Showing 9001 words to 12000 words out of 79955 words

Chapter 4 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

ya koya mishi yinta a ko
ina zai shiga
"Daddy baka yi mun sallama ba ka shigo"

Ya kan fadi har saida ya saba da yin sallamar da a baya bata dame shi ba, kai tsaye yakan tura
kofa ya shiga waje. Yanzun kam a kasuwa ko shagon wasu zai shiga da yake a bude sai yayi
sallama, yana ganin yanda hakan ke siya mishi kima a idanuwan mutane da yawa. Ba kowa a
falon sai Salim da ya kara shigewa cikin kujera kamar yana son hadewa da ita, tv nata aiki
amman babu sauti hakanne ma yasa Julde jin sallamar shi da Salim ya amsa can kasan
makoshi. Idan wani da baisan yaron ba yagani zai dauki hakan a matsayin rashin girmamawa.
Kuma a wajen Salim ba haka bane ba, yawancin maganar shi duk daga kasan makoshi take fita
da yanayin kamar an mishi dole dauke a fuskar shi.

"Daddy..."

Nawfal daya fito daga dakin baccin shi jin sallamar Daddy ya kira yana dorawa da

"Ina kwana"

Murmushi Julde yayi

"Lafiya kalau, kun tashi lafiya ko?"

Kai Nawfal ya jinjina

"Ina Khalid? Ku shirya muje gidan Daada, amman ba kwana zakuyi ba"

Dakuna fuska Nawfal yayi

"Da ma ina so inje fa Daddy, munyi maganar zuwan da Adee"

Kai Julde yake girgizawa

"Kwana daya to, dan Allah, gobe idan ka dawo kasuwa saika biyo ka dauke mu"

Numfashi Julde ya sauke yana dai-dai da lokacin da Salim ya fitar da wani sauti dake nuna
alamar hirar su ta takura shi yana kara shigewa cikin kujera. Murmushi kawai Julde yayi

"Ku shirya to"

Sai da Nawfal ya jinjina mishi kai tukunna ya juya yana fita hadi da ja musu kofar. Nawfal kallon
Salim yayi, baisan lokacin daya yanke hukunci dawowa bangaren da kwana da yini ba. Shima
tunda yazo hutun nan yagan shi, kafin kaji hirar Salim zaka dade, zai iya tashi da safe baice wa
kowa komai ba, ko hanya ta hadaku wucewa zakaga yayi kokarin ganin ya kauce karma iskar
da kuka kwaso ta hadu da ta juna, magana ma idan yanayi kamar bakin shi cike yake da harshe
saboda yanda take fitowa.

Nawfal zai iya cewa duk da Salim na cikin mutane shi kadai yake rayuwar shi, ko kasa shi cikin
harkar ka da wahalar gaske ya shiga. Duk wani abu da zaisa ayi rikici Nawfal na guje mishi,
shisa tunda ya dawo yaga Salim a bangaren da yake kira nashi ya daina zaman falo sam, akwai
tv a dakin shi idan kallo yake son yi, shima zai saka sautin dai-dai kunnen shine kafin Salim
yazo ya kwankwasa mishi yana fadin

"Ka rage volume din TV dinka Bajjo yana shigar mun kwakwalwa"

Duk wani surutu ma shigar ma Salim kwakwalwa yake kamar kunnen shi yafi na kowa ji

"Anya Hamma Salim ba vampire bane ba?"

Khalid ya taba tambaya bayan ya baro dakin shi a bangaren Nanna ya same su a falon da
tazarar shi take wajen taku goma harma da wani dan sirqakon lungu a tsakani yana watsa
musu wani irin kallo

"Me yasa ba zakuyi magana irin ta mutane ba? Ta ya mutum zaiyi bacci kun cika gida da ihu?"

