Showing 111001 words to 114000 words out of 182238 words
Chapter 38 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
mahaifiyarta? Saboda miskiniya ce.
"Ya Hamdi meye haka ne? Ji idonki har ya soma caɓewa fa." Cewar Zee ta ƙara miƙawa mai kwalliyar tissue domin a gyara idon.
Sajida wayarta ta shiga dannawa tana cewa "bar ni da ita."
Sai ji su ka yi tana gaishe da Taj. Ta kuma faɗa masa kukan da Hamdi take yi da dalilinsa.
"Saka mata wayar a kunne."
Da canjin numfashin da yaji ya gane ta saka mata ɗin. Da rarrashi ya yi mata magana.
"Zan kawo miki Yaya in sha Allahu. Ki daina kuka idan ba haka ba kuma yau sai mun yi kuch kuch hota hai a gaban mutane. Mu yi ta rangwaɗa kai kamar ƙadangaru."
Dariya ce ta kama Hamdi. Sajida, Zee da maikwalliya su ka saki baki suna kallon ikon Allah.
"Waƙar bata da hayaniya sai na taya ka."
"Haka ki ka ce?" Ya tambayeta yana murmushi "Wayarki na kusa?"
"Eh"
"To ki dubo waƙar I am a disco dancer a youtube. Ni kuma idan baki daina wannan kukan shagwaɓar ba in baki mamaki a gaban mutane. Ita zan yi. Kin kuma san zan iya. 80s aka yi ta ba ta zamaninku bace."
"To Baba Happy. Na ma share hawayen" ta goge idonta da kanta don barazanar Taj ba abin da za ta share bane.
"Wannan ladabin ba na gaske bane. Sai na tambayi Sajida naji ko kin ƙara yin kuka."
"Allah na daina."
"Hamdiyya" ya kirata a tausashe.
Kasa buɗe baki ta amsa tayi saboda kiran nasa na daban ne.
"Uhmm"
"I'll see you later."
"Bye" ta miƙawa Sajida wayar.
"Iiiiiikon Allah" Sajida ta faɗi baki buɗe "me zan gani ni Sajida ƴar Habibu? Hamdi? Dama rashin jin muryar mijinki ne yasa ki kuka? Shi ne ki ka ɗorawa baiwar Allah Yaya. Ai kuwa bari nace mata tayi zamanta."
Da sauri Hamdi ta miƙe tana kici kicin karɓe wayar "ɗaukota fa zai je ya yi. Shi yasa ki ka ga nayi dariya."
Zee tayi dariya "anya kuwa? Naji fa kina zancen wata waƙa wai bata da hayaniya."
"Ke, kira Ya Baballe ku gaisa kema ki ji daɗi."
"Baballen lafiya? Sunansa Sadiq" ta faɗa tana kallon yayyen nata.
A tare su ka bushe da dariya sannan Hamdi ta koma ta zauna aka gyare fuskarta kamar bata yi kuka ba. Ana gamawa ta koma gefe ta buɗe youtube. Hannunta yana ƙaiƙayin ganin waƙar da Taj yake cewa zai yi. Da ta kunna ɗaya tayi kama da ta 80s ɗin daga ɗaukan ma. Ɗayar kuwa ɗaukan zamani ne. Bata ma ɓata lokacin kallon ta zamanin ba wadda ta kasance remake ɗin tsohuwar. Danna tsohuwar tayi inda kunya ta kusa sumar da ita da rawar da Mithun yake yi. Saboda raye raye nan taƙi jinin waƙe-waƙe. Idan Taj ya yi wannan girgizar da karya jikin tabbas a wurin dinar za ta tafi ta barshi.
Su Zee dai kallonta kawai suke yi. Tana duban waya da ido ɗaya tana kawar da kai.
"Ta fa ci kai wannan." Sajida ta faɗi su ka yi dariya ko kula su bata yi ba duk da taji.
*
Da Taj ya gama wayar, ji ya yi an ture shi. Sai lokacin ya ankara ashe a jikin Kamal ya jingina da shauƙi na ɗibarsa. Ya rasa me yasa shi da Hamdi basa iya yiwa juna baƙunta. Kamar ba jiya jiyan nan da sauran ƴar rigimarsu ba. Yau kam komai ya wuce!
Ɗaure fuska Kamal ya yi "Na ma rasa abin da zan ce maka Happy? Wato haka ake soyayyar ni ka barni ina fama da instagram da daddare?"
