Showing 45001 words to 48000 words out of 182238 words
Chapter 16 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
yawo. Idan ta dawo ayi faɗan, dukan da nasihar duk a bayan kunnuwanta. Shafawa idanunta toka kawai tayi tana abin da ranta yake so. Cikin watanni kaɗan ta ɗashe fata ta koma fara tas. Ga magungunan da take sha na supplement masu ƙara wasu sassan jiki. Halittarta duk ta sauya ta koma wata daban. Duk inda ta ratsa maza ke bibiyarta suna kashe mata kuɗi. Wayo da dabara irin nata yasa taƙi yarda ta bada kanta. Amma fa tana bari su fanshi wahalarsu ta hanyoyi daban daban. Hukuncin faɗa da duka ya ƙare. Sai nasiha da addua tsakaninta da iyayenta.
Halin da ta shiga yana ci wa Abba da Yaya tuwo a ƙwarya. Gani su ke kamar sanadiyarsu rayuwar ƴar aminansu ta gurɓace. Yayinda su Baba Maje kuma su ke ganin dubunta ce ta cika. Halayen da take ɓoyewa su ka bayyana. Ba don abin da ta yiwa Hamdi ba da haka za ta yi ta ha'intarsu ƙila har gidan miji tana rayuwa biyu ba a sani ba.
Ummi ta sake ɗaura ɗammarar watsa rayuwar Hamdi a duk lokacin da nata auren ya tashi. Kuma tsakin da tayi ba komai ya janyo ba sai takaicin lokacin ramuwarta da bai yi ba.
***
Kimanin sati uku kafin bikin Sajida aka gama komai da ya dace a HAPPY TAJ. An kashe kuɗi domin ƙawata wajen yadda zai janyo mutane. Taj da Abba da kansu su ka dinga yiwa mutane gwaji idan sun zo neman aiki. Banda yaran Abba, sai da su ka ƙara mutane masu ayyuka daban daban a kitchen ɗinsu. Girki, wanke wanke, serving abinci, waiters, cashiers da masu yin fruit juice, mocktails da icecream. Gabaɗaya kitchen ɗin maza ne. Sannan ya nemi inda za su dinga sayen kayan abinci. Komai ya tafi cikin tsari. Ƙannensa Bishir da Abba su ya damƙawa ragamar tabbatar da kayan buƙatar kitchen ba za su yanke ba. Sun daidaita da masu kayan masarufi na kasuwa akan wannan. Spices kuma na recipe ɗinsh za su dinga haɗawa saboda haka raw ɗin kawai su ka nemi mai kawowa. Dankali da kayan miya kuma fresh masu kyau da tsafta daga wajen ƙawar wata sister ɗinsu Rumanatu mazauniyar Jos (08065530483) za su dinga saya. Ya zamana dai babu inda su ka bari haka nan.
Masu naman tsire ko gashi su ma interview da gwaji aka yi musu. Iyawa kaɗai bata da garanti sai an duba tsaftar mutum da ingancin kayansa. Haka kuma aka yi a ɓangaren kayan fulawa. Saboda kawai Taj yana son ɗaukar Hamdi sai ya ce bakery ɗinsu mata za a saka.
Application babu kama hannun yaro. Da ƙyar su ka zaɓa don babu laifi a Kano akwai masu sarrafa fulawa daban daban da kayansu suke da inganci. Wata ƙanwarsa da ta dinga zuzuta masa ƙawarta Zahra wadda aka fi sani da Donutfairy (08065156303), dole yace a nemota. Ya ɗanɗana doughnut, banana bread da youghurt ɗinta. A take ya nemi signing contract da ita tunda matar aure ce. Aka ƙayyade adadin abin da za ta dinga kawowa kullum da farashinta.
Ɓangaren Kamal ma boutique ya tashi sai wanda ya gani. Garden da wurin wasan yara duka an gama zuba ma'aikata. Ranar Juma'a aka yi sauka domin kore kowanne shaiɗanci da neman albarka daga Allah. Sai kuma aka sanya sati mai zuwa a matsayin ranar buɗe restaurant ɗin. Anyi ta sanya talla ta gidajen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta. Akwai discount ga mutanen da za su zo a wannan rana. Ga kyaututtuka na yara domin za su yi gasa da wasanni.
Garin Kano ya ɗauka. Ko ina ka zaga ana jiran ranar buɗe Happy Taj.
