Showing 12001 words to 15000 words out of 79955 words
Chapter 5 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
mu, ko a tunanin ki karki hada mu, ba zan sake cewa daga jikin shi na fito ba.
Amman ni daban ne, ni bashi bane ba, ba zan watsar da ku kamar baku da muhimmanci a
rayuwata ba, karatu zan tafi, karatu zanyi in dawo Daada... Zan dawo"
Ya karasa cikin dishewar murya, ba zai ce ga ranar karshe da yayi kuka ba, amman yanzun
alamun shi yake ji. Ya san zafin da Daada take ji, amman baya son inda tunaninta yake son
daukarta ya kaita balle ta ja shi su tafi tare. Shafine daya dade da rufewa. Abinda ya wuce ko
kayi tunani a kai ba zai canza komai ba, shisa yake zabar barin shi inda yake, a matsayin
abinda ya wuce.
"Zan dawo Daada... Ni bashi bane"
Ya sake fadi, murmushi tayi mai sauti duk da kukan da take ta kokarin tsayarwa. Yanda Nawfal
yake jaddada bambanci da yake tsakanin su da Bukar na karya mata zuciya. Kila tsayin
shekaru yasa shi manta muryar Bukar da take ji a cikin tashi muryar, duk idan zai shigo gidan
da sallama sai zuciyarta ta doka a cikin kirjinta, ko shigowa yayi fuskar Bukar take gani, ko a
dabi'a bambanci da yake tsakanin su ba mai yawa bane ba. Ba ta da karfin fada mishi haka, ko
tana da shi ma ta ina zata fara?
"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi"
Ta furta tana saka Nawfal sauke numfashin da yake rike da shi
"Duk karshen shekara fa anan zanyi shi In shaa Allah..."
Kai Daada ta jinjina, zuciyarta taki natsuwa da tafiyar, in da zai hakura zata fi son haka. Da tana
jin ta isa ta hana shi tafiyar zata hana ko dan gudun da takeyi na kar tarihi ya maimaita kan shi.
"Daada"
Nawfal ya kira, baya son yanayin da yake cikin idanuwan ta da kan fuskarta
"Ina Madina? Ba tace anyi hutun islamiyya ba? Ina taje?"
Ya tambaya cikin son sauya maganar gabaki dayan ta, fuskarta Daada ta goge sosai, dan har
gefen zaninta ta kama tayi amfani da shi. Sai da tayi gyaran murya sannan ta amsa Nawfal din
"Nan bayan gida suke taron suna gobe idan Allah ya kaimu, shine taje tayi musu kunshi, tun jiya
ma take tayi"
Dan dakuna fuska yayi
"Kin sansu ne Daada, kince jiya ma taje fa"
Kai ta jinjina mishi
"Bata nisa ai, suma dan ana mutunci da sai dai su same ta a gida....baki ma nake gudu, kowa
zancen kunshin ta da kuma karancin shekaru yakeyi"
Numfashi Nawfal ya sauke, dole za'ayi magana, idan har kalar zanukan da yake gani tanayi ne
a littafi, tun ba yanzun bama idan yazo ya same ta tana aikin da aka basu a makaranta, littafin
duk da zai dauka ba zaka rasa yar flower da ta zana a jiki ba. Idan yace
"Madina ana ina kika ga wannan zanen?"
Zata amsa shi da
"Ba ko ina fa, kawai na zana ne"
Yanzun da ta dan fara hankali ne take ware litattafan da take zanen a ciki daban dana
makaranta. Yanzun gashi alamu sun nuna kunshi zai iya zame mata sana'a. Kawai baya son ta
da zuwa wani waje da sunan kunshi ne, kowa yazo gida ya same ta. Kasa hakuri yayi sai da
yayi wa Daada mitar
"Bajjo nace maka dan makota ne kawai shisa taje, karka isheni dan Allah... Ka fita ka tambaya
gidan su Salaha, ka kirata ka rabu dani"
Shiru yayi yana gyara zaman shi a kujera, zai dai jira tazo ya ganta sai ya tafi. Alawoyin daya
siyo da hannun shi yake son ya bata, ba kwana zaiyi ba, yanda yake lallaba Julde ba zai sake
tambayar shi wani abu ba har yabar kasar, ciki kuwa harda kwana gidan Daada.
