 63000 words out of 79955 words

Chapter 21 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

Advertisement

daga kai ya kalli Salim

"Me zanzaro na yayi?"

Kai Salim ya girgiza, idan yayi magana dariya zaiyi, kwanaki yaga Lukman na kallon wani
cartoon a bangaren Saratu, ta gefen ido yaga giccin wani a ciki sai da ya dawo baya ya kara
kallo da kyau, ya kwana biyu ko shi kadai yake zaune sai yayi dariya saboda kamar sun kalli
kugu da kafafuwan Khalid ne kafin suyi zanen. Har yanayin belt din da yake da yakinin sai da
Khalid ya kara huda a jiki sannan ya zauna. Duk gidan babu siriri irin Khalid, ya gama
makarantar amman yaki yin kumari.

Cajar ya karba yana share kallon rashin fahimtar da Khalid yake mishi, har ya juya ya dawo

"Randa duk ka zo asibitin mu, in dai da wannan zanzaron ne, kar ka cewa kowa gidan mu daya

Khalid, dan Allah kace kawai kana nemana"

Bude baki Khalid yayi, kafin yace wani abu Salim yaja kofar, numfashi yaja ya fitar yana jinjina
kai

"Bakomai, Allah na ganin ka Hamma"

Ya furta a hankali yana kwance belt din ya cire shi hadi da zaro rigarshi waje. Salim baya bude
bakin shi ya fadi maganar da zaka so kaji, yanzun da hirar arziki ce da wahala in ba zai zage shi
ba yace ya saka shi magana. Amman da yake ci masa mutunci yayi niyyar yi ya bude baki ya
fadi abinda babu wanda ya tambaye shi. Har yayi wanka ya fito yana tunanin yanda duk
shekarar babu wanda yayi mishi irin zagin da Salim yayi mishi. Masallaci ya fita yayo sallar
Magriba ya dawo.

Inda Nawfal yaje yake tunani, ko gidan Daada zai kwana ne? Ya tambayi kan shi kafin ya dauki
wayar shi da nufin kiran Madina yaji ko Nawfal din yana can sai gashi ya turo kofar da sallama,
kafa ma ya saka, hannuwan shi rike suke da ledoji

"Madina zan kira yanzun inji ko kana gidan Daada"

Kai Nawfal ya girgiza mishi yana zare takalman shi a gefe ya sake amfani da kafar shi ya tura
kofar. Kasa ya zauna kan kafet yana ajiye ledojin da Khalid ya kawo hannu da nufin dauka
Nawfal din ya janye gefe da sauri

"Ba hali me kyau bane wannan Hamma... Daga ajiye abu"

Kafar shi Khalid din ya saka yana harbin Nawfal a baya kafin ya sake kai hannu yaja ledar

"Hamma mana!"

Ko inda yake Khalid bai kalla ba

"Ka aike ni ne?"

Robobine na take away da zafin su rau na kuwa, fito da su Khalid ya shiga yi

"Gidan Adee kaje"

Ya fadi yana saka Nawfal din kallon shi

"Robobin gidan ta ne wannan, dan ita kadai naga tana amfani da irin su"

Kai kawai Nawfal ya jinjina

"Allah ya yafe maka halin nan da ka kwaso"

Jin Khalid din bai kula shi ba sai ma roba daya daya bude yasa shi dorawa da

"Bakin halin da ka koya nake nufi"

Kafar dai Khalid ya sake sawa yana kai mishi harbin daya kauce wannan karin yana dariya. Yayi
kewar su, yayi kewar gida da dukkan zuciyar shi. Zama haka a daki daya da Khalid kawai na
kara tuna mishi da duk wani dalili da yake da shi na dawowa gida, duk wani dalili da babu inda
zaije ya kira gida sai Najeriya. Yana gama baccin shi Adee ya fara kira, ita kadai ya fadama
yana airport, dan sunyi hira ma har sai da ya shiga jirgi. Mashin tace yahau suka hadu a hanya
dan ta fito karbar ma mijinta wani sako da aka aika mishi daga Abuja.

