Showing 6001 words to 9000 words out of 79955 words
Chapter 3 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
ba zaka zo ba ai, kawai jiyan na so tahowa..."
Takalma Khalid ya cire yana sake yin sallama ya shiga cikin falon, jakar shi ya fara saukewa
dan a cikin ya zubo duk wani abu da yake tunanin zai bukata, yaji me Julde yace, amman yasan
wahalar dai yazo gidan Daada. Idan ta saka baki dole yabar su su kwana biyu. Fada ne Nanna
zatayi idan ya koma, to ko bai zo ba Nannar shi ba zata rasa dalilin yin fada ba, shisa bai koma
ta gidan ba yayi tahowar shi, zaice mata Daddy ne yabar shi.
"Ina Daada?"
Ya tambaya
"Wai zatayi barka sai ta taho da Madina daga makaranta kuma..."
Kai Khalid ya jinjina yana mikewa
"Ni yunwa nake ji"
Kitchen ya wuce ya zuba abinci iya wanda yake tunanin zai iya cinyewa yana hadowa da wani
filet din daban ya dawo falon, kan kafet ya zauna ya ajiye filattan a gaban shi yana janyi jakar
shi ya bude. Mangwaro ne manya guda biyu ya dauko
"Mangwaron ne a jaka Hamma?"
Nawfal ya fadi yana dorawa da
"Ko dan meye ba za'a samu a jakar ka ba"
Dariya kawai Khalid yayi, inda sabo ya saba jin suna mishi wannan surutun. Kawai yafi yarda da
ya saka duk wani abu da yake tunanin zai iya bukata a cikin jakar shi ta makaranta. Har
paracetamol zaka samu cikin jakar, inka tambaya zaice maka
"Idan naji kaina yana ciwo fa? Tunda ba sanar dani zaiyi kafin ya fara ba"
Akwai ranar da suke dawowa daga islamiyya takalman Salim suka tsinke. Khalid ya zage
aljihun gaban jakar islamiyyar shi ya zaro takalma silifas yana mikawa Salim din yayi gaba abin
shi. Su duka binshi sukayi da kallo na wasu dakika kafin su kwashe da dariya. Wata rana dan
tsokana ko sabulu ne ya kare musu a bandaki zakaji suna
"A duba jakar Khalid ba za'a rasa ba"
Shiru yake ya kyale su kamar yanda yayi ma Nawfal din yanzun. Abincin shi ya gama ci ya tashi
da filattan yana zuwa ya wanke mangwaron, a fridge ya saka saboda Nawfal ya siyo daman, ya
kuma san ba zai sha ba sai yayi sanyi ko yaya ne, idan ma yayankawa akayi zai dauki na shi ya
saka a fridge. Yanda Nawfal baya mura har mamaki abin yake ba Khalid, idan ya sha sanyin da
Nawfal yake sha na rana daya a sati saiya kwanta gadon asibiti. Da ya fito ma bai zauna ba,
dakin da suka saba sauka ya nufa, wanka yayi ya fito ya dawo falon daga shi sai gajeran wando
"Geez Hamma..."
Nawfal ya fadi yana kare idanuwan shi, kallon kan shi Khalid yayi, yanda Nawfal din yayi wani
zai iya zaton babu kaya Khalid ya fito, karamin tsaki yaja
"Kasan shekara bata fi daya ba a tsakanin mu ko? Ba zaka daina ce mun Hamman nan kana
dora mun girma ba"
Batare da Nawfal ya sauke hannun shi daga kare idanuwan shi da yayi ba yace
"Ka dai girmeni, zan daina in ka daina ce mun Bajjo"
Wucewa kawai Khalid yayi abin shi. Mikewa shima Nawfal din yayi, sai da ya kara watsa ruwa,
lokacin daya fito har Khalid ya gama shirin shi ya fita. Shima shiryawa yayi cikin farin yadi harda
hula bula ya saka kamar takamin shi daya dauko. Kafin ma ya fito yaji dawowar su Daada
saboda rakadin Madina da take kwala mishi kira, sanda ya fito Khalid na fadin
"Lallai Madina, kamar baki ganni ba ko?"
