Showing 57001 words to 60000 words out of 79955 words
Chapter 20 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
da shi, baya so, ko kadan, tunda sun ga juna ai ya wadatar, kowa ya ga lafiyar
kowa, meye na wahalar motsa labba in ba neman surutu da sassafe ba.
"Sai munyi waya ko?"
Madina ta bukata ganin ya shiga motar shi baice mata komai ba, yau yan rashin surutun sun
motsa mishi, kai kawai ya daga mata yana jan motar shi, tsaye tayi da murmushi a fuskarta
harya bace ma ganin ta. Hamman ta kenan, kamar mai aljanu, lokaci daya suna cikin hira zaiyi
dif kamar bai taba surutu da ita ba, duk abinda zatace da kai zai ta amsa ta, karshe ma yace
mata shi tafiya zaiyi, ko da wasa ranta bai taba baci ba tunda ta san haka yake, shisa yanzun
ma ta koma cikin gida abinta, idan bai kirata ba, ita zata kira shi.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149
*RAI DA KADDARA 1*
16
Ina son rubutu
Fiye da yanda duk kuke tunanin kuna son karatu
Ba yanga bace ba
Ba jan rai bane ba
Ba kuma dan naga ana son littafi na bane ba
Idan har banyi rubutu ba ina da uzuri mai karfi
Nagode da fahimtar ku.
*
Da farko tayi tunanin bugun da take ji cikin kanta kwakwalwar tace take kokarin yaki don samun
hanyar fita daga kokon kanta bayan shafe tsayin daren da littafi rike a hannun ta, ba karamin
mamaki tayi najin kiran assalatu a kunnen ta ba. Dakyar ta karasa azkar tana zuwa ta gaishe da
Daada da fada mata kan ta na ciwo zata kwanta, ta kai wasu dakika kafin ta fahimci hayaniyar
ba daga cikin kanta bane ba, bugun kofa ne da yake fitowa daga wajen dakin
"Ughhh"
Ta fitar da wani sauti daya fito daga makoshin ta, me yasa yanzun? Duk ranaku me yasa yau?
Me yasa sanda take matukar bukatar jin shiru don samun rama ko kadanne daga cikin baccin
da tayi sakacin rasawa a daren jiya? Hannu ta kai gefen gadon ta in da tasan gilashinta yana
nan ta dauka ta saka a fuskarta ta batare da ta bude idanuwanta ba, dakyar ta iya sauko da
kafafuwanta daga kan gadon tana jin kanta kamar an dora jakar kaya saboda nauyi.
Ba karamin yaki tayi da jikin ta kafin ya yarda ta rabashi da gadon ba, tana samu ta bude
idanuwanta ta nufi hanyar kofar da bugunta yake ta karuwa. Sai da tayi wata hamma kamar da
bakinta zata bude kofar sannan ta mika hannu tana murza hannun kofar tunda ba mukulli bane
a jiki. Kafafuwan shi ta fara gani, babu takalma, sai alamar wandon farin yadin da yake sanye
da shi, ta kasan gilashin tasa hannu tana murza idanuwanta, ta san mai kafafuwan, tana son
dai tabbatar da ba bacci bane yake sakata gane-gane.
"Hamma kafar ka kamar ta mata, zatayi kyau da kunshi"
Maganar da ta taba fada mishi na dawo mata, tana sakata daga kanta ta sauke shi kan fuskar
Nawfal da yake tsaye ya harde hannayen shi a kirjin shi yana kallon ta da murmushi a fuskar shi
"Hamma..."
Ta kira kamar wadda tayi gudu saboda mamakin ganin shi
"Daada tace kan ki na ciwo, nace karya kike, bacci ne bakiyi ba kin tsaya karatu"
Dariya tayi, kafin tayi murmushi mai sauti, tana sake wata dariyar saboda ba zatace ga abinda
take ji ba, cikin su dai harda sautin bugun zuciyarta da take jin ya karu, da yakan karu ko da
tunanin shi tayi, ko kuma taci karo da sakon shi a wayarta kamar yanda sukan yi magana ko da
ba kullum bane tunda tayi tata wayar.