Har miyar da zata mishi wajen kwana hudu Adee tayi mishi, da farfesun kifi mai yawa. Takarcen
da ta hado mishi tsayawa yayi kawai yana kallon ta

"Kafin matar ka ta dawo ne..."

Ta fadi tana dariya, murmushi kawai ya iya yi mata, kuma ta dawo da shi, danma sai da ta tsaya
a hanya yayi sallah a wani masallaci tunda ta san yanda baya son rasa sallar a cikin jam'i in ba
da wani babban dalili ba. Adee bata shiga gida ba, saboda shine kuma, tare da Adee ba saiya
furta abubuwa da yawa ba, ba sai yace mata bai shiga bangaren Saratu ba, ta sani. Idan suka
shiga tare dole zaiji kamar bai kyauta ba, shisa taki shiga dan ta kara mishi lokacin da yake
bukata.

"Kai ba zaka ci bane ba?"

Khalid ya bukata yana katse ma Nawfal tunanin da yakeyi

"Bangane bana ci ba? In zo da abu kana mun wannan tambayar?"

Zaman shi Khalid ya gyara yana jinjina kai hadi da tsoma hannu cikin robar farfesun kifin daya
bude yana fadin

"Okay..."

Ganin da gaske yake yasa Nawfal din mikewa. Gudun kar suyi bari yasa Khalid sauke robar
kasa suka ci tare kafin su fita sallar isha'i su dawo.

"Bari inga me aka dafa"

Cewar Khalid, har Nawfal ya jinjina mishi kai zai wuce bangaren su sai kuma ya fasa

"Muje nima ban shiga ba"

Sai da Khalid yayi mishi kallon da yake fassara ka tabbata yaga ya da dan daga mishi kai
tukunna ya shiga gaba shikuma Nawfal na biye da shi har bangaren Saratu da suka shiga tare
da yin sallamar da ta amsa, yanayin fuskarta na sauyawa lokacin da ta dora idanuwanta kan
Nawfal. Zaune take kan kujera da dan karamin kwano a hannun ta da farfesun naman rago ne
ta zubo, tama tsame duk naman, romon ne take dan diba da cokali tana sha.

"Nanna..."

Nawfal ya furta, Khalid na karbewa da

"Sannu da gida"

Ya wuce hanyar kitchen da sauri, idon dai Saratu ta kafa mishi cike da tambayoyin da ya rasa
wanne zai fara amsawa duk da bata furta su ba.

"Da zun na zo, ina wuni"

Ya ce cikin sanyin murya

"Lafiya lau"

Ta amsa a takaici tana dauke idanuwan ta daga kan shi alamar ta gama bashi iya lokacin da
take tunanin zata iya. Juyawa yayi da nufin barin dakin, zuciyar shi yake jin babu dadi, ita kadai
ta tsane shi, duk duniya ita kadai ta tsane shi kuma bai san dalili ba, tunanin duniya yayi ko zai
tuna wani abu daya taba yi mata banda zama karkashin kulawar mijin ta da Kawun shi ne, yana
da hakkin da zai rike shi ko da ba ita yake aure ba. Me yayi mata da zafi haka?

Numfashin kirki ma bayajin yana shaka in tana waje saboda gudun kar sautin shi ya takura
mata, yana da rai amman idan Saratu na nan kokarin gani yake ya zama gawar da ba zata iya
gani ba, duk dan ya gujema bacin ranta. Ya gaji, bai san yanda ya gaji ba sai yau din nan. Shisa
ya koma yana takawa yaje har kan kujerar da take zaune mai daukar mutum uku ya zauna a
gefe yana dora murmushin da bayaji a zuciyar shi kan fuskar shi

