Showing 48001 words to 51000 words out of 79955 words
Chapter 17 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
shi
"Komai zaiyi dai-dai, kina jina, ko babu su, kina da mu, mu kadai ne daman, tuntuni mu kadai
ne, kar tunanin su ya dame ki da yawa"
Numfashi ta sauke
"Mu kadai ne daman, tuntuni mu kadai ne"
Ta maimaita cikin kanta, kalaman na zauna mata, tunda ta bude ido su kadai din ta gani, ita da
Daada, kafin ta ga su Daddy, su kadai ne kamar yanda Salim ya fada, daga Yelwa har Kabir
basa nan, basa tare da ita tun daga farko, ganin takardar nan ba zai kawo su ba in har suna
raye, shekaru sha shida suke da shi su zo inda take, duk basu zo ba. Ba zasu dame ta da yawa
ba, ba zata basu wannan muhimmanci ba, watakila a gaba, amman yanzun bata jin zasu same
shi. Kamar Salim yaji tunanin da take yi
"I love you"
Kalaman suka subuce suna komawa cikin kunnen shi da wani yanayi da ba zai misaltu ba,
tunda yake, ko da wasa, ko a mafarki bai taba furta su ba, babu wanda ya taba furtawa, duk da
su Adee na yawan fada mishi, amman bai taba mayar musu ba, idan basu gane yana son su a
kananun abubuwan da yake musu ba, to baya jin dan ya fada zai canza wani abu, sai gasu yau
kalaman sun subuce mishi kamar bashi da iko da su. Dariya Madina tayi tana kallon fuskar shi
"Nawa yafi yawa, nagode Hamma"
Ya kasa ko motsin kirki sai ta fita harta rufe mishi murfin motar, ba shiri ya zare seatbelt din
yana fitowa, harta shiga gida, da kusan gudu ya bita yana kiran sunan ta, da mamaki ta juyo,
numfashi ya sauke yana kai hannu ya yamutsa sumar da yake askewa kasa sosai, amman
yanda take a nannade duk da bamai yawa bace zai sa kagane ya hada jini da fulani.
"Ki fada in ji"
Ya tsinci kan shi da fadi, yana so yaji ta furta kalaman ko zai samu saukin cewa shi sun kubce
mishi, yana so yaji ta furta dan ta nuna mishi itama a wajen ta suna da saukin fita kamar a
wajen su Khalid, kalaman basu da nauyin da yake jin sun mishi
"I need to hear you say them Mug"
Ya fadi yana saka idanuwan shi cikin nata, ita kuma da mamaki take kallon shi, saboda tana
tunanin meye yake so ta fada din
"Mug..."
Ya kira wannan karin muryar shi na fitowa a kagauce, numfashi ta ja
"Oh..."
Tana tuna me ya fada a karshe
"Mi yedi ma Hamma Am, ina son ka"
Numfashin da bai san yana rike da shi ba ya saki yana jinjina kai, kafin ta sake fadin wani abu
harya juya. Motar shi ya koma ya kunna yana janta ya fita daga unguwar, yakan ja gilasan ne ya
rufe saiya kunna AC din ciki saboda ya rage ma kan shi hayaniyar kan hanyar. Amman yau
iskar da take cikin motar yake jin tayi mishi kadan, shisa ya sauke gilasan gabaki dayan su,
yana shakar iskar da ta shigo, tana fifita mishi wajajen da baima san yayi zufa ba.
Ba gida yayi niyyar nufa ba, shisa da ya gan shi bakin gate, yaga an bude mishi yasan Allah ne
kawai ya kawo shi lafiya, hankalin shi gabaki daya baya jikin shi, shiga yayi da motar ciki, kila
idan ya watsa ruwa ya dawo dai-dai. Sai dai yana fitowa daga motar yana cin karo da Julde
cikin wata shadda mai maiko da ta karbi jikin shi. Shisa duk yanda za'ace yana da kyau baya
mamaki, in har yayi rabin kyawun Julde to tabbas za'a kira shi me kyau, ko shi da kan shi ma
zai ga kyawun na shi.
