Showing 24001 words to 27000 words out of 79955 words

Chapter 9 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

gefe yana fita. Kaf unguwar su Ahmad harma
kasuwar su daya shiga babu mutum daya bayar da shaidar banza akan Ahmad, asalima tarin
nagarta da alkhairin shi suke fadi. Idan Salim ya kalli Fadila baya ganin shekarunta, yar kanwar
shi yake gani, yar mitsitsiyar yarinyar da zaiyi komai dan kareta daga duk wata hatsaniya ta
duniya. Dan baya hango aure a cikin jerin abubuwan da yake da niyyar yi a rayuwar shi baya
nufin baya son yaga wani yayi.

Musamman kanwar shi da duk idan yaga wani da namiji a kusa da ita sai zuciyar shi tayi tsalle
zuwa wuyan shi. Tsallen da bai taba hana shi bin kannen wasu ba, zuwa yanzun ya daina jin
girman laifukan shi, baya hango kowa sai nishadin da zai samu na dan kankanin lokaci. Ya dai ji
dadi har kasan ran shi da yaga zata nutsu waje daya, ya sake jin dadin samun Ahmad da
nagartar da bashi da ita. Har hamdala ya tsinci kan shi dayi da jarabtar su ba zata taba Adee ba
don ita dinma mutuniyar kirki ce. Ko yanda suka gaisa da Ahmad yasan a tsorace yake

"Idan nace in ka ci amanarta Allah zai kamaka kamar ina fada maka abinda ka sani ne. Ga
kanwata na Ahmad, dani zaka fara haduwa idan hawaye ya zuba daga idanuwanta saboda kai"

Kai Ahmad ya jinjina mishi yana hadiye wani abu da yayi mishi tsaye a wuya. Murmushin da
Salim din yayi mishi ma kara tsorata shi yayi, idan yana tsaye da Adee sai ya ganshi babba,
amman yanzun a gaban Salim saiya raina girman shi.

"Allah ya tabbatar muku da alkhairi"

Salim ya sake fadi yana mika ma Ahmad din hannu cikin alamar sallama sannan ya nufi
bangaren su. Itama Adee data fito bata wani dade ba saboda tasan Julde na gab da dawowa.
Ai kam ko mintina goma batayi ba tsakani ya dawo

"Daddy..."

Ta furta cikin sigar sannu da zuwa tana mikewa dan ta karbi ledojin da suke hannun shi

"Adee, sannu da kokari"

Cewar Julde yana mika mata ledojin dai-dai shigowar Khalid

"Daddy sannu da zuwa, yanzun naji motar ka"

Hararar shi Adee tayi

"Shisa ka shigo kenan...to sai ka juya ai tunda ka mishi sannu, bai kawo tsarabar komai ba"

Dariya Khalid yayi yana shiga cikin dakin sosai hadi da kaima daya daga cikin ledojin da tayi
saurin janyewa wawura

"Daddy..."

Adee ta kira

"A'a kunga yanzun na dawo ko? Kaina ba zaiyi ciwo ba tunda kamar kaji haka kuke"

Julde yayi maganar yana raba su ya wuce, a gajiye yake jin shi sosai. Dakin su ya wuce yana
samun Saratu a kwance, tun daren jiya da tace tana son magana da shi yasa kai ya fice bai
saurareta ba take shan kamshi har yau da safe ma da zai fita. Bata gaban shine, in dai zai
dawo ya samu daya daga cikin yaran shi to hankalin shi ya gama kwanciya, wucewa yayi ya
watsa ruwa ya fito yana neman wani yadi marar nauyi ya saka a jikin shi

"Tun jiya nace maka ina so zamuyi magana kaqi saurarena"

Alamar ciwon kai da yake ji ya sashi zama gefen gadon wajen kafafuwanta da ta tashi zaune ta
mike akan gadon

"Ina jinki"

Ya furta

"Akan maganar auren Adee ne, idan suka bukaci ganin dangin mahaifinta fa?"

