Showing 78001 words to 79955 words out of 79955 words

Chapter 27 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

Advertisement

na ragewa da ganin Daada.

"Ina wuni..."

Ta furta a hankali tana dorawa da

"Ya karfin jikin? Ku zauna mana Madina"

Zaman Daada tayi sannan ta amsa gaisuwar da Saratu tayi mata, Madina na gaishe da ita

"Ina jakar?"

Dan juyawa Madina tayi dai-dai shigowar Salim da yayi sallama cikin sanyin murya. Saratu ta
karasa tana kai hannu zata karbi jakar hannun Salim din

"Ina zan kai?"

Da hannu ta nuna mishi hanyar dakin da nashi ne a cikin gidan kafin ya bar bangaren ya koma
in da yake yanzun. Can kuwa ya nufa ya kai jakar ya dawo falon

"Ina Daddy?"

Ya bukata, dan murmushi Saratu tayi

"Yanzun zaka ga ya shigo"

Ta kirashi bai dauka ba, daman bata sa ran zai dauka ba, idan da ta kira fiye da sau daya zai
san dole akwai wani abu muhimmi. Ace kai da mijin ka ba zaka kira kaji lafiyar shi ba, ba zaka
kira ka tambaye shi wani abu ba balle kasa ran zakuyi hira idan yayi maka nisa. Bakowa bane
zai fahimci ciwon abin sai macen da take cikin irin halin da take ciki.
"Madina a zubo muku abinci mana"

Saratu tace tana maida hankalinta kan su, kai Madina ta girgiza

"Ko zaki ci Daada? Baki ci wani abu mai yawa ba fa"

Kai Daadar ta girgiza a hankali

"Ni kam banajin yunwa fa"

Numfashi Saratu ta sauke

"Bari a kawo ruwa to"

Tayi maganar tana nufar hanyar kitchen, bata jima ba ta dawo da ruwa da kofi, Madina ta karba
ta zuba ma Daada tana mika mata. Karba tayi ta dan kurba ba dan tana jin kishi ba, ta ajiye
kofin a kasa. Sai lokacin Madina ta kula da Salim ya bar dakin, sai Saratu da ta samu kujera
can nesa da su ta zauna. Wani irin shiru marar dadi na lullube dakin, su duka ukun an rasa
wanda zai ce wani abu. Sai dai motsin Madina da kan gyara zamanta lokaci zuwa lokaci. Ta ji
dadi da Saratu ta mike ta kunna kayan kallon da suke cikin dakin tana daukar emote ta koma in
da ta tashi ta zauna.

Sai ita da Madina suka maida hankali kan labaran, Daada kuwa kara shigewa tayi cikin kujerar
da take zaune, kanta cunkushe yake da tunani kala-kala. Ko shigowar Julde bata ji ba sai
muryar Madina da take gaishe da shi

"Daada kun gama shiryawa ko?"

Ya bukata yana murmushin da kallo daya zakai mishi kasan na karfin hali ne, kai Daada ta daga
mishi a hankali tana mikewa. Sai take ganin kamar ta dade bata kalle shi ba, kamar duk
shekarun nan akwai wani labule a tsakanin idanuwan ta da shi da yake hana mata ganin shi irin
yanda take ganin shi yau. Ba Julden da yake da mata da yara ba, ba Julden da ake ma kallon
babban mutum a wajen kasuwan ci da cikin unguwa ba. Julde take kallo shi kadai batare da duk
wannan abubuwan ba, dan ta take kallo yau tana jin littafin da ta dade da rufewa a cikin kanta
yana budewa kafin ya tsaya a wani shafi da yake da muni a rayuwar su gabaki daya.

Duk shekarun nan, watannin da suke a cikin shekarun, ranakun da suka dinga zuwa suna

wucewa bata san dalilin da sai yau ba, sai yau ta zabi ta kalli Julde da idanuwan da tayi mishi
alkawarin ta kauda su da kan shi har abada

"Allah ya tsine maka albarka Julde. Allah ya kunyata ka a idanuwan zuri'ar ka yanda ka zame
mun abin kunya!"

Idanuwanta ta runtsa, gabaki daya kirjin ta na daukar dumi kamar an hura mata wuta a ciki.