Har yanzun hasken fitilar kyawun Julde zai dishe na shi duk da bambancin shekarun da yake
tsakanin su
"Daddy..."
Salim ya kira yana dorawa da gaisuwar da Julde ya amsa fuskar shi dauke da murmushi
"Ya makarantar? Har an dawo?"
Kai Salim ya jinjina
"Zan sake fita, ina so in dan watsa ruwa ne"
Da murmushi a fuskar Julde har lokacin yace
"Allah ya taimaka yayi jagora. A dinga kula dai"
A cikin zuciya Salim ya amsa addu'ar Julden yana wucewa, har yayi gaba ya juyo
"Daddy"
Ya kira yana sa Julde juyowa shima ya kalle shi, dan har ya bude murfin mota
"Wacece Yelwa?"
Ya jefi Julde da tambayar da yaji kamar fadowar gini, babu shiri ya nemi majingini da motar da
yake tsaye a jiki, saida ya tabbata muryar shi ba zatayi rawa ba tukunna ya amsa da
"Kanwata ce"
Kai Salim din ya jinjina, haka kawai ya tsinci kan shi da son sani, ko iya hakane, alakar da take
tsakanin shi da Madina, ya san yar uwar shi ce, amman yau yana son sanin me suka hada.
Juyawa yayi, Julde na bin bayan shi da kallo har ya bace mishi, tambayar ta dake shi, a ina yaji
sunan Yelwa? A ina Salim yaji sunan da yake da tabbacin ko Saratu ba zatayi kuskuren furtawa
a gaban yaran ba. Ba zama sukayi sukai shawara ba, basa bukatar sanin ya kamata su kare
yaran daga abinda ya rabo su da asalin su.
Sai dai wasu sirrikan basa binnuwa
Wasu sirri kan ko ba'a tono su ba sai sun bayyana kan su.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149
*RAI DA KADDARA 1*
14
Da yawa zasu ce tana jin ranar ne daban saboda ta kasance daya daga cikin ranakun da ya
kamata ace suna da muhimmanci a tare da ita, tunda a yau din ta kammala jarabawar aji shidda
da ake kira da WAEC. Sai dai ita din ba kamar kowa bace ba, yanda ta ga yan ajin su na murna
da rawar kafa tunda ma suka shiga aji shiddan sai ya dinga bata mamaki, zaka rantse da sun
gama sakandire shikenan sun rabu da karatu har abada, bayan tana jin tarin burikan da
kowanne a cikin su yake lissafawa.
"Ke ba zakiyi su calender din da naga Adee tayi da suka gama makaranta ba?"
Salim ya tambayeta, dan shima yaga da yawa matan ajinsu sunyi a wancen lokacin, tunda duk
sun bashi, wasu a ciki yana da tabbacin sun bashi fiye da abinda suka rarraba, da yake shima
jeka ka dawo yayi, kuma Julde ya bashi mota tun yana aji biyar, da ba da ita yaje ba, bashida
inda zai zuba kayayyakin da aka dinga bashi
"Um um fa, ni babu abinda zanyi..."
Dan ba burgeta sukeyi ba, bata da wata kawa da zata nuna ta kira da tata a cikin ajin gabaki
daya. Sai dai tace abokan karatu, zasu gaisa dai, sunma fi kulata idan an bada wani aiki mai
wahala da suka kasa fahimta suna son ta taimaka musu. Shisa yau ana gama jarabawa ta fito,
taji dadin samun Salim yana jiran ta, sai hade fuska yake sanda ta shiga motar, ta kuma san
baya rasa nasaba da hayaniyar da ta karade wajen da zaice mata yana jinta har cikin
kwakwalwar shi.
"Mug..."