Taj ya kama dariya "ba dai ka tsaya wasa ba? So kake sai Dr. Mubina ta kawo maka katin aurenta ka zo ka ce min zuciyarka za ta fashe ko?"
"Allah ma Ya kiyaye. In sha Allah ba zan ga aurenta ba." Cewar Kamal yana mantawa da wa yake magana.
Wata irin juyowa Taj ya yi yana kallonsa "saboda kai za ka aureta ko kuwa ƙasar za ka bari idan ta tashi auren wani a dalilin nauyin bakinka?"
Wayancewa Kamal ya yi "likitoci na auren ƴan kasuwa ne? Idan rabon wani ce sai in tafi China odar kaya kafin a gama bikin."
Tsaki Taj ya yi "ta nan kuma ka ɓullo? Hmmm, kai ka san yanayin aurena da matsalar Alhaji ne su ka shige min gaba. Ba don haka ba da yanzu kai ma kana kwanciya kamar gasara a ruwa idan kuna waya."
"Wannan karin magana ne ko me?" Kamal yana dariya ya tambaye shi.
"A bakin Ƴar Ficikar nan naji."
Dariya su ka yi sannan Kamal ya ce zai fita waje ya tada mota kafin Taj ya fito sai su ɗauko Yaya. Ɓata lokacinsu faɗan iyaye zai jawo musu.
Yana fita Taj ya bishi da ido. Jikinsa yana bashi tabbas akwai abin da ɗan uwan nasa yake ɓoyewa. Kwana biyu ma tunda ya dawo ya gan shi a rame. Yanzu ne ma ya ɗan ciko. Zuciyarsa ta bashi ko ma mene ne ya shafi Dr. Mubina. Kuma yafi tunanin ƙila soyayyar Happiness ce bata karɓa ba. Da an gama bikin nan zai je ya sameta har asibiti ko ya nemi gidansu. Indai ba wani aka bawa ita ba zai nuna mata cewa rashin karɓar Kamal asararta ce. Happiness is a rare gem. Ko shi da ya same shi a matsayin ɗan uwa ba ƙaramin dace ya yi ba.
Ƙarasa shirinsa ya yi su ka fice daga gidan. A daidai bakin layin su ka ga motar Ahmad wanda dawowarsa kenan daga Bauchi. Horn su ka yiwa juna. Basu kula da Salwa a gaban motar da kuma Mami dake kwance a baya ba.
Kiran wayarsa Kamal ya yi yana sanar dashi kayansa wanda duka ƴan mazan gidan zasu saka banda ango suna ɗakinsa. Sun bawa Anti Zahra ta ajiye masa kafin ta tafi.
"Zan ɗan makara amma. A gajiye nake."
"Wai ina ka je ne? Ance tun safe ka fita."
Ahmad ya kalli bayan motarsa ya sauke numfashi.
"Sai mun haɗu dai."
Da taimakon Salwa su ka shigar da Mami cikin gidan. Gabaɗaya ta rikirkice saboda ƙamshin turaren Taj da hancinta yake iya bambancewa duk inda ta ji shi. Ɗakin da take zama Ahmad ya ce su shiga da Mami.
"Bari nayi wanka naje wajen dinner ɗinnan. Ba zan jima ba in sha Allah. Gobe da safe sai mu tafi asibitin."
Da azama ta miƙe ita ma bayan ta kwantar da Mami "Nima bari na shirya kafin ka fito."
Haɗe fuska Ahmad ya yi "Salwa."
"Na'am." Sai kuma tayi murmushi "wallahi sauri zan yi Yaya."
"Ba ki da hankali ashe." Ya nuna kansa yana juya ɗan manunin yatsansa cikin ɓacin rai "wa za ki barwa Mamin da kike zancen zuwa dinner?"
Murmushi tayi "lahh, Ya Ahmad ai kai ma ka san ba zan tafi haka kawai ba. Tun a hanya nayi magana da Anti Zabba'u (ƙanwar Mami). Tana hanya ma don na faɗa mata mun shigo gari."
"Yaushe ku ka yi maganar ban sani ba?" Ahmad ya tuhume ta.
"Tun jiya ne bayan mun yi waya da kai."
Zama ya yi a gefen gadon yana matse gaban goshinsa kafin ya ɗaga kai ya kalleta da takaici.
"Dama shirinki kenan shi yasa ki ka yi min ƙaryar Alhajinku ba ya kula da lafiyarta?"
"Wallahi Yaya..."
A harzuƙe ya tashi kamar zai kifa mata mari "Shut up Salwa. You are very stupid."