Hada idanuwa kawai sukayi shi da Khalid suka mike suna barin bangaren gabaki daya. A cikin
su babu wanda zaice ga rana daya da Salim ya taba lafiyar jikin su, amman akwai marin da yayi
wa Adee kan tana wanke-wanke tana kida da cokula a cewar shi. Amman dukkan su suna
shakkar Salim din. Nawfal ya juya zai koma inda ya shigo Khalid ya bankado kofar yana fadin
"Wai kasan wa nagani ku..."

Maganar ta koma mishi saboda idanuwan shi da suka sauka cikin na Salim da ya dage girar shi
duka biyun, ko dan girar Salim kusan kullum a sama take, kamar baya sauke ta, hannuwa
Khalid ya daga cikin ban hakuri yana motsa labban shi batare da yayi maganar da sauti ba yace

"Yi hakuri"

Yana takawa a hankali ya karasa inda Nawfal yake ya tura kafadar shi suna nufar dakin baccin
Nawfal din da kamar jira yake Khalid ya tura kofar dariya ta kubuce mishi

"Ban san vampire na zaune a dakin ba ai"

Khalid ya fadi da alamar dariya a muryar shi, har mamakin ji irin na Salim sukeyi

"Daddy yace mu shirya zamu je gidan Daada"

Nawfal ya fadi har lokacin da alamar dariya a muryar shi

"Ni ai nayi wanka..."

Kai Nawfal ya jinjina

"Nima nayi wanka, ban dai ci komai bane ba... Zan karya a gidan Daada kawai"

Da gabaki dayan su suke karyawa a bangaren Nanna din, yanzun tunda kowa ya fara girma sai
suke zaben lokacin yin karin idan ba ranakun makaranta da Julde ba zai bar su fita basu saka
wani abu a cikin su ba ko yaya ne kuwa. Nawfal yana da kayan Tea din shi, akwatin da Adee ta
bashi nata harda katon gwangwanin madara da bata fasa ba sai na Milo karami, da kifin wajen
gwangwani ashirin. To kuma ma ya ga Salim ya sake kwaso wasu kayan tea din ya ajiye a
kitchen din bangaren nasu, da kofuna da yawa ma da kananun kayan amfani, ya ga har gas din
kitchen din an hada.

"To mu jira Daddy ya fito sai mu wuce..."

Cewar Khalid yana dorawa da

"Nasan da Adee zamu je, Lukman dai ba zai bar Nannar shi yaje wani waje ba"

Murmushi Nawfal yayi

"Auta kam babu inda za shi"

Suna nan zaune suna hira, ta window din dakin Nawfal da yake ta waje yake suka hango
Daddy, kusan a tare suka mike suna fita

"'Hamma sai mun dawo"

Khalid ya fadi, hannu Salim din ya daga yana musu alamar su fita. Dariya sukayi a tare suna

ficewa, daman dan neman tsokana yasa Khalid yima Salim din magana. Har wajen motar
Daddy suka karasa kusan a tare da Adee da take sanye da riga da wandon da zaka iya gani
saboda hijabinta iya gwiwa ya tsaya, ta rataya jaka a gefe sai robar take away a hannunta.

"Dare yayi sanda na gama jiya..."

Ta furta tana mikama Nawfal robar da ya karba yana jinta da sanyi alamar a fridge ta kwana,
dubawa yayi ta kasan robar yana ganin farfesun kifi ne ko miyar kifi, ba zai iya ganewa ba, ya
dai san taliya aka dafa jiya da dare da miyar kifin da yasan ba zai iya ci ba dan yaga Khalid da
ita, sanda ya shiga bangaren ma dan su gaisa da Daddy ne.
"Meye kika bashi ni baki bani ba"

Cewar Khalid da ko inda yake Adee bata kalla ba. Yanzun da suka kara hankali Nawfal yasan
Adee dare take bi idan Nanna tayi bacci ta dafa mishi abu irin haka. Hannun shi na dama da
baya rike da robar da ta bashi ya dora akan kirjin shi inda yafi tunani zuciyar shi take dan nan
yaji ya dauki dumi sannan ya daga hannun yana nuna Adee da tayi murmushi, yasan ta
fahimta, bashi da kalamai in dai akan kulawarta ne, amman tana da waje mai girma a zuciyar
shi, Allah yake roko daya bashi aron rayuwa mai tsayi a tare da Adee dan ya kwatanta biyan ta
duka kirkin da takeyi mishi.