Ya kira, murmushi tayi mishi, bakar rigace a jikin shi, kamar yanda tunda ya fara aiki yake cikin
su, sai ya dora farar rigar da zata nuna maka alamar likita ne a sama, yanzun take kara ganin
dalilin da yasa wasu a ajin su suke tambayarta meye hadinta da Salim, yana da kyau, yana da
kyawun da ba saika kalle shi sau biyu ba zaka gane hakan. Musamman yanzun da ya ajiye
gashi kwance luf a fuskar shi, saiya kara wani irin kyau da Madina ta san ba ita kadai take ganin
shi ba. Kaf gidan su babu mai kyawun shi, shine ya biyo Julde sak, sai dai takan ga idanuwan
Saratu a cikin na shi.
"Hamma Am, yau fuskar ka ta mun wani iri"
Numfashi ya sauke yana murza mukullin motar, kamar ba zai amsa ba dan har yaja motar ma
sun fara tafiya
"Nagaji ne, na kwana a wajen aiki, tunda safe ina can kuma...sai yanzun na taho"
Har ta daina tambayar shi akan maganar shifting da tasan anayi a asibiti, wasu suyi aikin safe,
wasu na rana, wasu na dare, tunda ya fara zuwa asibiti ta kula rabin rayuwar shi acan yake
yinta, kamar bashi da wani abu a yanzun da yafi majinyatan asibitin da yake aiki muhimmanci.
Kuma kusan hakanne, tunda yana jin kamar yana wani abu da rayuwar shi wanda ya kamata,
kamar da duk wata dakika da zaiyi wajen taimakon tarin marassa lafiyan da ke asibitin da yanda
daudar zunuban shi take dan ragewa, duk da a satikan yana jin da ya rage daudar daya sake
maye gurbin ta da matan da yake bi.
"Ki dauki gifts dinki a baya"
Salim ya fadi bayan ya tsayar da motar kofar gidan Daada, duk hirar da ta dinga mishi da um
yake binta, yar maganar ma bata samu ba, kamar yanda yace mata a gajiye take duk wata
alama ta nuna a gajiyen yake.
"Kasan ina son ka ko?"
Ta fadi tana murmushi, idanuwan shi kawai Salim ya saka cikin nata, shi ya fara cewa yana son
ta, sau daya ne, bai kara ba har yau. Sai dai ya bude mata hanyar fada mishi tana son shi duk
lokacin da zai mata wani abu da taji dadi. Bai sake fadi bane saboda ya ga soyayyar da yake
nufi da wadda take nufi tayi hannun riga. Sai dai baya nufin soyayyar ta bata nukurkusar shi,
bayajin ta har kasan ran shi, ya sha farkawa cikin dare ya duba zuciyar shi yaga itace dalilin
tashin na shi. Bai kara sanin da gaske soyayyar da yake mata take ba sai lokuttan da ya samu
kofar rungumar ta a jikin shi yaki yin hakan.
"Madina ce"
Shine abinda zuciyar shi ta gaya mishi, a lokuttan ne kuma yaga yanda yake da zabi a rayuwar
da ya daukar ma kan shi, idan yana son jinta a jikin shi da duka rayuwar shi amman ya iya rike
kan shi, me yasa yake kasa rike kan shi akan sauran matan? Ya dauki tunanin ne yayi kasa
dashi yasa wani abu mai nauyin gaske ya danne shi, Madina tana nan, babu inda taje, babu
inda zataje, zai kara jira, zai tabbatar zuciyar ta na in da tashi take kafin bakin shi ya kara furta
mata kalaman yana son ta.
"Ledoji biyu ne Hamma"
Batare da ya juya ba ya amsa ta
"Duka zaki dauka"
Da ta dauka din ma, bayan addu'a sai da ta kara cewa tana son shi, baice komai ba yaja motar
shi yana ficewa daga lungun. Ita kuma gida ta shiga da sallama tana kiran Daada tun kafin ta
karasa cikin dakin
"Daada..."
