Showing 18001 words to 21000 words out of 79955 words

Chapter 7 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

Khalid in
muku dukan dana dade ina tarawa"
Yanda ya karasa maganar yasa Nawfal yin dariya, duk da hawaye ne cike taf da idanuwan shi,
jakar Salim ya sakar mishi yana fadin

"Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya"

Kai kawai Nawfal ya iya dagawa, idan yayi magana kukan da yake tarbewa ne zai kwace mishi.
Takawa yayi kawai yana cigaba da tafiya kafin ya juyo ya hange su tsaye, hannun shi ya daga
musu, da Khalid da Daddy ne suka daga mishi hannu suma. Salim kai kawai ya jinjina, baya
shiga harkar kowa saboda baya son jin wani abu kusa da zuciyar shi, baya son saka kowa da
komai cikin ran shi, duk wani abu daya danganci hayaniya baya so. Yau yayi ma Nawfal
magana saboda kunnuwan shi sun sha kwaso mishi maganganun Saratu da take yiwa Nawfal
din da baya son ji.

Yanda yaron yake rayuwa da wannan hayaniyar har mamaki yake yi. Fata daya ya tsinci kan shi
da bin Nawfal da shi yanzun da suka juya hanya. Allah yasa da jirgin su ya tashi ya bar duk
wata hayaniya da take cikin rayuwar shi, tafiyar ta samar mishi da wani shiru a rayuwar shi.

Sai dai abinda Salim bai hango ba shine addu'ar shi da ta karbu
Nawfal ya bar duk wata hayaniya da tafiyar shi
Ya barta tana jiran dawowar shi
Dawowar da idan tayi mishi maraba sautin ta bashi kadai zaiji ta ba
Har su da suke zagaye da shi sai ta taba.

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*RAI DA KADDARA 1*

06

"Karatu ne ya rike ni Daada..."

Shine uzurin farko daya fara kawo mata a cikin shekaru biyu, a kuma karo na farko da taji
muryar shi ba sakon gaisuwar shi a bakin Julde ba. Yanda take kwana tana tashi a cikin
shekarun Allah ne kawai shaida, sai kuma ita da ta san kalar damuwar da take ciki, tunani babu
kalar wanda batayi. Duk idan Julde yace mata
"Munyi waya da Bajjo, yace a gaishe da ke sosai"

Sai ta dauki dakika tana kallon kwayar idanuwan shi ko zata ga karyar da take tunanin yayi
mata. Amman saiya fada murmushin shi da cewa

"Kinsan akwai banbanci awa kusan biyar tsakanin mu da su, sanda zai kira zakiga sai wajen

karfe goma da rabi na dare, da na kira kinji muryar shi"

Tun tana yarda harta fara saka kokwanto a cikin ranta, ta san damuwar da Julde yake karanta a
fuskarta yasa shi hada mata wayar tafi da gidan ka ta telephone tunda salular ta hannu da ake
yayi tace bata so. Sanyin daya ratsa zuciyar ta bayan jin muryar Nawfal sai da ya saukar mata
da wata kasala ta ban mamaki.
"Bajjo"

Ta kira kamar ta kasa yarda muryar shi ce take ji cikin kunnenta kamar yana gabanta. Sai ma
da yayi dariyar nan tashi sai taji idanuwanta sun cika taf da hawaye, tsoron da take kwana tana
tashi da shi ta nema ta rasa.

"Ka dinga kirana kullum ina jin lafiyar ka kaji ko? Shirun nan shine yake daga mun hankali fiye
da rashin dawowar ka"

Ya kuma ji maganarta, kullum karfe tara na dare agogon Najeriya yake kiranta, wasu ranakun
sukan dauki fiye da mintina talatin suna hira, wasu ranakun kuma gaisawa kawai sukeyi zaice
mata yana da ayyuka da yawa da zaiyi.