Ko kallon shi batayi ba ta ruga da gudu tana fadawa jikin Nawfal hadi da zagaya hannuwanta
jikin kafafun shi
"Hamma na dauka ka tafi kabarni"
Kanta ya shafa
"Nace miki ina nan har ki dawo makaranta ai... Masallaci dai zamu tafi ni da Hamma yanzun mu
dawo, me zan siyo miki?"
Daga kai tayi tana kallon fuskar shi
"Biskit"
Khalid da yake zaune yace
"Ni ina da biskit din ai, ba zan baki ba tunda baki kulani ba"
Juyawa tayi ta kalli Khalid
"Hamma na zai siyo mun ai dai, ko Hamma?"
Kai Nawfal ya jinjina yana dariya
"Ki je ki cire uniform, Daada tayi abinci mai dadi"
Murmushinta ne ya fadada
"Tuwo ta dafa?"
Wannan karin har Khalid dariya yayi da Madina bata ga dalilin su nayin dariya ba. Nawfal yace
anyi abinci mai dadi, shisa tayi tunanin tuwo ne
"Shinkafa"
Lokaci daya fara'ar fuskarta ta dishe tana raba jikinta da Nawfal din
"Shinkafa kuma"
Ta furta ranta a bace tana sake saka su dariya. Daki ta wuce harda jan kafafuwa a dole ranta ya
baci da aka dafa shinkafa ba tuwo ba.
"Daada zama dake yarinyar nan kaf ta kwashe halin tsofaffi, ace ga shinkafa amman tuwo ne a
ranta"
Khalid yace yana dariya
"Ku da bakuyi halin tsofaffin ba ai sai kuyita fama da shinkafar ku, amman ni tuwo zan mana
anjima"
Mikewa Khalid yayi
"Tafdin, aci tuwo lafiya..."
Dan shi baya so, tuwo da danwake na cikin abincin da yunwar da zata saka shi cinsu ba
karama bace ba. Sallama suka yiwa Daada suna fita masallaci.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*RAI DA KADDARA 1*
03
2003
"Adee..."
Ya kira ta da sunan da Khalid ya saka mata tun lokacin baya iya kiran sunan ta, maimakon
Fadila din sai ya gajarce shi zuwa Adee da kowa yake kiranta da shi yanzun
"Ke bakya jin rana?"
Kai ta girgiza mishi, duk rashin magana irin ta Nawfal bai kai Adee ba. Dan ta ita duniya bata
tashi ba, komai da sanyi-sanyi takeyin shi. Kusan ita ta kwaso jikin fulanin. Yanzun haka idan
kaganta ita da Nawfal din babu wanda zaice itace babba, kanta da wahala idan ya kai kafadar
shi, bata da tsayi kuma bata da jiki. Sai hasken fatar da kusan gadon shi sukayi. A gajiye take
jinta, ta rasa inda Daddy ya tsaya da yau baizo daukar su ba. Ta riga da ta saba da anyi hutu ta
fito a bakin gate take samun motar shi yana jiran ta.
"Yau Daddy ya dade..."
Tayi maganar cike da kosawa. Nawfal bai amsa ta ba, baisan me zaice mata ba. Inda yana da
zabi zai zauna a makaranta abin shi. Duk satin duniya sai Daddy yazo ya gansu. Wasu satikan
da Khalid yake zuwa. Sai dai a wani bangaren idan ya tuna zai ga Daada sai yaji komawa gida
ba abu bane mai muni kamar yanda zuciyar shi take fadi. Sati ukune kawai hutun nasu, idan ya
rike numfashin shi kafin ya sauke zaiga kwanakin sun wuce kamar ba'ayi su ba. Zai kokarin
gujema Nanna a satikan.
"Daddy muna ta jiran ka"
Muryar Adee ta katse mishi tunanin da yake, yana daga kai ya kalli Daddy da yake mishi
murmushin da yake mayar mishi. Sai yaji kamar anfi sati rabon da yaga Daddyn saboda yanda
yayi kewar shi
"Ba kun gujeni kun zabi boarding ba yaran nan?"
