Showing 33001 words to 36000 words out of 79955 words
Chapter 12 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
a
tunani balle kuma yasan yanda zai shiryama daukar shi
"Aure nake sonyi Daddy, ina so a daura kafin in koma"
Kalaman Nawfal din suka dake shi kamar wanda babbar mota tayi sama da shi tana sauke shi
da wani irin yanayi da bayajin akwai kalaman da zasu kwatanta shi. Kallon Nawfal yayi yana so
yaga ko zolayar shi yake, sai yaga wani yanayi shimfide cikin idanuwan Nawfal din kafin ya dora
zancen shi da
"Tun a waya zan fada maka, sai na bari tunda zan zo bikin Adee, da na zo din ma ina neman ta
inda zan fara fada maka ne..."
Yar dariya ce da Julde ba zaice ga ta inda ta fito ba ta kubce mishi, sosai yake kallon Nawfal
"Shaye-shaye ka fara Bajjo?"
Idanuwan shi Nawfal ya saka cikin na Julde yana fadin
"Daddy..."
Wani numfashi Julde yaja yana saukewa, kwata-kwata ya rasa inda zai ajiye kalaman Nawfal
balle yayi tunani akan su harya sami kalaman furtawa
"Daddy karka ce inje inyi tunani, kar kace in sake dubawa, ko kace shekaru na sunyi karanci..."
Cewar Nawfal din shima yana fitar da numfashi kafin ya dora da
"Watakila duk hakane, amman ina son ta, ko yanzun, ko nan da wasu shekaru babu abinda zai
canza, me yasa zamu jira wasu shekaru in muna da wannan tabbacin?"
Kallon shi kawai Julde yake, cikin tashin hankali yace
"Baka da hankali ko Bajjo? Aure? Kasan meye aure? Yaushe ka fara karatun? Duka nawa kake
da zaka rungumo maganar aure? Da me zaka rike ta? A ina zaka ajiye ta? Ko soyayyar ce ta
hana kai da ita yin wannan tunanin?"
Kai Nawfal yake girgiza mishi, ya bude baki zaiyi bayani Julde ya katse shi
"Waye zai dauki yarinya ya baka? Kana fadamun kafin ka koma kake son a daura aure? Sati
biyu kace zakayi, yau kwanan ka shidda, a cikin sauran kwanakin za'ayi maganar aure har a
daura... Kaga Bajjo baka taba batamun rai ba kar yau ya zama na farko"
Julde ya karasa maganar yana ma Nawfal din wani irin kallo mai cike da tarin ma'anoni. Saboda
tun tasowar Nawfal yana da manyance, yaune rana ta farko daya fara ganin haukan yaron,
rashin hankali na sa'annin shi da kuruciya duk Nawfal baiyi ba, duk da a baya yana danganta
hakan da rashin iyayen shi a kusa, duk da yana iya kokarin ganin ya bashi duk wata kulawa da
zai bukata gwargwadon yanda lokaci ya ara musu
"Zasu bani, sunce zasu bani, kawai zaka ga Kawunta da yake Abuja ne, saboda suna son sanin
ina da dangi a Nigeria, ba wani abu za'a kai ba banda sadaki..."
Kallon da Julde yayi mishi wannan karin na kashedi ne
"Bajjo.."
Haka ma yanda ya kira sunan shi da bai hana shi cigaba da magana ba
"Ina aiki, kudin bamai yawa bane ba, saboda yanayin karatu ba wasu awanni nakeyi ba, itama
kuma tanayi, duka karatu muke, zamu gina kalar rayuwar da muke so a tare... Daddy kar kace
banda hankali, karka ja layi akan abinda addini bai haramta mun ba"
Mikewa Julde yayi
"Daddy..."
Nawfal ya kira muryar shi na karyewa
"Ka taso muje"
Yanda yayi maganar ne yasa Nawfal din bai mishi musu ba ya bi bayan shi, babu wanda yake
magana a motar har suka karasa gidan Daada, ko da ma suka shiga banda sallama babu
abinda Nawfal ya kara cewa ya nemi kujera mai zaman mutum daya ya zauna. Yana kallon
yanda Julde ya amsa tambayar
"Julde, lafiya dai ko?"