"Rochester institute of technology"
Sunan makarantar ya fado mishi a rai yana saka shi sake sauke numfashi a karo na ba adadi
tun wayewar garin. Wani yanayi yake ji tunda ya ga hotunan makarantar a Café din da yaje
domin yin binciken makarantar da zatayi dai-dai da ra'ayin shi, daga hotunan yake jin kamar
wani abu mai girma da ya wuce karatu zai faru da shi a kasar New York da take yankin amurka,
a cikin makarantar da sunan ta kawai ya sa murmushi kwace mishi.
*
"Sai yanzun kake dawowo Julde? Karfe biyu uku saura? Ka kasa yima kanka fada, idan anyi
maka ba zaka saurara ba"
Muryar Saratu ta daki kunnuwan shi, da alama a hanyar da zata hadaka da dakin baccin su
take tsaye, sake rakubewa yayi jikin bangon kitchen din yana dana sanin shigowar da yayi.
Wani irin kunnuwa gare shi da komin baccin da yakeyi takun tafiya idan akayi kusa da kofar
dakin shi saiya bude ido. Ko dakin da yake kusa da nashi da Lukman ne a ciki yasha shiga da
dare ya watsa mishi zagi saboda yana buga kofar bandakin da yake cikin dakin idan ya farka
zai shiga.
Fadan su Julde da tun bashi da hankalin gane inda ya dosa ya sha tashin shi cikin dare. Daya
fara hankalin gane yawancin maganganun su saiya ke tsintar kan shi da kallon Julde da wasu
irin idanuwa na daban, yana kuma cika da mamaki ko da yaushe na yanda yake Daddyn su a
gaban su, yake cikin rigar mutunci da kamala idan yana gaban su, amman sai ya cire ta ya
yarda daga yayi tunanin sun dauke idanuwan su daga kan shi. Mutuncin da suke tunanin yana
da shi, mutuncin da suke ganin zasu daki kirji a kai a waje shine yake zubarwa da duk rana.
"Meye a jikin matan nan da kake bi da ni na rasa?"
Maganganun Saratu kenan da suka kasa gogewa daga cikin kunnuwan Salim
"Idan na miki bayani ba zaki gane ba, idan ba kafafuwan ki kika saka a takalmana ba..."
Shine amsar da Julde ya bata wani dare da ba zai tuna a cikin wacce shekara ko wata yake ba,
amman dare ne a cikin dubban darare da ba zai taba mantawa da shi ba. Saboda dare ne da
wayewar garin shi ta zo mishi da wani sabon al'amari. Yana son Daddy, soyayya da ba zai taba
iya kwatanta yawanta ba, shisa yake so ya fahimce shi, fahimtar da yake kiran Saratu ta kasa
mishi ita, tabbas ba zata iya saka kafafuwanta a takalman Julde ba, amman shi zai iya. Ba shi
da kyawun sauran yaran gidan, akan ce Khalid duk yafi su kyau. Shima ya yarda, amman ya fi
kowa hasken fata, sannan kuma dogo ne, irin dogayen da ko a cikin masu tsayi sai ka dade
baka gan su ba.
Kuma da yake da tsayi shi din ba siriri bane, dirarren namiji ne da tun yana sakandire yake kula
da yanda yan mata suke son magana da shi, hayaniyar da baya so take saka shi share su.
Amman tunda ya samu gurbin karatu a jami'ar Bayaro bangaren likitanci sai hakan ya kara
haska shi a idanuwan mutane da yawa, baya mu'amala da kowa a ajin, sallama ce take rabasu,
amman tun sakamon jarabawar su ta farko da aka kafe ya zamana shine a saman kowa wajen
samun maki yasa mutane suka kara sanin shi.
