Showing 180001 words to 182238 words out of 182238 words

Chapter 61 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

cinyarsa ya ɗorata. Rabi cin abinci rabi rarrashi da kalamai masu daɗi.

*
Murnar ƙaruwar da za su samu su ka gama yi sannan Kamal ya langaɓe kai ya ce
"Doctor zo ki gani ban warke ba har yanzu?"

Tayi dariya "Sai nan da wata uku."

"Come on Angel. Kada fa ki fara ɗaukin haƙƙina. Ni dai gaskiya so nake ki tare."

"Yanzu ba tare muke ba?"

"Tariyar gaske nake nufi. Ni ma so nake ki fara rigimar ice cream."

"Sai dai hot cream."

"Wasa ma ki ka mayar da maganar ko? Do you even love me Angel?"

Mubina ta koma gabansa ta durƙusa a gabansa ta kwantar da kanta a cinyarsa sannan ta sanya hannuwanta ta zagaye shi.

"Har ka fara kokonton son da nake maka?"

"I ....I am sorry." Ya shafa fuskarta "na fiye rashin haƙuri ko?"

"No, ni ce dai na fiye tsoro. I just don't want to take any chances."

"Ke ce likitan, dole nayi biyayya. Allah Ya kai damo ga harawa dai kawai."

Dariya tayi "In ce amin kuwa? Wannan addu'a kamar ana yi min tanadin cin zali."

"Meye wani cin zali? Ai kawai ki ce addu'ar mugunta nayi miki."

"Ni dai ban ce ba"

"Ni na ce"

Sun ɗauki lokaci suna zolayar juna da nunawa juna soyayya kafin yunwa ta hana su sukuni. Ya tashi zai je falo ɗauko mu su nasu abincin Mubina ta ce ya yi haƙuri domin kuwa bai kamata ya je inda ƙannensa su ke ba a wannan lokacin.

"Kema dai kin fiye assumptions. Ina gidan ai babu abin da zai faru."

Mubina ta ce "do you want to bet?"

"Happy fa ba kunya gare shi ba. Na haƙura." Ya koma ya zauna yana yamutsa fuska.

Sai da Mubina ta gama yi masa dariya sannan ta tuna masa da za su iya kiran su a waya. Taj ɗan duniya sai cewa yayi wai Kamal ya so yiwa Mubina horon yunwa ne, if not me ya hana shi fitowa?

"Mu da har muna tunanin rufo muku ƙofa on our way out."

"Ni ne fa Happy, na san ka farin sani. Mayar da maganar kaina kake son yi?"

Mubina da Hamdi dariya su ka dinga yi musu kawai.

***

Sati biyu ya rage bikin Zee wanda aka sanya wata shida bayan komawar su Abba Habibu Saudiyya. Sajida a lokacin watanta guda da haihuwar Ihsan mai sunan surukarta. Gidan Abba Habibu ya sha gyara amma ba mai yawa ba tunda yanzu babu mai zama.

A zuwan su na farko Abba Habibu ya nunawa Baba Maje rashin jindaɗinsa da ya tayar da maganar raba auren nasu. Aka tambayi Zee ko tana son rabuwar ta ce a'a.

Su Yaya sun nuna musu cewa zumunci yanzu aka fara in sha Allahu. Har gidan Ummi ma sun je. Babu alamun yunwa a tare da ita amma fa ba sai an faɗa ba fuskarta ta nuna bata jindaɗin rayuwar auren. Duk masifarta dole ta sanyawa zuciyarta haƙuri domin kishiyoyinta sun dama ta sun shanye. Uwargidan ma ƴar sara suka ce kafin aure. Ta biyun kuwa ƴar damfara ce ta buga misali. Da su ka shigo hannun Kofur Ɗanliti zance ya sha bamban. To ga Ummi ma ta zo hannu. Jiki magayi!