"Wata rana ki rike mun Madina da hira mana Daada, kar tayi bacci mu gaisa"

Nawfal ya roke ta, sai dai ta amsa shi da to, dan bata san ta inda zata fara mishi bayanin canjin
da Madina takeyi da duk rana ba, a yan shekarun yarinyar komai nata da ka'ida takeyi, in ta
dawo daga makaranta karfe shidda zata sake share gidan ko da kuwa Daada ta share, tayi
sallar Magriba, taci abinci, a tsakanin ne kafin isha'i zatayi nazarin litattafan ta, ko tayi aikin gida
idan tana da shi, tana idar da sallar isha'i take kwanciya. Wani kallo duk yanda take son shi
baya shiga tsakaninta da baccin da tasan tana bukata. Yan kunshi yanzun har sun gane, in dai
ba alhamis da juma'a ba da yamma, in kazo ma ba zaka samu ba.

Sai dai ko lokacin hutu, kallo kuwa ran asabar da lahadi zata zauna tayi da rana haka, karatu
dai dakin Madina cike yake da takardu da litattafai, shisa lokacin da ta fara wani irin ciwon idon
da bayan kaita asibiti saida suka yi mata gilashin da gashi nan tana ta fama da shi Daada tace

"Kallon takarda, ace mutum idon shi ba zai huta ba, kullum cikin karatu ba dole ido ya lalace ba"

Yanda duk Madina da Julde suka so fahimtar da ita cewa ba karatu bane ba ya ci tura, sai
gajiya sukayi suka kyale ta. Har yanzun bata daina mita lokaci zuwa lokaci idan ta ga Madina
manne da littafi, takarda ko ta kosai ce suka siyo suka cinye sai Madina ta dauka ta karanta
taga meye a ciki. Littafi duk wanda ta rubuta sai Julde ya siyo mata.
"Hamman ki na gaishe ki, yace in rike ki da hira har lokacin kiran shi yayi dan ku gaisa"

Daada ta gwada fadawa Madina da ta saka hannu tana gyara gilashin daya cinye kusan rabin
fuskarta kan karan hancin ta tana yin murmushin da baka raba fuskarta da shi sannan tace

"Hamma baya kira da wuri Daada, kice in yana so mu gaisa ya kira kafin lokacin bacci na yayi"

Shima da ta gaya mishi abinda Madina ta ce dariyar yayi yana amsawa da

"Daada komai na a tsare yake, bana son shigar da wani abu cikin lokacin yin wani abin"

Kai kawai ta girgiza, Nawfal yayi mata nisan da bata ganin canjin da yau da gobe take yi wa
rayuwar shi, amman iya hakan ta fahimci sun hadu waje daya tare da Madina, sun dauki wata
akida ta kayyadaje yanda ranakun su zasu kasance, har suna ganin ba zasu iya canza hakan
dan wani ba. A kauye ta tashi, kauyen da karatun addini ma sai da ta shigo binni ta neme shi da
kanta, shisa bata shiga cikin irin wannan rayuwar ta su Madina da tafi karfin fahimtar ta, Madina
ma da take gabanta da yawan abubuwa sai dai ta bita da addu'ar neman shiriya ko samun
sauki, balle Nawfal da yake wata duniyar.

Sallamar da akayi ta katse ma Daada dogon tunanin da take zaune tana yi, sai da ta sauke
numfashi sannan ta amsa tana mikewa jin kamar karar sauke wani abu mai nauyi, tana fitowa
kuwa Salim ne ya ajiye buhun shinkafa a tsakar gida

"Karka ajiye anan, ka shigo da shi daga ciki"

A hankali ya daga idanuwan shi yana kallon ta, idan wani yana wajen zaice kamar a takure
yake, wani ma idan yaga kallon zai dauka shine karo na farko da ya taba ganin Daada, yana
kallon ta ne da mamakin dalilin da zaisa tayi mishi magana, kamar ba zai amsa ba yace

"Akwai wasu kayan..."