Yanda duk yakan so zamewa sai sun saka shi yayi musu bitar wasu cikin darussan da sukan yi,
musamman ma wa'anda suka hada da lissafi. Mata bashi yake kula su ba, sune suke kula shi.
Ranar farko da yayi watsi da duk wani gargadi da zuciyar shi take mishi akan abinda ya kudurci
yi tun safiyar da zai fita bayan yace wa Saratu
"Zan kwana a makaranta yau Nanna, akwai abubuwan da zanyi"
Bai san ya akayi bata ji muryar shi na rawa ba, da kuma tsoron da yake shimfide a cikin
idanuwan shi, watakila da ta tambaye shi menene abinda zaiyi a makaranta a ranar daya canza
komai, amman bata tambaya ba
"Allah ya tsare, kar dai ka zauna da yunwa"
Shine amsar daya samu, daya hadu da Khalid ma a hanyar fitar shi, gefe Khalid din ya rabe ko
magana baiyi mishi ba. Shidin ba ma'abocin ciye-ciye a waje bane ba, ko zai yini a makaranta
ruwane zai siya yayi ta sha. Ko yana gida idan zaiyi kyakkyawan karin safe zai iya kaiwa dare
bai sake saka komai a cikin shi ba
"Dogaye da cikin zani aka sansu, amman kalli dan abincin da ka zubo"
Julde kan tsokane shi, wani lokacin har Saratu na shiga
"Kuma fa tun abincin safe banga ya kara cin komai ba, da abinci ke saka jiki yaron nan tsayin
nan ma ba zaiyi ba"
Murmushi yakan yi ya wuce su, tunda da wahalar gaske kaga ya zauna anci abinci dashi gabaki
daya, baya son yin zagi a gaban su Julde, to kuma ko Lukman saiya saka shi yayi magana
saboda yanda yake tauna abinci kamar yana cin karfe. Duk kudin da Julde zai bashi na
kashewa da kuma na hidimar makaranta bai cika amfani da su ba. Idan Adee tazo gidan yafi
kashe kudin shi, tunda in taga zai fita ba zata rasa cewa ya siyo mata wani abin ba.
Wata yarinya yar asalin garin Kaduna, kabilar Bajju ce ta manne mishi, yana aji biyu tana aji
hudu ko a lokacin, ta sha kai tsaye ta fito mishi da asalin abinda take so daga wajen shi, tunda
tasan ko hauka take soyayya a tsakanin su ba zata yiwuwa ba, idan nashi addinin ya amince
mishi auren mabiyiya wani addinin, ita nata ba zasu amince ba, kuma ga bambanci shekaru a
tsakanin su. Shisa itace zabin farko da yake da shi. Harya gama darasin shi karfe shidda na
yamma yana jin shi kamar akan allurai, karfe tara na dare suka yi da ita.
A masallacin makaranta yayi sallar isha'i, da suka hada idanuwa da dalibin da yayi musu
limancin da sauri ya sauke nashi, saboda ya tsargu, sai yaga kamar yana mai kallon "Nasan
abinda kake shirin aikatawa". Tun daga lokacin da suka fita daga cikin makarantar da Victoria ta
saka hannunta cikin nashi tana dumtsewa yake jin kuskuren da yake a cikin duk wani taku da
zasuyi. Shiya bata kudin da ta kama musu hotel na kwana daya, sai dai suna shiga cikin dakin
ta mayar ta rufe yaji ta rufe da wani abu daya bari a wajen dakin.
Bayan sun fito da safe, kowa yayi wajen shi daban yaji canjin da yayiwa gabaki dayan rayuwar
shi. Dararen da kuma ranakun da suka biyo bayan wannan daren na biyu daya hadu dana farko
wajen yin jagorar canza gabaki daya rayuwar Salim zuwa sukeyi suna wuce mishi da wani irin
yanayi da yake kara dishe wani haske da baisan dashi a kirjin shi ba saida ya fara dakushewa.
