Showing 69001 words to 72000 words out of 79955 words
Chapter 24 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
raji'un"
Ya iya furtawa saboda ba zaiga hoton da baisan yanda zai fara goge shi daga cikin kan shi ba,
jikin shi ko ina bari yake saboda tashin hankali. Wacce irin bakar rana ce wannan yaci karo da
ita? Me zai gani? Salim? Hamman shi? Hamman shi da kimar shi take kamar jirgin sama a
wajen shi har sai ya daga kai yake iya hango nisanta, me yasa ya zo wajen nan? Me yasa kimar
nan zata ruguzo a saman kan shi kamar daman bata da nauyin rike kanta a saman shi? Me
yasa Salim ma zai karya mishi zuciya haka?
"Kar kayi saurin yanke hukunci"
Wata murya da bata da kuzari ta karfafe shi, bayajin wani lokaci mai tsayi ya wuce, amman ji
yayi kamar zamani ne ya zo ya wuce yana nan zaune saboda tashin hankali, sanda ya daga kai
baiga yarinyar ba, baiga Salim ba sai motar shi da yake ja yana fita daga wajen. Ko ringing din
wayar shi Khalid baiji ba, Allah ne ya taimaka Micheal din ya hango shi zaune cikin mota, idan
yace ga yaren da suka gaisa ciki zaiyi karya, ya karbi file din dai, ko sallamar kirki baya tunanin
yayi da Micheal balle ya tambaye shi ya shirye-shiryen bikin shi suke tafiya. Duka wannan
abubuwane da muhimmanci yayi baya yana tazara mai nisa da abinda Khalid din yake ji.
Da sanyin da jikin shi yayi yake tuki har gida. So kawai yake ya shiga ya tambayi Salim dan ya
karyata mishi abinda ya gani, dan ya tabbatar ma da tunanin shi abinda ya gani a wajen Guest
Inn din ne kawai. Amman sai shirun Khalid din ya karfafa tunanin shi yana ruguza wani bangare
na zuciyar shi. Saura wa kuma ya rage yayi disappointing din shi haka? Sosai zuciyar shi ta
sosu, ba farin cikin duniya kawai Salim yake wasa da shi ba, har lahirar shi ma lilo takeyi
amman yake rayuwa kullum kamar babu mala'iku har biyu a kowanne gefen shi, kamar baisan
suna rubuta duk wani motsin shi ba.
Rashin tsoro irin na dan adam abune mai ban al'ajabi, ko wani abin Khalid yayi da yasan babu
kyau sai yazo kwanciya yaji kirjin shi na bugawa cike da taraddadi, kan shi na wankewa yana
barin tunani kwara daya tak, zai iya runtae idanuwan shi na har abada, baccin da zaiyi da nufin
ya wayi gari zai iya bude idanuwan shi a cikin kabari. Ta ya mutane masu tarin zunnubai suke
rayuwar yau da kullum kamar ba zasu hadu da Allah ba? Abin da al'ajabi, ba kadan ba. Laifin
na Salim ne amman shi ya kasa bacci duk tsayin daren, ga zuciyar shi da take zafi.
Kwanakin nan biyu haka yake yin su a daddafe kawai, ko da sukai waya da Nawfal
shekaranjiyan wajen tara sai da ya tambaye shi me yake damun shi
"Gajiya ce kawai"
Amman ya san Nawfal bai yarda ba shisa ya dawo garin jiya. Yanayin yanda yake ta tsokanar
shi yana sanar mishi da cewa ko meye yake damun shi in dai yana son su tattauna Nawfal din a
shirye yake da ya saurare shi, in kuma yana ganin zai iya shawo kan abin shi kadai ma Nawfal
din ba zai matsa ba. Tsintar kan shi yayi da godewa Allah da Nawfal ya kasance jinin shi,
mutum daya kuma da yake da yakini mai karfi akan cewa ba zai taba karya mishi zuciya kamar
yanda kowa yake ta zabar yi ba.