Su baya suka shiga shi da Khalid ita tana shiga  gidan gaba. Har lokacin da murmushi a fuskar
ta

Bata san duka labarin Nawfal ba
Amman tana hasaso rayuwar ta babu Daddy da Nanna
Tana hango dararen kadaicin da take tunanin yana fama da shi
Ita din ko kusa da matsayi na uwa ba zata hango ba balle ta taka
Amman in dai tana numfashi zata sama ma Nawfal duk wani sauki da yake a karkashin ikon ta
In dai har yaya mace na zama mahaifiyar da mutane ke fada zata zamewa Nawfal.

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*RAI DA KADDARA 1*

04

Idan yaji ana cewa lokaci na gudu ada sai yayi ta mamaki, saboda shi sam baya ganin gudun
lokaci. Musamman idan yana gida, yini daya sai ya zame mishi kamar yini biyu. Amman wannan
karin zai saka baki idan ana maganar gudu na lokaci, saboda da gaske kamar idanuwan shi ya
rufe a aji hudu ya bude su ya ganshi yana zana jarabawar gama sakandire ta aji shidda da ake
kira da WAEC. Randa suka zana ta karshe sai yake jin abin kamar a mafarki, har Julde yaje ya
dauko su bai dana jin shi kamar a mafarki yake yawo ba.

Sai dai ya koma kirga kwanakin da suka rage mishi a cikin gidan. Adee ta samu gurbin karatu a
jami'ar Wudil, nisa ta sake yi musu.

"Ga BUK, me yasa sai Wudil? Quantity Survey din ne basu da shi a BUK?"

Ya tambayeta, bai taba zuwa Wudil ba, amman yasan kauye ce, kuma yaji wani a ajin su yana
magana cewa babu mata da yawa a makarantar, duk wani abu da zata takura baya son shi
sam. Murmushi kawai tayi

"Ka ce mun BUK zaka je kaima Bajjo, in har can din zaka sai in hakura da Wudil..."

Shirun da yayi murmushin Adee kawai hakan ya fadada

"Idan kana gida zan dinga kokarin dawowa weekend In shaa Allah"

Bai dai sake cewa komai ba, burin shi mai girma ne, bai kai da furtawa ba. Amman nisan da
zaiyi wa gida da sunan karatu ba zai tsaya makarantun da suka sani ba. Ya fi kowa jin rashin
Adee a cikin gidan, dan ma yanzun Julde kudin kashewa yake basu kusan kullum, ba zaici yana
da matsalar abinci ba. Mai dadine kamar wanda Adee zata tsaya ta dafa mishi sai dai yaje
gidan Daada yake samu. Islamiyya da ya koma yanzun bashi da lokaci mai yawa na zuwa
gidan. Yanzun ma daya taso masallaci ya wuce yayi zaman shi yana nazarin darussan da akayi
na ranar har sai da yayi sallar Magriba da Isha'i tukunna ya dawo gidan.

"Ina kaje tun dazun?"

Khalid da yake kwance cikin kujera ya tambaya

"In da ka aikeni"

Ya amsa yana wucewa, dakin su ya nufa ya ajiye jakar makarantar shi, ruwa ya watsa ya sake
kaya sannan ya sake fitowa yana nufa kitchen, fridge ya bude yana ganin robobin ice cream din
shi har biyu inda ya bar su tun daren jiya. Guda daya ya fiddo yana mayar da fridge din ya rufe
ya karasa ya dauki cokulla har biyu ya dauraye su, yana daukar wani plate shima ya dauraye ya
taka zuwa falon, teburin da ke tsakiyar dakin yaja zuwa kusa da kujerar da zai zauna ya ajiye
plate din ya dora cokullan a sama yana ajiye robar ice cream din shi a gefe.

