Showing 39001 words to 42000 words out of 79955 words

Chapter 14 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

kwacen, wani yanayi ne a
tsakanin abu biyun da bata san wacce kalma zatayi amfani da ita wajen fassara shi ba

"Madina..."

Salim ya kira a hankali yana dan daga mata Menu din da yake hannun shi bayan ta kalle shi

"Abinda duk aka baka"

Ta ce cikin sanyin murya, su Nawfal ya kalla, kowa ya fara jero abinda za'a kawo mishi

"Madina yaushe zaki zo gidana? Kinsan ina fushi daman, baki je kaini ba, na kula ai"

Murmushi Madina tayi, har ranta tayi niyyar zuwa kai Adee din tunda harda Daada, a wajen
motocin daukar amaryar taji an riko mata hannu ana janta, kafafuwan shi ta fara kallo ta gane
waye

"Hamma..."

Ta kira, bai amsata ba ya cigaba da janta har suka inda motar shi take ya bude murfin yana
sakin hannunta, yanayin fuskar shi yasa ta shiga batare da tayi musu ba, ya ja motar da bai
tsayar ba sai a kofar gidan Daada, nan sukayi zaman su a ciki suna hira, ko tace tana mishi
surutun da yake amsawa dai-dai. Har fita suka kara yi ya siyo musu tsire mai yawa da lemo.
"Zan zo, Hamma zai kawo ni. Kibari kunshin ki ya karasa gogewa, sai ki kira Daada kinga idan
nazo sai in miki sabo"

Kai Adee ta jinjina

"Kin kusa ki wanke laifin ki"

Yar dariya tayi tana kallon Nawfal

"Hamma Ango"

Hararta yayi

"Yanzun ne zaki kula ni? Bana so"

Hannuwanta ta hade waje daya cikin ban hakuri

"Ance angwaye basa fushi fa ko Hamma Khalid?"

Dariya Khalid yayi

"Ni zan shiga fadan ku? Ku shirya ku ware ni yanda kuka saba? Babu ruwana, sai dai babban
Yayaa"

Ya karasa maganar cikin sigar tsokana. Wani kallon kashedi Salim ya watsa mishi yana saka shi
gyara murya

"Idan na taso saina mare ka"

Salim ya fadi yana sa Adee kwashewa da dariya

"Me nayi ni kuma?"

Ko da ba'a fara kawo musu abincin su ba yasan ba amsa zai samu ba. Hira ce ta barke
tsakanin Nawfal, Khalid da Adee, Salim abincin shi yake ci duk da maganganun su da yake ji
har cikin kwakwalwar shi, Madina ma abincin take ci tana tsintar dankalin dai-dai. Salim na
kallonta ta gefen idanuwan shi, dan ture plate din shi yayi yana jan nata bai damu da kallon
mamakin da take mishi ba, wuka ya dauka yana yayyanka mata cinya guda biyu kanana yanda
zata iya dauka kafin ya tura mata plate din batare da yace komai ba yaci gaba da cin abincin
shi.

Lemon da yake gabanta ma shi ya bude yana zuba mata a kofi ya tura mata kusa da ita. Da ya
gama cin nashi abincin ma ita yake kallo. Lokaci zuwa lokaci takan dago su hada ido, ta saba
ciye-ciye a gaban shi, tasan dai idan ta ajiye cokalin magana zai mata tunda ba wani ci tayi ba,
ita kuma tana turawa ne badan tana gane dandanon abincin a bakinta ba, sai da taci kusan
rabin naman da yayayyanka mata tukunna ta ajiye cokalin a ciki tana dan ture plate din. Ganin
girar da Salim ya daga mata cike da alamar tambaya ya sata fadin

"Na koshi Allah, tuwo Daada tayi mana"