"Hamma..."
Ta sake kira a karo na biyu sauran kalaman na makale mata, ko jiya ya tambayi ya take ita da
Daada, amman baice mata zaizo ba
"Ki koma baccin ki, zan ganki ne kafin in wuce"
Yanda ta zare mishi idanuwa yasa shi girgiza kai yana dariya
"Gida zanje in huta, daga airport nan nayo... Zan dawo sai anjima..."
Nata kan ta jinjina mishi da murmushin da yaki barin fuskarta har lokacin. Tana kallon shi har ya
juya, tana jin tarin maganganun da take son fada mishi, amman ta rasa ta inda zata fara
"Hamma!"
Juyowa yayi
"Sannu da zuwa"
Dariyar shi ya sake yi, sai ta ga kamar ya kara canzawa, kamar shekaru sun nuna a jikin shi, ya
kara yi mata girma. Ba kuma gashin daya bari a fuskar shi bane kawai, harda wata kamala da
take tare da shi ko a yanayin takun shi ba wai iya fuskar kawai ba. Har ya fita daga falon tana
kallon shi ta kasa komawa cikin daki, sai ma kofar da ta rike tana lilo a jikinta batare da ta sani
ba. Lokacin da ta raba jikinta da kofar dakin Daada ta nufa tana samun ta a zaune rike da
Qur'anin ta da Hizb biyu ne.
"Daada Am"
Ta furta cike da farin cikin da take ji ya cika zuciyar ta taf, ta karasa cikin dakin tana zama gefen
Daada hadi da dora kanta a kafadarta kafin ta zame gabaki daya tana kwanciya a jikin Daadar
"Hamma ya zo"
Cewar Madina tana rufe idanuwanta, dayan hannunta Daada takai tana zare ma Madina
gilashin da yake fuskarta
"Dagani ki koma kan gado"
Batayi musu ba ta tashi tana jan jikinta zuwa inda tasan gadon yake badan tana ganin komai
yanda ya kamata ba, tunda babu gilashinta. Numfashi ta shaka, hancin ta na cika da kamshin
da dakin Daada ne kawai yake yin irin shi, wani dan turare ne madara da tun tashin ta tasan
Daada na amfani da shi, in ta diba ta shafa sai taji kamshin bai mata a jikin ta ba, ta daifi son ta
shigo dakin Daada ta kwanta ta shaki kamshin anan, ko ta kwanta a jikinta, sai taji shi ya
bambanta, har tunani take ko wasu mutanen na da nasu kamshin ne.
Dan in dai hakane to da Salim da Daada suna da wannan kamshin nasu na daban, ita bata da
tarar turare, kowanne iri ya sha gabanta amfani takeyi da shi in dai taji yayi mata dadi, tana da
su kala-kala, Adee ma in dai zataje tayi mata kunshi bayan kudin da sai sun kai ruwa rana take
karba sai ta hada mata da turaruka, Julde kan siyo mata shima, haka Daada, Salim kan shi ba
zata kirga adadin lokuttan da ya bata kyautar turare ba, duk kuwa da ta littafai ta shallake
kowacce kyauta da take giftawa a tsakanin su.
Ita kam tasan bata da wani tsayayyen kamshi, zata iya jera sati kowacce rana da kalar turaren
da zata fesa, amman banda Daada da Salim, kamshi daya sukeyi ko da yaushe, in dai bana
jikin su bane ba, to ba karamin kokarin su take gani wajen yin amfani da kalar turaren da har ya
zame musu jiki haka ba. Nawfal ba zata tantance yana kamshi ko bayayi ba, saboda kamshin
shine karshen abinda yake zuwa mata duk in zata gan shi, takan samu bugun zuciyar ta daya
kan karu ya koma mata dai-dai ne, zuwa lokacin kuma sun shiga wata hirar da take saka mata
manta duk wani abu da yake wakana a wajen abinda suke tattaunawa.