Me yasa sai yau? Shine tambayar da bata da wanda zai amsa mata. Ta kuma kasa daina kallon
shi. Ko da ta runtsa idanuwan, tana bude su akan shi suka sauka, sai dai yanzun taga kamar
yana cikin wani abune mai kama da kwallon kafa, amman duhun abin bai hanata ganin shi a
tsaye a ciki ba, kamar yana tsaye ne a cikin tsinuwar mahaifin shi da take jiran cikar lokaci ta
fashe tare da shi. Da Madina bata riketa ba da kafafuwanta sun kasa daukar ta saboda firgicin
da ya ratsa ruhinta

"Daada ba dai jikin bane ba?"

Madina ta bukata cike da kulawa da kuma damuwa, kai kawai Daada take girgiza mata, addu'ar
duk da tazo mata karantawa takeyi tana neman samun nutsuwa. Haka suka lallaba suna fita
waje. Saratu daga bakin kofa tayi musu fatan Allah ya kiyaye hanya, lokaci ya koya mata kama
kanta da kinyi musu abinda ta dauka a matsayin shisshigi a cikin rayuwar su. Tun farko Daada
bata karbeta ba, tayi biris da cewar ko da bata auri Julde ba jinin da yake yawo a jikin ta yana
yawo a jikin shi, ita din dangin shi ce ko da aure bai hada su zumunci ba.

*

"Hamma kana soka mun kashin hannun ka a hakarkari na fa"

Nawfal yai maganar yana sake gyara zaman shi. Motar da Julde ya so su dauka ya manta
rabon da ya hau ta, kin tashi tayi, Daada, Madina da Salim baya suka shiga su. Khalid ya bude
ta bangaren da Salim yake ya watsa mishi wani kallo da yasa shi mayar da murfin yana rufewa
hadi da furta
"Allah ya baka hakuri"

Ta kasan makoshi, zagayawa yayi ya koma gaba in da Nawfal yake zaune

"Ka dauko motar ka mana, matsewa fa zamuyi anan...dan Allah ka dauki mota Hamma"

Amman Khalid yaki sauraren shi

"Zaka matsa ko sai na kwade ka"

Nawfal turo labba yayi yana kallon Julde da ya shiga mazaunin direba ya rufo kofar

"Daddy kace Hamma ya dauki motar..."

Bai rufe baki ba yaji Khalid din ya turmotso rabin jikin shi akan na Nawfal

"Kasheni zakayi ne wai, ka tsaya in matsa maka mana"

Ya karasa yana ture hannun Khalid har yana gabje hanci da murfin motar da yake kokarin
jawowa ya rufe

"Wai dan uban ka Bajjo ni sa'anka ne?"

Sake tura shi Nawfal yayi

"Daddy kaji Hamma na zagi ko?"

Dakyar Khalid ya rufe murfin motar, yanda suke tutture juna zaka dauka yarane yan shekara
bakwai ko kasa da haka. Murza kan shi da yake ciwo Salim yakeyi tun da suka fara

"Bajjo ku fita daga motar nan"

Ya furta babu alamar wasa a muryar shi, nutsuwa sukayi

"Ba ku jini ba kenan"

Ya sake maimaitawa

"Daddy kace ya barmu dan Allah, ba munyi shiru ba"

Khalid ya fadi, numfashi kawai Julde ya sauke, ya riga da ya koyi shiru ya kyale su, tuntuni
kamar suna Khalid da Nawfal na ganin hanjin juna wasu lokuttan, sun girma, Nawfal harda mata
amman ba zasu daina fada kamar yara ba. Da Salim yakan bar su tunda can ma. Yau bashi da
karfin surutun kwata-kwata shisa yaja motar suka tafi. Da suka ga an hau hanya shine suka
cigaba

"Wallahi zaku sauka a hanya ku biyo mu a napep. Maganar da zan karayi akan ku sai kun
sauka daga cikin motar nan"

Salim ya fada, saboda Daada na tare da su, kuma a tsakiya take zaune. Madina ce ta bangaren
da su Nawfal din suke zaune, daga inda yake zai iya mika hannu ya kai musu duka, amman
baya son su duka su gwada hali a gaban Daada. Kan shi har juyawa yake saboda surutun da
sukeyi. Amman dan su san da gaske sauka zasuyi shisa ya rantse suka ji, yana kallon Nawfal

na ture hannun da Khalid yake kara dora mishi. Madina kanta murmushi takeyi, tana son ganin
Khalid da Nawfal a tare, fadan su nishadi yake sakata, ko yanzun ma sun saukaka mata
damuwar da take ciki.