Da Daada tayi mishi, da kuma yanda ta kalle shi bayan Julde ya gama magana.
"Idan kaga ban aure ka ba, matsalar daga bangaren ka ne. Zasu tambayeni idan ina son ka,
idan aure ne abinda nake sonyi a yanzun, zasu bani shawara bayan jin amsata, daga karshe
zabi na zasuyi amfani da shi. Haka rayuwar ahalina take, shekaru na sha takwas, sun yarda ina
da 'yan cin da hankalin sanin me ya dace da ni"
Maganganun Murjanatu suka dawo mishi, da gaske matsalar daga bangaren shi ne, shakkun
da yake cikin idanuwan Julde kawai ya isa ya tabbatar mishi da haka, bai kuma son kalmomin
da zaiyi amfani da su wajen gamsar da shi ba. Bayan tsayawa da kafafuwan shi, aure ne abu
na biyu a cikin jerin abubuwan da yake son yi, saboda yana son samun nashi ahalin, wanda duk
ruwa duk rana yasan zasu kasance da shi. Ta ina zai fara fadawa Juldea da Daada cewa
babban tsoron shi a duniya shine kadaici. Shine ranar da duk zai neme su a duniyar shi ya
rasa?
Yanda duk yake son ace ya kira su da nashi shi kadai kaunar su rabata yake da sauran mutane,
yana son abinda zai kira na shi, yana bukatar a kaunace shi, kaunar da ba zaiji tsoron rabata da
kowa ba balle har azo a ture shi daga dan inda yake a tsugunne.
"Idan na tambayeka me ka dawo yi zakace mun bikin Adee, kana da naci Nawfal, bana kaunar
ganin ka kusa da ahalina, in zan iya rabasu da kai ba karamin dadi zanji ba, amman ba zan
taba daina kokarin hakan ba..."
Maganganun Saratu ne suka kara mishi karfin gwiwar tunkarar Julde da tun bayan bikin Adee
yake juyayin yanda zai same shi. Yanda duk yake kaunar su yana da tabbacin soyayyar da take
tsakanin su da Saratu ta girmi wannan, kauna ce da ba zai kwatanta dorata a sikeli da tashi ba
sam
"Aure zanyi Daada..."
Yayi maganar muryar shi na fitowa da wani irin sanyi yana sa Daada jin kamar ya juye mata
bokitin ruwan kankara kafin wani irin zafi ya maye gurbin sanyin da ya ratsa ta, jikinta gabaki
daya ya dauki dumi, zuciyarta na soma wani irin tsalle-tsalle kamar tana neman sabon wajen
zama a sauran jikinta, yanayin bugawar da take har cikin idanuwanta da take kallon Nawfal da
su take jin karfin shi
"Kema kina tunanin banda hankalin ko Daada? Wannan ba shi bane lokacin daya kamata in zo
da maganar aure ba..."
Nawfal ya fadi yana dora da
"Dan Allah idan kina da dalili ya sha bamban dana Daddy..."
Kallon shi dai takeyi zuciyarta na cigaba da dokawa kamar zata fito waje, dalilinta ko daya
bashida alaka da duka tunanin su, dalilinta bata san ta inda zata fara furta shi ba
"Kina jin shi ko Daada, kice wani abu"
Julde ya fadi yana kallonta, da idanuwan shi yake rokonta da ta taimaka mishi don yanayin
Nawfal din kawai ya tabbatar mishi da cewa bawai ya fada mishi bane saboda yana neman
izini, goyon baya yake so kawai, amman ko bai amince ba da wahala idan maganar auren nan
ba zata zama abu na farko da zai haddasa wata tsaga a alakar su ba.
"Yarinyar yar ina ce?"
