Showing 1 words to 3000 words out of 182238 words
Chapter 1 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
RAYUWA DA GIƁI
Batul Mamman💖
Bismillahir Rahmanir Rahim
_In loving memory of Aisha Aminu Balbalo (mai lalurar numfashi da take sayen cylinder ɗin oxygen wadda aka fi sani da Carofee). Allah Ya jiƙanta Ya gafarta mata. Amin_
***
Wanki take a tsakar gida tana sauraron hirar mahaifiyarta da ƙanwarta Zee. Ba ta saka musu baki saboda tun ainihinta ba mai son hayaniya bace. Sai murmushi kawai idan sun yi abin dariya.
"Wannan wankin naki zai sami shanya kuwa Hamdi?"
Sararin samaniyar da Yaya ta kalla ita da Zee su ka zuba wa ido. Ga dai rana ana gani tana haska ko ina. Amma idan mutum ya miƙar da ganinsa zai yi tozali da baƙin hadarin da yake ta gangami daga nesa. Tunanin taƙaita wankin ta soma yi yadda wanda ta gama za su sami wuri akan ƙofofin ɗakunan gidan su ka ji sallamar wasu mata.
Da farinciki Yaya ta tashi daga kan tabarmar da take zaune ta nufi zaure tana cangala ƙafarta ta hagu wadda shan inna (polio) ya cinye. Da alama baƙin da aka kwana aka wuni ana zancen zuwansu ne su ka ƙaraso.
"Maraba lale da Altine."
Shewar Yaya da baƙuwar su ka ji daga zauren da taje ta taro su kafin su dawo tsakar gidan hannun da baƙuwar a kafaɗarta.
"Oh ni jikar mutum huɗu. Ashe rai kan ga rai Jinjin? Ya bayan rabuwa?" Matar ta jero mata tambayoyi su na daga tsaye.
"Sai alkhairi. Rayuwar nan sai godiyar Allah." Su ka sake rungumar juna su na dariya.
Ƴan matan da baƙuwar tasu mai suna Altine ta zo dasu da kuma Hamdi da Zee sai su ka tsaya kallon abin al'ajabi. Labaran da su ke ji game da juna ashe gaskiya ne don ga zahiri sun gani. Iyayen nasu sun yi zumunci sosai kafin a haifesu lokacin suna zaman Agege a Lagos. Abubuwa da dama sun faru waɗanda su ka yi sanadiyar dawowar su Jinjin garin haihuwarsu Kano. Ƙarancin hanyoyin sadarwa da faɗi tashin yau da gobe ya dakusar da wannan zumunta ta makwabtakar gidan haya ɗaya. Shekara bakwai kenan da dawowar su Altine Kano su ma amma basu taɓa haɗuwa ba sai da Allah Ya haɗa mazansu da wani da ya san duk su biyun. A wurinsa su ka sami labari harma da lambobin wayar juna.
Altine kakkaurar mata ce mai fara'a kamar gonar auduga. Mijinta Maje mahauci ne yana sana'arsa ta fawa. Da yake kakanninsu ɗaya duk su na da billensu na gadon sana'ar a kuncinsu. Akwai ta da kazar kazar don in tana abu sai ka rantse wannan jikin ba nata bane. Da wannan yanayin nata ta ja Jinjin a jiki duk da farkon zuwanta saboda yanayin mijinta da lalurarta bata sakewa da kowa. A gidan nasu na iyali goma sha biyu ƴan ka zo na zo aka taso ta a gaba da tsokana. Don ma maigidan nata ba ƙyalle bane. Bakinsa kaɗai ya ishe su ƙwatar kai. Idan ya fita ne dai ko banɗaki ta fito zagawa an dinga dariyar tafiyarta kenan. Sai da Altine ta gama lura da ita ta gane tsoron ƴan gidan da su ke duk hausawa take yi. Sai ta zame mata baki harma da hannuwa. Don idan abin bawa hammata iska ya kama dukan tsiya take yiwa mace la'ada waje. Ɗan Altine ɗaya lokacin ita kuma Jinjin da ciki su ka rabu.
"Ina Baballe kuwa?" Cewar Yaya cikin yanayi na kewa.
Da jindaɗi Altine wadda ƴaƴanta su ke kira Iyaa (kamar yadda Yarbawa su ke jan sunan) ta bata amsa.