"Na dawo ne gabaki daya Nanna, ba nida nufin zama a garin Kano saboda dalilai da yawa, zaki
cigaba da gaba da gani na lokaci zuwa lokaci saboda banda yan uwan da suka wuce su
Hamma, ban san me nayi miki ba, koma menene ba zai taba zama dalilin da zanyi nisa da yan
uwa na ba, yaran kine duka, kiyi hakuri zaki cigaba da raba su tare dani..."
Ya karasa maganar yana mikewa ya nufi hanyar kitchen din, yanajin yanda take bin shi da kallo,
nauyin da yake ji a kirjin shi duk idan yagan ta yaji ya daga mishi, tsanar da tayi mishi zabinta

ne, ya gaji da raba nauyin tare da ita. Taje ta dauka ita kadai, ko babu wani abu ta bashi su
Khalid, shisa take kasancewa cikin addu'o'in shi. Tana da wannan darajar a idanuwan shi, fridge
ya bude yana daukar ruwa roba daya

"Zuba abinci ne kamar zaka dafa sabo"

Ya ce ma Khalid da yake rike da filet a hannu

"Ina ruwan ka?"

Khalid din yace, Nawfal ya amsa da

"Babu"

Yana ficewa daga kitchen din, murmushi Khalid yayi, ranar farko da yaji dadin karfin halin da
Nawfal yayi. Sai dai yana juya maganar Nawfal din da yace bashi da nufin zama a garin Kano,
ina yake nufin zai zauna? Shi bai fada mishi ba, watakila sai sun samu zama tukunna. Koma ina
ne in dai yana kasar komai zaiyi dai-dai. Tuwon shinkafa ne, zubawa yayi yana dibar malmala
biyu dan shi bai cika rike mishi ciki ba, yana iya kai sha biyu a zaune yaji yunwa.

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149

*RAI DA KADDARA 1*

17

Dakyar yake iya daga idanuwan shi, ya san Allah ne kawai ya tsare mishi hanya daga asibiti
zuwa gida

"Idan ka gaji haka ka dinga kwanciya a asibiti ko baccin awa biyu ne kayi tukunna ka hau titi, ko
ka kira Hamma Khalid ya zo ya dauke ka"

Rokon da Madina tayi mishi kenan kwanaki tana dorawa da

"Kaji Hamma, dan Allah, kaji"

Bai amsa ta ba, saboda inya amsa zai zama kamar yayi mata alkawari ne. Bacci a asibiti ba zai
iya shi ba kamar yanda yaga sauran abokan aikin shi sunayi, saboda akwai hayaniya, duk da
ofishin shi ne can karshe, amman karar takun tafiya na zirga-zirgar mutane kamar cikin kunnen
shi akeyi haka yake jin su, yana iya jiyo karar wayar wani daga ofishin shi. Duk kananun
hayaniyar nan ba zai iya bacci a cikin ta ba. Tun kafin ya tura kofar ya jiyo sautin hayaniyar da
yake da tabbacin tv ce a kunne.

Da tsaki a bakin shi ya tura kofar, sai da ya dan runtsa idanuwan shi saboda karar da yaji ta sa
kan shi sarawa. Nawfal na zaune kan doguwar kujera ya jingina bayan shi sosai, yanda
idanuwan shi suke a rufe ya tabbatar ma da Salim din bacci ne ya dauke shi, wani sautin
mamaki Salim ya fitar yana karasawa cikin dakin sosai ya kai hannu ya dauki remote din da
yake gefen Nawfal ya rage karar tv din gabaki daya sannan ya zauna gefe don ya zare takalmin
da ke kafar shi.