Cikin muryar shi da take a bude amman yanayin kalaman sun fito ne cikin sanyi da abinda
mutane izzar da tasa mutane da yawa suke daukar ya fito tsatson sarauta, ko da Daada tayi
niyyar fadin wani abu Salim bai tsaya ba balle yaji, juyawa yayi abin shi, tana bin shi da kallo,
shigar kananun kayane, dogayen kafafuwan shi basu sa yaji akwai bukatar ya dinga suturta su
ba, wandon da yake jikin shi ruwan madara da kadan ya wuce gwiwa, sai riga da tayi ma Daada
kama da ta sanyi kalar ja, mai dogon hannun da yadan tattare yana ja sama, sai hular sanyi
daya tura baya rabin gashin shi a waje, ita kuma kala daya da wandon shi.

Gashin in da yake a bude, yanzun daya dawo dauke da kwalaye biyu da alamu suka nuna na
taliya ne, Daada ta kula da a cukurkude gashin yake, yayi wani irin aski da in ka ganshi cikin
masallaci mamaki zai kamaka na kasancewar shi musulmi, ko hausa kaji yayi saika juyo ka
kalle shi. Daga yanayin kirar jikin shi, tsayin shi har shigar shi bata nuni da cewar ba bahaushe
bane shi, bafullatani ne gaba da baya, kuma mabiyi addinin musulunci. A cikin yaran Julde duka
daga Adee sai Khalid ne suke zuwa wajen ta akai-akai.

Da dalili ko babu sukan zo harma su kwana, Salim in ba aiko shi akayi ba, ko kuma motar Julde
ta samu matsala yasa ya kawo shi, da kan shi bai taba wanko kafa yace yazo ya gaishe da ita
ba. Idan zuwan yayi ma gaisuwa ce take hadata da shi, yanda yake magana kamar an shaqe
shi an saka shi dole na daya daga cikin dalilin da yasa ko tambayar shi ya sauran yan uwan shi
batayi. Tas ya gama shigo da kayan abincin da suka hada harda doya da mai fari da na ja,
tukunna ya kalli Daada yana furta

"Ina kwana"

Murmushi tayi

"Lafiya kalau babban dan aike, sannu da kokari, Allah yayi albarka"

Salim ya amsa da

"Kitchen zan shiga da su?"

Maimakon amsa addu'ar da tayi mishi, ya jita, ya kuma amsa a zuciyar shi, maganar duk da zai
motsa labban shi yayi ta in yana da halin takaitata zaiyi. Kai Daada ta jinjina mishi tana komawa
cikin dakin dan ta bashi hanyar wucewa, haka ya dinga daukar kayan yana kaiwa Kitchen, ya
kuma yi mata magana dan ta nuna mishi inda zai saka mata komai, yana karasawa yace
"Gas fa? Daddy yace in dauka a sake filling"

Kofar da zata hadaka da bayan kitchen din inda cylinder din gas din take Daada ta nuna mishi
ya wuce ya kwanto, daman ya kare, ko da safen a risho Madina ta soya musu dankali, basa
rabuwa da kalanzir a rishon su tunda gas idan ya tashi karewa babu ruwan shi da ka cika
tukunya da shinkafar da ta dauko dahuwa.
"Da ka taimaka in kira Madina sai ka kaimun ita kasuwa tayo mana cefane...siyayyar da dan
dama kar in saka yawo a kasuwa"

Numfashin Salim ya fitar yana dan daga mata kai a hankali, in ba ita ba, babu mai saka shi
wannan aikin. Shi Madinar ma rabon daya saka ta a idon shi harya manta, idan zai fadi gaskiya
ya ma manta da ita ne gabaki daya sai yanzun da Daada ta ambace ta, ba zai manta surutun
yarinyar da yake hau mishi kai tun tana yar mitsitsiyarta ba. Balle kuma yanzun da yasan ta fara
jin tashen yan matanci, yasan waye shi, tun kafin mata su kara nuna mishi shidin wani ne yasan
ko da bashi da kudi yana da kyan da suke bi kamar zasu lashe shi. Yanzun ko matan da yake bi
yana da mugun zabe, kuma kashe din shi na farko shine

"Bana son surutu, komai zai mun dai-dai idan zamuyi abinda zamuyi mu gama banji muryar ki
ba..."

