Showing 36001 words to 39000 words out of 182238 words

Chapter 13 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

meatpie, springrolls, chinchin irin na ƴan gayu, gashin nama da kifi kala kala. Da kuma uwa uwa haɗaɗɗen plain youghurt, coconut infused youghurt da yogo fura.

A gida irin farincikin da Anti Labiba ke gani a tare da ita har mamaki take bata. Mijinta ma sai da ya ce wai gani yake kamar an canja ta da wata. Yaran gidan kuwa tunda an yarje mata gwada abin da ta koya, sun kwashi gara ba kaɗan ba. A ci a gida kuma aje makaranta.

***

Wannan wata gudan harda ƴan kwanaki a ɓangaren Taj cikin wahala su ka zo masa. Kacokan ya ajiye aikinsa bayan ya wayar nan da ya yi da Hajiya. Ya karkata akalarsa zuwa ga son lallai sai Abba yayi aiki tare da shi. Kamal da yaga ba zai iya hana shi ba sai ya bashi goyon baya.

Ranar farko tun safe ya shirya yaje ƙofar gidan Abba. Bai aika a sanar da zuwansa ba. Ya yi zamansa a cikin mota har Abban ya zo fita sannan ya tare shi. Ai kuwa yana ganin shi ya sauya fuska.

"Baka sami saƙona a wajen ɗan uwanka ba?"

Gaishe shi Taj ya yi. Bawan Allah yana faɗan ya tsahirta ya amsa sannan ya cigaba.

"Bana son rigima da mahaifinku. Ban san me ku ka ji game dani ba. Amma ko ma mene ne nufinku ni da Allah na dogara."

"Don Allah ka saurareni. Da alkhairi na zo maka."

Cikin gida Abba ya koma. Bai ƙara fitowa ba har la'asar. Taj ya tafi amma bai karaya ba. Washegari ma ya sake zuwa. Ranar Abba ko sauraronsa bai yi ba ya wuce ya yi tafiyarsa. A haka su ka cinye sati guda. Wasu kwanakin duk sammakonsa idan ya zo zai samu Abban ya fita kafin ya zo.

A kwana na tara Taj sai ya canja tsari. Tare su ka zo da Kamal wanda ya ce zai bada haƙurin abinda ya yi kwanaki. A zatonsa ko shi yasa Abban yaƙi sauraron Taj. Yaro ya tura ya ce a faɗawa Abba su Taj sun zo kuma wallahi yunwa suke ji.

Sajida ce kaɗai a gida da Yaya. Halifa da Zee suna makaranta. Sajida tana jin saƙon yaron ta figi mayafi ta fita. Yaya tana ta kiranta taƙi dawowa. Abba kuwa ƙwafa ya yi.

"Bawan Allah zamu haɗaka da ƴan sanda wallahi. Bar ganin kuna da kuɗi" ta harare su duka "wallahi muna da masu tsaya mana mu kara daku a hukumance."

"Ki yi haƙuri ƙanwarmu. Aiki kawai ƙanina yake son yi tare dashi. Shi ma sana'ar girki yake."

"To ya ce baya so. Ai.ya faɗa mana ko ku su waye." Ta ce da tsiwa.

"Ɗan tsaya mu yi magana" Taj ya ce bayan ta gama magana. Tsayuwar tayi tana karkaɗa ƙafa ita a dole ranta ya ɓaci.

Tarihinsa ya bata a taƙaice.
"I believe yadda nake son in dawo da ƙimata a wurin Alhaji haka Abbanku zai so mutane su yi masa uzuri su karɓi sabuwar rayuwar da ya gina."

Cikin mutuwar jiki ta ce "haka ne."

"Ina son yin aiki da Abba amma a setting da ya bambanta da wanda ya saba. A inda maza masu yin komai na maza su ke girki. Burina idan an kwana biyu rayuwarsa tayi daidai ta yadda masu aibata shi a bayansa za su ji kunyar abin da su ka yi."

Ƙwalla ta saukowa Sajida "zai yiwu? Kana ganin wannan abubuwan na mata za su barshi?"

Kamal ya sanya baki "Allah aka ce. Ba yadda za ayi ka bar kowa ka kama Shi sannan kasa rai da ganin ba daidai ba. Taj only wants to help."

"Mece ce ribarsa idan ya taimaka masa?"