Daada ta tambaya tana saka Nawfal sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba
"Murjanatu... Sunan ta Murjanatu, duka iyayenta suna zaune ne acan kasar da nake karatu,
amman asalin su yan garin Adamawa ne, dangin su da yawa suna can, wasu suna zaune a
Abuja, suma aikine ya kai babanta can, yayyen ta guda biyu duk suna nan Abuja suma...ni ba
zama zanyi acan ba Daada, zan dawo, zamu dawo tare idan muka gama karatun mu"
Ya karasa maganar yana kallon Julde da har lokacin akwai shakku cikin idanuwan shi
"Daada kiyi magana da yaron nan, da gaske fa yakeyi..."
Baki Daada ta bude sallamar Madina ta katse mata maganar ta, Nawfal ne ya amsa
"Hamma... Daddy"
Cewar Madina cikin sigar gaisuwa
"Zafi nake ji wallahi"
Ta furta tana wucewa nufar hanyar dakinta, sai lokacin suka ga Salim da yayi sallama cikin
budaddiyar muryar shi, daga makaranta ya wuce yaje ya dauko Madina saboda tunaninta ya
hana shi sukuni har a aji, motar shi ta fara tsaitsayawa, dakyar ya iya samun waje gefen titi yayi
parking dinta ya kira mai mishi gyara. Sai da yazo ya bashi mukullin tukunna suka tako shi da
Madina tunda sun kusa gida, tun a hanya take ce mishi zafi take ji tana shiga gida zata fara
watsa ruwa kafin tayi shirin islamiyya. Motar Daddy daya gani ne a wannan lokacin a gidan
Daada yasa shi yanken hukuncin shiga dan yaga ko lafiya, in yaso sai su wuce da Daddy ko bai
mayar da shi makaranta ba ya rage mishi hanya.
Kallon su yayi yana zare takalman shi hadi da shiga cikin dakin, yanayin su bai nuna kome suke
tattaunawa mai dadi bane ba
"Ina wuni"
Ya furta kamar wanda akayiwa dole yana kallon Daada
"Daddy..."
Ya kira, duk yanayin da Nawfal yake ciki bai hana shi kallon Salim ba, daga shi har Madina suna
son kiran sunan mutum a maimakon gaisuwa. Sai dai kafin Daddy yayi magana Salim din ya
juya, baya son hayaniya. Yana da tabbacin kome suke tattaunawa bai shafe shi ba, baya son
sani balle kuma suyi tunanin saka shi ciki.
"Ina zaka je?"
Julde ya tambaya, dan juyawa Salim yayi yana amsawa da
"Naga kuna magana ne..."
Kamar hakan kawai hujja ce da zai bar musu gidan
"Ka dawo ka zauna ayi maganar da kai"
Dan runtsa idanuwan shi yayi yana bude su, dole dai sai sun tsoma shi cikin zancen nan da ya
san bai shafe shi ba ko kadan. A nutse ya taka yana samun hannun kujera ya zauna a kai
"Aure Nawfal yake son yi, so yake a daura kafin ya koma"
Kallon Nawfal din Salim yayi, sai dai a nashi idanuwan babu komai sai mamaki, saboda aure
baya cikin tsarin abubuwan da yake hango rayuwar shi da shi, hayaniyar nan ba zai iya ba.
Amman hakan baya nufin dan wani yana so yayi sai ace kar yayi. Adee ma gashi nan tayi,
kuma har ran shi yayi farin ciki da auren nata
"Kana ganin auren ne abinda kake son yi a wannan matakin na rayuwar ka?"
Salim ya tambaya, kai Nawfal ya jinjina mishi
"Karka amsa ni idan kana da shakku, ka tabbata?"
Kai Nawfal ya sake dagawa, girar da Salim ya daga mishi yasa shi cewa
"Ban fada ma Daddy ba sai da na tabbata, shekara daya ina neman tabbaci a kowacce rana..."
Mikewa Salim yayi ya kalli Daddy
"Nanna tace sanda kukayi aure da kadan ka girmi Bajjo, karkayi amfani da shekarun shi a
matsayin hujja Daddy, in baka da dalili mai karfi karku hana shi..."
Numfasawa yayi saboda kan shi harya fara sarawa da maganar da yake yi
"Ku barshi yayi auren shi..."