Yana jin wata iska da ta ratsa kafafuwan tun kafin ya cire safar shi, numfashi ya sauke yana jin
wani na mishi wahalar shaka saboda Nawfal da ya doro kan shi a kafadar shi batare daya yi
tsammanin hakan ba, kafin yayi wani motsi Nawfal din ya zagaya hannuwan shi duka biyun a
damtsen shi yana kara kwantawa a jikin shi
"Ina ta missing din ki"

Nawfal ya fadi cikin bacci, shima gajiyar ce a tattare da shi. Bai taba hasaso cewa haka kafa
kasuwanci yake da matukar wahala ba sai yanzun da tun wajen karbar lasisin shi na tuki ya fara
jin kan shi na nauyi, balle kuma daya fara zirga-zirga tsakanin Kano da Kaduna tun da nan din
ya zaba a matsayin garin da zai zauna ya kuma kafa kasuwancin na shi
"Me yasa sai Kaduna? Duk fadin Kano Bajjo? Baka ganin wasu daga Kadunan suna dawowa
Kano don kafa kasuwancin su, ka zabi duk inda yayi maka a Kano zan sai maka fili idan akwai,
in babu zan sai maka ko meye a wajen in dai zasu siyar mun saika rushe ka gina abinda kake
bukata, ina da kudin, in banda su kai kana da kudin... Kaduna tayi nisa"
Julde ya karasa maganar muryar shi dauke da nauyin da yake ji a zuciyar shi

"Kadunan dai nake so Daddy, ai babu wani nisa fa, zan zo in ganku duk sanda nake so. Don
Allah karkace a'a, kamun addu'a kawai"

Yana kallon yanda Julden yake kokawa da zuciyar shi kafin ya jinjina kai a hankali

"Allah ya zaba abinda yafi alkhairi, amman ka kara tunani dai"

Shima ya amsa ne da to ba dan akwai wani tunani da zai kara ba. Ya dauke shi tsayin shekara
daya kafin ya yanke hukunci zama a Kadunan. Tun kafin ya dawo kuma yake binciken hanyoyin
da komai zai zo mishi da sauki. Sai dai ko da kudi ba zasu zamar mishi matsala ba, hanyar tana

da tsayin da bai hango ba. Yau din ma yana dawowa ruwa ya watsa ya fito da nufin shiga
kitchen ya hada shayi, sai ya zauna ya fara hutawa tukunna, bai san lokacin da bacci ya dauke
shi ba. Kamar jiya ya zo, gashi harya shafe watanni biyu da dawowa amman bambanci lokaci
ya kasa barin shi.
Da daddare idanuwan shi kamar an soya gyada a ciki, amman da rana kamar an bubbuge mishi
gwiwoyin kafa haka yake ji saboda baccin da zaita dawainiya da shi. Sunyi waya da Murjanatu
yana hanya, da tunanin yanda yake kewar ta ya shigo gidan, har bacci ya dauke shi ma yana
tunanin yanda zata matsa mishi kafafuwan shi da suke a gajiye da tana kusa. Shisa
kwakwalwar shi tayi mishi tunanin itace yaji ta zauna a gefen shi kamar yanda ta saba. Suna da
bambanci lokuttan dawowa gida, tana rigan shi fita, yana kuma riganta dawowa.

Ranaku da yawa sai tsakiyar dare take komawa, saboda yanayin karatun su ma ba daya bane
ba, kuma in ta tashi daga makaranta zata wuce aikin da takeyi na awa uku wani lokacin awa
hudu, ya danganta da yanda take jin gajiya

"Bajjo..."

Salim ya kira a tsakanin jan numfashi da saukewa saboda ya kawo iya wuya. Amman kamar ya
tunzura Nawfal din daya kara riko shi

"Jikina ciwo yake"

Cewar Nawfal din, hannun shi Salim yake kokarin fisgewa amman rikon da Nawfal yayi mishi
bana wasa bane ba, shisa yayi amfani da gwiwar hannun da yake rike da shi din ya zungure shi
a hakarkari, babu shiri ya bude idanuwan shi yana kokarin gane inda yake da kuma abinda
yake faruwa, a hankali ya juyo ya kalli Salim da yake watsa mishi wata irin harara da yasan
yana gab da kwada mishi mari idan bai daina koma meye Salim din yake tunanin yanayi ba,
hannuwan shi da suke sakale da na Salim ya kalla yana tunanin abinda sukeyi a wajen.