Baice komai ba ya mike yana karasawa inda zai biya kudin ya kuma bama Madina damar yi
musu sallama, idan yabarta zasu mayar da ita gida ya sani, bai san ko tana so ta zauna ba, ba
tambayar ta zaiyi ba. Yanda suka zo tare haka zasu koma tare, saboda hakan yake jinyi badon
yana da wani kwakkwaran dalili ba.
"Allah yasa alkhairi Hamma, Allah ya kawo zuri'a dayyi ba"

Madina ta fadi tana rasa dalilin da yasa take jin wani iri

"Zan zo anjima"

Nawfal ya amsa, kai ta jinjina mishi tana mikewa, Khalid ne ya kalle ta da fadin

"Ki bari mu tafi gabaki daya mana, ba sai mu sauke ki ba"

Kai ta girgiza mishi

"Hamma zai ce a'a"

Dakuna mata fuska Khalid yayi

"Ka kyaleta Khalid, kiyi tafiyar ki Madina, saina kira Daada..."

Numfashi ta dan sauke bata ma amsa ba ta juya

"Kai ina ruwan ka? Baka ga tare suka zo ba?"

Ruwa Nawfal ya kurba ya hadiye sannan yace

"Ni kadai naga Hamma ya yankawa Madina nama?"

Dariya Khalid yayi

"Wallahi kiris in shake da taliya... Anya Hamma?"

Kai Adee ta girgiza

"Kuna da bala'in gulma yaran nan, ina ruwan ku? Sai na fada mishi"

A tare suka kalle ta, dan kasa tayi da murya kamar tana tsoron Salim din zaiji ta

"Amman da gaske me yake faruwa ne?"

Kallon 'maganar da nakeyi kenan ai' Khalid yayi. Hirar suka dan karayi kafin su saki zancen
suna kama wani tunda sun san koma menene ba zai wuce su ba, suna zaune zai zagayo kowa
ma ya gani.

*

"Yanzun wanne mai hankali ne ya dauki yarinya yaba Bajjo?"

Saratu ta fada tana tabe baki

"Mai irin hankalin wanda ya daukeki ya bani"

Julde ya amsa ta, amsar kuma tayi mata zafi

"Ubana kenan?"

Bai ce komai ba, sakon ya isa baya bukatar jan magana kuma

"Idan wulakanci abinyi ne ka cigaba da wulakantani Julde, Allah ya baka sa'a, hirar arziki ma ba
zan taba samu inyi da kai ba saika gasa mun magana"

Shirun dai shi ya kara yi mata yana cigaba da neman kayan da yake son sakewa dan ya fita
yabar mata gidan ma gabaki daya, a gajiye ya dawo daga Abuja tunda acan ya kwana aka
daura aure da safe ya tsaya wata hidima da ta shafi kasuwan cin shi tukunna ya juyo

"Kuma sanda na aure ka aika girmi Bajjo, shekarar ka wajen ashirin da biyar"

Gani tayi da gaske bashi da niyyar amsata, wasu hawaye taji masu zafi sun taru cikin
idanuwanta. Duk kawayen ta haka suke cewa tayi sa'a, mijinta ga arziki ga kyau

"Ko yanzun mijinki yaso zai auri budurwa wallahi da zata bi kyawun shi"

Wata kawarta ta taba fada, dan yanzun ma sun raba jaha, daina sakar mata fuska tayi tun da
aurenta ya mutu, saboda matar ba karamar gogaggiya bace ba. Ko da aurenta ma duk yanda
kuke karka fara yaba kyawun mijinta yanzun zata daina sauke girarta a gabanka. Wani irin
kishin shi takeyi na ban mamaki, shisa duk idan taga zai fita haka take jin kamar baza'a waye
safiyar ranar da ita ba saboda bacin rai. Da mutanen da suke mata kallon tana zaune a wannan
tankamemen gidan tana kuma auren namiji kamar Bajjo sun san me take hadiya da ta daina
basu sha'awa.