"Mutane su fahimci akwai sana'o'in da basu keɓanta ga mata ba kawai. Sannan ƙyama ba ita ta dace da irin wanda ya yi rayuwar Abba ba. In an bi hanyoyin da su ka dace shi ma zai karɓu a cikin mutane kamar kowa" Kamal ya sake bata amsa.

Abin nema ya samu Sajida ta koma gida da murnarta. Abba na ganin hawayenta ya tashi.

"Me su ka yi miki?"

Ta fashe da kuka "don Allah Abba ka sauraresu. In sha Allah wannan wahalar neman wurin hayar zai ƙare."

Fita ya yi ya sallame su. Taj sai ya ƙi motsawa.

"Zan sa a nemo min mahaifinka ya zo ya tafi da kai."

"Zan tafi amma don Allah ka bani abinci. Yunwa nake ji."

Abba ya kallesu. Duk sun yi laushi.

"Ba ku karya bane?" Ya tausasa murya. Sai muryar tasa ta sake yin ƙasa.

"Ni dai na sha tea. Happy kuma bai ci komai ba."

Abba ya kalli Taj da mamaki "Happy kuma?"

"Eh. Sunansa kenan" Kamal ya bashi amsa.

"Yana sallah kuma?" Abba ya tambaya harda matsawa baya.

Me kuwa za su yi banda dariya. Taj yana yi ya riƙe ciki. Abba ya sami kansa da yin murmushi bayan sun yi masa bayanin sunayen nasu.

"Innza ku ci ko indomie ce sai na karɓo a shago Sajida ta dafa muku."

"Don Allah abinci muke so. Wanda ka girka." Taj ya ce da sauri.

Girgiza kai Abba yayi yana ɗan murmushi.
"Ku jira nayi muku iso a ciki."

Sajida ce ta leƙo ta kira su bayan ya shiga ciki. Aka yi musu shimfiɗa a tsakar gida. Yaya ta fito da lulluɓi su ka gaisa. Taj ya dinga kallon gidan yana ayyana wai fa a nan yarinyar nan da ya gani take rayuwa. Yana son tambayar ina take amma dole ya kama bakinsa.

Abba ya shiga kitchen suna iya hango duka motsinsa ta tagar dake tsakar gidan. Kai kawo kawai yake yi cike da ƙwarewa. Yaya da Sajida kuma suna jansu da hira jefi jefi. Kamal ne kaɗai yake amsawa. Hankalin Taj ya yi kitchen. So yake kawai yaga yadda Abba yake aiki.

Yaya ce ta lura da hakan ta yiwa Abba magana. Yaran sun burgeta saboda babu girman kai a tare dasu.

"Nace ko za ka bari ya shigo ciki ya taya ka?"

"A'a, nagode."

Taj ya tashi "gani kawai zan yi. Ba zan saka hannu ba."

Sai bayan fiye da minti ɗaya sannan Abba ya ce ya shigo amma iyakarsa ƙofa. Ai kuwa da saurinsa ya shiga. Aikin daɗewar shekaru wato experience yafi aikin iyawa. Taj yaga abin mamaki a tattare da kuzarin dattijon. Ga tsafta don ko ledar maggi babu a ƙasa. Ƙamshi mai rura wutar yunwa ya cigaba da matse masa hanji.

Fried spaghetti ce yayi musu babu nama a ciki sai busasshen kifi. Ya juye a tray. Sajida ta kawo musu. Sannan ita da Yaya su ka koma falo. Samarin Alh. Hayatu su ka zauna suna zuba santi har su ka cinye.

Da za su tafi ne Taj ya bashi nambar wayarsu rubuce a takarda.

"Don Allah Abba kayi shawara."

"Naji. Ku tafi."

Faɗan nasa bai hana shi raka su har mota ba. Kuma yaƙi tafiya har su ka bar layin. Yana komawa gida ya samu Sajida tana naɗe tabarmar da su ka zauna. A ƙarƙashinta sai ga farar takarda. Ta miƙa masa ya buɗe. Roƙo da magiya ne daga Taj. Sai kuma ƙarin bayani game da restaurant ɗinsa.