Wanda duk yazo da maganar aure a cikin kannan nashi zasu samu dukkan goyon bayan shi,
zaiyi duk wani abu da zai iya wajen ganin basu fada irin rayuwar da yake ciki ba
"Aure zai hanaka biye-biye, zai nutsar da kai waje daya"
Haka yaji wani a ajin su ya fada. Yana da yakinin Nawfal na da dalili mai karfi da yasa yake
sonyin aure a wannan matakin na rayuwar shi, kasar yabari don karatu, Allah kadai yasan kalar
mutanen da suke zagaye da rayuwar shi
"Ka tabbata bakayi dana sanin zabin nan ba Bajjo"
Ya fadi yana saka Nawfal din yin murmushi
"Hamma..."
Hannu ya daga mishi, shi duk irin wannan abubuwan baya son su
"I love you"
Nawfal ya fadi yana fadada murmushin shi ganin yanda Salim din ya bata fuska yana taku biyu
da nufin karasawa kan kujerar da Nawfal yake yana saka shi mikewa babu shiri, kallon shi
Salim yayi cike da kashedi yana ficewa juyawa ya fice daga dakin.
Kamar bai fadu maganganun da zasu canza komai ba
Maganganun da zasu zama silar faruwar komai
Kwallar da Daada taji ta fara tarar mata cikin idanuwa tayi saurin saka hannuwa ta dauke su
kafin ma wani ya kula. Shikenan abinda ta gina a cikin zuciyarta ya rushe, hangenta ya datse
lokaci daya. Wata ta maye wajen da take fatan Madina ce zata zauna a wajen. Yanda kaddara
take wasan kura da rayuwar su a kowanne juye na karya mata zuciya. Ba dan kar tayi sabo ba
da ta tambayi dalilin da yasa ko sau daya rayuwa ba zata tafi kan tsarinta ba.
"Hamma ma yace karku ce a'a, kaji Daddy, dan Allah karka ce a'a..."
Nawfal ya katse ma Daada tunanin da take yana sata kallon Julde da fuskar shi take dauke da
yanayin rasa tudun dafawa
"Daada..."
Ya soma ta girgiza mishi kai
"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, kaje kaga dangin yarinyar kafin ka yanke wani hukunci..."
Murmushin da Nawfal yayi bayan ya dawo inda yake ya zauna na saka zuciyar Daada kara
tsinkewa saboda kamannin shi da Bukar da suka kara fitowa fili. Kafin wani ya sake cewa wani
abu Madina da ta fito cikin shigar islamiyya ta riga su da fadin
"Hamma kana nan har in dawo amman ko?"
Kai Nawfal ya girgiza mata
"Zamu dan fita da Hamma anjima, kilan in dawo dai, me zaki ajiye mun?"
Dariya tayi
"Zan dafa maka kifi"
Kai Nawfal ya jinjina
"Zan dawo"
Dunkule hannunta tayi tana daga mishi babban dan yatsan ta alamar hakan yayi mata
"Daddy na tafi...Daada sai na dawo"
Binta da kallo Daada tayi, Julde ne ma ya iya cewa
"A dawo lafiya"
Wani abune Daada taji yayi mata tsaye a kirjinta, lokaci daya duk wani tunani da takeyi akan
goben Madina ya sauya. Ta ina zata fara yanzun?
"Daada yanzun duka Nawfal nawa yake?"
Julde yace cikin nauyin murya, ko shi da Salim yake magana akan auren wuri da yayi, bawai
zabi aka bashi ba a lokacin, kawai hadasu akayi da Saratu
"Zamanin mu da nasu ba daya bane ba"
Murmushi Daada tayi kirjinta yayi mata nauyi, hakan yasa Nawfal mikewa yana nufar dakin
daya kan kwana ciki duk idan yazo gidan dan ya basu damar yin magana
"Shisa zaka barshi yayi auren shi, zamanin ba daya bane ba...kar kaja maganar nan da shi
Julde...ka kyale shi tunda ba wani abu marar kyau bane ya dauko"
Wani irin numfashi Julde ya sauke, ranshi a jagule yake jin shi, a saman bukatar ta da fatanta
kasancewar Bajjo a cikin su yafi muhimmanci, hana shi aure don bukatar ranta ta cika ba zai
zama sanadin da zata rasa shi gabaki daya ba. Idan har jinin Datti ne yake yawo a jikin Nawfal
to tasan wannan maganar auren ba izinin su yake nema ba, goyon bayan su kawai yake
bukata, ko sun yarda ko basu yarda ba bazai canza komai ba.
