Showing 30001 words to 33000 words out of 79955 words
Chapter 11 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
Adee, yanda abokan arziki suka mishi tsaye ta yanda wani dan uwa na shi bai taba mishi ba
tunda yake. Daga tambayar auren har daurin shi da ya wakilta abokin shi ya kuma karba.
Tabbas yaga halaccin mutane, a tare da dangin mijin Adee kuma yaga wautar mutane ta yarda
da wani kamar yanda suka yarda da shi.
Dan shi bai basu wannan yardar ba, kaunar da yake ma Adee tasa sai da yayi cikakken bincike
a kan su kafin ya amince. Ba zai dauki yar shi ya kai inda wata matsala zata biyo baya ba.
Sauran maza ne, yana da tabbacin babu wani abu da zai taba su da zasu kasa dauka. Adee ce
yake son karewa da dukkan kumajin shi. Kuma hankalin shi ya kwanta da kalar mijin da zata
aura.
"Karfe goma da wani abu, in dai ba anan zaku kwana ba ya kamata ace kun tashi kun kama
hanyar gida yanzun"
Julde ya fadi yana kallon agogo, sake shigewa cikin kujera Nawfal yayi yana dauke idon shi
daga cikin na Khalid da yake kallon shi
"Da gaske Bajjo?"
Adee ta fadi bayan ta mike
"Gobe da safe zan taho, sai mu taho da Madina..."
Yace yana kin hada ido da su, su yake son gani daman, kuma ya gan su, ko da can kalar baccin
da yakeyi a gidan Daada ya sha bamban da na ko ina, bacci yake batare da tunanin komai ba.
Yana son ko da na yau ne kawai kar ya hadu da Nanna.
"Muje Khalid, Allah ya kaimu goben. Daddy sai da safe"
Adee ta fadi tana kallon su Daada
"Daada sai Allah ya kaimu... Madina ina jiran ki"
Kanta da yayi mata nauyi Madina ta jinjina, bacci takeji ba dan kadan ba, ba zata tuna ranar
karshe da tayi wannan daren ba. Julde ma mikewa yayi
"Nima ai tafiyar zanyi"
Dan tunda aka fara hidimar bikin ya tattara ya koma hotel da zama, har fada sukayi da Saratu
kan hakan
"Daman kofa kake nema, in ba haka ba ko bangaren su Khalid ai zaka iya komawa"
Shine abinda ta fadi da ko amsa bata samu ba, saboda ba sai da biki ba, idan yaga dama zai
iya kwanakin shi a hotel tunda ba zamanta yakeyi ba. Sai da Nawfal yaga Julde ya mike
tukunna ya raba nashi jikin da kujera, tare duk suka fita, Daada iya bakin kofar daki ta raka su,
Nawfal ne ya fita har kofar gida. Sai da su Khalid suka fara sannan Julde ya kalli Nawfal
"Menene? Me kake son fada mun?"
Da mamaki Nawfal yake kallon shi, murmushi Julde yayi
"Na sanka Bajjo, kana ta kallo na da na shigo, na san akwai abinda kake son fada mun..."
Murmushi Nawfal yayi, shisa a duniyar shi gabaki daya babu kamar su, sune kawai suke kula
da kananun abubuwa haka a tare da shi
"Zai iya jira Daddy, abinda nake so in fada maka din... Zai jira sai an gama hidimar Adee..."
Numfashi Julde ya sauke
"Ka tabbata?"
Ya tambaya a idanuwan Nawfal din yaga ko wacce irin magana ce ba ta rashin dadi bace ba,
babu damuwa ko daya a tattare da yaron na shi
"Daddy... Allah da gaske"
Murmushin dai Julde ya karayi
"To shikenan. Ka koma ciki, sai da safe"
Kiyawa Nawfal yayi, sai da yaga tafiyar Julden tukunna ya koma yana mayar da kofar gidan ya
kulle hadi sa sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba. Kamar yanda ya fada ne,
tashi maganar zata iya jira har a gama bikin Adee.