*
Gidan Alh. Hayatu ya hargitse da shiryawa wannan rana. In ka duna status da stories ɗin ƴaƴa da jikokin gidan ds su ka tasa, gabaɗayansu abin da su ke ɗorawa kenan. Sai kuma hoton Taj sanye da wasu fararen kaya na girki ya riƙe irin kaskon nan na zamani mai ɗan zurfi da dogon mariƙi a hannu ɗaya, sai kuma cokalin juyawa a ɗaya hannun. Harɗe hannuwansa ya yi dasu irin yanayin tsayuwar Black Panther idan sun yi alamar Wakanda Forever. Yayi matuƙar kyau da kwarjini a hoton. Ƙaryar mutum ya gan shi ya danganta shi da mace. Murmushin fuskarsa yafi komai tafiya da hankalin mai kallo.
Yadda ake ta shiri da farinciki a gidan Alh. Hayatu, haka ma su Sajida su ke ta murnar wannan ɗaguwar daraja da mahaifinsu zai samu idan ya fara aiki a Happy Taj. Har anko Abba ya yiwa ƴaƴansa. Yaya kuwa nata kayan sun fi nasu tsada ma. Kowa ya yi murna banda Hajiya Hamdi. Gani take ba a rabu da Bukar bane an haifi Habu. Abbanta zai baro local ƴan daudu su Ƴar Ficika, ya koma hannun international ɗan daudu wai shi Taj. Ita dai da tana da iko da ta hana shi wallahi. Har mamakin yadda kowa na gidan yake ƙaunar Taj ɗinnan take yi.
***
Komai nisan dare gari zai waye. Bayan shafe shekara guda da ƴan watanni, gobe ne ranar da za a buɗe Happy Taj.
Tunda aka saka rana Hajiya, Mama, Umma da Inna duk kawaicinta su ke roƙon Alhaji da ya yi musu izinin zuwa. Amsar da ya basu ita ce ba zai hana kowa fita ba amma idan sun tafi kada su dawo. Mama da Inna har kuka su ka yi. Ya ce ai bai hana su ba. Kowacce tana da damar zuwa amma tabbas bai yarda su dawo gidansa. Hajiya ta kai ƙararsa wajen Yaya Babba sai dai dattijon ya ce ba zai ƙara yiwa rayuwar ƙanin nass katsalandan ba. Har yau yana ganin laifinsa ne korar Taj da Alhaji ya yi.
Suna ji suna gani ƴan uwansu da na mijinsu da ƴaƴansu duk zasu amma ya yi musu shamaki. Walwala da farinciki sai su ka yiwa gidan kaɗan.
Taj bai fasa sanar da Alhaji duk abubuwansa ba kamar yadda Amma ta koya masa. Saboda haka duk wani abu da ya danganci restaurant ɗinnan tamkar dashi ake yi. Har hotuna da bidiyo yake tura masa. Bidiyon ƙarshe da aka yi kamar film na minti ɗaya da rabi shi yafi komai ƙayatarwa. An bi ko ina a wurin daga gate har ƙurya. Ga ma'aikata da shi kan shi CEO Taj cikin farinciki suna ta aiki a wajen. Ya kwanta tun wajen tara na dare sai ya kasa bacci. Kewar ɗan nasa tayi masa wani irin kamu. Ya yi kusan awa biyu yana juyi a kwance ƙarshe ya tashi ya ɗauki muƙulli ya fice.
Kowa ya yi mamakin fitarsa a wannan lokacin. Kamal zai bi shi Hajiya ta hana.
"Wallahi kewar Taj yake. Ku rabu dashi. Bashi da aiki sai kallon waya. Rannan da kunnena naji muryar Taj a wannan bidiyon da yara ke yawan kunnawa. Tunda girman kai ya hana shi dawo dashi gida sai ya yi ta wahala shi ɗaya."
"Hajiyarmu yau da kanki?" Abba ya faɗi da mamaki. Don ita bata da zafi kamar sauran matan.
"Fita idona ni."
Ta koma ɗakinta ta kwanta. Sauran matan ma duk su ka watse. Inna ce da ta shiga ɗaki ta dinga addu'ar Allah Ya daidaita lamura tsakanin uba da ɗan.