"Don na ce zan je bikin ƙaninka kake zagina Ya Ahmad?"
"Ba za ki ba! Ko ƙalau Mami take babu inda zaki. Haba! Yarinya kin bi kin haukace kuma kina neman haukata kowa. Taj baya son ki, kuma ko yana so ina cikin masu hana shi aurenki saboda baki san bambancin so da obcession ba."
Kuka ta fashe masa dashi. Tana jin saukar maganganunsa tamkar sukar mashi. Sai ta mallaki Taj a matsayin miji kuma akan idonsa ta ƙudurta a ranta.
Mami tana daga kwance tana ɗaga lafiyayyen hannunta akan su yi shiru. Kallonta Ahmad ya yi ya fice kawai domin dai ba a canjawa tuwo suna. Alh. Mukhtar ya faɗa masa komai da yaje ɗaukarta. Ya kuma sanar dashi cewa ya saketa sannan idan sun tafi to ta tafi kenan daga rayuwarsa. Har abada baya son sake ganinta. Ƙannen Salwa mazan suna wajensa. Ita kuma ya ce idan sun gama zaman asibiti ya dawo masa da ita domin aurar da ita zai yi. Sun gama magana da wanda zai aureta ma.
Wannan ne dalilin da yasa ya taho da ita. Ba wai ƙaryar da tayi masa ba. Don tabbas komai na buƙata Ahmad yaje ya samu suna dashi. Kawai mijin nata ne dai ya fita harkarta.
"Zan jira Anti Zabba'u ta iso kafin na tafi." Ta ce da Mami.
"Uhmm uhmm Salwa" Mami ta ce da ƙyar.
"Mami zani fa. Na san da lafiyarki ƙalau za ki bani goyon baya."
Banɗaki ta shiga ta sillo wanka. Ta fito tana cikin shiri Anti Zabba'u tayi mata waya cewa tana bakin gate. Garin saurin ta buɗe mata abu ya faɗo daga jikinta bata sani ba. Yunƙurawa Mami tayi ta leƙa abin. Sai da jikinta ya kama rawa. Sabuwar laya ce don zaren fari ne tas irin wadda take taunawa idan za ta yiwa Alh. Mukhtar magana. Zarginta akan Salwa ya tabbata. A asibiti Salwan tayi zaton bacci take ta ɗauki wayarta ta kwafi lamba. Kuma taji buƙatar da ta faɗa...tana son mallake wani. Sai yanzu ta gane malamin tsibbunta ne Salwan ta ɗauki lambarsa. Kenan duk abin da take yi ƴar na lura? Bata son inda tabi har rayuwa tayi mata wannan atishawar ƴan tsakin ita ma Salwa ta bi. Da ƙalau take duk inda ake takawa zata je domin farincikin ƴarta, amma bata so ƴaƴan su yi wannan rayuwar.
Bakin Salwa kasa rufuwa ya yi da ta buɗe ƙaramar ƙofar gate su Anti Zabba'u su ka shigo. Don ma babu motar Ahmad ta san ya tafi. Gayya guda har su shida. Ita da ƴan matan ƴaƴanta guda uku. Sai babbar bazawara da goyo. Kowacce ta bawa shabiyar baya. Ita ma Anti Zabba'un ta gaji da aure aure ta haƙura. Dama kuma ta jima tana roƙon Mami ta tilasta Ahmad auren guda cikin ƴaƴan nata amma taƙi yarda saboda kar ta san kar ne. Sai gashi Salwa ta faɗa mata halin da Mamin take ciki. Da murna ta kwaso jiki. Ko Ahmad yana so ko baya so sai ya auri ɗaya kuma ya saki wannan mai dara daran idanuwan.
Ita dai Salwa bata san Mami taga layarta ba. Ɗaukewa tayi ta tura a jaka. Ta gama shirinta tsaf ta haɗa da turaren wajen su Ummi ta fita. A rashin sani turaren aikin Alh. Usaini ta ɗauka tunda shi ne aka ce mata zai kawo soyayya tsakaninsu.
A daidaita sahu ta samu har event centre ɗin. Motoci ko ta ina. Ta zo bakin gate tayi turus don babu kati!
***
Shafawa ido toka Taj ya yi da ya shiga ciki ya ce da Abba ya roƙi da Yaya ta fito su tafi saboda abin da Hamdi ta ce. Yayan da Inna Luba suna zaune a wajen.
"Ayi haka Taj? Muna da gefe bai fi ba?"