Manyan mata ma, riqaqqu suna rikicewa a kan shi balle yan yaran nan da yake gani yan aji
daya a makaranta suna bin shi kullum da

"Yayaa Salim dan Allah zaka duba mun assignment dina"

Har rasa yanda akayi ya zama Yayaa a wajen su yake yi, yakan karba a wajen ya nemi bango
ya dora idan na abin rubutawa ne ya rubuta musu, su kadai kuma yake tsayawa har ya danyi
wa bayani wasu lokuttan, saboda 'yan yara ne, saboda yana da kanwa shima, zai so in ta nemi
wani ya taimaka mata da abinda ya shige mata ta harkar karatu ya taimaka mata din. Balle
kuma Madina da ba zai iya kiyasta shekarunta a yanzun ba, ko yace zai iya hasaso matakin
karatun ta.

In da yake tsaye anan Daada ta dawo ta same shi

"Ka zo ka zauna kafin ta fito"

Kai ya girgiza saboda baya son cire takalmin da yake kafar shi, in dai zai karasa cikin falon ya
zauna dole saiya cire, ba zai taka mata kafet din da yake shimfide kusan cikin dakin da takalma
ba, ko da zai shiga kitchen ta gefe-gefe wajen tayal ya dinga bi. Agogon da yake daure a
tsintsiyar hannun shi ya dan daga hannun yana kalla. A cikin kan shi yake hango wasu mintina
sha biyar zuwa ashirin kafin Madina ta fito, ya tabbata zata tsaya iyayin kwalliyar nan da yake
saka shi kwankwasa dakin Adee ya watsa mata zagi in dai tare zasu fita, baya son jira.

"Banga biro bane ba fa, da zan rubuta abubuwan kar in manta, amman na samu fensiri"

Muryar Madina ta fara dukan kunnuwan shi kafin ya sauke idanuwan shi akan ta, wani dan
karamin sauti ya kwace daga makoshin shi da yafi alaka da tsantsar mamaki. Yanda ya ganta
yanzun ya goge duk wani hoton yarintarta da yake da shi cikin kan shi balle ya nemo ya gwada
ya tabbatar da wannan yar mitsitsiyar halittar ta gaban shi itace Madinar da ya sani. Zai dawo
da batun kankantar ta da ya gani, shigar jikin ta, shigar ta ita ce abinda yasa sautin kwace
mishi. Wando ne jeans da ta lankwashe daga kasan kusan ninki biyu kamar yayi mata yawa, sai
takalmi kafa ciki, rigar da take jikinta yana da tabbacin ko shi ya saka zai iya yawo a ciki saboda
girmanta, hijabin da ta saka da alamu yar karama ce fara, sai ta dora rigar a sama ta yanda
kanta da wuyanta kawai hijabin ta rufe.

Bai san me zai kira rigar jikin Madina da ita ba, kaurinta yayi yawan da bai kamata ace ta sakata
a yanayin zafin da akeyi ba, ga dogon hannaye rigar take da shi da ta dan ja baya kamar yanda
yayi. Rabon da yaga kalar yellow harya manta, sai yau da ya ganta a riga da takalman da suke
kafar Madina. Ji yayi kalar har shigar mishi idanuwa takeyi, gilashin da yake idonta ya kai
kuncinta saboda girman shi. Daga inda yake yana hango maikon da fuskar Madina takeyi ga
kurajen da suke fuskarta da ake kira da pimples, ita din gabaki dayanta kamar an cirota daga
wani shirin fim din kasar ketare aka direta a inda take yanzun.