Ita a bakin yaran da ta haifa da cikinta ma bata ji zancen cewa Nawfal zaiyi aure ba. Yara kamar
ba daga jikinta suka fito ba, yanda suke nanike ma Nawfal din yana bata takaici. Sai jiya da
Julden zai tafi Abuja yace mata

"Gobe da safe za'a daura auren Bajjo"

Tambayar duk da tayi mishi kuma bata samu amsa ba. Haka ya tsallake ta ya wuce, son da
take mishine abinda ya sata yi mishi addu'ar dawowa lafiya. Sai Adee ta kira, itace take fada
mata kowa zai aura da inda suka hadu. Duk da bangare mafi rinjaye a zuciyarta na tare da
bakin cikin kalar matar da ya samu, sauran karamin kashin yaji dadi da kuma fatan su karata
can, ta rike shi karya dawo. Kar ya sake waiwayo su, inda yake ya zauna kamar Bukari, danma
yanzun zamani ya canza ko ba'a ga fuskar juna ba za'aji muryoyi, da tace aji shi dif, ayi zaman
makokin da babu gawa idan anyi cigiya an gaji.

Ya zamana sunan shi ma zaiyi ma kowa nauyin ambato kamar yanda na mahaifin shi yayi.
Wannan shine fatanta, Nawfal yayi ma rayuwar ta da ta ahalinta nisa

Wannan karin ma kaddara ce ta riga fata
Kaddarar da take bibbiyar mutanen da ta kira ahalin ta da Nawfal din da ta zabi ta ware a cikin
su
Bata sani ba
Bata san shi din haske bane a tare da su
Bata san shi zai zame musu katanga a lokacin da tarihi ya maimaita kan shi ba

"Sai da safe"

Julde ya fadi yana nufar kofa, hannu tasa tana share hawayen da ya zubo mata. Yana fita yaja
mata kofar, a jagule yake jin zuciyar shi harya fice daga gidan, inda ya tsaya ya siyi lemon zaki
yaji wani yace

"Mero!"

Sai da zuciyar shi ta nemi fitowa daga kirjin shi saboda tsallen da yaji tayi, da sauri ya waiga
yana ganin yarinyar da bata wuce sa'ar Adeen shi ba da take tattare kwanoninta da alama
abinci ta gama siyarwa a wajen, lumshe idanuwan shi yayi ya bude su

"Maigida ga canjin ka"

Mai lemon ya fadi, karba Julde yayi ya karasa motar shi ya zauna a ciki yana dora kanshi da
abin tukin, har lokacin numfashi yake fitarwa cikin kokarin dai-dai ta bugun da zuciyar shi

"Naji maganganu kala-kala akan ka, wanda duk yake tunanin ya isa dani yace mun kar in aure
ka... Ya zanyi da zuciyata Julde? Ya zan fito musu da ita su fahimci hakuri da kai baya cikin

zabin da nake da shi?"

Kalaman Mero suka dawo mishi kamar tana cikin motar a tare da shi, sake runtsa idanuwan shi
yayi

"Na yadda kowanne rai da nashi kaddarar, kai ne kaddara ta Julde..."

Ya rasa yanda lokaci zai zama mai adalci kuma marar adalci a lokaci daya, yanda yake wucewa
batare da ya jira kowa ba shine babban adalcin shi, amman yanda idan ya wuce baya dawowa
kowa a wajen Julde hakan rashin adalci ne, ya zaiyi da kadan daga cikin kurakuren da yake jin
zaiso ya sake samun aron lokaci dan ya sauya zabukan da yayi? Yau bama wani waje yake son
komawa ba, rana daya ce, dakika ne kayadaddu a cikin ranar da zai sauya amsar da ya bama
Mero, so yake ya kalleta ya fada mata ita ce kaddarar shi bashi bane kaddararta.