Ganin Salim din na ta wasa da cokalin shi cikin abinci yasa Khalid ture na shi plate din, daman
ba wai yana jin wata yunwa bane ba
"Har kayi me? Shisa kake ta kara ramewa kullum"
Julde ya fadi, murmushin karfin hali Khalid yayi, kafin ya amsa Lukman ya riga shi da fadin
"Meye babu a fuskar ka Daddy?"
Saboda tun dazun yake ganin kamar akwai abinda ya kamata ace akwai a fuskar Julden, hakan
yasa daga Khalid har Salim kallon Julde kafin Khalid ya kwashe da dariya
"Inalillahi... Daddy waye yai maka wannan yankar kaunar?"
Murmushi Julde yayi, bai san dalili ba, amman ji yayi kamar idan ya aske gashin fuskar zai rage
nauyin da kirjin shi yayi, kamar ita kanta sumar na da wani nauyi na daban da bai taba sani ba,
banda iska da yake ji tana shigar mishi fuska ta ko ina babu abinda cire gashin yayi mishi
"Ni na aske abu na, furfura ta fara cika shi, shine na aske sai baki ya fito"
Wannan karin har Salim sai da yayi dariya
"Nanna kina ganin shi ya aske?"
Khalid ya tambaya, murmushi Saratu tayi, bata cika saka musu baki a irin wannan lokacin ba,
saboda a cikin shine take samun ganin dariyar Julde, ta kuma ji zolayar shi da bai taba
gwadawa a kanta ba, sai taga kamar wani ne daban ba mijin da ta aura ba, ba mijin da take
zaune da shi ba kuma. Ko dan wannan ba mijin ta bane ba, mahaifi ne tare da yaran shi, ubane
da kaunar yayan shi take a bayyane.
"Ko da ya aske din dai babu wanda zai nuna mishi kyau a cikin ku"
Lukman ne ya fitar da wani sauti a kasan makoshin shi da ya sake saka Khalid fashewa da
dariya
"Son kai dai Nanna"
Cewar Salim
"Son Daddy dai zaka ce"
Khalid ya amsa suna hada ido, yanayin da yake tsakanin su na sake giftawa kamar labulen da
su kadai suke ganin shi. Kamar yanayin ya ba Khalid damar mikewa dai-dai lokacin da suka
fara jiyo kiran sallar isha'i
"A gajiye nake ni kam, ina dawowa sallah zan kwanta. Sai da safen ku"
Cewar Khalid din yana dan amsa tambayar Nanna da take mishi na ko karfe nawa zai fita da
safe kafin ya juya yana barin dakin. Sai dai bai koyi minti biyu ba yaji takun tafiya a bayan shi da
yasa shi juyawa
"Khalid..."
Salim ya furta sauran kalaman da bai gama hadawa a cikin kan shi ba suna makalewa, wani
abu ya kamata yace, amman shi din ba mai yawan magana bane tun da can, balle kuma
magana irin wannan da bai taba tunanin zata hadasu da Khalid ba. Murmushin da bai kai cikin
idanuwan shi ba Khalid yayi
"Bani zaka yiwa bayani ba Hamma, ba fahimta ko yafiya ta zaka nema ba, bani da iko akan
anjiman ka balle har a tsallaka lahirar ka...kawai kabari, ko menene dalilin ka bashi da tushe, ka
daina, ka roki Allah ya yafe maka kafin lokaci yayi maka karanci..."
Idan ya fito da sanyin jiki, kalaman Khalid sun sa yaji kamar kashin gwiwar shi ya sulale zuwa
wani waje da bai sani ba
"Zanje sallah..."
Khalid din ya furta yana sake juyawa yabar Salim a tsaye. Ya so ya shiga bangaren su ya sake
daura alwala, amman yana gudun kar Salim din ya sake bin shi, shisa ya fice daga gidan. A
masallaci yayi alwalar, ana idarwa ya gama lazumin bayan sallah ya daga hannuwan shi sama
sai kanshi yayi wani irin wayam, ga tarin bukatu a zuciyar shi amman kwakwalwar shi taki bashi
hadin kai. Ya dauki lokaci da hannayen shi a sama, zuciyar shi a bude cike da yakini da kuma
sallamawa har sai da yaji wani sanyi da tsoron Allah ya ratsa sassan jikin shi tukunna ya mike.