Murmushine ya bayyana akan fuskar shi da yake jin girman shi na kara fadada da duk dakika,
rabon da wani abu ya saka shi nishadi irin yanda ganin Madina ya samar mishi harya manta, ko
matan da yake bi da ya ture su daga jikin shi yake jin wani duhu ya rufe shi ruf, nishadin daya
samu ya dishe kamar anyi ruwa an dauke. Dariya ce mai sauti ta kubce mishi da Madina ta
kalle shi tana yin murmushin ta daya bayyana duka hakoranta, sannan ta dan daga hannunta
cikin alamar gaisuwa tana son tuna in da ta san shi, kafin cikin mamaki ta ja gilashinta kamar
zata cire shi tana sake gyara mishi zama

"Hamma Salim... Hamma Salim ne ko?"

Ta karasa maganar da alamar tambaya tana kallon Daada da ta jinjina mata kai, itama
murmushin takeyi. In dai akan zabin suttura ne na Madina ta hakura. Ba don ita ta wanketa tun
jariranta ka ba, haduwa sukayi a hanya zatayi zaton ko mata-maza ce, sai jinsin namijin yayi
rinjaye a kanta, ba kwalliya takeyi ba, mai ma kafafuwan ta kawai take shafawa da Daada zata
rantse ko tambayar Madina akayi abinda tafi so a jikinta to kafafuwan zata zaba, fuska kuwa in
ba muku-mukun sanyi ya shigo ba da sauran jikinta bata damu da shafa musu mai ba,takance
fuskarta da kanta take maiko ko bata shafa mai ba.

Yanda bata kaunar hada hanya da duk wani abu daya danganci kyale-kyalen mata yana ba
Daada tsoro. Kafafuwan dai sune matsalarta, kullum cikin safa suke, takan ce

"Daada bakya jin iska na shigar miki kafa?"

Ko

"Daada haka zaki fita baki saka safa ba? Kar wani ya taka miki kafa"

Haihuwa ta fara bambanta Madina da sauran mata, yanzun kuma kaf dabi'unta. Bata son
kazanta, kamshine abu daya da tafi so a rayuwarta, ko dakinta ka shiga wani kamshi mai sanyi
ne zai fara dukan hancin ka. Sai dai tana cikin mutanen da basu damu da su mayar da duk wani
abu da zasu dauko a mazaunin shi ba, kayane akan gadon ta a cike, Daada tayi fadan harta
gaji. Banda litattafan ta, babu wani abu da yake a kammale cikin dakin, ga wajen ajiye
takalmanta, Madina wani kwali ta samu tana zuba su a ciki, kayan wanki ma kwalin ne ta samu,
har kwando Daada ta siyo mata, a store ta tsinto ko sati daya ba'ayi ba tsakani

"Kwandon ne kika watsar Madina? Asarar kudi nayi kenan?"

Ta tambaya

"Wallahi duk ya cika mun dakine fa Daada, ba watsarwa nayi ba, ajiyewa nayi idan na sake
shirya dakin sai in masa waje"

Kyaleta kawai Daada tayi, tasan babu wajen da zatayi mishi, duk shirgin da yake dakin ta,
kwandon ne bata so a ciki, tafi gane ta zuba su cikin kwali, irin Madina kam, Daada bata jin ko
an tona a fadin Kano zasu kai su biyu. Da wahala ma idan ba ita kadai bace ba, kullum cikin
neman wani abu nata da bata san in da ta ajiye ba take. Safa kuwa ko makaranta zataje da
wahala kaga iri daya a kafarta, hankalinta a kwance zata hada bakar safa da ja taci gaba da
hidimarta, idan anyi magana zata ce

"Banga yan uwan bafa, kuma a cikin wata jaka na saka"

Tunda dai taji kafarta a rufe shikenan, shisa duka fata da addu'ar ta akan Madina take zagaye
da Nawfal. Burin ta mai girma ne, zata kirga lokuttan da ta taba ganin fara'a a fuskar Salim,
amman yau ba murmushi bane kawai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login