"...idan ka amince za ka yi aiki dani, zan kama mana wuri inda za mu yi developing recipe kafin a gama ginin. Bana son yin business ɗin da zai rushe kafin yaje ko ina. Ka taimaka min..
Happy Taj"

Da Yaya su ka zauna shawara. Sai dai washegari da kwanakin da su ka biyo baya kullum sai Taj yaje cin abinci. Har su ka yi masa kwano. Tun Abba yana basarwa har dai ya karɓi tayin da yayi masa. Ba kuma komai ya janyo haka ba sai rasa wurin da zai kafa sana'arsa. Duk inda yaje sai an biyo shi da ƙabali da ba'adi wanda shi ya san gaskiyar dai ita ce ɗan daudu ne. Ba sa ma damuwa da jin ko ya daina. A gida idan yace zai yi kuma akwai iyalinsa da ba zai so mutumcinsu ya zube ba.

Haka dai bayan kwanaki yana kai gauro da mari ya ce ya amince. Ya kuma duƙufa addu'ar neman taimakon Allah.

A lokacin kullum Hamdi tayi waya da gida sai anyi mata zancen Taj. Yaya da ƴan uwanta sunansa a bakinsu raɗau. Ita kuwa lamarin bai burgeta ba. Wanda zai zo ya mayar da Abbanta cikin sana'ar girki ba masoyi bane.

Su Taj da su ka tabbatar sun sami kan Abba sai aka fara shirin zuwa wajen Anisa. Lokacin bai fi kwana goma ya rage masa ya koma ba. A motar Kamal su ka tafi. Da yake ya san gari basu wahala ba da bin kwatance ta google map su ka isa gidan.

***

Aikin snacks da Anti ta ce a tanada saboda zuwan su Taj, Hauwa aka bawa. Hajjo tuni ta fesa musu dalilin zuwan nasa. Anisa sai murna. Sai dai anyi rashin sa'a ana gobe ranar tafiya ta kama ta. A waya ta basu haƙuri ta ce amma akwai ɗalibarta da duk abubuwan da su ka zayyano za ta iya ba tare da sun ji bambancin taste ba.

"Haɗani da ita" Anisa ta ce don in ba kayan Luciousbites ba, bata ganewa snacks ɗin.

A waya aka gama komai. Hamdi murna da godiya ta dinga yiwa Hauwa. Ita kuma ta dinga roƙonta kada ta kunyata musu brand.

Ƙoƙari kam bakin gwargwado tayi. Meatpie, doughnut da samosa su ke so. Sai coconut infused youghurt. Shi ne kaɗai Hauwan ta aiko mata da shi. Sauran kuwa babu komai a ƙasa dole sai anyi. Bayan ta gama ta kira numbar Anisan da aka bata ta sanar da ita an gama komai.

"To ki bawa mai delivery. Zan turo address."

Nan fa ɗaya. Bata san kowa ba. Anti Labiba ma ta dinga kiran mutanenta amma kowa sai ya ce mai delivery baya kusa. Hamdi ta kuma kiran Anisa. Lokacin ita kuma bata jima da yin waya da Taj ba. Yana ƙara neman kwatance. A yadda ta ƙiyasta bai fi minti goma zai kawo su gidan ba. Gashi babu wanda za ta iya aika. Gari an tashi da rashin mai. Duk wata motar gidansu tana layi sai guda ɗaya ta Daddy.

"Hamdiyya ko za ki ɗauko bolt ki kawo min. Zan biyaki kuɗin tranport ɗin. Fitar ce babu halin yi yanzu."

Hamdi ta faɗawa Anti Labiba. Su ka rasa yadda za su yi. Mijin Anti Labiba a wajen gari yake aiki. Ita kuma babu mota. Tayi shahada kawai ta samarwa Hamdi bolt ɗin.
RAYUWA DA GIƁI 13




Batul Mamman💖



Kada ku manta da bibiyar shafin Hauwa a instagram _@luciousbite.ng_ ko nemeta a waya ta wannan layin domin
_09078075182_ odar snacks da nau'ikan youghurt masu daɗi.





***

Irin rawar jikin da Anisa da Anti suke yi da Taj tuni ya sha jinin jikinsa. Shi da ya zo don su haɗu a sirrance ya zame ashe Hajjo tayi masa handsfree da alama. Kuma a ɓangarensu zancen ya sami karɓuwa.

Ɗakin Hajjo aka kaisu. Tana ganinsu ta washe baki tana tarbar Kamal.

"Sai ga Haffiness ɗin Haffi a Abuja. Sannu da zuwa Kamalu."

"Har kin ƙara masa wasali a sunan nasa kenan." Taj ya faɗi yana zama akan kafet. Ƙafafunsa ya miƙe da yake jin sun sage saboda zama.