Dariya sukayi gabaki dayan su. In da zasu biye Julde sam ba zasu hada hanya da makarantar
kwana ba. Ya fiso ya dawo gida ya gansu kafin ya kwanta, idan ya tashi da safe ma ya gansu
kafin ya fita. Saboda su baya tafiya ta wuce kwana biyu, kewar yaran shi zata fara tambayar shi.
Sai dai a lokaci daya kuma bashida zuciyar hana su abinda yaga muraran suna so. Da zai iya
da ba zasu zo makarantar kwana ba, musamman Nawfal da baya kaunar yaga yayi mishi nisa.
Su Adee yaran shine, jinin shine, daga jikin shi suka fita. Ba zai karya ba suna da matsayin da
za'a kai ruwa rana kafin wani ya taka shi a zuciyar shi.
Amman Nawfal, matsayin Nawfal abune da ba zai iya furtawa ba, babu kalaman da zai iya
amfani da su ya misalta yanda yake jin Nawfal gab da zuciyar shi.
"Amana ta ne Julde, yaron nan amanata ne"
Abinda Daada ta dinga jaddada mishi, abinda yake so ya kalli ba ita ba har kowa yanzun yace
"Nawfal amanata ne, ni ya kamata Bukar ya ba amana..."
Saboda Nawfal ya fito daga jikin bukar ne kawai, amman dukkan wata kauna da uba zai yiwa
dan shi itace yake yiwa Nawfal. Kuma yana godewa Allah idan yaga irin murmushin nan a
fuskar Nawfal. Idan yaga yanda Nawfal yake nuna mishi ko duniya zata hade waje daya tare da
mutanen cikinta in dai zata sake budewa to zai riko hannun shi a matsayin Uba.
Soyayyar da take tsakanin su mai girma ce
Sai dai rubutacciyar kaddarar da take tsakanin su tana son danne girman soyayyar
"Bajjo jiba idanuwan ka, kana ma cin abinci?"
Dariya Nawfal yayi me sauti
"Baka ga yanda Adee ta koma ba"
Kallon su Adee tayi
"Rabon da in koma wani abu anfi shekara uku, ina nan yanda nake... Da gaske idanuwan ka
sun rame"
Akwatin shi daya tashi daga kai yake kokarin dauka kafin Julde ya karasa ya karba, baiyi musu
ba ya sakar mishi. Ko siyayya ya fita dasu shi yake rike ledojin, duk yanda zasuyi su karba zai
ce
"Yaushe hannuwan ku zasu iya daukar wannan kayan. Da nauyi sosai"
Da akwatin Adee ya hada ya saka su bayan motar
"Yanayin abincin ka ya sa bana son ka da makarantar kwana Nawfal, nasan wahala zaka sha"
Gaban mota Nawfal ya bude ya shiga. Adee ta hau baya. Daddy ya zagaya ya zauna mazaunin
direba ya rufe murfin. Har ya tayar da motar ya juya yana mitar yanda Nawfal din baya cin
abinci duk ya rame. Murmushi kawai Nawfal yayi
"Ina ci fa Daddy, dan baka gani na kullum ne shisa..."
Kai Julde yake girgizawa, ko satin daya fita da yazo ganin su bai ga yayi zuru-zuru haka ba.
Shiru kawai Nawfal yayi, dan baisan me zaice ba. Julde baisan cewa yafi koshi a makaranta
fiye da gida ba. Tunda yana da zabin na yaci abinda aka dafa ko akasin haka. Idan shinkafa da
miya ne, ya amshi fara yana da kifin gwangwani zai juye a ciki yaci abin shi, wata rana zaici
snacks. A gida bashi da wannan zabin, akwai kifin gwangwani da Daddy kan ce saboda shi
yake siyowa. Kamar kuraye haka su Khalid suke akan nama, shine kawai bayacin nama
Kwata-kwata.