*
A tsaye ta fito ta same shi, ya mika mata hannu ya karbi jakar da take rike da ita, batayi musu
ba ta mika mishi tana rugawa ta shiga kitchen, numfashi kawai Nawfal ya sauke, ya kai minti
talatin yana jiranta, sai yanzun ya gane me yasa Daada tace mishi
"In dai Madina ce da ka samu waje ka zauna..."
Ko Salim ya kai minti sha biyar yana tsaye kofar gida, dan da tace ma Nawfal shi zai zo ya
dauketa bai yarda ba har sai da yaga zuwan na shi, ita take kara bata lokaci shi gaban shi yake
faduwa saboda Salim ne, Salim ne a waje yana jiran su. Zai fara tsayawa a cikin soron gidan
Daada, idan yaji Salim din baiyi fada ba saiya fita, dan bai shirya a sauke mishi hayaniya da
sanyin safiya ba. Ba zaice ga abinda ta kara tsayawa yi ba, amman a tsakanin kitchen da kuma
dakinta sai da ta kara bata kusan mintina goma. Sannan ta sake komawa kitchen tana dauko
wata karamar roba mai murfi ta fito.
Kai kawai Nawfal ya girgiza yana sata yin dariya
"Daada... Mun wuce"
Ta furta saboda Daada ta koma daki, daga can tayi musu Allah ya tsare tana fada musu su ja
mata gidan idan sun fita. Daga baya Nawfal ya tsaya dan ya hango Salim ya jingina kanshi da
kujerar motar da alamar ya gaji da jira, yana kallo Madina ta bude gaban motar, sai da yaji
gaban shi ya fadi, musamman da Salim din ya dago yana kallon ta a kasalance.
"Oh goodness"
Nawfal yace yana matsawa baya, jira kawai yake yaji Salim din ya fara fada, amman ga
mamakin shi zama ya gyara yana tashin motar, juyowa Madina tayi
"Hamma ka taho"
Kai ya daga mata yana takawa, kafin tayi wani motsi ya bude bayan motar ya shiga yana mayar
da murfin ya rufe, dan babu wanda zai saka shi zama gaban motar Salim, yana kallo Madinar ta
shiga ta zauna ta rufo kofar. Sai da Salim ya fita da motar tukunna ta fara korar shirun da fadin
"Doya da kwai na soya, ga naka na dibo maka..."
Dan kallon ta Salim yayi yana mayar da hankalin shi kan tukin da yake yi
"Shisa kika bata mun lokaci?"
Kai ta girgiza tana dariya
"A'a Allah, inata sauri fa, ko Hamma?"
Ta karasa maganar tana dan juyawa ta kalli Nawfal da ya sadda kan shi kasa, wannan labarin
ba dashi za'ayi ba. Baya son ta fara tsoma shi ciki. Baisan me yake faruwa ba ko yanda akayi ta
sa bakin Salim ya bude, ko yanda maganar ta bata mishi hayaniya cikin kunnuwa, amman shi
yasan yana bude idon shi zaice yana ihu. Hirar Madina ta cigaba da yiwa Salim da yake amsata
dai-dai. Suna karasawa cikin gida Nawfal na budewa ya fice daga cikin motar, yana sane da ko
gaisawa basuyi da Salim ba, amman Salim ne in zaku hadu ka wuce ya wuce yafi mai wata
gaisuwa da zakayi mishi.
Madina ma bai mata sallama ba ya wuce abin shi. Murfin motar ta kama da nufin fita itama
Salim yace
"Ina zaki?"
Kallon shi Madina tayi
"Su Adda na ta jira na nasan"
Dan daga kafadun shi yayi
"Nima na jira ki ai, ina doyar?"