"Ya tafi bautar ƙasa Binuwe (Benue)"
"Allah Sarki. Shekara kwana. Yaron da na tafi na bari yana tatata"
Dariya su ka yi farinciki da jindaɗinsu ba zai kwatantu ba. Duk wannan abin da su ke yi Hamdi da babbar cikin ƴan matan Iyaa kallon gane juna su ke yi. Ganewa mai cike da tsoro da fargaba a ɓangaren kowacce bisa dalilai daban daban. Kamar iyayen sun sani kuwa su ka zaɓi wannan lokacin wurin gabatarwa juna ƴaƴan nasu.
"Kina nufin da cikin Hamdi ku ka taho?"
"A'a, yayarsu dai Sajida. Tsiranta da Hamdi ma ya kai shekara biyar. Bata nan ne. Ta tafi Abuja gidan ƴar yayata da ta haihu."
Iyaa ta murmusa "Allah Sarki" ta nuna babbar ƴar "Sajidan ce sakuwar Ummi kenan, don baku jima da tafiya ba na haifeta."
Yayinda Yaya take da ƴaƴa huɗu, Sajida, Hamdiyya, Zinatu (Zee) da Halifa, na Altine uku ne. Baballe, Ummi da Siyama.
Sai da su ka nutsu da gaishe gaishen Yaya ta aiki Zee.
"Maza jeki gidan Lami ki ce ta baki lemukan da na bata ajiya." Ta yiwa Iyaa bayanin sace musu transformer da aka yi kusan wata uku babu wuta sannan ta fuskanci Hamdi "ke kuma ki je wajen babanku ki faɗa masa Altinen Maje ta iso."
Iyaa ta sanar da ita ai babansu Ummi na sauke su a ƙofar gidan ya yi waya da maigidan nata.
"Ina jin ya kwatanta masa wurin sana'ar tasa don ya ce can zai je sai su taho tare."
Cigaba da hirarsu su ka yi wanda hakan ya bawa Ummi damar yiwa Hamdi inkiya da su tashi tana son magana da ita. Ita kuwa sai ta ɗauke kai kamar bata gani ba. Hakan ya tunzura Ummi matuƙa sai kawai ta miƙe tsaye ta ce tana son shiga banɗaki. Hamdi na jin haka ta san kwanan zancen. Cikin ɗakinsu ta gayyato ta ba don ta so ba. Duk da gidansu mai tsakar gida ne amma kowanne ɗaki da banɗakinsa a ciki. Wannan tsarin babansu ne da ya ce baya so ace komai dare, ruwa ko iska sai an fito tsakar gida idan za a zaga.
Shigarsu ɗakin ke da wuya Ummi ta juyo fuskarta a murtuke.
"Zan faɗawa Iyaa makarantarmu ɗaya amma kada ki kuskura ƙaiƙayin baki yasa ki faɗawa kowa sirrin rayuwata a makaranta"
"To" ta iya cewa don hankalinta a tashe yake. Yau ruwa ya ƙarewa ɗan kada. Sirrin ɓoye zai fito fili.
Rai a ɓace Ummi ta bangaji kwalarta yadda ta saba cin zalin ƴaƴan mutane a makaranta.
"Bar ganin nan gidanku ne kin dai san an kusa komawa makaranta. Kin kuma san ko ni wace ce ba sai an faɗa miki ba."
Ficewa kawai Hamdi tayi daga ɗakin wani abu na hawa da sauka a ƙirjinta. Barazanar Ummi ba ita bace damuwarta kamar yadda zuwanta gidan yake nufin tonuwar asirinta. Gudun rana irin wannan da wata ƴar makarantarsu za ta zo gidansu yasa ta zaɓi makarantar kwana. A can ɗin ma bata da ƙwaƙƙwarar ƙawa ko ɗaya. Tsakaninta da kowa mutumcin gaisuwa ne da kuma taimakon da take yi musu na ƙarin haske akan karatu. Allah Ya yi mata baiwar ɗaukar darasi da zarar an koyar. Bata taɓa tsallake matakin ukun farko ba tun shigarta. Sau biyu makaranta na neman iyayenta domin a karramata a gabansu tana daƙilewa. Na farko ta ce mahaifinta ya yi tafiya. Na biyu kuma ta ce yana kwance tun kafin ta taho ya yi hatsari ya karye. Da taga alamun za a bishi gida gayyatar Yaya ta nuna ai maman ke jinyarsa. Malamin ajinsu da kansa ya gane akwai abin da take ɓoyewa sai ya sanar da hukuma kada a matsa mata. Sun riga sun saba ganin abubuwa marasa daɗi game da dangin ɗalibai. Tunda dai ba karatu aka hanata ba sannan duk dawowa daga hutu da kuɗin makarantarta take zuwa ya ce a ƙyaleta kawai. Daga lokacin sai dai idan an yi taron ta taho da kyautarta gida. Bata tsoron duniya ta ga lalurar Yaya amma mahaifinta da shi ya ɗorawa kansa bata son ana alaƙanta su a waje. Sau tari ita da ƴan uwanta su kan zauna su kwashewa wanda ya haɗa auren mamansu da mutum irin mahaifinsu duk kirkinsa albarka.