Da za su koma da Zee da Halifa aka tafi. Abba Habibu ya gayyato Ƴar Ficika da wasu cikin yaransa masu igama su ka koma tare. Nan fa sana'a ta kankama babu kama hannun yaro. Ta ƙarfin cin tuwo su ka canja akalar rayuwarsu daga ƴan daudu abin ƙyama zuwa maza masu sana'ar abinci. Sai ga Ƴar ficika ya sami mata, wata ƴar dattijuwar takari. Mata ta zage ana ta sana'a da ita maimakon yawon unguwa unguwa neman abin yi. Cikin watanni kacal rayuwarsu ta sauya gabaɗaya. Duka kuma albarkacin sadaukarwar da Yaya tayi wadda bata taɓa tunanin wani mahaluƙi zai saka mata a kai ba.

*

Dinner ta ƴan boko, ƴan gayu kuma masu kuɗi Kamal ya shiryawa Zee. Bai yarda ko sulai biyar wani ya saka masa ba. Taj ya ce zai ɗauki nauyin abinci amma yaƙi. Zama ya yi aka yi lissafi ya cake wa Happy Taj kuɗinsu. Ango Sadiq wato Baballe kuma ya sha gargaɗi da jan kunne akan ya riƙe amanar ƙanwarsa. Abin na Kamal dai harda ƴar barazana.

Yaya saka shi tayi a gaba saboda ɓarin kuɗin yayi yawa.

"Kamal don Allah ka saurarawa kanka haka nan. Wallahi domin Allah na baka ƙodar nan. Kana saka ni jin nauyinka da na su Hajiya. Ɗawainiya da kashe kuɗin ya yi yawa."

"Yaya da ke ki ka haifeni za ki ce kyautatawar da nake muku da ƙannena ta yi yawa?"

Yaya tayi shiru.

"Yaya da kin san yadda ɗan Adam yake ji idan ya hango ƙarshen rayuwarsa kuma babu hanyar gudu da baki ga wauta ta ba. Ga ciwo ga tashin hankalin sanin bani da wata mafita." Idanunsa su ka yi jawur amma bai bari ƙwalla ta zubo ba "ga kuɗi, ga dangi amma babu mai ceto. Yaya, a wannan lokacin ban dinga tuna komai ba sai ranar da kowa zai juyawa masoyinsa baya saboda tsananin tashin hankali. Duk wanda Allah bai taimaka ba a lokacin to dole ya cire rai da samun kowane irin taimako." muryarsa ta soma rawa "na hangowa kaina rayuwar barzahu da tashin hankalin da mara rabo zai riski kansa... bani da tabbacin tsallakewa. Komai ya zo gab sai Allah Ya kawo ki. Yaya babu tunanin taki makomar da ta iyalinki ki ka kwanta aka cire taki ƙodar domin na sake shan iskar duniya. Domin iyayena su share hawayensu..." ya miƙe tsaye "ban isa na biya ki ba amma kuma ba zan taɓa gajiya da yi miki hidima ba in sha Allahu. Kin isa, kin cancanta. Don Allah kada ki sake nuna rashin jindaɗin ki idan nayi wani abu."

Ƙwallarta ta goge tayi masa murmushi "idan da ni na haifeka zan karɓi duk abin da ka kawo min cikin farinciki amma duk da haka zan ce maka ka dinga yi saisa-saisa saboda kaima ka kusa zama baban wasu. Haihuwa ba a yi mata tanadin gobe ko jibi sai ta baka mamaki. Sayen pampas kaɗai ya ishe ka ka gane ba ka da wayo" ta ƙare maganar tana dariya.

"Ki yi min addu'a kawai, Allah Ya ƙara buɗa min. Tanadi kuma in sha Allahu zan kiyaye shawararki."

"Allah Ya yi maka albarka Kamal banban ɗan Jinjin"

"Abu Khadija za ki ce." Ya sunkuyar da kai yana susar ƙeya.

Tare su ka yi dariya sai ga Abba Hayatu nan.

"Agolan gidana me ka ke yi a nan ka zo ka saka min mata kuka?"

"Sirrin uwa da ɗa ne Abba."

"Nima yanzu mu ka gama namu sirrin da Taj babban ɗana."

Kamal ya ce "Sirikinka dai. Mijin ƙanwata."

Yaya da Abba Habibu dariya su ka yi. Kamal ya fita ya shiga mota su ka tafi gida da Taj da yake gidajensu babu nisa da juna. Mubina tana gida laulayi ya make ta amma ta gama shiri Hamdi kuma ciki ya tsufa sosai. Haihuwa ko yau ko gobe.