Da ya koma gida kai tsaye dakin su ya wuce, ya samu Nawfal zaune kan kujerar teburin daya
dora hannayen shi yana latsa waya da kofin da Khalid ya san shayi ne a ciki. In zai farkawa
biyar zai iya ganin Nawfal din a zaune kamar ba dare ba
"Wai kai ba zakayi bacci bane ka huta ma ran ka?"
Ya tambaye shi kwanaki hudu bayan ya zo
"Bana ji ne Hamma, bambanci lokacin nan yana ta bani wahala... Gara in dan rage wani abin da
safe na rama In shaa Allah"
Amman hakan baya hana shi yi mishi magana idan ya farka ya ga dare ya raba. Ko ba zai bacci
ba dai ya kwanta kwakwalwar shi ta dan samu hutu. Zai so ya watsa ruwa amman kasala yake
ji, shisa ya rage kayan jikin shi yana samun T-shirt marar nauyi ya dora akan singlet din shi, sai
gajeran wando yabi lafiyar gadon da ya sha gyara sai kamshi ke tashi. Shi kanshi dakin yafi
mishi dadi idan Nawfal yana nan, matar shi dai ta huta, Khalid din ya sani. Tsantsainin Nawfal
ba zai barshi ya jira sai tayi gyaran gida ba, tana ma iyayi ya sake maimaitawa, dan duk yanda
zakayi shara sai kaga ya kara yin wata.
Addu'ar bacci yayi, yana runtsa idanuwan shi, a hankali yake motsa labban shi yana fara
karanta ayoyin da suke cikin Suratul-Mulk dan neman saukin kwanciyar kabari, baya taba
mantawa tunda ya mallaki hankalin shi ya kuma ci karo da muhimmancin hakan, jarabawar
duniya ma neman hanyoyin samun saukin ta yake, balle kuma samun lahira da komai ya zo
mana a bayyane. Daya dire cikon ayar karshe harya juya baya sai kuma ya sake juyowa yana
bude idanuwan shi akan Nawfal da yake zaune yana danna wayar shi har lokacin
"Bajjo..."
Ya kira da sanyin murya, yana kasa tsayawa ma Nawfal din ya amsa shi dan harya dan juyo da
kai
"Dole ne sai yara sun biya zunuban iyayen su? Kana ganin Allah zai iya duba zuciyar yaran yaki
jarabtar su?"
Girar Nawfal ta hade waje daya cike da mamaki da kuma son fahimtar in da tambayar Khalid
din ta dosa
"Kamar zina da akace maiko take da shi, kana tunanin yara zasu iya kubuce ma wannan
maikon kuwa?"
Wannan karin akwai bayanannen tsoro a muryar Khalid da yasa Nawfal mika mishi hankalin shi
duka, a iya sanin shi Khalid bashi da wani hali marar kyau, ko a mugun mafarki kuwa ba zai
hada shi da aikata laifi mai munin zina ba. Shisa yake neman dalilin da tunanin Khalid din zai
dibe shi zuwa inda yake yanzun har ma wannan tambayoyin su hade mishi
"Banajin na fahimci tambayar ka Hamma..."
Nawfal ya fadi da dukkanin gaskiyar shi, numfashi mai nauyi Khalid ya sauke, idanuwan shi cike
da wani firgici da Nawfal ya rasa dalilin shi hadi da furta
"Hmmm..."