Dan ya fahimci Julde ya fara, sai ya budema kan shi wata irin duniya da bai taba sanin akwaita
ba.
Ruwa ya kare a bangaren su, na famfon gidan kuma burtsatse ne ba dadi gare shi ba, shisa ya
shigo bangaren su Julde da fadan su yasa shi tattara komai nashi yabar musu. Da badan
karatun jarabawar da yake yi ba sam ba zai shigo ba, zai hakura da ruwan. Duk maganganun
da suke fadama juna a cikin kunnuwan shi suke direwa suna karasawa zuciyar shi da yanayin
da yake nisantata da son kusantar aure da duk wani rikici da zai biyo bayan shi. Rayuwar
hayaniya ce sam ba zai iya ba, aure kuma cike yake da hayaniya, nashi iyayen babban misali
ne.
Sai da ya sauke numfashi da yaji karar rufe kofa, tsaya yayi sai da ya sake jin budewa da
rufewar kofa a karo na biyu tukunna ya fito daga kitchen din da robar ruwan daya rike kamar ya
sato. A hankali yaja kofar gidan bayan ya fita, iska yake shaka yana fitarwa kamar mai son raba
huhun shi da iskar daya shaka a cikin gidan. Yau ya kara fahimtar Julde, akwai shirun da yake
tattare da dayar rigar dayake sakawa a wajen gidan aure, ba mai tsayi bane shirun, na kankanin
lokaci ne, amman shiru ne, shi da baya tare da hayaniyar aure yakan bukaci wannan shirun.
Balle kuma Julde, shisa yanzun da yake komawa bangaren su yake kara hango tazarar da take
tsakanin shi da kusantar duk wani abu daya danganci aure.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*RAI DA KADDARA 1*
05
Ya bude zip din jakar shi ya rufe ya kai sau goma sha biyar ko fiye da hakan, da ba sabuwar
jaka bace ba shi kan shi yasan zip din da ya samu matsala. Ba tunani yake ya manta wani abu
ba, amman jakar tayi mishi kadan, abubuwan da yake son dauka sun girmi wajen da ya rage a
cikin jakar. Daya daga cikin misalin abubuwan ya hada da Khalid da yake tsaye ya jingina
bayan shi da bangon dakin
"Har yanzun fushi kake mun Hamma? Jirgi zan hau, komai zai iya faruwa..."
Kallon da Khalid ya watsa mishi yana saka sauran maganar koma mishi, sai da ya hadiyi yawu
kafin ya sake cewa
"Idan kasan zakayi kewa ta har haka me yasa da Daddy yace mu tafi tare kaqi?"
Numfashi Khalid ya sauke, shi bai taba tunanin barin gida da sunan karatu ba, asalima banda
jami'ar Bayero babu wani waje da yake sha'awar zuwa da sunan karatu. Shima fannin ilimin
kimiyya da fasaha ya karanta, baiyi tunani mai tsayi ba da ya tashi neman gurbin karatu wajen
cike bangaren magunguna wato Pharmacy a matsayin zabin shi na farko. Duk lokacin da zai
ma Nawfal din zancen zabin makaranta sai yayi kokari wajen canza maganar kamar baya son
amsawa.
Shisa ya kyale shi, a zaton shi Nawfal na daya daga cikin mutanen da sukan kasa tsaida
hankalin su waje daya akan zaben makaranta ko kuma fannin da zasu karanta. Akwai su a ajin
su, dan da yawa har suka siyi Jamb suna tararrabin abinda zasu cike, wasu suna da zabi fiye
da biyu, wasu kuma basu da ra'ayin kansu ne sai abinda iyaye suka cusa musu tun tasowa. Ya
san Nawfal baya daya daga ciki, banda shi baya tunanin wani ya taba tambayar shi abinda yake
son zama ko inda yake son yin karatun shi.