Wani irin tsalle zuciyar shi tayi har saida kirjin shi ya amsa. Badan ya shafe wani abu dangi
daga babin rayuwar shi ba, a'a, bukatar su a cikar neman aure ne ya manta, wani abu da yake
neman taso mishi ya danne

"Zan san yanda zanyi"

Ya furta yana mikewa, bin shi da kallo saratu tayi

"Julde kana ganin komai zai tafi dai-dai? Kana ganin laifukanka ba zasu taba yaran mu ba?"

Iskar da ya shaka dakyar ta wuce mishi yana fito da ita a wahalce, baisan me yasa take son
hautsina mishi duniyar daya dauki lokaci yana dai-daitawa ba, amman daya kalleta babu komai
akan fuskarta sai tarin damuwa, damuwar da tunda zancen auren Adee ya taso ta danne mata
zuciya. Akwai sirrikan su da auren nan zai iya bankadowa, abinda tafi tsoron fitowar shi fiye da
laifukan Julde da zai iya taba musu yara.

"Nace miki zan san yanda zanyi"

Ya maimaita yanajin yanda muryar shi take rawa. Kafin tace wani abu ya fice daga dakin, duk
surutan da su Adee sukeyi iya kunnuwan shi yake tsayawa, baya kaiwa kwakwalar shi balle ya
fahimta, abincin ci kawai yake badan yana gane dandanon shi ba, har Adee saida ta taba shi

"Lafiya dai ko Daddy? Fuskarka kamar babu jini"

Dan murmushin karfin hali yayi mata

"Kaina ke ciwo ga shi akwai gajiya a tare da ni"

Sannu sukayi mishi dukkan su, Adee ta tashi ta dauko paracetamol ta balli guda biyu ta bashi,
karba yayi ya sha badan zai mishi maganin matsalar shi da ta girmi duk wata kwayar magani ta
bature ba, sai dan damuwar da yake gani a fuskokin yaran, har yayi musu sai da safe suna bin
shi da sannu. Daki ya koma, Saratu na inda ya barta, zagayawa yayi yahau gadon ya kwanta
yana juya mata baya. Har alamun zazzabi saida yaji ya rufe shi. Yau fiye da kowanne lokaci
yake jin kewar Mero, yana da yakinin ba zata rasa kalaman da zata fada mishi da zai kwantar
mishi da hankali ba, ko jinta a kusa dashi da kamshin nan nata ya isa yasa hankalin shi ya
kwanta.

Lumshe idanuwan shi yayi ko da hoton ta ne ya gani a zuciyar shi, amman sai hoton yazo mishi
tare da kalamanta

"Yanda kayi mun rami a zuciya, in Allah ya yarda duk lokacin da kake tunanin hankalin ka ya
kwanta sai Allah ya aiko abinda zai birkita maka komai Julde..."

Babu shiri ya bude idanuwan shi. Zuciyar shi na ciwon daya dauka lokaci ya saba masa da
radadin shi. Mero ce mutum ta biyu da take da muhimmanci a rayuwar shi da ta jefe shi da
kalamai masu zafi irin haka, rashin sa'ar shi mai girma ne, batun yanzun ya san haka ba, shisa
tunda ya samu su Salim kacokan duk wata addu'a da zaiyi, duk ma wani aikin kirki da zaiyi da

niyyar Allah kar yasa rashin sa'ar da yazo duniya da shi karya taba su. Tambayar Saratu ta
tokare mishi kahon zuciya.

Anya laifukan shi ba zasu taba yaran su ba?

Tambaya ce mai nauyin da shi kadai yasan shi, laifuka tace, laifukan shi idan zaiyi waiwaye
masu yawan gaske ne, ko daya daga ciki za'a dauka ya isa ya tsaida duk wani jin dadi da yake
gani a fuskokin yaran shi. Har Saratu ta mike ta kashe musu fitilar dakin bai ko motsa ba, wani
irin tsoro ne yake ratsa dukkan sassan jikin shi, kome zai same shi in dai zai tsallake su Adee
mai sauki ne. Bacci a daren ranar barawo ne ya sace shi cike da mafarkin rayuwar da zaiyi
komai dan ganin ya shafe babinta.