Fitowarta tayi daidai da dawowar Zee. Ta ajiye ledar hannunta ta tafi ɗauko tray za ta ɗora musu. Sai ga Ummi ta fito ta dubi Hamdi tana murmushi kamar gaske.
"Don Allah ba ke ce Hamdiyya Habib ta Rumfa Hostel ba?"
Murmushin dole Hamdi tayi ganin iyayen nasu sun dawo da hankali garesu.
"Ni ce. Kema kamar na gane ki."
"Ummi ce, Ummi Maje. A 'F class' nake shi yasa ba lallai ki sanni ba."
Iyaa ta hau murmushi wanda kuma da wuri ya koma shan kunu da ta gane me hakan yake nufi.
"Kin dai ji kunya wallahi. Karatu kamar cin ƙwan makauniya. Ƙanwar bayanki ma ajinku ɗaya?"
Ta gyara zama ta yiwa Yaya ƙarin bayanin asalin daƙiƙanci irin na Ummi wanda ya janyo ake ta yi mata repeating. Wannan shekarar ma don an riga an saka ranarta ne babansu ya roƙi alfarma aka kaita aji shida saboda ta gama a aurar da ita. Basu san rashin ƙoƙari ba shi kaɗai ne matsalarta ba kamar yadda Hamdi ta sani. Idan kana neman irin ɗaliban nan da ko bayan shekara ashirin in ka tambayi abokan karatunsu game dasu sai dai su bi su da 'Allah Ya isa' ko ka ji ana cewa 'a dai yi shiru' idan mutum ya riga ya mutu to Ummi Maje ce. Bully ce lamba ɗaya!
*
Lokaci guda rana ta ɗauke, hadarin ya sake duhu ga iska mai ƙarfi tana kaɗawa. Babu shiri hirar ta koma cikin falo. Zee ta ƙarasa shanya wa Hamdi kayanta ita kuma ta shiga kitchen ta haɗa salad bisa umarnin Yaya. Abu ɗaya hakan yake nufi. Abbansu yana tafe da abinci kuma tabbas a yau Ummi za ta sami makamin cutar da ita. A baya ko kallo basu ishi juna ba tunda duk jarabar mutum dole ya haƙura indai Hamdi ce. Bata shiga sabgar kowa balle a kai ga yin faɗa da ita.
Tsananin faɗuwar gaban da taji lokacin da aka yi sallama daga zauren gidan yasa ta sharɓe hannu wurin yankan albasa. Yayyafin da aka soma bai hana kowa jin sallamar mace ba. Yaya da Iyaa su ka amsa da fara'a yayinda Ummi ta ƙagu ta ga wace baƙuwar akayi mai zaƙin murya haka.
"Za mu shigo da Alh. Maje" su ka ji muryar ta faɗi. Sai kuma dariya ta biyo baya inda Baba Maje yake cewa "ai ka rigani indai amsa sunan Alhaji ne."
Kan Ummi da Siyama ya ɗaure. Zee kuwa duk abinta na rashin damuwa yaƙe ta kama yi da taga yanayin fuskokinsu. A kitchen kuma numfashin Hamdi ya kusa ɗaukewa da Yaya tayi musu izinin shigowa.
Abbansu ne a gaba. Sanye yake da jallabiya yana tafe jiki na rangaji irin na riƙaƙƙun mata. Ga hula zanna bukar da ta ɗan sha jiki ya kafa a karkace. Shigarsa dai da ta sani ta yau da gobe. A bayansa wani mutum ne mai jiki wanda da alama shi ne baban su Ummi.
Suna shiga falon ta leƙa ta tagar kitchen ta hango yadda yake magana yana tafa hannuwan mamaki yadda mata su ke yi harda riƙe haɓa.
"Altine kece haka? Ikon Allah." Ya zauna a kujerar kusa da matarsa. "Gaskiya rabuwar zumunci bata yi ba ko kaɗan."