"Me kika ci?"
Madina tayi tambayar a tsakanin hammar da ta subuce mata
"Kwai na soya na sha shayi"
Sake gyara kwanciya tayi, tasan akwai ruwan zafi a flask tunda ita ta dafa da daddare, kuma
Julde da yazo ya kawo musu biredin da tafi so mai kwakwa, shisa ma ta koma baccin ta bayan
tayi sallah dan tasan Daada zata sha shayi babu wani abu da zatayi banda share-share in ta
gama baccin. Lumshe idanuwan ta tayi, Daada na kallon ta, ko ba bacci takeyi ba yanzun da
babu makaranta sai takai karfe tara na safe bata karya ba, yau gashi goma na neman yi. Baccin
kuwa Madina ta koma dan shine a idanuwanta.
**
A gidan Daada yabar akwatin shi saboda ba zai iya daukar kayan ba a yanda yake jin shi. Jakar
ratayawar kawai ya dauka. Kudin da ya sallami mai mashin din daya kaishi gidan daga airport
ma a wajen Daada ya karba, haka wanda zai kaishi Hotoro. Murmushin da yayi ma maigadi ma
yanajin yanda ya bayyana kan fuskar shi da duk gajiyar da yake tare da ita kafin ya wuce shi
yana kara ma takun shi sauri. Harya daga hannu zai kwankwasa kofar yaji muryar Salim cikin
kan shi
"Dole sai kun kwankwasa zaku shigo?"
Murmushi yayi yana kama hannun kofar da tunanin watakila Salim din ma yana falon. Tunanin
shi baiyi karya ba kuwa, zaune Salim din yake ya jingina bayan shi da kujerar, hannun shi na
rike da remote, yanda idanuwan shi suke a lumshe yasa Nawfal tura kofar a hankali dan yaga
kamar bacci yake. A hankali ya karasa shiga cikin dakin, farar rigar da take kan hannun kujera
ta tabbatar ma da Nawfal din Salim daga wajen aiki yake
"Ina jin idanuwan ka a fuskata"
Salim yai maganar yana sa Nawfal ja da baya saboda ya dan tsorata shi
"Hamma mana..."
Ya furta yana saka Salim din bude idanuwan shi daya sauke su kan Nawfal
"Sai ka gama kare mun kallo zaka wuce? Me yasa mutum ba zaiyi bacci a nutse a falon nan
ba?"
Kallon shi Nawfal yake yana murmushi kafin ya bude hannayen shi yana nufar inda Salim yake
zaune hadi da fadin
"Na dawo lafiya, kuma nima nayi kewar ka Hamma"
Yanda Salim din ya zaro idanuwa yana kaucewa ganin da gaske Nawfal rungumar shi zaiyi
yasa Nawfal din sauke hannayen shi yana kwashewa da dariya, har kirji Salim ya dafe kamar
yaga wani babban abin tashin hankali, wucewa ciki Nawfal yayi ya karasa dakin su, komai a
hargitse yake, babu datti dai, amman ko ya rantse bayajin zaiyi kaffara, anfi wata rabon da a
gyara gadon. Kwanciya kawai akeyi ana tashi, da zanin gadon da bargon duk sun hade sun
cakude waje daya. Numfashi ya sauke yana zame hannun jakar shi daga kafada ya sauke ta
kasa.
Sai da ya fara rage kayan jikin shi tunda farin yadi ne manyan kaya. Yabar singileti da gajeran
wando tukunna ya hau gyaran dakin, ya dauko wankakken zanin gado ya shimfida, wannan din
dama wasu kayan Khalid din da yayi tunanin masu dattine ya tattara yana saka su cikin
kwandon da ya ajiye a dakin don zuba kayan dauda da Khalid baya amfani da shi. Har shara ya
sake ya dauki turaruka kala biyu ya fesa. Wanka ya shiga ya fito, wata singiletin ya samu cikin
jakar shi da gajeran wando ya saka, da yake babu kaya suna gidan Daada cikin kayan Khalid
ya samu wata bakar riga marar nauyi ya saka a jikin shi, bai wani bi takan wando ba dan
bayajin Khalid na da wandon da zai mishi.