Sosai Nawfal ya juya dan saida ya motsa kujerar da yake da kai
"Banda amsar tambayar ka, abu daya na sani, kaima kuma ka sani, babu wani abu da yafi
karfin Allah, wanda Ya so a cikin kowanne hali zai iya kubutar da shi"
Kai Khalid ya jinjina ma Nawfal yana juyawa da alamar da take nuna ya gama maganar. Mikewa
Nawfal din yayi ya karasa wajen kwan fitilar dakin ya kashe ma Khalid din, ba zai daice ya
kashe ba, amman yasan hasken zai iya takura mishi. Ya bada wajen mintina sha biyar a
tsakani, baiji Khalid din ya motsa ba, cikin sanda ya karasa ya leqa fuskar Khalid, idanuwan shi
a rufe suke, da alama bacci ya dauke shi. Abin rufa Nawfal yaja ya rufe shi yana tsaye akan shi,
duk wata addu'a ta tsari da neman sauki sai da yayi yana tofa mishi, baisan me ya same shi ba,
amman baya son tsoron da ya gani a cikin idanuwan shi
"Allah zai kare mun kai Hamma, daga dukkan abin ki"
Ya furta a kasan numfashin shi yana komawa ya zauna, Khalid na jin shi, yana ji yaja mayafi ya
rufa mishi, yana jin addu'ar daya tofa mishi, haka kuma kalaman shi da suka rufe Khalid din ruf,
fiye da mayafin da Nawfal ya rufa mishi, kirjin shi yanayin nauyi da sirrin da yake tunanin shi
kadai ya san da shi.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149
*RAI DA KADDARA 1*
19
Mutane zasu tsammaci ganin kunshi a hannuwanta ko da yaushe kasancewar ta wadda ta iya.
Amman tana daya daga cikin mutanen da lalle bai dame su ba sam. Asalima sai ta dade ko a
farcenta bata saka ba, baifi kagani a jikin babban yatsan ta da kuma mabiyin shi, shima baka
raba kowacce mai kunshi da shi, sai dai wanda suke saka safar hannu. Tana da su da yawa, irin
na asibiti ma, kwali daya Salim ya bata, rashin sabo yasa duk sai taji ta takura, kwarkwaron
kunshin ma yana zamewa daga hannunta idan ta saka. Tun yana mitar baya son ganin tana
bata hannun ta harya gaji.
Yau din ma sauran wanda ya rage a kwarkwaron da tayiwa wata yar islamiyyar su ne kawai ta
zauna tana zanawa a jikin hannun ta, ba wani mai yawa bane ba, amman ko ita da tayi sai taga
yayi mata kyau bayan ta gama tun ma bai bushe ba, hannun harya zama na mace, tana tunanin
yanda in ta wanke lallen har wasu zobuna masu yawa da Adee ta bata zata dauko ta bude
kwalin ta gwada ko da kwara biyune a yatsun taga yanda zasuyi. Adee akwai son kwalliya,
kuma kyau takeyi ma Madinar, zobe zaka gani a kasa da saman yatsun ta, in gidanta kaje
yanzun da tayi aure ma har a yatsunta biyu na kafar dama zaka sameta da su ta saka.
Daki ta koma ta dauki remote sannan ta samu kujera ta zauna duk da la'asar ake kira tunda
Allah ya hutar da ita, shisa ma ta zana kunshin ta hankali a kwance. Tashar India ta kai ana
tsakiyar yin film din Kabhi Khushi Kabhie Gham, labarin film din take ji ana yawan yi, tana kuma
sakawa a ranta da zata nema ta kalla, sai dai ba littafi bane ba, film ne. Kallo na karshen
abubuwan da ta damu da su, idan tana zaune kamar yanzun ma tana iya taita wasa da remote
din tana rasa inda zata tsaya ta kalla, karshe tashar labarai ko documentary ne abinda zaiyi
nasarar rike hankalin ta. Da yake ana rubuta fassarar da turanci sai ta bama tv din dukkan
nutsuwar ta.