Sai dai wasu shafukan na kaddara suna da zumunci, ko baka waiwaye su ba sai sun sake kawo
maka ziyara.
©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*RAI DA KADDARA 1*

08

A cikin kunnen shi aka bude kofar dakin duk da baccin da yake mai nauyi ne, kuma da alamu a
hankali aka so budewa. Tunda satin bikin Adee ya kama baya samun wadataccen bacci, baisan
me akeyi a harabar gidan ba, amman yana jin kai kawon mutanen da ba zaice duk daga ina
Nannar su ta samo su ba. In har suna da wasu dangi da suka hada jini dasu a garin Kano daga
Daada sai Madina ya sani. Ko da wasa bai taba jin daga Daddy har Nanna sunyi zancen wani
dangin su bayan Daada ba. Bai san ko su Khalid ba, amman shi bai taba tambaya ba, ya yarda
cewar idan akwai dangin daya kamata su sani za'a nuna musu su.

A ranshi dai yaga kamar wata uku da aka saka bikin Adee yayi kusa, amman Julde na da halin
da zaiyi mata komai, watakila shisa basu jashi da nisa ba. Watannin ma sauri sukayi mishi
matuka. Yau dai ya daya rage saura kwanaki biyu daurin aure, ya hada yar jakar shi, zai kama
hotel ne har sai an gama hidimar bikin gabaki daya kafin hayaniya ta haukata shi. Karar
haduwar takalmi da tayals din dakin kamar sukuwar doki ta sa shi jan wani dogon tsaki

"Ubanka kakeyi da baka wuce ba har yanzun Khalid?"

Salim ya fadi yana jin kanshi kamar ba zai bude ba, kamar ma jan kafa Khalid din ya sakeyi

saboda ya mayar dashi sa'an shi, bude idanuwan shi yayi yana sauke su cikin na Nawfal daya
kwashe da dariya

"Bajjo"

Salim ya fadi cike da kashedin da bai boye murnar shi ba. Ya dauka Khalid ne, ko da wasa baiyi
tsammanin zuwan Nawfal din ba

"Normal mutane ko basu rugo sun tarbeni ba zasu tashi zaune daga kwanciyar su suyi mun
sannu da zuwa"

Cewar Nawfal yana murmushi

"Da dariya a muryar su"

Juyawa Salim yayi, yafi son kwanciya akan kujera fiye da yanda yake son kwanciya akan gado.
Bai kuma san dalili ba, amman in har yana gida da rana kuma ko da daddare ma zaka gan shi
kwance a falo kan kujera

"Hamma..."

Nawfal ya kira da karfi yana saka Salim jin kamar ya saka lasifika ne

"Kayi na bakunta Bajjo...karka kara"

Dariya Nawfal din yayi, tunda ya hau jirgi yake jin shi sama-sama, daya sauka airport ya samu
taxi zuwa gida zuciyar shi dokawa takeyi ba kadan ba. Kan shi tsaye bangaren su ya wuce,
ranar da aka sa ranar Adee ta kira shi, su tsakar dare ne ma

"Bacci kake ko? Ban tsaya kirga awanni ba yau, sai da naji muryarka na tuna tsakar dare ne"

Tashi zaune yayi, banda Adee a gabaki daya rayuwar shi babu wanda yake kiran shi a lokacin
da baya daga waya ya dauka, ko da Daddy ne, kusan zaice saboda Adee ne baya saka wayar
shi a silent in ba yana cikin aji ba. Shima daya fito yaga kiranta yake bin bayan shi

"Kace zaka zo bikina Bajjo, idan ba zan takura ka da yawa ba"

Shine rokon da tayi mishi

"Zan zo Adee, In shaa Allah zan zo"

Duk da ba saboda bikinta kawai yazo ba, bikin natane ya karfafa dayan dalilin na shi. Filon
kujera da yaji an jefe shi da shi yasa shi rike bayan kan shi

"Kofato ne a kafarka wai?"