Yanayin jikin su ba daya bane ba, yafi Khalid tsayi, kuma ya fishi jiki. Kafafuwan Khalid sosai
suke mishi kama da sandar snooker, amman bai fada ba saboda Khalid zai zage shi. Kitchen ya
nufa saboda yunwar da yake ji, banda shayi baiga wani abu da zai iya ci ba, yunwar da yake
tare da ita tafi karfin shayi. Shisa ya fito falon wajen Salim da yanzun ya kwanta kan doguwar
kujerar yana fadin
"Hamma ka bani mukullin motar ka da kudi in fita in siyo wani abu, yunwa nake ji"
Hannu Salim yakai ya laluba kujerar da yake kwance a kai yana mika ma Nawfal din mukullin
"Wallet dina na cikin motar, akwai kudi a ciki"
Karba Nawfal yayi
"Zan taho maka da wani abu?"
Numfashi Salim ya sauke
"Ka kyaleni Bajjo"
Juyawa Nawfal yayi yana komawa dakin su, dakyar ya iya samun wani 3 quarter da yake
tunanin na shine ya saka ya fita. Cikin abokan da yayi yan Najeriya acan sai yaji suna maganar
yanda suka ga komai ya canza da sukaje gida, har wasu na nuna kamar aiwatar da hidimar yau
da gobe a kasar Najeriya tana musu wahala. Da idanuwa Nawfal yakan bi su kawai. Saboda in
yai magana tashi zata iyayin zafi, duka shekarar su nawa a kasar wajen? Shekarun da sukayi a
Najeriya ya ninka wanda sukayi a can.
Karatu ya kai shi, yanzun kuma daya kammala ya dawo, yana da tarin burukan da yake son
fitowa da su daga cikin kan shi, shisa ya dawo, shisa bai bata lokaci ba duk kuwa da yanda
yake ganin son hakan a idanuwa Murjanatu. Zaman su basu fara shi da boye-boye ba, ta sani,
tun farko ya fada mata zaman kasar waje ba nashi bane ba, ta yarda, ta aminta da inda duk ya
saka kafafuwan shi zata bishi.
"Turai na tana tare da kai Gidado, in da duk zan saka kafa idan taka bata biye ba zanji dadi ba,
zan fi so ace ka cire kafar ka ne a wajen kafin in dora tawa"
Ba zai manta yanda ya riketa a jikin shi ba, kamar yanda kalaman ta suka samu wajen zama a
zuciyar shi. Bai bata lokaci ba, duk da yana jin shi kamar dan koyo saboda yanayin tukin nan da
can ba daya bane ba, taka manyan dokokin tuki ba wani abu bane a wajen mutane da yawa a
Najeriya balle kuma wasu kananu, ya sha zagi yafi a kirga daga fitar shi zuwa dawowar shi,
dariya kawai suka dinga bashi. Sai da ma ya tsaya inda yaga alamar ana saida kati ya siyi
sabon sim din MTN ya kuma siyi katin da zai saka a ciki.
A hankali ya tura kofar dakin ya shiga, sai dai Salim baya falon, shisa ya wuce dakin su. Zagi
zai sha idan yace yaje ya kai mishi mukullin mota ko da kuwa ba bacci yakeyi ba. Dankali ya
siyo soyayye da gasasshen kifi sai ice cream roba biyu, canjin da ya rage ma Salim a wallet din
gabaki daya dari takwas ne. Ba magana zaiyi ba ya sani, ko da kudin sun fi haka, Salim din ya
koya musu kashe kudin shi kamar suna kashe na su. Ko motar shi ka shiga, ko dakin shi,
abinda duk yai maka in kasa hannu ka dauka Salim ba zai kalle ka ba.