"Karka ja maganar nan da shi..."
Ta kara jaddadawa, yanayin muryarta nasa wani abu tsirgama Julde saboda yasan inda
tunaninta yake son kaita
"Ai shikenan..."
Ya furta yana sauke ajiyar zuciya
"Amman ba zai zauna kasar nan ba, yana gama makarantar nan dawowa zaiyi"
Dan murmushin karfin hali Daada tayi
"Daman yace ba zama zaiyi ba"
Sai dai ita kanta ta maimaita kalaman ne ba dan ta aminta da su gabaki daya ba
"Zan dawo Daada"
Taji wannan kalaman har sun isheta a tsayin rayuwar ta, sai dai a duk mutanen da suka furta
mata su Nawfal ne na farko daya fara cikawa, shakkun da take da shi kan kalaman ya dade da
kafa rassa a cikin zuciyarta, dan ya dawo yanzun baya nufin in ya koma zai sake dawowa,
wannan ma tagan shi akan Yelwa. Da zatayi fata ne, fatan kar ya zamana Nawfal bai cika
alkawarin shi na zai dawo ba. Sai dai numfashi kawai ta sauke.
Kowanne rai da nashi kaddarar, yau ma ta sake ganin wannan kaddarar da take tunanin ta
shiga tsakanin Nawfal da Madina kamar yanda tayi fata, shisa ba zata sake wani fatan ba a
yanzun, idan kaddarar Nawfal ta hada da dawowa zai dawo, idan bata hada ba sai dai ta sake
rungumar kaddara a duk yanda tazo mata a karo na ba adadi kenan. Fatanta bashi da tasirin
canza komai.
**
Wayar shi Nawfal ya mika mishi, karba Khalid din yayi
"Na fara gajiya fa...ni bana ma amfani da wayata yanda nake so saboda kun isheni kai da
ita...ka siyi layi Malan"
Dariya Nawfal yayi
"Kai Hamma, yaushe muke isarka din? In ba irin wannan lokacin ba ai bama waya... Layin zai
zama asara tunda ba dadewa zanyi ba. Haka zakayi ta hakuri da mu"
Kai kawai Khalid yake girgiza, ya kalli inda ya ajiye kayan wankin da aka kawo mishi da yamma
"Na kwashe na shirya maka duka wardrobe dinne ma"
Kallon shi Khalid yayi, yana sake kallon yanda dakin ya samu kulawa ta daban tun zuwan
Nawfal din, bawai shara bace bayayi, yana share dakin kusan kullum, kawai dai bashida lokacin
mayar da wasu abubuwan wajen daya dauke su. Nawfal kuma ya kasance cikin jerin mutanen
da suke son ganin komai a tsare, har litattafan shi idan ka duba jakar shi ta makaranta a wani
irin tsare suke, bi da bi. Inda yake ajiye fensiran shi da biro ma daban ne. Ko yaya ka taba mishi
kaya yana dawowa wajen zai nufa ya gyara abin shi yanda yake son ganin shi.
Wajen wardrobe din Khalid ya karasa ya bude yana ganin yanda Nawfal ya shirya komai, harta
kananun wandunan shi layi daban ya saka su. Sai yaji kamar ace karya taba kayan, ya hargitsa
shirin nan
"Aure zanyi Hamma"
Nawfal ya fada cikin sanyin murya, wardrobe din Khalid ya rufe
"Na sani, kowa ma ai aure zaiyi idan lokaci yayi, ko dan kayi