Ta kara fadi ganin ta a kwance kan doguwar kujera, takalmanta ta cire tana takawa har inda
Daadar take, sai da ta ajiye ledojin hannunta a kasa tukunna ta kai hannu daya ta taba jikin
Daada, har lokacin akwai zazzabi, mai zafi ma
"Daada zazzabin nan har yanzun?"
Madina tace cike da damuwa, murnar da ta shigo da ita na dishewa
"Da sauki, dazun ya sauka ma, dawowa dai ya kara yi kuma na sha magani"
Bata yarda ba, tasan Daada da karfin hali
"Ko dai in kira Daddy?"
Da sauri Daada ta girgiza mata kai
"Ki kyale shi, da sauki har abincin da kika dafa na dan ci fa"
Numfashi Madina ta sauke, da yake sai karfe sha daya take da jarabawar ranar, tana tashi da
asuba ta shiga kitchen, sai da ta dafa farar shinkafa, suna da miyar kifi a fridge, dumamata
kawai tayi. Ta gyara ko ina tsaf tukunna ta fita, dan ko lafiyar Daada kalau ma, da daddare take
wanke-wanke, sai ta share ko ina take tafiya makaranta, girki kawai Daadar takan yi musu kafin
ta dawo daga makaranta, da ta gane yin miya da yawa ta saka a fridge ma sai dai ta dafa musu
ko shinkafa ko taliya.
"Me kika samo haka?"
Daada ta tambaya tana son canza akalar zancen
"Hamma ne ya bani... Bari in watsa ruwa in sake kaya"
Kai kawai Daada ta jinjina mata, wankan kuwa tayi ta fito, wando ne daya dan wuce gwiwarta
yana da madauri daga kasan, sai riga ta kusan kamo tsayin wandon, ta saka bakar safa
doguwa. Hulace a hannun ta tana rike da ita, kan kujera ta zauna tana kwance abin da ta daure
gashinta dashi dan ta gyara kan duk ya cakude mata, kallon ta Daada takeyi, da gaskw gashi
rabo ne, waye zaice Madina zatayi gashi? Babu kitso a kanta saboda ta tsani kitso, sai sun kai
ruwa rana take zuwa ayi mata, shima guda biyu ne ko hudu. Duk idan tayi biyun nan tana kama
jelunan dan ta nannade su sai wani abu ya soki zuciyar Daada.
Yanzun ma yanda take tattara gashin bayan ta warware shi tana kokarin gyarawa sai da taji
zuciyarta ta matse, bata yi kama da Yelwa ba, sai dai ko jini, Yelwa na da kyau kamar
mahaifinta da sauran yan uwanta da suke biyo shi, duk da itama Daadar fulani ce gaba da
baya, ba zatace gashi ya saka Yelwa a tsakiya ba, tunda bata da wadatar shi, amman
mahaifinta na da shi, a nannade ma. Na Yelwa ya sauka har kan gadon bayanta, gashi da
santsi, kamar yanda na Madina yake yanzun, bambancin kawai shine Yelwa na son gayu, tana
kuma ji da gashin ta, Madina bata damu da shi ba
"Badon kar Allah ya kamani ba ko Daada? Da nayi aski, ko rabine dana yanke"
Ta kan fada kusan duk lokacin da zata taje kan ko inta dawo kitso, gashin bai dameta ba, yanda
zata kama shi ta nannade ta daure ta saka hula, ba zaka tana sanin tana da gashi ba sam-sam.
"Kinki zuwa kiyi kitso ko?"