*

Kukan Hamdi na huɗu kenan yau saboda Taj ya ce ba za ta je dinner ba. Da ya shigo kallon juna su ka yi kowa ya ɗauke kai. Yana fitowa daga wanka da gangan ya leƙo falo.

"Taso ki fito min da kaya."

"Suna kan gado."

"Turare fa? Wanne zan saka?"

Ta sake kawar da kai "Na fesa a jikin kayan"

"Body spray fa?"

"Akwai akan dressing mirror." Ta san jan magana ne kawai tunda abubuwa ne da yake yiwa kansa.

Ya koma ya shirya cikin ankon su na shadda shi da su Kamal. A gabanta ya tsaya ya cika mata hanci da ƙamshi mai daɗi.

"Menene ne kuma?" Ta ce da muryar kuka.

"My goodbye kiss."

Da kumburarrun idanunta ta harare shi "na ajiye a ƙofar gida."

"Wannan kuma ba ki isa ba. Ki min kawai na tafi."

"You are looking for my trouble." Ta tura baki tana jan hanci.

"Yep."

"Wai me nayi maka ne?"

"Kin kasa kallona saboda kina fushi ki ce nayi kyau."

Satar kallonsa tayi ta ce "kayi kyau."

"Ko ke fa. To tashi ki shirya mu tafi."

Maganar a bazata ta shiga kunnuwanta. Ta tashi da ƙarfinta ta rungumo shi tana dariya.

"Da gaske kake?"

"Idan naƙuda ta taho ki tabbatar kin riƙeta tunda rigima ta sa ba ki son zama a gida."

Da dariya Hamdi ta ce "ni fa ba bikin ne ya dame ni ba. Ƴan matan da za su ji ka burgesu nake son na hana samun dama. Ka sanni da kishi."

Taj ya tuntsire da dariya. Ya zauna ya ce mata nan da minti shabiyar idan bata fito ba zai tafi. Da sauri ta dinga komai. Ta fito a minti ashirin da biyu. Taj yana zaune yana waya. Hannunta ya riƙe su ka fita daga gidan tare.

*
Biki yayi biki domin ya sami halartar mutane da dama cikin ƴan uwa da abokan arziƙi. Ƴan uwan Yaya da ƴaƴansu sun zo daga Batsari tare da Inna Luba. Ya'u ya zama na hannun daman Yaya Kubra domin har ta mayar da shi makaranta. Amma da su Anisa harda Hajjo su ma sun zo. Ƴar ficika da matarsa ba a barsu a baya ba. Haka dangin Alh. Hayatu da na matansa na kurkusa duk sun zo.

Ahmad ya taho da Zahra sannan ya ce Salwa lallai sai ta zo saboda shi bai ga amfanin ƙauracewa mutane ba. Idan ana haɗuwa ko yaya yau da gobe za a iya yafe mata.

To ashe Ummi ma da kishiyoyinta harda maigidan Kofar Ɗanliti su ma sun taho. Hamdi ta tako da ƙyar take ɗaga ƙafa taji kamar da mutane a gefenta. Ta juya hagu ta haɗa ido da Salwa gayauna. A ɓangaren dama kuma Ummi yangaura. Kowacce ta lalace ta fita hayyacinta. Su ukun suna yiwa juna kallon kallo su ka tsinkayi muryar Taj daga bakin ƙofar hall ɗin.

"Ke da na ce ki jira ni a mota in fara sama miki wurin zama? Na zo na ɗauke ki?"

Salwa da Ummi su ka bi shi da kallo. Ya fi Taj ɗin da su ka sani cika, kyau da ɗaukar ido. Aure ya karɓe shi kamar yadda ya karɓi matarsa. Ko me su ka ji a ransu ba su furta ba.

"Ka zo ka tayani tafiya dai."

Taho wa ya yi Hamdi ta saƙale hannu a waist ɗinsa saboda support su ka dinga takawa tare har su ka ɓacewa ganinsu. Sai su ka sake kallon juna, kowacce ta buga tsaki. Za su fara cacar baki sai Ummi ta kula Alh. Usaini yana tahowa. Yadda Salwa ta fige shi har ya fi ta. Wata muguwar dariya ce ta suɓuce mata bata sani ba. Kamar daga sama taji muryar Kofur.