"Mero tayi aure"

Labarin ya riske shi shekaru hudu bayan rabuwar su, labarin da saida yayi yar karamar jinya a
kan shi, hangota da wani, hango rayuwar da tayi da shi tana yinta tare da wani ba zai daina
kassara zuciyar shi ba. Shi kadai yake dawainiya da ita a ran shi, ita ta shafe babin shi daga
rayuwarta harta bude wani sabon shafin tare da wani. Bai tambayi a ina ko wa ta aura ba,
abubuwan da yake gujema cikin sanin masu yawa ne. Da duk rana da yanda yake jin kusancin
ta a zuciyar shi yana kuma jin nisanta da rayuwar shi

Da ya san kaddara ta adana musu shafin sake haduwa a titi daya da ya sauya tunani
In da yasan haduwar da zasu sake yi da Mero zata tono mishi abubuwan da za'a hada da
rayuwar shi ta baya da ta yanzun a waje daya daya duba zabukan da yake da su

Dago kan shi yayi yana sauke wani irin numfashi ya tayar da motar fitilar ta na haske wajen har
yana shirin kashe mishi idanuwan daya dan jima da su a runtse, sai da yasa hannu ya murza
idanun, duk da haka ji yake hasken kamar yayi mishi yawa

Da yasan duhun da yake bibiyar shi watakila da ya nemi duk wani haske da zai iya kafin lokaci
ya kure mishi
Kaddara
Kaddarar dai...
Ya baro tushen shi saboda ita
Tana biye da shi har wajen da yake tunanin ya boye mata

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan

IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*RAI DA KADDARA 1*

12

Bai san ko ya kamata ace yana jin shi wani iri tun safiyar ranar ba, da Julde ya kira shi yace an
daura ma baiji wani abu ba. Wasu kance sunji su kamar suna yawo kan gajimare saboda farin
cikin an daura musu aure. Shi baiji duk wannan ba, farin ciki, yana cikin shi tunda ya samu
goyon bayan su Julde akan auren, na rana daya bai taba jin ba zai samu Murjanatu ba, sai dai
in rashin tabbas na rayuwa, mutuwa ta raba tsakanin su. Shi da ita din basu fara soyayya lokaci
daya ba, daya ganta in da ance zaiji wani abu a kanta, ko zai kirata matar shi wata rana zaiyi
mamaki.

"Ka zauna mun a waje"

Shine maganar farko da tayi mishi a coffee shop din daya shiga cikin harshen turanci , an kuma
hado mishi irin yanda yake so da kankaru a ciki. Ya zabi teburin ne saboda yana can lungu,
kuma mai kujera biyu ne da ba lallai inka zauna kaga wani ya zo ya zauna kusa da kai ba.
Harya hango yanda Coffee shop din zai zamana wajen zuwan shi duk rana. Yanda take kallon
shi haka shima ya daga kai ya saka nashi idanuwan cikin nata, da yake lokaci ne na sanyi,
shigar sanyi ce a jikinta, iya abinda yake gani na daga fuskarta ya gane ita din me kyau ce,
kyau irin wanda zaka gani a kallo daya.

"Banga sunan kowa a wajen ba kafin in zauna"

Hannuwanta da babu safa ta murza kamar sun daskare mata

"I'm a regular a wajen nan. Kowa zai fada maka corner dina ce nan"

Ta karashe maganar da hausa wannan karin dan yayi mata kama da bahaushe

"Kaga karfin hali"

Ya fadi da fulatanci a muryar da yayi tunanin dai-dai kunnen shi ta tsaya

"Ba karfin hali bane ba, gaskiya ce"

Ta amsa shi da fulatancin tana ganin mamakin daya bayyana akan fuskar shi, dayar kujerar taja
ta zauna

"Bafullatana ce ni, tunda kaji nayi hausa bai kamata kayi mamaki dan nayi yare na ba"

Dariya yayi, ba dan akwai abin nishadi a muryar ta ba, sai kwarin gwiwar ta da yanda take mishi
magana kamar ta dade da sanin shi. Kamar ta san cewa ita da shi din ranar ne labarin su ya
fara, sai da aka kawo mata abinda tayi order harda cookies ya gani sannan ta sake ce mishi

"Murjanatu Faruk"

Kai ya jinjina mata

"Nawfal Bukar"

Ba zaice sunyi hira ba, ta dai riga shi tashi daga wajen dan lokaci zuwa lokaci tana duba
agogon da yake wajen, yanayin ta ya nuna cikin sauri take.