Fuskar Iyaa wasai ta amsa gaisuwarsa sannan ta mannawa yaran nata harara. Ba shiri kowacce ta miƙa gaisuwa da girmamawar dole. Ga mamaki ƙarara bayyane a fuskokinsu.
Namiji har namiji Ummi ta ayyana a ranta. Dogo ne don sai yau ta raina tsayin babanta. Jikinsa babu rama amma yadda yake karairaya shi yasa babu mai cewa jikin namiji ne da ya amsa sunansa. Fatar nan dabbara dabbara alamun an sha bleaching a shekarun baya. Yana buɗe baki kuwa haƙoran Makka ne na azurfa a sama har biyu suna maraba da baƙi.
"Kan uban can...ƊANDAUDU ne?"
Ta yiwa kanta tambayar a zuci ba don tana neman ƙarin bayani akan zahirin da idanuwanta su ke gani ba.
Abba kuwa da zafin nama ya fita shigo da kulolin abinci ita kuma gwanar ta ɗauko ƴar wayarta tamkar mai duba wani abu ta soma yi masa hoto a fakaice. Sautin wayar ma a silent ta saka don kada kowa ya gane. Siyama ce kaɗai ta kula kuma a take jikinta ya yi sanyi don ta sani babu ko tantama irin murmushin fuskar yayarta a lokacin na nufin abin da take yi ba na alkhairi bane.
RAYUWA DA GIƁI 2
Batul Mamman💖
Banda hotuna har sautin muryarsa Ummi ta ɗauka daidai inda yake kiran Hamdi ta kawo salad. Tana jin kiran ba amma saboda tsoron yanayin da za ta tarar da fuskar Ummi na farincikin samun lagonta sai ta kasa amsawa.
"Abba bari na kira ta." Zee ta miƙe tsaye.
"Matso mu su da plates bari naje."
Tashi ya yi ya tattare gefen jallabiyarsa ya riƙe da hannu ɗaya ya fita. Ya samu ta gama haɗa komai ta lulluɓe da clig (farar leda ta rufe abinci) kamar yadda ya koya mu su. Haɗin ya yi kyau gwanin ban sha'awa. Ya murmusa cikin jindaɗi yana ɗaukan tray ɗin. Ko ƙanƙani bai san wani abu girman kai ba musamman a tare da iyalinsa.
"Allah Ya yi albarka Hamdi. Mu je a ci abinci."
Jingina tayi da sink ta juya masa baya kamar wani abu za ta wanke ta gyaɗa kai. Amsawa da baki zai iya ankarar dashi kukan dake barazanar ɓalle mata.
Shi kuwa kamar ya sani ya ajiye tray ɗin ya juyo da kafaɗunta.
"Hamdi?"
Ai suna haɗa ido sai kawai ta fashe da kuka. Zuciyarta tamkar ta fashe saboda baƙincikin da take ji. Wani abu mai masifar ɗaci ya dinga kai komo a cikin ƙirjinta. Duk gidan tana da yaƙinin tafi kowa takaicin fita tsatson bawan Allahn nan. Ranta yana ƙyamarsa. Albarkacin karatun addini yasa ta daina danganta shi da munanan kalmomi da fata a zuci kamar yadda take yi a baya. Asalin da mutane ke tutiya dashi Yaya ta janyo sun rasa ta da haifesu tare da tubabben Ɗandaudu. Mutumin da har yau idan aka yi rashin sa'ar gamuwa da tsofaffin abokansa sai kaji ana kiransa Simagade.
Hankalinsa tashi yayi da ganin hawayenta ya dinga tambayarta damuwarta. Da bata ce komai ba ya yi yunƙurin rungumeta domin rarrashi amma sai ta banƙare jiki ta ja baya. Dama can ta saba yi masa haka don shi tarairayar yara sai dai wani ya koya a wurinsa. Na yau ne da ya sanya masa shakku tunda ya san ta kan bari sai dai ta zare jiki da wuri. Kallon tuhuma ya bita da shi sai ta wayance ta ɗago hannun da ta yanke ta nuna masa.
"Ya Salam" ya ce da ƙaramar muryarsa "Sannu. Jeki falo ki jira ni."
Tray ɗin salad ɗin ya ajiye ya fita cikin ruwan nan mai ƙarfi ya shiga ɗakinsa. Haƙƙin iyaye da a kullum shi ne jigon dake hanata fito masa da zahirin abin da take ji game da shi yasa ta ɗauki tray ɗin. Idonta da na Ummi su ka haɗu taga abin da take gudu muraran a tare da ita. Jikinta ya sake yin sanyi.
