Showing 99001 words to 102000 words out of 182238 words

Chapter 34 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

niyya ba."

Muryarta ta sake karyar masa da zuciya.
"Duka ba halina bane. Ki yi haƙuri."

Da ka ta amsa. Ya sanya hannayensa duka ya rungumota. A lokaci guda kuma zuƙatansu su ka dinga harbawa da faɗuwar gaba. Kamar hakan laifi ne gagarumi. Kusan a tare su ka saki juna.

"Mu yi sallah sai na samo miki abinci. Me za ki ci?"

Zumɓura masa baki tayi "ni bana cin girkin maza."

Ya ɗage gira yana ɗan murmushi "da gaske?"

Ta san manufarsa shi yasa ta ce "sai na Abbana kaɗai."

"Za ki ci nawa nima." Ya ɗauko copy ɗin menu ɗinsu daga kan table ɗinsa ya bata.

Ko buɗewa bata yi ba ta ce " abin da babu a nan zan ci."

"No problem."

Sallar azahar su ka yi. Ya ce ta jira shi zai iya kaiwa awa ɗaya kafin ya dawo. Tana ji ya rufeta da muƙulli ta waje. Ta koma kan kujerar da ta taɓa yin bacci ta kwanta ta rufe ido. Ƙamshin turaren Salwa da ya kama office ɗin yana cigaba da shigarta a hankali. Shi ma kuma da ya shiga kitchen ɗin, ƙamshin da ya rage a wuyansa tunda ya wanke hannayen a wajen alwala ne ya dinga bugarsa. Yaransa suna son zuwa ganin sabon girkin da babu a menu ɗinsu amma a karon farko ubangidan nasu bai bada wannan fuskar ba. Ya gama dafa Afghani pulao ɗinsa yana kaucewa haɗuwa da Abba. Saboda gani yake suna ganin juna zau gane me ya yiwa ƴarsa.

***

Ummi da Salwa rungume juna su ka yi cikin farinciki bayan ta koma. Alh. Usaini yana daga cikin mota yana kallonsu. Murmushi ya saki na samun nasara. Malamin tsibbun da ya bashi turarukan ya tabbatar masa da cewa babu abin da zai hana shi samun biyan ɓukata. Duk abin da zasu yi basu isa su kara dashi ba. Turaren farko na raba Taj da matarsa wanda shi ba abu bane dake gabansa, ya dai karɓa ne saboda Ummi da Salwa da za ta yi musu aikin. Sanin halin mata na barbaɗa da surutu, idan Ummi taji shiru tunda ta san inda yake za ta iya tona masa asiri. Ba dai tsoronta yake ji ba. Wani ƙuduri ya ɗora akanta wanda baya son a sami tangarɗa a gaba. Babban aikin yana ga turare na biyu wanda Taj da Hamdi basu ma ji ƙamshinsa ba. Shi ne mai muguwar tsadar wanda a sannu zai kassara Happy Taj sai dai a dinga faɗinsa kawai a labari.

"Baki ga idonta ba da ta ganni a jikinsa." Cewar Salwa tana ƴar dariya. Magana ta gaskiya ita ce yau tayi abin da bata taɓa ba. Shigarta da rungumar Taj babu guda da ta saba dashi bisa tarbiyar mahaifinta da Ahmad. Son zuciya da rashin haƙuri yasa ta tsallaka titin da Mami taso tayi amfani da kyanta taje gareshi tuntuni.

Ummi ta bata hannu su ka tafa
"Muna nan dake za ki ji anyi saki nan da ƴan kwanaki"

"Banda rashin kamun kai ma ba ayi bikinsu ba amma take binsa har office? Me kike tunanin zai faru da ban je ba? Kuma fa babanta a wajen yake."

"Ɗan daudu har wani uba ne? Ƙila ma shi zai kitsa mata ya ce ta dinga zuwa. Kin san fa su sana'arsu tambaɗewa tayi yawa. Da ba ƴarsa ya aura ba ma zai iya kawo masa wata."

Salwa ta jinjina kai "ai kuwa dole ma su rabu. Ba zan ma yi zaman kishi da ƙazamai irinsu ba."

"Turaren nan ƙarshe ne. Kuma ko asiri tayi ta same shi to wanda ya bani wannan ya ce min babu wanda ya kaishi iya sihiri."

"Idan anyi aurenmu za ki kaini wajen Ummi. Ko don gudun matsala a gaba. A bani shi a hannu in dinga juyawa."

Wata uwar shewa su ka sake yi. Ummi tana ta son Salwa tayi ta tafi amma taƙi motsi. Ita kuwa ba don ta matsu ayi aikin ba da ba za ta fito ba. Ɗan jarabar gidansu Baballe yana hanya. Idan Iyaa ta faɗa masa yawonta da ya ƙaru a kwanakin nan bata san me zai yi mata ba. Wata zuciyar har tana raya mata ko su ma ƴan gidan ta samu a rufe musu baki. Kuma a kautar da idanunsu daga kanta.