Kamar ba da ita yake ba.Ta cigaba da yiwa Kamal magana
"Ya ka baro mutanen gida? Ya baban naku?"

Kamal ya amsa ta sake sako wata tambayar. Taj ya gaisheta har sau biyu bata amsa ba. Ya dai gane fushi take dashi. Bayan kuma shi ya kamata ya nuna ɓacin ransa da tayi saurin sanya shi cikin tsaka mai wuya. Yanzu duk gidan nan za su so jin matsayarsa kan maganar Anisa. Tunda yarinya dai alamu sun nuna ta amince, ana jin zance ya sauya salo nan gaba kaɗan za a ɗora masa laifi.

Share su ya yi ya kira uwayensa ɗaya bayan ɗaya ya sanar dasu sun iso lafiya. Sai kuma ya kira Abba shi ma. Su ka yi magana akan ɗan gyaran da za a ƙarasa a wurin da Taj ya kama musu kafin ya dawo.

"Hajjo in kin gama gaisawa da Haffiness ɗin nima ki ɗan bani lokaci don Allah. Yau za mu koma. Bana son mu yi dare."

A sukwane ta juyo rai a ɓace "banten uba! Ku iso yanzu ka ce kuma komawa za ku yi?"

"To ya za ayi? Aiki ya sako ni a gaba."

Dariyar Kamal a dalilin zolayarta da Taj yake sai ta gane ba tafiyar za su yi da gaske ba. Sha kunu gami da nuna masa yatsunta biyar.

"Buhun ubanka Tajo."

"Toohhh" Kamal ya kalleta da rashin jindaɗi. Dole taji kunya don bata ga alamun yana da idanu a tsakar ka irin na Taj ba.

"Ɗan uwan naka ne bashi da kirki Haffiness. Na yi masa maganar ƙanwarsa ya amsa rimi-rimi sai kuma ya shuka ni. Yanzu ma gajiya nayi ina ta tunanin ko yarinyar ce ta ce bata so shi ne na kira uwar na tambayeta."

Kai tsaye Tay ya tambayeta "Me su ka ce?"

Hajjo ta danƙara masa wani irin kallo "me kuwa za su ce sama da murna. Ko kai makaho ne ya dace ace ka fahimci yadda ake ta nan nan da kai ya sha bamban da lokutan baya."

Shirunsa a yanzu daidai yake da cutar kai. Idan ya kuskura ya fita daga ɗakin nan bai faɗi abin da yake ransa ba to tabbas aurensa da Anisa da wahala in ba ayi ba. Gyara zama ya yi ya ce,

"To ni dai gaskiya Hajjo..."

Yau da gobe tafi ƙarfin wasa. Kuma dai Kamal ya riga ya san ba so yake ba. Amma akwai kunya da kawaicin malam bahaushe. Rashin girmamawa ne idan Taj ya kalli tsabar idon Hajjo ya faɗa mata baya son jikarta.

"Hajjo magana ta gaskiya yanzu Taj tsoron ɗauko zancen aure yake."

"Saboda me? Yana da lalura ne?" Ta soma yi masa kallon ƙurilla.

Ya girgiza kai "a'a, amma kin san matsalar da yake fuskanta daga wajen Alhaji."

"Alhajin me?" Ta fara sababi "in kai ma baka da labari ka sani daga yau. Kakarku wadda ta tsuguna ta haifi Hayatu aminiyata ce ta ƙud da ƙud. Duk taurin kansa bai isa na faɗa ya faɗa ba."

Kamal ya jinjina kai yana kallon Taj ko zai agaza masa. Shi kuwa shiru ya yi yana kallonsu.

"Nima ba nufina zai ƙi maganar bane. Kawai dai shi Taj yafi son lokacin da zai yi aure ya kasance Alhaji ya daina fushi da shi. Baya son yadda ya kore shi daga gidan kuma ya hana ƴaƴansa shiga su ma."

Hajjo ta jinjina lamarin "da gaskiyarsa kuma. To amma indai auren gida ne irin wannan ai ita Anisan ta san komai. Ga ku duka kuna ta zumuncinku. Su Haj. Gambo ma dai ko da satar hanya na san za su fito ganin jikokinsu."