Sake komawa daki yayi ya dauko kifin gwangwani guda biyu tukunna ya samu waje ya zauna.
Gabaki daya Khalid hankalin shi ya mayar kan Nawfal da yake bude kifin harya juye shi cikin
plate, gani yayi ya bude robar ice cream din ya saka cokali a ciki, tashi zaune Khalid yayi

"Jikin ka na shan wahala a hannun ka Bajjo, kifi da ice cream?"

In dai akan zabin abinci ne ya saba da surutun Khalid din, bude baki Khalid yayi zai sake
magana shigowar Salim ta saka shi ya mayar ya rufe

"Na dauka ba'a hada kifi da madara"

Salim yayi maganar cikin sigar da bata bukatar amsa kamar yanda ya saba, kana iya amsa shi
yayi maka kallon "Da kaina nake magana, me yasa kake amsawa?". Kowa a gidan ya koyi
zama da Salim, duk da haka kafadu Nawfal ya daga

"Har yanzun ban ci da yawan da zai mun illa bane ina jin"

Dan ba zaice ga ranar da yake hada shayi kuma da madara yaci da kifi ba. Kai Salim ya girgiza
yana wucewa abin shi

"Da gaske abin nan dadi yake maka?"

Hararar Khalid yayi yana cigaba da cin kifin shi hankali kwance. Yana gama cinye kifin ya mike
ya dauke plate din ya kai kitchen, yana dawowa ya hangi Khalid da robar ice cream din shi ya
dibo a cokali yana shirin kaiwa baki, da gudu ya karasa amman har Khalid ya kai cokalin cikin
bakin shi
"Ewww...Hamma...kace mun shine cokalin farko..."

Wuyan shi Khalid ya rike da alamu ke nuna dakyar ice cream din ya wuce ta cikin shi, fuskar shi
a hade take gabaki dayanta, harya ciro cokalin kokarin tattara sauran dandanon ice cream din
daya rage a bakin shi yakeyi amman ya kasa, hannu kawai ya iya dagawa Nawfal da ya dakuna
fuska yana jujjuya robar hannun shi kamar zata sanar mishi idan Khalid din ya sha abinda yake
cikinta fiye da sau daya. Kurkuro bakin shi Khalid yayi amman bai daina jin dandanon ba

"Nawfal meye a robar nan?"

Asalin sunan shi da Khalid ya sa Nawfal din amsawa da

"Ice cream"

Yana dorawa da

"Sau daya ka sha?"

Babu abinda ya tsana irin kurbi in kurba da abu a cikin kofi, ko kuma yana shan ice cream, ko
yana cin wani abu kazo ka dauki cokalin ka ci da shi ka mayar a ciki, saiya ga kamar da sauran
yawu a jiki ka mayar mishi. Idan Khalid na son ya bar mishi abu haka yake masa wannan rashin
kirkin
"Wanne irin ice cream ne wannan?"

Numfashi Nawfal ya sauke

"Chocolate mint... Me ya faru?"

Kai Khalid yake girgizawa, komai na Nawfal ya fita daban, kamar kullum dalilin da zai sake
banbanta da mutane yake nema. Kamar McLean yayi kankara haka ice cream din yake

"Sau daya na sha, na farko kuma na karshe da yardar Allah"

Khalid yace muryar shi na fitowa a gajiye. Dariya Nawfal yayi

"Me ya samu ice cream din? Me ya faru? Ba dai zaka ce babu dadi ba"

Wani irin kallo Khalid yake mishi

"Akwai dadi, a sha lafiya"

Da murmushi a fuskar Nawfal ya nufi kitchen dan ya dauko wani cokalin, daga can dakin su ya
wuce ba sai Salim ya dawo falon ya kore su ba. Ko da Salim ba zai fito ba lokacin baccin shi
yayi, kome zaiyi da wuri yake yi ya gama, karfe tara idanuwan shi sun fara nauyi, har mamakin
Khalid da zai iya kai karfe daya na dare zaune yana kallo yakeyi, kuma washegari ya tashi su
tafi sallar asuba kamar lafiyar shi kalau. Shi kanshi zaiyi kamar an dora dutse, bacci na da
muhimmanci a wajen Nawfal.