"Ummi ban hana ki dariya irin wannan ba?" A gefensa hagu da dama kishiyoyinta ne.

"Wai, sannu fa." Salwa ta ce sannan ta rama dariyar da tayi mata.

*

A falon gidan Abba Habibu, shi ne da Alh. Hayatu su ke hira irin tasu ta manya. Hirar yawanci ta iyalansu ce da abubuwan da su ka shafi rayuwar yau da gobe.

Can dai Alh. Hayatu ya ce "ni kuwa Habibu akwai abin da nake sha'awar ci amma na kasa faɗawa iyalina tunda ban saba ba."

"To ya aka yi ka san kana so tunda baka ci?"

"Ka san jikoki akwai kyauta. A baki aka zo aka bani rannan da aka yi. Si ka tayar min da kwaɗayi amma ban isa na nemi ƙari ba kada na zama abin surutu a gidan."

Abba Habibu ya miƙe yana dariya "ban yi ritaya ba har yanzu. Ya sunan sa in dafa maka?"

"Wainar fulawa" Alh. Hayatu ya faɗa yana wani basarwa don kada Abba Habibu yayi masa dariya. Bai tsira ba kuwa don sai da ya yi masa dariyar sannan ya shiga kitchen.

Bayan minti talatin Alh. Hayatu ya ɗora babbar rigarsa a saman kujera wai kada ta ɓaci da manja. Ya zauna a kan kafet yana cin wainar fulawa yana jindaɗi sai ga wayar Kamal sun wai wuce asibiti da Hamdi shi da Mubina da Taj. Iyayensu sun biyo bayansu.

Ya kalli plate ɗin ko rabi bai ci ba kamar kada ya tashi don wannan tafi wadda aka yi a gidansa daɗi. Sai da ya ƙara loma guda sannan ya tashi su ka tafi asibitin. Suna shiga Mubina na fito musu da jariri.

Abba Habibu ya ce a miƙawa Alh. Hayatu. Yana karɓa sai cewa ya yi "wainar"

Abba Habibu ya yi saurin cewa "Wai ina wa?"

"Wai ina maigidan nata?" Alh. Ya wayance.

"Gamu nan fa Alhaji."

Ya juya ashe sun wuce kowa a wurin bai sani ba. Farin kaya mai tonon silili Inna ce ta fara cewa

"Mene ne wannan a gaban rigarka Alhaji?"

"Ina babbar rigarsa za ki ce" in ji Mama.

Hajiya ta ce "Ƙamshin manja nake ji kamar wainar fulawa."

Alh. Hayatu da Abba Habibu su ka soma kame kame duka wajen ya kaure da dariya.

Basu bar asibitin ba sai da aka fito da Hamdi kowa ya ganta lafiya. Alh. Hayatu ya miƙa mata jaririn da amarya Zee ta ƙanƙame bayan iyaye sun gama saka masa albarka. Ya miƙawa Hamdi bayan ta zauna akan gado.

" Hamdi ga Habib Tajuddeen Hayatu. Allah Ya raya shi bisa sunnar Ma'aiki SAW. Allah Ya sa ya yi koyi da kyawawan halayen mai sunansa."

"AMIN" kowa ya amsa da farinciki.

Abba Habibu da bai taɓa zaton wannan karamcin ba ya rasa me zai ce sai kawai ya dinga murmushi yana godiya ga Allah da Ya nufe shi da ganin wannan rana.

Alhamdulillah bata gushe daga bakinsa ba har ya kwanta yana tunanin rayuwar duniya mara tabbas. Ace har ya yi ƙimar da za a yi masa takwara?

"Allah na gode Maka. Ya Rabbi Ka ƙara shiriya da albarka ga iyalanmu da mu kan mu. Ka raba mu da bin hanyar taɓewa. Ka dawo da ɓatattun cikin mu hanya madaidaiciya. Amin"




HAMDAN KATHIRAN ƊAYYIBAN MUBARAKAN FIHI.
Ya Allah Ka yafe min kurakuran da su ke ciki. Ka sa mu amfana da darrusan. AMIN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login