Dariya Nawfal yayi, da gaske ya dawo gida. Sai ma daya tura kofar dakin su yana jin kamshin
turarukan Khalid sun daki hancin shi, kafin ya hade tunanin shi waje daya yaji Salim ya watsa
mishi zagi. Da gangan da yazo tura kofar ya buga ta, mukulli yabi da shi kar Salim din ya same
shi cikin dakin, jakar shi ya fara saukewa yana jan karamin akwatin shi ya ajiye gefe daya. Sai
da ya shiga wanka ya fito sannan ya bude dakin, akwatin shi ya janyo ya dauki wata farar riga
da wani wando fari iya gwiwa ya saka. Shima baccin ne a idon shi saboda jikin shi ya saba da
bambanci lokaci. Kwanciya yayi abin shi.

Cikin bacci yaji kamar ana jijjiga shi, inda yake jin hannun ya kama ya ture yana juya kwanciya

"Bajjo... Bajjo... Dalla ka tashi"

Khalid ya fadi muryar shi cike da farin ciki yana sake jijjiga Nawfal din daya daga idanuwan shi
dakyar

"Ka barni inyi bacci Hamma..."

Ya furta yana shirin gyara kwanciya Khalid din yana kai hannu ya janye filon da kan Nawfal yake
kai

"Tashi zakayi muyi labari"

Wani irin numfashi Nawfal ya sauke

"Kayi missing dina na sani, amman ina nan, ba yau zan tafi ba ko wani abu, ka kyaleni inyi bacci
na"

Baki Khalid ya bude zai magana Nawfal ya tashi zaune da sauri yana katse shi da

"Kana da kati a wayar ka? Ara mun..."

Fuskar Khalid dauke da alamun mamaki ya zaro wayar shi kirar Nokia yana mika ma Nawfal din
da ya karba yana mika hannu ya dauko tashi wayar, kallon shi Khalid yakeyi yana danne-danne
da alamar sako yake turawa. Yana gamawa ya mika ma Khalid wayar

"Nagode"

Yayi maganar hamma na kwace mishi saboda baccin da yake idon shi

"Ka kwanta, zan fita ne nima, Nanna ta aikeni"

Da wani yanayi a fuskar Nawfal yace

"Shine ka tashe ni?"

Dariya kawai Khalid yayi ya mike yana ficewa daga dakin. Kasa komawa baccin yayi, kamar
cikin shi jira kawai yakeyi ya farka ya cigaba da tunasar da shi yunwar da yake dawainiya da ita
da ta saka shi mikewa zaune babu shiri yana saukowa daga kan gadon gabaki daya. Rigar jikin
shi ya kalla, duk ta yamutse saboda baccin da yayi da ita a jikin shi, cire ta yake kokarin yi yaji
ana kwankwasa dakin

"Come in"

Ya furta yana karasa cire rigar dai-dai lokacin da Salim ya turo kofar yana runtse idon shi

"Ewwwww, Bajjo"

Dariya Nawfal yayi dan yanda Salim din yayi wani zaiyi zaton babu kayane a jikin shi gabaki
daya

"Ka sa kaya, idanuwa na"

Cewar Salim da har lokacin idanuwan nashi suke a runtse, rigar daya cire ya mayar a jikin shi
yana dariya, a hankali Salim ya dan bude idon shi daya kafin ya bude su gabaki daya yana mika
ma Nawfal ledar da sai lokacin ya kula da tana hannun shi, karba yayi cike da mamaki

"Kifi da dankali na siyo... Bakomai kake ci ba, akwai kayan tea a kitchen"

Kai kawai Nawfal ya iya jinjinawa saboda wani abu da yaji ya mishi tsaye a zuciya

"Idan baka ci...."

Da sauri Nawfal yake girgiza mishi kai

"Zanci, ina ci... Miyetti"

Kallon shi kawai Salim yayi, kafin kaji fulatanci a bakin shi zaka dade, Julde yana musu, Nanna
ma lokutta da dama shisa duk suke ji, amman kana iya ma Nawfal magana ya mayar maka da
hausa.