Tana iya juyo sautin bugun zuciyarta da ya zarta har cikin kunnuwan ta da wani yanayi da ba zai
misaltu ba, bakinta na gaurayewa da dandanon gishirin da bata san inda ta samo shi ba, ko
dandanon hawayen da take jine cike taf da idanuwan ta da take kokarin hanawa su zubo suka
koma suka gangara cikin bakinta, shakuwar da take tsakanin jarumin film din da mahaifiyar shi
na jijjiga duniyar da take zaune tana sa hanjinta yamutsawa kamar suna son sake mazauni
saboda hargitsin da take ji har su ya tarar a cikin nata. Idan tace Yelwa bata fado mata lokaci
zuwa lokaci tun kafin ta karanta wasikar nan zai zamana karya, duk lokacin da idanuwanta zasu
sauka akan wani shafin littafi da yake magana kan mahaifiya sai tunanin tata ya kutsa mata.
Haka idan taji wasu suna labarin ta su, ba zatace ta rasa nagartacciyar soyayya da kulawa a
wajen Daada ba, amman akwai ramin da take ji a zuciyar ta kamar wajen an halicce shi domin
Yelwa ne, kasancewar ta a rayuwar ta ko akasin hakan baya nufin wani zai taba iya zama a
gurin. Sai take jin da za'a bata dama guda daya zata koma ta goge ranar da taga wasikar nan,
yanda duk ta so ta koma dai-dai, ta koma kamar kafin ta ga wasikar nan sai ta kasa. Abu kadan
daya danganci mahaifiya take jin yanda yake samun tasirin raunana mata zuciya.
Ko jiya taga kallon da Daada take yiwa Julde, batasan ko raunin zuciyarta bane ya sa ta ganin
zuciyar Daada a cikin idanuwanta duk idan tana kallon Julde, kaman in dai yana karkashin
kulawarta zata kareshi daga dukkan wani abu da yake ikon ta, kamar rayuwar ta na da
muhimmanci ne tare da dan nata. Da bata gani, amman yanzun tana ganin wannan kaunar,
murmushin Daada ma akwai banbanci a cikin shi idan Julden yana kusa. Tsakanin mahaifiya da
yaranta wata sirrantacciyar kauna ce da Allah daya halitta musu ne kawai Ya san girman ta.
Sai take tunanin meye bambancin sauran iyaye da tata mahaifiyar? Me yasa tabar ta? Ko dan
rashin tabbacin da yake cikin halarcin haihuwar ta? Idan ta duba wannan kawai ya isa ya zama
babban dalili a wajen Yelwa, takan ji kamar tana neman wani uzuri ne da zai saukaka mata
abinda takeji. Salim yace ta jira Daada idan ta shirya zata fada mata komai a lokacin da take
tunanin ya dace, tana kuma kokarin ganin tayi hakan, sai dai da duk wata rana da zata wuce da
yanda tarin tambayoyin ta suke kara ninkuwa. Har mamaki takeyi yanda Daada ta kasa karantar
tambayoyin a cikin idanuwanta.
Wanne lokaci ne ya dace? Yaushe ne Daada zata fada mata komai? Ko ma tana da niyyar fada
mata din? Duka amsoshin tambayoyin nata na wajen Daada. Zuciyarta da nauyi kamar an dora
mata dutse ta kai hannu ta dauki remote din tana canza tashar. Mikewa ma tayi tana komawa
daki, bayi ta wuce ta wanke kunshin da yanzun ya fita daga kanta saboda zuciyar ta da take ji
cunkushe. Sai kewar Salim ta danneta har tana sakata karasawa kan gadon dakin nata ta dauki
wayarta ta duba taga bai kirata ba, bai kuma tura mata ko da text bane ba. Sun yi waya da safe,
amman gaisawa kawai sukayi, tun shekaranjiya rabon da ta saka shi a idanuwanta.
Jikin ta yana bata akwai abinda yake damun shi, amman shi din ba mai yawan magana bane
ba, bai taba bude baki yace mata ga damuwar shi ba, sai dai ta karanci yanayin shu taita jan shi
da hirarrakin da take tunanin zasu saka shi murmushi ko kadan ne, ta kuma dinga tuna mishi
yaci wani abu, dan in yana cikin yanayi