To dai Alhaji bai zame ko ina ba sai Happy Taj. Shi da ya jima bai yi tuƙi ba ko a jikinsa yau. Ga dare amma haka ya fito ya tsaya a bakin gate ɗin. Ya kalli ginin da wani irin pride yana jinjina kai. Tabbas yana cikin farinciki. Taj bai lalace yadda ya zata ba. Kuma a yau ya ɗauki sama da mutum ashirin aiki da kuɗin halalinsa.
"Allah Ya yi maka albarka" ya furta a zuciyarsa.
Ya kai hannu ya dafa gate ɗin. Jiniya har ta fara wiii, wiii sau biyu sai ɗif ta ɗauke. Alh. Hayatu ya sake dafa gate ɗin a karo na biyu yaji shiru. Addu'a sosai ya karanta ya tofa a jiki sannan ya koma mota ya tafi.
Taj dake ciki yana ƙarasa wasu cike ciken takardu ya share ƙwalla bayan tafiyar Alhajin. A gaban kwamfuta yake aikin inda take nuna masa ko ina da taimakon cctv. Yana ganin zuwan Alhajin ya ajiye aikin gabansa. Zuciyarsa ta shiga wani irin bugu mai tsanani. Ya tashi zai fita sai kuma ya fasa. Yana gudun kada zuwan nasa ya janyo wata matsalar tsakaninsu. Shi ya kashe jiniyar alarm ɗin tsaro da Alhaji ya taɓa gate ɗin. Yana ganin ya tafi ya fito ya ɗora hannunsa a inda ƙiyasinsa ya nuna mas Alhajin ya saka nashi ya sumbata. Wannan abu ya sanya shi farkawa da wani irin farinciki, jindaɗi da annashuwa washegari.
*
Amma da iyalin gidanta harda Hajjo a Kano su ka kwana. Da misalin ƙarfe biyu da za a buɗe gate ɗin ita da Anti da ƴaƴansu suna sahun gaba. Iman ɗinta dake Lagos ma ta zo da ƴaƴanta. Ga Anisa da Anti takanas tasa aka kira mai kwalliya ta gyare mata fuska. Ita kanta wani irin nishaɗi take ji a zuciyarta. Idan Allah Ya bata Taj, sai tafi kowa murna.
Ya Ahmad ma da iyalinsa suna kan layi. Anti Zahra da su Hayat an sha ado kamar za su biki. Salwa kuwa musamman Mami ta aiko mata da sababbin kaya daga Bauchi. Light make up tayi amma ba yadda za ayi ta wuce lafiyayyen namiji ya kasa yi mata kallo na biyu.
A cikin wani adaidaita sahu dake fake a wurin kuwa Hamdi ce take cika tana batsewa. Sajida da su Zee sun fito suna tsaye a bakin gate. Yaya kuwa duk yadda Abba ya kaɗa ya raya taƙi zuwa. Wai abin yara ne. Sai dai shi da ya santa yafi kowa fahimta. Har kullum bata fiye son su fita lokaci guda ba. A ganinta suna zubar da darajar ƴaƴansu ne. Uba ga yadda yake, ita kuma tun ƙuruciya har da girmanta ba a rasa yaran dake kwaikwayon tafiyarta. Sai ta zaɓi ɓoye kanta a gida don kawai ta tsira da mutumcinta.
Yau Abba har fushi ya yi amma taƙi. Wurin sana'arsa da take sa ran samun ɗaga darajarsa bai dace da ita ba. Yaran nasu basu san wainar da ake toyawa ba. Da Hamdi ba za ta taɓa yarda ta fito ba. Su duka suna ƙaunar Yaya kuma basa jin kunyarta.
"Ya Hamdi ki fito mana" Halifa ya dawo ya kuma kiranta don shi baya fushi. Su Zee ne su ka gaji da jiran ta sauko su ka yi tafiyarsu.
Da ƙyar ya samu ta fito. Haka kawai da su ka isa gate ɗin ta fara jin yanayinta ya sauya. Ita da bata son zuwa sai farinciki ya ziyarceta har tayi murmushi bayan ta saka ƙafarta a ciki. Tunda ababen hawa basu shiga saboda cikowa, a hagunta Salwa ce take shigowa, a damanta kuma ba tare da ta kula ba Anisa ce da su ka taɓa haɗuwa a Abuja watannin baya.
"Assalam alaikum wa rahmatullah"
Muryar Taj ta karaɗe wurin ta speaker a daidai lokacin da su ke shiga.