**

"Daada..."

Ya kira muryar shi can kasan makoshi, hannu tasa tana share hawayen da suka kasa daina
zuba daga idanuwanta, ya dauka da Julde zaifi samun matsala, sai dai soyayyar da ke tsakanin
su da take tasiri akan Julde ko yaushe ita tayi nasara. Nawfal na ganin yanda tafiyar shi wani
gari da sunan karatu ne karshen abinda Julden yake so balle kuma ace wata kasa.
"Cikin kudina, kai da Daada kunce ina da kudi, in dai zasu isa..."

Julde bai barshi ya karasa ba, da wani nauyi a muryar shi yace

"Me yasa kake tunanin kudi ne matsala ta da tafiyar ka? Bajjo ina da kudin da zan fitar da ku
dukan ku karatu kasar waje, ba kudin bane matsalata, nisan ka, nisan da zakayi ne damuwata"

To ga damuwa fiye da wadda ya gani a tattare da Julde nan shimfide kan fuskar Daada, kukan
da takeyi gabaki daya ya kashe mishi jiki, zuciyar shi daya ke tunanin ba mai raunanata kan
tafiyar ce yake ji tana mishi rawa

"Daada..."

Ya sake kira kamar hakan zai isar da sakon da baisan ta inda zai fara fada mata shi ba. Yana
bukatar tafiyar, jin shi yake kamar yana cikin wata yar karamar kwalba, watakila tafiyar ta fito da
shi daga cikinta, duniyar shi yar karama ce, haka ma mutanen da suke cikinta. Ba fadadata
yake son yi ba, asalima yana jin wajen mutum daya ya rage mishi, daya cike shikenan. Yana dai
son tafiya saboda da dalilai da ba zai iya rabawa da kowa ba.

"Daada makaranta ce kawai fa, zan dawo... Ki daina yi kamar na tafi kenan"

Kai ta jinjina, zuciyarta na wani irin ciwo, tafiya ta rabata da mutane da yawa, tafiya tayi mata
sanadin abubuwa da ba zasu lissafu ba. Idan tace ko sunan tafiya bata son ji wasu zasuyi
mamaki, amman dalilanta masu karfine. Shi da Madina ne mutane biyu rak da suka rage mata
da take jin in dai tana numfashi ba zata bar wani abu ya rabata da su ba. Ko da yace
makarantar kwana zai tafi hankalinta ya tashi, sai da Julde ya fada mata makarantar a cikin
garin Kano ne, duk da haka sai da taji duk satin duniya Julden na zuwa ya dubasu.

Amman baccin kirki batayi duk asabar din duniya sai Julde ya biyo ya sanar mata da cewa
Nawfal din na lafiya take samu nutsuwa. Yanzun kuma yazo mata da zancen tafiya wata kasar
amurka, yana tuna mata abubuwan da ba mantawa tayi ba, amman ta samu waje ta adana su
idan ba ranaku irin yau ba basa kwacema adaninta sai ta basu damar hakan.
"Dan Allah Daada... Kina daga mun hankali"

Hannu tasa tana sake dauke kwallar da ta taru cikin idanuwan ta

"Naji tafiya da sunan karatu Bajjo, tafiyar da batayi mun dadi ba, naji tafiya da dalili da tafiya
babu dalili, duka basuyi mun dadi ba..."

Kai yake girgizawa tunda ta fara magana, ga wani abu daya taso daga zuciyar shi yana tokare
mishi makoshi

"Karki hada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login