"Next time ka nemi wajen ka, this is my spot"

Dariya kawai yayi, kafin ma ya amsata tabar wajen. Ko da ya tafi ba zaice yayi tunanin ta ba,
daga ranar ma zuwa safiya ko sau daya bata fado a ran shi ba. Watakila duk littafine da
fina-finai ke zuzuta wannan kalar soyayyar. Sai ace idanuwa sun sarke cikin na juna shikenan
har soyayya ta kullu, ko an gogi juna jiki da ruhi sun girgiza. Watakila kuma kaddara ta hada
hanyar shi da Murjanatu ne dan su kafa tarihin da zai karyata wannan kalar soyayyar. Sunyi
haduwa wajen goma bayan nan, ta shigo Coffee house din shi zai fita, ya shigo ita zata fita,
banda gaisuwa babu wani abu da yake hada su.

Maganar su ta fara tsayine randa ta same shi zaune da sketch book dinshi yana nazarin wasu
zanunnuka

"Kai Artist ne?"

Ta tambaya, zai tuna ya girgiza mata kai, kamar ba zai ce mata komai ba kafin ya amsa

"I'm a furniture designer, ko ince abinda nake karanta kenan"

Gabaki daya hirar su akan abinda yake karantawa ne har suka rabu. Zaice ita ta fara neman
shakuwa da shi, ta fara neman alakar su ta wuce haduwa a Coffee Shop din bayan ta gayyace
shi wani furniture showcase da za'ayi a cewarta baban dan ajin su ne a wajen ko wani bayani
da ba zaice ya fahimta ba gabaki daya, an gayyace ta, ita kuma ta gayyace shi. Ya amsa ta da
cewar zaije ta rubuta mishi lambar ta a takarda tana ajiye mishi sukai sallama.

Ranar ta bude musu sabon shafi, dan duk wani yunkuri da zaiyi sai ya gan su a tare a wani
wajen, sai yaji kamar dama can ya santa ne, babu wata bakuntar juna a tare da su. Kamar
yanda a cikin duk wata dariya da zasuyi ya fara jin ba ita bace ta karshe. A cikin shekara daya
sunyi wani irin sabo da kalamai zasuyi karanci wajen fassara shi, dan a gidan su Murjanatu

babu wanda bai san shi ba, har idan an nemeta ba'a samu ba, yana cikin jerin abokanta da
Mamanta ko babanta zasu fara kira suji ko suna tare ko kuma ta fada mishi inda taje.

Rana daya ya tashi da safe yaji baya son hango tana da kayadadden lokaci a rayuwar shi, baya
son hango wasu ranaku a cikin rayuwar shi da babu ita a cikin su

"Ina son kasancewa da ke, fiye da abokanta"

Ya fada mata batare da shakku ba, ta dauki mintina biyar, har saida shirunta ya fara tsoro ta shi
kafin ta dago tana saka hannuwa ta dauke kwallar dake cikin idanuwanta

"Na dauka ba zaka taba tambaya ta ba"

Tayi maganar muryarta na rawa

"Ka san tun yaushe nake son ka"

Kai ya girgiza mata, jin tayi shiru na sa shi fadin

"Wannan na da muhimmanci ne yanzun?"

Dariya tayi mai sauti

"Babu, kana jin yanda nake ji, shine a saman komai"

Daga nan suka fara, bai san a inda zasu tsaya ba. Ya dai san zai karasa sauran rayuwar shi
tare da ita yana mata godiyar yanda ta yarda da shi da zuciyarta, da farin cikinta harda
abubuwan da tasan shi kan shi bashida tabbaci akan su.

"Zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login