RAYUWA DA GIƁI 15
Batul Mamman💖
Sautin amsa sallamar cika wajen ya yi kamar zai fasa kunnuwa. Kusan a lokaci guda Hamdi, Salwa da Anisa su ka toshe kunnuwansu. Sakamakon ƙatuwar sipikar dake kusa dasu wadda ta ƙara ƙarfin sautin. La'akari su ka yi da toshe kunnen da su ka yi a lokaci guda sai su ka kama dariya.
Anisa dakatawa tayi da ta kalli fuskar ƴan matan dake gabanta. Bata san Salwa ba, amma ta so ta tuna Hamdi. Ita ma Hamdin sai aka yi dace ta kalleta a lokacin. Mamaki ne ya kama ta domin kuwa babu yadda za ayi ta ce ta manta kamanni da sunan Anisa.
Girarta ce ta ɗage tana mai yi mata kallon sani ta ce "Anisan Abuja?"
Gaban Anisa ya yi wani mahaukacin faɗuwa. Ba wai son ganin Hamdin ne bata yi ba. Abin da ya kawota taron buɗe restaurant ɗin Taj wanda bata manta ba shi ya dinga rarrashinta a waya har su ka isa inda take a lokacin nan. Kada dai irin abin da take karantawa a social media a ce vendor tayi snatching miji ko saurayin costumer ne zai sameta?
Hamdi kuwa tunda gari ya waye sai yanzu tayi dariyar da ta kai mata zuci. Fuskarta ta haskaka da farincikin da yake ranta.
"Allah Sarki. Naji daɗin sake ganinki. Lokacin da mu ka haɗu bani da waya. Daga baya da nayi kuma Anti Labiba ta ce ashe bata yi saving number ɗinki ba."
Da ƙyar Anisa ta haɗiyi yawu ta ƙirƙiri murmushi. Yanayinta na rashin nutsuwa duka a idon Salwa. Har ta kai ta matsu da son sanin me ya kawo wannan canji a tare da Anisan. Zuwan Sajida da Zee wajen ne ya taimakawa Anisa ta samu ta daina murmushin dolen da take ta yi.
"Hamdi zo mu zauna ga seat Yaya Kamal ya ce sai an gama speech za a buɗe ko'ina a shiga."
"Har Kamal kin sani?" Anisa ta ce a gigice, sai kuma tayi saurin canja zancen da taga suna kallonta da rashin fahimta "kuna da alaƙa da Kamal?"
Hamdi bata da amsar bayarwa don Kamal ɗin ma bata taɓa gani ba. Sunansa kawai ta sani. Ta kalli Sajida tana jiran tayi bayani sai jin baƙuwar murya tayi tana yiwa Zee magana.
"Abba Habibu ya shigo kuwa Zee? Taj ke tambayar...."
Kasa ƙarasa magana yayi. Ya tsaya kallon Hamdi ba shiri da irin mamakin da ta gama na ganin Anisa. Ya kalleta, ya kalli Sajida da Zee sannan ya yi magana.
"Ke ce Hamdi?"
Murmushi tayi da kunyar tuna abubuwan da tayi a gabansu wannan ranar.
"Ina wuni?"
"Ba zan amsa ba don naga alama da gangan ki ka dinga wasan ɓuya don kada mu haɗu." Ya kalli saman stage inda Taj ya juya musu baya yana magana "bari Happy ya gama speech ya zo ya ga mai kukan bolt."
Ba don hayaniya ba da sai kowa yaji sautin wucewar wani abu kamar dutse da ya tokarewa Anisa wuya tun ɗazu. Maganganun Kamal sun tsefe mata zargin da zuciya ta fara kitsa mata. Ba kunya ta saki fuska tana dariya harda cewa,
"Ai kuwa na san zai yi mamaki."
Kamal kuma ya dubi Sajida bayan ya gabatar musu da Salwa a matsayin ɗaya daga cikin ƙannensa.
"Na jima ina son tuna inda na taɓa ganin mai kama daku na kasa. Da yake ban ma riƙe sunanta ba lokacin haɗuwarmu a Abuja shi yasa ban taɓa alaƙanta ku ba."
"Ikon Allah kenan. Muma fa ta bamu labarin haɗuwar taku." Sajida ta faɗi tana kallon yadda duk wani haske na fuskar Hamdi ya ɗauke kamar an ɗauke wuta.