Inda ta ajiye ta dauko robar tana mika mishi
"Allah suna ta jira, karfe tara nace musu...na san zan kai dare kilan ban gama ba, zan ara wayar
Adda in kiraka idan na gama"
Ta karasa maganar tana bude murfin motar ta fice kafin ma yace wani abu, baya ta sake
budewa ta dauki jakarta da Nawfal yabar mata. Sannan ta wuce cikin gidan, numfashi Salim ya
sauke yana juyawa ya ga har ta bace ma ganin shi, yanda gajerun kafafuwanta suke da sauri
har mamaki yake bashi. Haka kawai yaji ganin tan da yayi ya mishi kadan, ko hirarta baiji da
kyau ba. Sake kunna motar yayi yaja ta yana kara ficewa daga gidan dan ba zai zauna ba,
hayaniyar tayi yawa. Gara yaje ya samu wani hotel din ya kira wata ko zata taya shi ya rabu da
yanayin kewar Madina da ya dabaibaye shi.
Ita kuwa cikin gidan ta wuce, tana shiga cikin falon da sallama, Saratu ta fara gani da ta amsa
sallamar da fara'a a fuskarta. Ko a cikin yaran idan taji ana cewa Salim baya son mutane abin
baya bata mamaki, itama din ba wai mutane sun dameta bane ba, kafin jinin ku ya hadu akwai
aiki. Idan wani ya ce mata me yasa take son Madina zata karyata, amman yarinyar ta shiga
ranta tun ba yanzun ba, bata san me yasa bata zuwa gidan ba, lokaci zuwa lokaci tunanin ta
yakan fado mata. Banda su Salim babu wani da zataji alkhairi zai shiga tsakanin shi da Julde da
zataji ranta bai mata bakikirin ba sai Madina.
Tana kaunar yarinyar, irin kaunar nan da bata da dalili. Share muryar da taji a cikin kanta tana
tambayar ta
"Anya kuwa? Kin tabbata babu wani dalili? Kaunar da kike mata bata da alaka da Yelwa?"
Tana kokarin dishe sautin muryar da yiwa Madina magana
"Madina ana ganin ki daman? Adee ta jawo mana ke ko?"
Dariya Madina tayi
"Nanna... Makaranta fa. Ina kwana... Ya hidima?"
Murmushin ta Saratu ta kara fadadawa, duk da yanayin muryar Madina din na son daukar
tunanin ta zuwa abubuwan da ta zabi ta adana
"Alhamdulillah...suna ciki suna jiran ki, amman da kin fara cin wani abu, an kawo waina yanzun
nan"
Kai Madina take girgizawa
"Sai dai anjima Nanna, doya naci wallahi"
Dan har bayan wuyanta take jin ruwan shayi na taso mata, wani irin koshi tayi na ban mamaki
"To shikenan..."
Har Madina ta wuce ta dan juyo
"Daada tace a gaishe ki"
Fara'arta dake fuskar Saratu sai da ta dan ragu, kai ta jinjina kafin dakyar ta iya cewa
"Tana lafiya?"
Da murmushi Madina ta amsata tana juyawa, karancin shekarun ta bai hanata fahimtar babu
wani shiri mai karfi tsakanin Daada din da Saratu ba, kawai wasu tambayoyin bata san ta inda
zata fara su ba, wasu tambayoyin tsoron amsar su na sakata sake adana su a cikin kanta.
Amman kam tana da tarin tambayoyi, masu yawan gaske
"Sai yanzun? Karfe tara fa mukayi dake"
Muryar Adee ta katse mata tunaninta
"Afuwan Adda, inata hidima ne ashe lokaci yana tafiya"
Cewar Madina tana ajiye jakar hannunta a kasa dan duka kayan lallen suna ciki, tsugunnawa
tayi ta kwance takalman da suke kafarta da sam sai lokacin ta tuna bata cire su ba. Kafin ta
dago har Adee ta daukar mata jakar
"Ki kawo Adda"
Harararta Adee tayi
"Ni dai muje, ki dauko takalmin ki kafin a dinga bi takan shi ana wucewa"
Juyawa kuwa tayi tana daukar takalman nata ta rike su a hannu tabi bayan Adee har zuwa
dakinta da alamu suka nuna duk an kwashe kayan ciki an bar gado kawai, dan dakin yayi fili
sosai. Yan matane kusan su sha biyar, in dai kallo ne Madina ta saba da shi tunda inta fita har
ta dawo bata cin karo da mace mai kalar shigar ta. Yau ma riga da wando ne, wandon na jeans
ne baki, kamar ko yaushe ta nannade kafafuwan har kusan kwaurinta sai safa baka a kafarta.