Su dukan su basu kara nutsuwa ba sai da suka fita suka shiga cikin filin jirgin, suka tsaya inda
zasuyi sallama da su Daada, lokacin tsoron da yake tare da Nawfal ya fito shimfide akan fuskar
shi

"Kace zaka biyo mu Daddy"

Yayi maganar yana kallon Julde da ya daga mishi kai, Madina karasawa tayi ta rungume Daada
tana jin wasu hawaye masu dumi na zubo mata

"Karki karya ni Madina"

Sake riketa tayi gam tana jin kamar ace in ta raba jikinta da na Daada zata taho da dumi da
kamshin Daadar a tare da ita, iya wanda zata rike har sai ta dawo

"Allah ya dawo mun dake cikin aminci Daada... Ina son ki sosai.. Kin sani ai ko?"

Kai Daada ta daga tana kama Madina ta rabata da jikin ta

"Bajjo zai kira mun ke ta hoton nan yanda naga kunayi"

Hannu Madina ta sa tana goge fuskarta, sai da ta dan ja hanci sannan tayi murmushi

"Video call Daada"

Dan daga idanuwa Daadar tayi

"Oho ni ban san sunan shi ba"

Dariyar karfin hali Madina tayi, wasu hawayen na sake zubo mata, hawayen da Salim yake ji
har kasan ran shi. Shisa ya saka hannuwan shi cikin aljihu saboda kaikayi suke mishi, kaikayin
ya rikota ya hadata da jikin shi ya lallasheta ta sigar da yafi kwarewa

"Hamma sai mun dawo"

Nawfal da yake tsaye gefen Daada ya fadi yana sa Salim janye idanuwan shi daga kan Madina
yana mayarwa kan shi

"Allah ya tsare...komai zaiyi dai-dai ka sani ko?"

Kai Nawfal din ya jinjina mishi, sallama suka kara yi gabaki daya, su suka fara juyawa suna
barin Daada da Nawfal a tsaye. Madina ce ta juya tana daga ma Daada da taji zuciyar ta ta
tsinke hannu, lokaci daya taji tsikar jikinta ta mike. Murmushi Madina tayiwa Nawfal da suka
hada ido, sai dai zuciyar shi tayi nauyin da ya kasa mayar mata da martani har ta juya, yabi
bayan ta da Kallo, da yanayin tafiyar ta.

Kallon ta Nawfal da Daada sukeyi
Kallon ta Nawfal yakeyi batare da ya san kaddarar da take bibiyar su ta kusan cika ba
Kallon ta yake batare da ya hango doguwar igiyar da take shirin kulle su a waje daya ba

Haka ya ga Salim yayi dabarar tsayawa Madina ta karasa suka jera tare, yanda ya juyar da kai
na tabbatar ma da Nawfal din magana yayi ma Madina

Salim magana yayi mata kamar ba su da wata damuwa da ta wuce jiran dawowar Daada.
Nawfal ya fara juyawa ya na ba Daada passport din su ta rike, ya dauki jakarta ya dora kan
akwatin shi yanda zasuyi mishi saukin ja, sannan ya kama hannun ta yana fadin

"Muje Daada..."

Tana tunanin me likitoci zasu gani idan sun bude kirjin ta saboda zuciyarta na tare da su
Madina, gabaki daya zuciyarta da ta kasa nutsuwa na tare da su. Haka tabi Nawfal suna tafiya,
tana jin littafin da yake cikin kanta yana bubbudewa yana komawa shafin farko, takun duk da
zatayi da nufin barin garin na zamar mata adon da yake janta don ta waiwayi in da komai ya
fara....!

*****

Anan zan kawo karshen kashi na daya. Bayanin lokaci da kuma in da kashi na biyun zai zo na
nan tafe ba da jimawa ba da yardar Allah.

Comments
Sakon fatan alkhairi
Addu'o'i
Ta wattpad
Whatsapp
Da masu kira har a waya

Banda kalaman da zanyi amfani da su wajen yi muku godiya. Allah ya saka muku da alkhairi.
Nagode da duk kwarin gwiwar da kuke bani.

Allah ya sadamu da alkhairin shi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login