Taɓota tayi sai tayi firgigit ta dubi Kamal ta sake kallon saman stage inda Taj yake tsaye. Dutsen da ya bar ƙirjin Anisa ashe nata ya koma. Ya haɗe mata da wani irin ɗaci na tsagwaron disappointment. Kallon mutumin da ta kasa cirewa daga ranta har rana irin ta yau a matsayin Happy Taj kawai take yi. Ubangidan Abbanta wanda take baƙincikin shigowarsa cikin rayuwarsu da ƙara ingiza mata uba ya cigaba da girki. Daina jindaɗin komai tayi a wajen sai tsananin son ta ganta ƙudundune akan katifarta a ƙuryar ɗaki. Ƙafafunta su ka koma tamkar leda don ji tayi kamar ba za su ɗauketa ba.
"Hamdi lafiya kuwa?"
Anisa ce tayi tambayar ganin ta dafe kai gami da runtse idanu.
Ƙaryar da ta fara zuwa kanta tayi musu.
"Jiri nake ji. Haka kawai kaina ya soma ciwo."
Da tausayawa Kamal ya kalleta "muje in sama miki inda za ki huta ba tare da hayaniya ba."
"Gida zan tafi" ta faɗi tana mai danne kukan da taji ya taso mata. Abin takaici bata ma sani ba kukan na mene ne yake barazanar kunyata ta a gaban mutane.
"Yanzu wajen nan fita ma aiki ne. Ki huta ɗin dai zai fi. Maybe kema ba mai son taro da hayaniya bace kamar Happy."
Kwatanta ta da Happy ɗinnan ƙara mata ciwo ya yi a zuci. Kamal ya ce su Zee su zauna zai je ya dawo. Sajida ta so bin su ya nuna gara ta zauna da ƙannenta. Zai nemi mai zama da Hamdi har taji sauƙi ta fito.
Suna tafiya Salwa ta gallawa Anisa harara irin wadda ake cewa aikin banza harara a duhu domin babu wanda ya kula. Sai ta ja tsaki da ƙarfi sannan ta bar wajen. Babu abin da bata sani ba game da Anisa a cikin gidan Ahmad. Hirar su ka yi da su Taj a waya a gaban Zahra. Ita kuma saboda yadda take ganin Salwa taƙi haƙura dashi shi ne ta faɗa mata anyi masa mata a gidan Amma.
Su Zahra da sauran ƴan gidansu Taj ta tafi nema. Ita ma Anisa ta tafi wajen su Anti. Zee da su Sajida ma su ka koma daga gaba inda za su ji kalmomin godiya da Taj yake yiwa duk wanda ya zo.
*
Ta wata ƙofar baya Kamal ya buɗewa Hamdi ainihin ginin Happy Taj. Wani ni'imtaccen sanyi da ƙamshi mai kwantar da hankali ya baƙunceta. Mantawa tayi da ciwon kai ta zuba ido tana kallon yadda aka ƙawata wajen kamar ba a Kano ba. Kodayake dama bata taɓa zuwa wajen da ya kama ƙafar wannan a kyau da tsari ba.
Sama ya su ka hau. A nan taga banda jerin tebura da kujerun masu cin abinci akwai ƙofofi a rufe. Ƙofa ɗaya ya buɗe mata ya tsaya daga gefe.
"Akwai ruwa da juice a fridge. Ga key sai ki rufe ta ciki. Idan kin ji ƙarfi za ki iya fitowa kawai ki ƙulle." Kujera ya nuna mata ta cushion mai irin ɗuma-ɗuman nan a can gefe da pillow na alfarma "ki kwanta a can. Ko kina so zan turo wata cikin ma'aikatanmu ta taya ki zama?"
"A'a nagode" ta sake kallon wajen "ni da ka barni na tafi gida ma."
"Not an option. Kina fita ƴan uwanki za su bi ki. Kinga kin shiga haƙƙinsu ko?"
Murmushi yayi ita ma ta mayar masa. Bata ga alamun samun nasara a tare da shi ba. Yana tafiya ta ƙulle ƙofar ta zare muƙullin tana juya shi a yatsanta ta haye kujerar ta kwanta. A gaban kujerar akwai two seater da one seater ɗinta a gefen hagu da dama. Tsakiya teburin gilas ne wato center table akan lallausan kafet sai TV da tarkacen kallo a kan wata irin tv stand ta alfarma mai kallo ƙofa. Ɓangaren lungu ya shige ta yadda ba a ganin mene ne akan kujerar sai an zagayo gabanta.
Da yake a office ɗin