Ba allergy bane ba, kawai bayajin zai iya cin nama tun yana da karancin shekarun shi. Da
yagan shi a cikin miya ma hankalin shi tashi yake, daga kaza har sauran nau'in nama. Baisan a
shekarun yarintar da ba zai iya tunawa ba ko yaci, iya wanda zai tuna kawo yanzun baya hada
hanya da duk wani abu nama. Amman kifin nan bai isa ya taba ba. Idan danyene aka kawo dan
ayi miya. Nanna zata sarrafa shi yanda zai zama haramiyar shi. Shisa bai taba saka rai a duk
wani abu da saiya fito ta hannunta sannan ya iso wajen shi ba.
Idan Adee tazo hutu yana jin dadi, yana cin abinci da miya, da kanta take shiga kitchen tayi
mishi miya ta kuma juye a rubber ta kai mishi dakin shi.
"Me yasa kike haka Nanna?"
Shine tambayar Adee duk idan Nanna tayi kokarin hanata. Wasu ranakun harda duka amman
ko bandaki Nanna ta shiga sai tasan yanda tayi ta kaima Nawfal din wani abu da zaiji dadin shi.
Kifin gwangwani kuwa ita da Khalid suna diba su kai mishi ya ajiye a dakin shi, Khalid da dai-dai
zai dauka. Adee zata iya daukar kwalin gabaki daya, wata rana nata na makaranta randa ta
dawo hutu take zuwa ta kai mishi. Kamar bata ci kwata-kwata tana tarawa ne don shi. Kananun
abubuwa irin wannan yasa yake jinta har ran shi.
"Ka daina jira sai Nanna ta baka abu, idan kagani kana so ka dauka ka tafi abinka"
Ta kan fada mishi wasu lokuttan idan ta kai mishi wani abin. Sai dai yayi dariya, baya son tashin
hankali sam, duk wani abu da zaiyi ya gujema fadan Nanna zaiyi, wani lokacin zai rantse ganin
shi kawai harzuka matar yakeyi. In ba Daddy yana nan ba baya shiga bangaren ta. Ko yunwa
zata kusan halaka shi daya leko ta window yaga tana falo saiya koma, in Khalid yana nan zai
mishi magana ya zubo mishi abinci. Idan baya nan kuma zaici duk abinda yake da shi a
bangaren shi.
Yanzun ma da suka karasa akwatin shi yaja zuwa zai nufi na shi bangaren
"Kamar jira kake Nawfal? Ba zaka shiga kaga Nannar taka ba?"
Murmushi yayi
"Daddy nagaji, zan watsa ruwa tukunna..."
Kai kawai Julde ya daga ya rufe bayan motar yana daukar akawatin Adee da tayi saurin
kamawa tana fadin
"Bajjo zaka ba, akwai wasu kayan shi a ciki, idan ya kwashe naje in dauka"
Ta karasa maganar tana kallon Nawfal da fuskar shi take dauke da alamar tambaya. Kai ta dan
daga mishi, cikin sanyin jiki ya karaso yana jan akwatin nata ya hada da nashi ya nufi bangaren
shi. Ita da Daddy suka wuce cikin gidan tana bashi labarin da bashi da kan gado dan kar ya
tambayeta wanne kayan Nawfal ne a akwatin ta.
*
"Takardun meye wannan?"
Saratu ta tambaya tana rarraba takardun a tsakanin hannuwanta, a karo na babu adadi tana jin
takaicin rashin ilimi, daya daga cikin rashin gatan da maraici yayi mata. Duk da boko ce karshen
abinda aka damu dashi a inda ta tashi, amman ko bakomai an sa taje makarantar allo, babu
wanda ya damu da yanda rayuwarta zata kasance.
"Takardun filayen Bajjo ne za'a siyar da wasu a sai mishi gida"
Wani abu taji ya taso da ba zata ce ga daga inda yake ba, amman dacin shi har akan harshen
ta. Filaye Julde yace, hakan na nufin ba daya ba ba biyu ba tunda yana kiran wasu daga ciki
za'a siyar a sai mishi gida.
"Yana da dukiyar shi Saratu, Nawfal na da dukiyar da tunanin ki ba zai taba hangowa ba. Ba
taimaka mishi nake ba dan ina biya mishi kudinn makaranta, ganin dama ta ne kawai..."