Sosai yaci ya koshi, ya dauki dayar robar ice cream din shi ya kai cikin fridge yana komawa
daki. Wayar shi ya dauka ya ciro sim din shi yana saka MTN din, ya kumayi loading din katin,
data ya siya saboda zaifi mishi sauki yayi ma Murjanatu magana ta whatsapp, in yaso ita sai ta
kira shi daga nata bangaren. Yana budewa kuwa sakkoninta suka fara shigo mishi, sunfi goma,
biyu daga cikine na tambayar lafiya da ko ya sauka lafiya, sauran na yanda take kewar shi ne.
Murmushi yayi, yana amsa kowanne a ciki.
In tana haka wani sai ya dauka ita kadai take kewar shi, idan yace mata yanda duk take ji bai
koyi rabin abinda yake ji ba sai tace zatayi mishi gardama. Sake tura mata wani sakon yayi
yana fada mata zai kwanta, zai kuma saka wayar a silent. Dan karta kira ta ga bai dauka ba.
Dan kan shi ya fara nauyi, kan gadon ya hau yaja bargo yana rufe kafafuwan shi hadi da
lumshe idanuwan shi kafin bacci mai nauyi ya dauke shi.
*
Ba sai wani ya fada mishi ba, yanayin yanda yaga dakin tsaf ya san aikin Nawfal ne.
"Cikin satin nan fa nake son dawowa"
Nawfal din ya fada mishi
"Allah ya bamu aron lokacin"
Shine amsar da ya bashi, idan ya tambaye shi cikin satin wace rana zai iya cewa shima bai sani
ba. Kawai abinda ya sani shine cikin satin zai dawo. Da wahala Nawfal ya tsayar maka da
lokaci, ko ya sakama abu lokaci, zai dai fadi abinda yake hasashen zai iya faruwa. Basu kuma
sake maganar ba dan lokacin duk da zasuyi waya ko suyi chatting sai yayi musu karanci,
zantukan su ba masu karewa bane ba. Da shi ya wuni a wajen aiki yau, duk wani abu da za'ace
maka alfarma da kudi basa yin shi a Najeriya zai iya karyatawa.
Dan yagani akan bautar kasar shi, Julde kawai ya sanarwa baya son barin garin Kano, camp
din ma da ake zama shi bai zauna ba, a ASAD pharmaceuticals ltd da yake nan Kano yayi
bautar kasar shi da bai shige watanni da kammalawa ba, kuma sai yayi sa'ar samun gurbin aiki
tare da su, ya karba tunda albashin babu laifi yana da kyau. Ba nan yake hari ba, asibitin Aminu
Kano yake so, zai kuma nema da zarar ya kammala digiri din shi ta biyu da yake jiran a fara
siyar da form ya nema.
Tunda yana hangen kacokan abincin shi a bokon yake gara ya zage dantse ya nema da kyau,
kafin ya sauke numfashin da ya shaka an kwankwasa kofar
"Shigo"
Ya furta yana kwance agogon da yake daure a tsintsiyar hannun shi
"Kabani charger din ka Khalid, na bar tawa a asibiti"
Jikin bango inda socket yake Khalid ya karasa yana ciro cajar, shisa yake da guda uku, daya a
mota, daya a gida dayar kuma a office din shi dan gudun samun irin wannan matsalar tunda ya
san halin shi da mantuwa. Abu muhimmi ma mantawa yake balle kuma wata cajar wayar da in
ba kiran shi akayi ba saiya wuni baibi takanta ba
"Dole sai kayi zanzaro?"
Salim ya tambaya da murmushi a idanuwan shi duk da yanata kokarin ganin bai karasa kan
labban shi ba, kugun shi Khalid ya kalla kafin ya