"To nima dai idan bata fito ba tabbas babu inda zani tunda amaryar tayi rantsuwar ba za ta fito ba."
"Barni da ita. Yanzu zan kira in yi mata faɗa." Cewar Abba yana ƙara kaurara murya don ya ƙara mata kwarjini.
Taj ya ce "Abba me ɓoyon zai ƙara ko ya rage? Waye bai san ƴarka nake aure ba? Wa kuma kuke son ɓoyewa kanku? Kuna jin gata ne kuke yi musu? Mushirikai da fasiƙan iyaye ake gudun nunawa. Amma idan kuna yin haka nan gaba sai sun fi ku jin kunyar a ganku tare. Kunga sai ayi ta rubuta musu zunubin rashin kyautatawa iyaye."
"Kai Tajo, me yayi zafi?" Inna Luba ta ce a tsorace "ke tashi ki shirya ku tafi."
"Ke fa Inna?" Taj ya ɗaga mata gira "nawa kakannin babu. Ki zo ki wakilci kowa."
"Ja'iri, to bari nasa kaya. Dama wannan ƴar ce ta hana ni zuwa amma na so bin su wallahi" ta miƙe da murnarta.
Murmushi Abba ya yi. Yaya da Inna Luba su ka shiga ɗaki. Basu daɗe ba kowacce ta fito cikin shiga mai kyau. Yaya lace ɗin da Mama ta aiko ta ce mata ankon manya ne ta saka. Kai kana ganinta banda lalurar ƙafa da ba ƙaramar mace za ayi ba. Fuska dai kam Masha Allah. Akwai kyau irin na Katsinawa wanda ƴaƴanta su ka haɗa da na Simagade su ka fito gwanin ban sha'awa.
***
Ƙarfe bakwai da minti arba'in da biyar daidai Amma ta kira Taj ya ce mata suna wajen parking.
"Bari a sauko da amaryar sai ku shigo."
"Amma tare muke da Yaya."
"Tun ɗazu nake lalubenta cikin baƙi. Gani nan fitowa."
Da kanta taje wajen motar ta riƙo Yaya su ka shigo. Mama na hangota daga wajen zaman iyaye ta tada Umma su ka ƙarasa. Hajiya ma ta ce da Inna lallai ta tashi. Tunda aka ce Taj ne ya kawota ta san tana tattare da jin nauyin shiga jama'a ne. Mutane sun fara kallon Yaya ana ƙusƙus da faɗin uwar amarya ce sai aka ga matan Alh. Hayatu Sule masu aji sun je inda take suna yi mata maraba. Kayansu ita da matan da Amma iri ɗaya. Sannan su duka har ƙasa su ka gaishe da Inna Luba. Wannan abu yasa duk mai abin faɗa ta haɗiye kayanta. Dukkan alamu sun nuna su ɗin suna cikin farinciki da son juna. Gutsiri tsomar ƴan gayya bata da tasiri.
A ɓangaren amarya kuma ƴaƴan Amma wato Ihsan da Amira da kuma Anisa sun haɗu da masu ƙananun shekaru cikin ƴan gidansu Taj da Anti Zahra sai kuma Sajida da Zee wajen rako amarya. Gabaɗaya matan doguwar riga su ka saka ta wani yadi sky blue da ɗigon fari da pale yellow wadda aka yiwa wani irin ɗinkin bubu mai kyau. Umarnin Hajiya Gambo kenan. Duk wata jininsu da tayi ɗinki mai fitar da shape a gida zata ci bikinta. Babu head sai rolling da su ka yi da pale yellow ɗin yadi mai santsi. Babu yadda za ayi ka gansu basu burgeka ba. Modesty and elegance at its peak!
Amarya Hamdiyya kuwa gown ɗinta fara mai dogon hannu kuma wadatacciya. Bata bi jikinta ta tona sirrin wanda ya bada sadaki a gaban kowa da kowa ba. A kanta anyi mata ɗauri da net silver wanda aka ɗorawa wani abin ado mai duwatsu sky blue na gashi ya kwanta ta ɓari ɗaya. Daga tsakiyar ɗaurin inda gashinta yake a suturce aka ɗora farin net dogo har ƙasa. Wuyanta sarƙar farin gwal ce. Sai clutch bag ɗinta da takalmi mai tsini sky blue. Tayi kyau har ta gaji.
Ƙasa suka sauko sannan aka zo bakin ƙofa aka jera yadda za a shigo. Kallo ɗaya Anisa ta yiwa Hamdi tunda sai yau su ka iso ta ganeta.