Akwai farar riga kal daga ciki, ta dauki mai dogon hannu ta dora a kai, tana jan hannun baya,
sai yar karamar hijab da ta saka.
Ko gilashin fuskarta abin kallo ne, waje ta samu gefe ta zauna tana karbar jakarta a hannun
Adee bayan tace ma yan matan da suke cikin dakin
"Sannun ku"
Rigar saman yellow ce, ita babu yanda za'ayi ta bata ta da lalle, amman tabbas a cikin yan
matan nan ko wajen wucewa ne wata na iya shafar ta. Kunshin gidan biki ba bakonta bane ba.
Shisa ta mike tsaf tana cire rigar tabar farar da tayi zanzaro da ita, ganin tana neman inda zata
ajiye yasa Adee karba, saida ta ninketa sannan ta fice da rigar tana barin Madina da ta zauna
zata fara hada lallen ta.
*
Sai wajen tara da rabi tukunna ta samu suka barta, shima dan Salim da yake ta kiran wayar
Adee ne, ita nata kunshin sai washegari ma da sassafe idan Madina din tazo ita zata fara yiwa
tunda ranar ne ya kama alhamis kuma shine za'a fara bikin gadan-gadan, za'ayi kamu. Sai dai
kowa yazo ya ga kunshin wasu sai yace shima za'ayi mishi, duk ta bar su a zuwan washegari
idan ta gama yiwa Adee duk sai ta samu tayi musu. Nanna ta so ta kwana anan din tace mata
tabar Daada ita kadai. Tunda take a rayuwarta bata taba kwana wani waje banda gida ba, bata
ma jin zata iya kwana wani wajen.
Wata babbar leda Nanna ta cika mata da kayayyakin da batasan ko meye a ciki ba. Adee ta rike
ledar tana rakata har wajen motar Salim din sannan ta bata kayayyakin tana mata godiya sukayi
sallama, bayan motar Salim ta bude ta saka kayan ta rufe tana kowama ta bude gaban motar
da kamar jira Salim yake ta zauna
"Ke ba zaki iya ce musu dare yayi ba? Ba zaki ce kin gaji kina so ki tafi gida ba, ko baiwar su ce
ke?"
Saboda yanayin ta kawai ya nuna a gajiye take, ko wayar farko daya kira wajen karfe bakwai
aka bata yanayin muryarta akwai gajiya
"Mutanen suna da yawa ne Hamma, shisa na tsaya na kara rarragewa, kanata kira da na kara
yiwa ko mutum biyar ne kafin mu tafi tunda kai zaka mayar dani gida"
Kallon ta yakeyi kawai, itama kallon shi tayi, yanayin fuskar shi na sata kai hannu ta gyara
gilashin ta
"Dan Allah kar kamun fada Hamma, nagaji sosai Allah, kaji..."
Numfashi kawai ya sauke, ba fada bane baya son yi mata, surutun ne ba zai iya ba. Yana kallo
ta rufo murfin motar tana yarfe hannun ta na dama tana mikar da shi kafin ta sake yarfe shi,
tsintsiyar hannun take ji kamar bata tare da hannun ta saboda yanda yayi mata sanyi, kafin tayi
wani motsi sai ganin hannun tayi cikin na Salim ya rike shi yana gyara zaman shi ya saka dayan
hannun shi yana murza mata dai-dai tsintsiyar hannun, kafin ya bude daga gaban motar yana
dauko wani abu cikin yar roba, sai da ya dangwalo taji yajin abin har cikin idanuwanta, murza
mata yayi sosai a gabaki daya hannun nata har yatsu sannan ya sakar mata hannu.