Nawfal ya sani, shine mutum na karshe da zaiki goyon bayan shi akan duk wani zabi da zaiyi, in
har zabin ba wanda zai cutar da shi bane ba. Zai karya idan yace jin zancen zabin Nawfal din
daga wajen Julde bai mishi ciwo ba
"Kasar waje Bajjo yake son tafiya, ko zaka duba makarantar kaga idan akwai abinda kake son
karanta sai ku tafi tare, bana son ya tafi shi kadai"
Shine abinda Julden ya fadi da Khalid bai ma bari ya karasa ba ya fara girgiza mishi kai
"Daddy ni bana sha'awar zuwa ko ina, anan zan zauna. Shi Bajjon da ya zabi tafiya Allah ya
taimaka, ba yaro bane ba, na tabbata zai iya kula da kan shi"
Amsar da ya ba Julde kenan yana mikewa yabar wajen zuwa bangaren su. A ranar ko da
Nawfal yabi bayan shi ya bude baki bai barshi ya furta komai ba
"Kar mu fara maganar nan Nawfal, baka so in sani ba, Daddy bai san baka so in san tsarin da
kayi wa rayuwar ka ba shisa ya fadamun, karka damu, in da akayi maganar nan na barta..."
Rubutun shi ya ci gaba da yi duk da a lokacin in zaka saka mishi wuka baisan me yake
rubutawa ba, Nawfal ya dade a tsaye kafin ya fita daga dakin. Duk wani shirye-shiryen tafiyar
Nawfal din da ake tayi baya saka baki a ciki. Kwanakin dai ne bai kula suna ta gudu tare da su a
ciki ba sai yau da tun safe yake jin zazzabi ya rufe mishi jiki ganin Nawfal na ta hada jaka.
Zazzabi ne mai hade da dana sani na satikan daya dauka yana fushin da ya ga rashin amfanin
shi a yanzun.
"Ban ki fada maka ina son barin kasar ba dan bana son kasan plans dina Hamma, wallahi ba
dan bana so ka sani bane ba...na kasa ne saboda zan dinga hango yau, bana son idan na kalle
ka in dinga jin ba kasar nan kawai zan bari ba har da kai..."
Iska Nawfal ya furzar ta bakin shi da yake jin kamar idan yaja numfashi maimakon ya wuce inda
ya kamata sai iskar ta dawo tana taruwa cikin bakin na shi, ga zufa da yake ji har a bayan
kunnuwan shi da tafukan hannuwan shi
"Kuma kana fada, ba zakayi ni sa da gida ba, ko da sunan aiki ba zaka iya barin gida ba shisa
kake mamakin yanda bi da Adee muka iya tafiya makarantar kwana, ban san ya zan fara fada
maka batare da na roke ka mu tafi tare ba, Hamma ba zan so kaina da yawa ba, dan Allah kayi
hakuri..."
Gyaran murya Khalid yayi dan bai yarda da kanshi yayi magana kai tsaye ba, yanda yaga
zuciyar Nawfal shimfide a cikin idanuwan shi, ya kuma ganta a karye, idan ya nuna alamar rauni
bai da tabbas kan abinda zai faru
"Me yasa sai wata kasar? Wani garin bai isa ba?"
Dan daga kafadu Nawfal yayi
"Kullum jina nake kamar tsuntsu, ina da fuka-fukai, amman ina tsare cikin keji tun haihuwata,
nasan suna da wani amfani tunda an halliceni da su, amman babu sarari a kejin da nake balle
in gwada miqe su har in san ya kamata in tashi..."
Sosai Nawfal yake kallon Khalid, kalaman shi yake zabe iya yanda zai iya, yana so koda kowa
bai fahimce shi ba Khalid ya fahimta
"Hamma ina numfashi kullum, amman