Kalaman Julde suka dawo mata wani lokaci can baya da tayi tsegumi akan yanda zaman
Nawfal din yake karin nauyi akan shi. Ba zata daina wahalar da kwakwalwar ta wajen tunanin
inda Bukar ya samu arziki har haka ba. Bukar fa, Bukar dai daya bar kauyen su da sunan zuwa
neman ilimi. Tsoron kar tunanin ta yayi karadin da wani zaiji shisa take tausar shi, amman akwai
ayar tambaya mai girma akan wannan kudin da Bukar yabar wa Nawfal kamar yanda akwai
babbar tambayar da kowa yaki yarda ya furta akan asalin haihuwar Nawfal.
"Dukiyar Nawfal bata karewa ne? Har nawa yake da..."
Sauran maganganun suka koma mata saboda yanayin juyawar da Julde yayi yana kallon ta
"Meye matsalar ki da dukiyar shi? Sanin yawan ta amfanin me zaiyi miki?"
Kauda kai tayi gefe, abinda take ji yana kara ninkuwa, wannan dukiyar da yake kira Nawfal na
da ita da su Salim take hangota, duk wani jin dadi da yake gidan duniya rayuwar yaranta take
hangowa a ciki.
"Su Khalid ma ya kamata ace suna da gidajen su yanzun tunda kana da halin"
Karamin tsaki Julde ya ja kafin ya taka ya fisge takardun da suke hannunta yana mayarwa cikin
jakar shi. Bai san me yasa daya dawo hannunta kan jakar shi yake fara sauka ba, sai kuma ta
dame shi da tambaye-tambayen da bayaso kan duk wata takarda da zata gani kamar ya aiketa.
"Duk takardar da zaki gani in ba zaki iya karantawa kiji ko ta mecece ba karki sake damuna da
tambaya"
Maganganun shi sunyi mata zafi ba dan kadan ba, duk da ba yau bane rana ta farko da yake
amfani da duk damar da zai samu na goranta mata rashin ilimi kamar laifin nata ne. Karatun
hausar da ya koya daga bayane da dan kalaman turanci daya tsinta akan titi suke kara bashi
damar zaginta haka.
"Ka sama mun makaranta ko ta yaki da jahilci ce..."
Ta furta cikin wata irin sanyin murya. Sosai Julde ya kalleta wannan karin kafin ya kwashe da
dariya yana girgiza kai kawai. Har ranshi dariya ta bashi. Duk tsayin shekarun nan batayi
tunanin shiga makaranta ba sai yanzun? Saboda tana son saka ma shige da ficen shi idanuwa
fiye da yanda takeyi yanzun. Takardun shi ya mayar tsaf ya gyara ya karasa yana samarwa
jakar waje ya ajiye. Fita yayi daga dakin baccin nasu zuwa falo yana jin motsin Adee a kitchen,
hakan yasa shi tunkarar kitchen din ya kuwa ganta tana wanke-wanke.
"Sannu da aiki..."
Da murmushi a fuskarta ta juyo
"Daddy Am... Ba wani aiki bane ba fa"
Kai ya jinjina, komai ma in dai ya danganci hidimar cikin gida amsa daya Adee zata baka, dan
wajenta ba aiki bane ba, har mamakin kokarinta yakeyi a kankantar da take da shi, gashi sanyin
halinta baisa tana da sanyin jiki ba
"Ni ma zan leka Daada ne"
Wannan karin fuskarta cike da roko tace
"Dan Allah zanje... Saura kadan in karasa..."
Dan jim Julde yayi sannan ya amsa
"Bari to in duba su Khalid, nasan zasuje suma sai su shirya duk mu fita gabaki daya"
Murmushi tayi har hakoranta suka bayyana kafin ta juya kamar tana son kara sauri wajen ganin
ta gama da wuri. Ficewa yayi daga bangaren nasu gabaki daya yana nufar nasu Khalid.
Hannun kofar ya kama ya murza yana shiga da sallamar da Nawfal ne