"Kar inji motsin ka"

Hannu Nawfal ya daga yana ma Salim din alamar salute hadi da jinjina kan shi. Sai da ya fice

daga dakin sannan ya samu waje nan kasa kan kafet ya zauna ya bude ledar. Harda ice cream
har roba biyu, wani irin numfashi ya sauke

"Allah ya biya maka bukatunka Hamma"

Ya furta a hankali saboda har ranshi yaji dadin ice cream din fiye ma da kifi da dankalin. Shi ya
fara sha tukunna ya ci sauran, yana cikin shan dayar robar Khalid ya shigo da sallamar da kafin
ya amsa ya mika mishi wayar shi

"An maka text"

Karba Nawfal yayi da sauri yana duba wayar yaga Khalid bai bude text din ba, sai da ya dan
sake kallon shi yaga waje ya samu ya zauna yana jan ledar da take gaban Nawfal din da kifin
da ko rabi bai ci ba, sake mayar da hankalin shi yayi kan wayar yana karanta text din, replying
yayi yana ajiye wayar da kamar haka take jira ta fara ruri, kamar ba zai daga ba, Khalid yake
kallo da yake cin kifin shi hankali a kwance, daukar wayar yayi yana daga kiran hadi da karawa
a kunnen shi, numfashin da bai san yana rike da shi ba ya sauke

"Jaan..."

Ya kira cikin wani irin sauke murya da yasa Khalid daga kai ya kalle shi fuskar shi dauke da
alamar tambaya

"Wanne zan fara amsawa yanzun? Bakomai fa, na danyi bacci ne"

Ya amsa kafin yayi jim yana sake fadin

"Um um, ina zaune, naci abinci, muna tare da Hamma Khalid"

Murmushi yayi yana mika ma Khalid din waya

"Ana son magana da kai"

Yanayin fuskar Khalid din na saka shi yin yar dariya, karbar wayar Khalid yayi ya kara a kunnen
shi hadi da yin sallama

"Kullum sai naji labarin ka"

Aka furta daga dayan bangaren bayan amsa sallamar shi, cikin wata murya mai sanyin gaske,
idanuwan Khalid na kan Nawfal yace

"Abin mamaki ganin yanda ni banji naki labarin ba"

Zunguri Nawfal ya kai mishi

"Hamma"

Ya kira a hankali, kafadu Khalid ya dan daga, yarinyar da har lokacin bai san sunanta ba tayi
dariya mai sanyin sauti kamar muryar ta

"Sunana Murjanatu. Yar asalin Nigeria, garin Adamawa, an haifeni a New York, I'm your
brother's girlfriend"

Ta karasa maganar cikin harshen turanci, yanayin yanda ta ajiye kowacce kalma na sake
tabbatar wa da Khalid din da gasken tashin turai ce, sai dai kalamanta na karshe sun saka shi
rasa abinda zai fada ko abinda ya kamata ya fada, har Nawfal ya miko hannu ya zare wayar
daga kunnen shi bai ce komai ba
"Hello..."

Nawfal yace yana dorawa da

"Ina da tambayoyi da tarin bayanai da zanyi, muyi magana anjima?"

Kai ya jinjina yana sauke wayar daga kunnen shi yana kallon Khalid

"Ban tabbatar ba shisa ban fada maka ba, da na tabbatar kuma bansan ta inda zan fara ba...
Kawai ya faru ne"

Numfashi Khalid yaja yana fitarwa a hankali, soyayya abune da yake hange da nisan gaske a
rayuwar shi, duka shekarar shi ta uku yake a jami'a, yana son tsayawa da kafafuwan shi,
tsayuwar da idan wata ta jingina da shi ba zasu fadi ba su dukan su.

"Kace wani abu dan Allah"

Nawfal ya fadi yana kallon Khalid din, Murjanatu ce abu na farko da yaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login