Lokaci daya yanayin fuskar Madinar ya canza, bakinta ta turo gaba, tana kai hannu ta gyara
zaman gilashin ta, bata ko amsa Daada ba ta janyo ledojin da ta ajiye, da alamar dayan litattafai
ne a ciki. Tana kuwa budewa taga sune har guda goma, murmushine ya kwace mata batare ma
da ta sani ba tana fadin
"Allah ne kawai zai biya ka Hamma"
Har ranta taji dadin kyautar, batajin akwai wani abu da zakayi mata kyauta da shi da zai faranta
ranta kamar littafi. Ko damuwar Yelwa da ta kasa cirewa a ranta, dan duk yanda ta so ta ture
tunanin iyayen nata can kasan ranta sai ta kasa, tana zaune zata ji sun fado mata. Idan abin ya
isheta zata dauki littafi, babu wani tunani da yake rage mata banda kalmomin da suke yawo a
idanuwanta duk idan ta dauki littafi. Ko rike littafin tayi a hannunta sai taji farin ciki. Dayar ledar
ta jawo tana budewa, wannan karin ihun da tayi sai da Daada ta dan runtsa idanuwan ta.
Waya, waya ce a kwalinta. Ta kasa daina ihun murna
"Waya Daada.. Waya..."
Take fadi kamar zata fasa dakin da karajin ta, tama kasa nutsuwa ta bude wayar da kyau,
zuciyarta har makoshin ta saboda murnar da takeyi, dakyar ta iya samun nutsuwar dubawa taga
Itel ce da sukayiwa laqabi da vision. Ta taba ganin wata itel a hannun Samira yar islamiyyar su,
da yake yarinyar bata gajiya da nuna cewa babanta mai hali ne, duk tsanani irin na makarantar
sai da ta zo da waya a boye, yana ta nunama kawayenta, wayar tayi ma Madina kyau, dan wata
taji tana cewa
"Itel ce, irin ta Yayana sak"
Tunda daga nesa take hangen su, waya na burgeta, ko dan ma ta dinga daukar hotunan lallen
ta, tana yawan jin ana zancen manhajar Instagram inda zaka iya dora hotuna irin wa'annan, ita
duk a cikin kafofin sada zumunta nan ne take zumudin budewa. Saboda jin yanda Instagram
yake ne yasa ta dan kulla abota da Nafi'un ajin su, shi yayi mata bayanin komai, har tana ganin
ta gama fahimtar yanda manhajar take, waya ce kawai ta rage mata. Inda tace Julde ya sai
mata, zai sai mata, amman tunda bai dauka ya bata da kanshi ba, tana da yakinin yana ganin
lokacin da zata rike ne baiyi ba.
Gashi Salim ya bata, sai da tazo budewa ta kula da an ma bude wayar, dan babu ledar
sabuntar nan, kwalin kawai ta cire, aikuwan an bude dan har pouch an saka mata baki, wayar
tayi mata kyau matuka, fara ce.
"Daada kingani"
Ta fadi cike da farin cikin da yasa Daada murmushi, karbar wayar tayi tana dubawa
"Ma shaa Allah. Allah yasa alkhairi yabar zumunci..."
Farin ciki baibar Madina ta amsa Daada ba, wayar kawai ta karba tana kunnawa, cike take da
caji, Salim kuma har sim ya saka mata, sa da ta gama kawowa ne taga kusan komai ma ya
saita mata shi, dan har email ma taga ya bude mata, yar takarda ta kula da ita a cikin kwalin
wayar ta dauko tana warwarewa, aikuwa email dinne da kuma password din shi ya rubuta mata,
shafa rubutun tayi cike da farin ciki, tana tunanin yanda wannan cakudin rubutun da likitoci suke
da shi na Salim ya bambanta, yana da rubutu mai matukar kyau.
Duba contact dinta tayi, ya saka mata lambar shi, ta Khalid, Adee, Julde, sai lambar Nawfal.
Duka da sunayen su yayi saving, sakewa tayi tana gyarawa zuwa yanda take so, ta shi lambar
ta saka "Hamma Am" a jiki. Murmushi yaki barin fuskar ta, earpiece din wayar da cajar ta dauko
tana gyara kwalin ta rufe ta mayar cikin ledar ta kulle, murna