Sallamar Abba ta dawo da ita duniyar mutane. Ya zauna akan hannun kujera ya ce ta kawo hannunta. Ɗan akwati gare shi irin na gidan ƴan boko da ya adana magunguna da kayan taimakon gaggawa. Ya umarci Zee da zubawa kowa abinci shi kuma ya zauna bawa ƴarsa kulawa. Spirit ya dangwala a jikin auduga ya goge ciwon. Ga azabar zafi saboda ba ƙaramar yanka bace amma ko uhumm ta kasa cewa. Allah Ya sani zafin da take ji a zuciyarta yafi raɗaɗin ciwon. Saboda yadda ta ƙyamaci rayuwar mahaifinta bata ƙaunar gabaɗaya abokan sana'arsa. A son ranta namiji ko ruwan zafi aka ce ya dafa ya dawo ya ce ya ƙone saboda rashin iyawa. Namiji mai shiga kitchen ba zai taɓa yi mata kwarjini ba balle har taga ƙimarsa.
Dressing sosai ya yi mata ya kawo auduga ya ɗora ya manne ta da plaster. Gwani ne sosai ta wannan fannin wurin son ganin komai ya tafi daidai kamar wani bature. Ire iren abubuwan nan harda Abban da yasa su ke kiransa kamar ba talakawa ba duk bata so. Cikakken namiji bahaushe a wajenta ai Baba ake kiransa ba wani iyayin Abba ko Daddy ba.
Kowa sannu yake mata tana amsawa da ka. Da kuma wannan damar ta samu ta gudu ɗaki ta kwanta. Ba ita ta sake fitowa ba har sai da baƙin su ka tafi bayan Iyaa da su Ummi sun leƙo sun mata sallama.
***
"This is crazy Taj. Waye yake tattara duka ƙwansa ya sanya a kwando guda?"
Wata kamilalliyar dattijuwa sanye da doguwar rigar bacci da ƴar hula ta furta da takaici. Huci take cikin ɓacin rai tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune yana murmushi kamar abin da take faɗi da wani take a talabijin ba shi ba.
"Tajuddin!" Ta kira shi da ƙarfi da gargaɗi.
"Yes Ma" ya miƙe tsaye gami da sara mata. Ta sake tamke fuska.
Shi ma da alama ya gama shirin bacci ne don wandon jikinsa three quarter da singileti basu yi kama da kayan mai shirin fita ba.
"Ina wasa da kai ne?"
Ya girgiza kai.
Abin da ta san za ta yi ya dawo da hankalinsa gareta yadda take so ta aikata.
"Ko don kaga ba ni na haifeka ba? Shi yasa ban isa..."
"Amma gorin haihuwa kuma za ki min. Has it realy come to that?" Ya yi ƙwalƙwal da ido.
Jikin Amma a take ya yi sanyi. Taj ya yi wani ɗan banzan murmushi a bayan idonta sannan ya cigaba da magana.
"Idan baki aminta da abin da nake so ba ai ina ganin ba sai kin tuna min cewa ni ba ɗanki bane."
"Ba haka nake nufi ba. Kai ma ka sani."
Marairaice mata fuska ya yi sosai ta yadda ya san hankalinta zai tashi. Ya kuwa yi nasara don faɗan da ta ɗauko da gaske sai ya koma laluma.
"Taj bana son kayi abin da zai zama ganganci. Bayan duk irin abubuwan da ka jure a baya kada wannan step ɗin ya bada ƙofar da za a yi maka dariya."
"Amma da Happiness mu ke komai. Mun yi survey na yadda malls su ke saurin dakushewa..."
"Durƙushewa dai ko?" Ta ci gyaransa ba tare da ta ɓoye takaicinta ba.
"Yeah, durƙushewa. So after the survey mun gano wasu reasons da suke kawo failure na business ɗin."
Zama tayi bayan ta gama sauraronsa tayi ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa take guje masa wanda idan ba ɗan fito dasu tayi ba da wuya ya gane inda ta dosa.
"Shekararka nawa a ƙasar nan Taj?"
"10 years" ya amsa kai tsaye.
"And for those years you have been working non-stop kana tara kuɗi. Cikin ikon Allah kuma ka sami nasarar cin gasar nan ka sami maƙudan kuɗaɗe da sponsorship. Sai kawai na