Bai san ihun da yayi cikin kan shi ya subuce mishi ba sai da yaji sautin shi a kunnen shi,
hannuwan shi na nuna mishi bai isa da su ba saboda sun ki sakin Salim din

"Ba zaka sakeni ba dan uban ka? Sai na karya ka tukunna ko?"

Sai lokacin ya saki Salim din yana mikewa cikin hanzari

"Me kake anan?"

Nawfal ya tambaya cikin tashin hankali, wani irin kallo Salim din ya watsa mishi

"Me yasa baka tasheni ba?"

Ya dora yana yarfe hannuwan shi hadi da goge su jikin rigar shi, kai Salim ya jinjina, an kwana
biyu wani bai raina mishi hankali haka ba, ganin yanda ya mike yasa Nawfal din rugawa da
gudu

"Ka dawo kaji me yasa tashe ka ba"

Cewar Salim din yana kallon Nawfal da har ya kai bakin kofar dakin su. Kwafa yayi yana
komawa kan kujerar ya zauna

"Karka dawo falon nan"

Salim ya fadi yana kwanciya akan doguwar kujerar, yasan in yayi wanka da ruwa mai dumi
sosai sai yafi jin dadin baccin, amman kan shi yayi mishi nauyi ba kadan ba.

"Hamma dan Allah... Shayi zan hada sai in koma daki"

Nawfal yayi maganar daga in da yake tsaye

"I will kill you if you make another sound"

Dariya Nawfal yayi yana nufar kitchen, kafin ya gama hada shayin Salim ya kira

"Bajjo!"

Cike da kashedi ya kuma watsa mishi zagi yafi sau biyar. Da gangan ya buga kofar dakin su
wajen rufeta yana jin zagin da Salim din yayi mishi, dariya yayi ya saka mukulli a jikin kofar
dakin. Yasan har yanzun baiyi girman da Salim din zai ki cin zalin shi in ya so ba, ko kafin ya tafi
Kaduna da ya zo ya same shi kwance a falo yana kallo sai da ya kai masa wani duka da ya
wuni yana murza wajen

"Bana hana ku zama a falon nan ba"

Da bai saurin tashi ba wani dukan Salim zai sake kai mishi. A ka'ida falo nasu ne su duka,
amman tuni Salim ya hada ya mallake da nashi dakin. Ko wucewa zakayi in yana kwance saika
dauke numfashi kar kayi ya karasa kunnen shi. Da suna zama suyi kallo in yana dakin shi, ya
zo ya hana saboda basa rage karar tv din a cewar shi, yana jin surutan har cikin kwakwalwar
shi kar wanda ya sake zama. Shayin shi Nawfal ya shanye ya kwanta ya dan runtsa ko na awa
daya ne tunda yaga har biyar ta wuce, yasan dai zai tashi jikin shi yayi mishi nauyi.

**

"Kin siyi jamb?"

Fatima Atiku ta tambayeta lokacin suna rubutu Neco, kai kawai ta girgiza mata. Ita bata ga
saurin da dalibai da yawa masu zana jarabawa sukeyi ba, tun kafin ma ta shiga aji shiddan tana
ganin sauran dalibai na wannan zumudin. In tace bata hango rayuwar jami'a da yanda zata
kasance mata zai zamana karya, amman banda haka bata wani zumudin shiga ko doki, a ganin
ta makaranta dai duk makaranta ce, karatu kuma karatu ne, babu wani abu da zai canza mata,
yanda bata da wasu da zata kira abokai haka ma acan din bata jin zata samu wanda zata kira
da wannan sunan.

Ta fi so sakamakon jarabawar ta su ya fito tukunna, ta ga taci duk wani abu daya kamata kafin
tayi wata jamb, har Salim sai da yayi mata maganar

"Ni nafi so jarabawa ta fito ne Hamma"

Kallon ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login