"Ko kin san zuwan nan har bakin mota Taj ya bishi amma su ka ja mota aka baɗe shi da ƙura? Shi ne ya yi alƙawarin ba zai yi aure ba sai Alhaji ya yafe masa."

Zancen ya fara shigarta. Kamal ya zama kamar wani lauya wurin jujjuya zance. A ƙarshe dai ya samu da kanta ta hango illar auren Taj a yanayin rashin jituwa da uba.

"Abin da za ayi ko Kamalu, ni zan sa a kira min Hayatun muyi magana. Na san ko babu komai idan yaji daga gareni zai girmama zancen. Ba zai wulaƙanta min jika ba."

Tamkar ya sanya ihu haka yaji a wannan lokacin. Ashe duk ɓaɓatun da yake ita wani angle ɗin daban take kallo. Miƙewa Taj ya yi ya fice ya barshi yana ta kame kame.

Falo ya koma inda ya yi sa'a babu kowa. Yana zama Kamal ya fito yana ta waigen baya.

"This woman is too smart Happy. Kana ganin ta toshe duk wata hanyar da zan ɓullo don a kwantar da zancen nan."

Murmushi Taj ya yi "kaɗan ma ka gani. Shi yasa na so faɗa mata gaskiya. Kai kuma ka hana."

"Haba Happy, wani abin ai sai da siyasa. Kara wani abu ce"

Kai Taj ya riƙe kawai. Kwanakin nan gajiya da damuwa suna yawan sanya masa ciwon kai. Tunda ya sami kan Abba abin ya ragu. Amma fa daga lokacin da su ka saka ranar zuwa Abujan shikenan bashi da wata walwala.

"Kan ne dai?" Kamal ya yi tambayar da kulawa yana dafa shi.

"Wallahi kuwa."

"Ka daina damuwa. Ba a yiwa namiji auren dole fa" Kamal ɗin ya yi murmushi.

"Happiness bana son takura ne. Sannan bana son ungratefulness. Ƙinta tamkar ban godewa kyautatawarsu bane."

"Don ka taimaki mutum kuma bai kamata ka ɗora masa nauyin da zai takura shi ba. Ni shawarata kawai tunda Hajjon ta ɗan fahimta ka cigaba da jan ƙafa. Kuna fara magana a fito mata as unromantic as possible. Kada ka sanya mata false hope. In anyi sa'a ta gudu da kanta."

Sai a lokacin Taj yaji sanyi a ransa. Ya miƙawa Kamal hannu.

"Happiness nawa ni kaɗai. Yadda ka ce hakan za ayi. Thanks bro"

***

Hamdi bata taɓa shiga motar haya a Abuja ba ita kaɗai. Ko yawon da su ka dinga fita da Anti Labiba farkon zuwanta, yawanci mijin Antin ke kai su. Ko kuma Anti Labiban ta kira bold ko uber. Hankalinta kwance yake tunda akwai idon garin. Yau da take ita kaɗai ne dai duniyar tayi mata zafi.

Na farko dai direban motar a ƙoyasinta zai yi biyunta. Ga jiki da bai ɓuya ba. Sannan babu tantama ba bahaushe bane. Inda zasu je kuma bata sani ba. Anti Labiba dai ta ce mata zasu bi ta titin hanyar Central Mosque ɗin da su ka taɓa zuwa. To gashi an fi minti shabiyar a titi amma babu masallaci babu alamunsa. Banda hawa da sauka akan wasu gadoji da ko wuƙa aka ɗora mata ba za ta gane ko ɗaya ba, babu abin da yake yi. Ga gudu da ta lura yana yi kamar walƙiya.

Hanjin cikinta su ka sami wuri su ka cure wuri guda. Zuciyarta tana harbawa kamar za ta fito waje. Sai kuma bisa rashin sa'a aka kira shi da wata wayar ba wadda take gabansa tana nuna hanya ba. Ya sanya earpiece a kunne ɗaya yana magana da yaren da bata ji. 'Passenger' da kuma 'get ready, I will be there soon' kaɗai ta iya tantancewa.

Habawa, duk wani labari da ta taɓa ji game da satar mutane sai da ya dawo mata. Jikinta ya dinga rawa. A hankali ta kama shessheƙar kuka don bata so yaji. Ta fiddo wayar da Anti Labiba ta bata da za ta taho ta tura mata message.

(Anti zai sayar dani a hanya ban san inda muke ba amma titin yayi kama da bayan gari)

Ta rubuta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login