Man ya rufe ya mayar inda ya dauko, wuyan shi yana yawan rikewa idan yayi zaman karatu
shisa baka raba shi da irin wannan magungunan na shafawa, sai daya tayar da motar sannan
yace mata
"Saura ki murza idon ki"
Dan yasan abinda zata iya ne, murmushi kawai tayi tana jinta wani iri, ko dan yau dinne ranar
farko da hannun shi ya taba nata. A kasan zuciyar ta take jin rashin kyautuwar da yake cikin
hakan duk da Salim din Yaya ne a wajen ta, amman ba muharramin ta bane ba.
"Kishirwa nake ji Allah"
Ta fadi tunda zasu fito taso ta cewa Adee zata sha ruwa sai ga Nanna kuma, sai ta manta
"Akwai ruwa ki dudduba"
Salim ya furta yana jin muryar shi ta fito a bude. Sake rike matukin motar yayi gam ko zai samu
zuciyar shi ta natsu waje daya. Mata ne kalar duk da yaso zai samu, daga lokacin daya fara
binsu zuwa yanzun ba zai kirga hannuwan da ya murza ba. Ko yau hannun mata biyu ne suka
shiga cikin na shi, zuciyar shi batayi tsalle irin haka ba. Baiji kamar yana murza wani abu a cikin
kirjin shi ba.
"Madina ce, Madina... Madina ce"
Shine abinda yake fadi cikin kanshi, ko bai duba komai ba zai duba karancin shekarun ta.
Gudun motar ya kara ko zasu karasa da wuri
"Hamma gudu kakeyi yau, sosai"
Ta furta muryarta na dan rawa saboda bata son gudu a abin hawa ko kadan, hankalinta tashi
yakeyi, yanayin yanda sautin muryarta ya fito yasa shi rage gudun motar, badon tsoron ta ba sai
dan nutsuwar shi da take neman rabuwa da jikin shi. Bai taba jin dadin hango kwanar gidan
Daada irin yau ba, hannuwan shi har rawa sukeyi da ya sauke ta kofar gidan, tsaye yayi ta bude
bayan motar ta dauki kayanta, sai da safen da tayi mishi ma da kai ya amsa mata ita. Sai da
yaga shigar ta gida tukunna ya ja motar yayi kwana yana hawan titi da wani irin yanayi da bashi
da kalaman da zai fassara shi.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*RAI DA KADDARA 1*
10
"Gashi nan Daada, ya fadi me yake ce mun a gabanki kiji, watakila ke kina da kalaman da zaki
fada mishi ya fahimci wannan bashi bane lokacin da ya dace..."
Julde ya karasa maganar yana kallon Nawfal da yake zaune cikin kujerar da take kallon tashi da
yanayin babu abinda zai canza ra'ayina kwance cikin idanuwan shi. Taurin kai ba bakon abu
bane ba, asalima in za'a koma wasu shekaru baya, tabbas da yawan mutane zasu iya cewa ko
kafar shi Nawfal bai kama a taurin kai ba, in harya saka ma ranshi yin abu to babu wanda ya isa
ya sauya mishi ra'ayi
"Idan kuskure ne kubarni, kuskure na ne, ni zanyi dana sani akan duk abinda zai biyo baya.
Kunyi naku bangaren, kun fada mun gaskiya nine dai ban dauka ba"
Yakan fada duk idan an nemi hana shi abinda yayi niyya, shima din idan yana dan ganin kanka
da gashi. Sai dai yau a karo na farko baya son ace taurin kai a ahalin sune, kar ace wannan
ra'ayin rikau din jini yake bi. Saboda Nawfal ya dauko mishi abinda bai taba hangowa ba ko