"Mai kukan uber?" Ta faɗa ba tare da wani tunani ba.
Hamdi ta ɗago su ka haɗa ido. Ta saki murmushi mai ban sha'awa. Haka kawai sai Anisa taji ƙuncin zuciyarta ya kau. Ta matsa kusa da ita tayi musu selfie sannan aka ce su tsaya kamar yadda aka tsara musu.
Matan layi layi suka yi hagu da dama har layi shida. Sai Hamdi a tsaye. A bayanta kuma Bishir da Abba. Sai kuma Kamal da Ahmad a bayansu. Sanye su ke da yadi pale yellow da aka yiwa ɗinki ma hannu da ya wuce gwiwar hannu da kaɗan. Daga hula har zuwa takalmi komai nasu iri ɗaya in banda agogo. Hamdi tayi zaton tafiya za su fara yi don hankalinta a tashe yake tun a nan ga hasken flash ana ta ɗaukar hoto. Ƙofar hall ɗin aka buɗe ta soma jin sanyi da ƙamshin wajen na buso ta sai ji tayi hannuwa sun kama nata da gentle riƙo. Tsigar jikinta tashi tayi da tsoro da kuma gane hannun waye. Tsayuwarsa kaɗai a kusa da ita ta sanya sanyin nan ya ragu don kansa. Ta ɗaga kai su ka haɗa ido.
Kayan jikinsa sky blue ne harda babbar riga irin wadda ake yi ta zamani ba burum-burum ɗinnan ba. Shi ma hannun rigarsa ta ciki ƙarami ne kamar na ƴan uwansa. Ya sanya hula da takalmi cover shoe navy blue mai duhu sosai. Gashin baki da gemunsa da basu cika yawa ba sun sha gyara.
"Ya Rabbi, har na fara tsoron ko ni kaɗai zan shiga" Hamdi ta faɗi a hankali tana kawar da kai don kallon nasa babu rissina a ciki.
"Ina tare dake kowanne taku. Ki daina jin tsoro." Ya bata amsa a kunnenta.
Hannunta zai saki yaji ta kuma damƙe nasa.
"Don Allah ka riƙeni har mu zauna. Zan iya faɗuwa da takalmin nan." Ta marairaice masa idanu har lokacin tana magana a hankali don kada na gabansu ko baya su ji.
"Awwwnnnn, zuciyata" Taj ya dafe ƙirji kuma da gaske yadda tayi ɗin ya shige shi ne sosai.
Fari tayi da ido tana harararsa "A nan ɗin ma sai kayi?"
"Kin gama dani ne Mrs Ha..."
Wani abu su ka ji kamar harbin bindiga da ya katse masa magana. Sai kuma muryar MC yana sanar da shigowar ango da amarya da umarnin kada kowa ya bar wurin zamansa da sunan ɗaukar hoto. Wani irin kiɗan taushi ne yake tashi babu waƙa a yayinda suke shigowa wajen cikin nutsuwa. Matan dake gaba basu mai rawa sai ɗan kwanon hannunsu mai fulawoyi masu kyau da su ke ta watsawa sama.
Da su ka iso gaba Yaya ta ƙyallara idanu ta hango ƴan matanta, bata san lokacin da idanunta su ka tara ƙwalla ba. Ta dinga hamdala a zuciyarta. Ashe Inna Luba ma hakan take a wajenta. Sai dai ita bata iya ɓoye nata hawayen ba. Jikokin kenan sai Halifa cikon na huɗu. Sai kuwa na yayarta abar alfaharinta har kullum. Amma dai jininta da take da cikakken iko dasu waɗannan ne. Da kanta ta dinga bin ƴan uwan Yaya wato ƴqƴan abokiyar zamanta mazansu da matansu a samu mai zuwa bikin nan amma yadda su ka ƙi zuwa na Sajida wannan ma ƙi su ka yi. Ta roƙi maigidanta ko sau ɗaya ne ya yi musu magana ko ya zo ƴarsa taji daɗi ya ce ba zai taɓa murna don ƴaƴan ɗan daudu sun yi aure ba. Su je can su ƙarata. Godiya kawai take ga Allah domin bai haɗa mata zuri'a da lalatattun mutane ba. Dukiyar bata tsole mata ido ba. Girmamawar daga surukan ƴaƴan shi ne komai a wajenta.
A teburin gefensu Iyaa ce da su Ummi, sai kuma surukar Sajida da ƙannen Safwan. Shi da Baballe