***

Irin mutumci da karamcin da Yaya take gani a wajen bayin Allahn nan dake gabanta sai hamdala. Mata huɗu ne. Ɗaya ance mata ƙanwar Alhaji ce Amma. Sunan ba baƙonta bane a wurin Taj. Matar ta haɗu iya haɗuwa amma she is so down to earth in ji bature. Girman kai da nuna isa duka babu su a tare da ita. Mata ukun kuma Hajiya ce da Mama da Umma. Su kam ko cikinsu ɗaya iyakar abin da ido zai gani kenan. Allah Yasa ita ma bata yi ƙasa a gwiwa ba. Ta kira Iyaa da kuma su Anti Zinatu saboda bata san me za su tattauna ba. An dai ce mata akan maganar biki ne.

"Ranar Asabar in Allah Ya yarda maza za su kawo lefe. Sati mai zuwa muke son ayi biki ta tare." Hajiya ce take wannan bayani.

Amma kuma ta ce "ayi mana haƙuri mun zo da maganar a taƙaitaccen lokaci. Mun ga babu amfanin ayi aure kuma duka ba wani uzuri ne a gabansu ba ace tana gida har yanzu"

Anti Zinatu ta nuna musu hakan ba zai yiwu ba
"Wannan gaskiya ne. To amma Hajiya kun san shiri irin namu yana buƙatar lokaci. Ina laifin wata guda ko biyu? Mai ƴaƴa mata baya rasa ɗan tanadinsa. To amma ba zai isa ace mun rufeta mun kai ɗakin miji ba gaskiya."

Jin haka Amma ta ce mata "Hajiya Zinatu mu ba baƙin juna bane. Wuri guda muka tashi. Babu zancen ɓoye ɓoye. Na tabbata kun san akan girki Yaya Hayatu ya kori ɗansa daga gida. Haka nan ba za mu manta yadda ya juyawa kyakkyawar zumuntarsa da Yaya Habibu baya akan ƙaddarar da ta same shi ba."

"Haka ne."

"Babu wanda ya taɓa kawowa zai amince da auren nan amma gashi anyi. Mu duka nan muna tsoron kada jinkiri yasa ya ɓullo da wani abin. Tunda ko me Taj ya yi baya burge shi. Don Allah ku barmu mu bawa duk maraɗa da mahassada kunya."

Ita dai Yaya jikinta ya soma sanyi. Anya ba wani abin su ka ji ba wanda yasa su ke so a gaggauta bikin nan? Kada fa azo a mayar mata da ƴa ƙaramar bazawara idan Alhaji ya canja ra'ayi.

Bata yi nauyin baki ba kuwa ta faɗa musu.
"Ni dai idan kun san da matsala don Allah ku faɗa mana sai a yiwa tufkar hanci tun wuri."

"Ko ɗaya. In sha Allahu alkhairi zamu ƙulla. Mu dai fatanmu ku bamu haɗin kai. Zancen shiri kuma wallahi Innar Taj da ƴan uwanta sun ce ko tsinke kada ku damu da saye. Komai na biki su za su yi." Cewar Umma don ta kwantar musu da hankali.

"Ayi haka?"

Amma ta ce "An ma yi. Ba don abubuwan da su ka gabata ba ina da yaƙinin da Yaya Hayatu ne zai aurar da ƴaƴan gidan nan. Haka nan Allah Ya haɗa jininsu wanda a yanzu idan ina kallon Taj da Kamal su suke tuna min. Bambancin shekaru bai hana su ƙulla kyakkyawar mu'amala ba."

Yaya da Anti Zinatu sun yi ta ja amma babu yadda su ka iya da waɗannan gogaggun matan. Ƙarshe Yaya ta ce bari ta sansanar da Abba. Ɗaki ta koma ta kira shi a waya. Ya tuna yadda su ka yi da Taj yace ta amince. Zai san yadda ya yi tunda anyi aure Hamdi ba ikonsu bace. Idan su ka cigaba da ja'inja ba zai amfanesu ba. Yau ko ƙofa Taj ya ƙwanƙwasa yace a bashi matarsa basu da hurumin hanawa a shari'a. Balle kuma bidi'o'in biki da ko babu su aure ya ɗauro.

Sun nuna jindaɗinsu da amsar da ta kawo. Cikin farinciki Mama ta zayyane musu yadda su ka yi nasu tsarin bikin. Idan akwai abin da su Yaya su ke so sai su faɗa. Alhamis mai kamawa za ayi kamu. Ranar Juma'a kuma dinner. Asabar ana la'asar za su zo su ɗauki amarya. A kaita gidan Alh. Hayatu. Daga nan Taj zai ɗauketa (wannan shirin Amma ne. Tayi rantsuwar Taj ba zai fara rayuwar aure ba sai ya taka gidan mahaifinsa. Kuma da izinin uban.)

Iyaa ta ce hakan ya yi musu. Ranar asabar za su yi yininsu a gida. Kuma tana roƙon a barsu su ɗauki nauyin abinsu. Dariya ta bawa su Hajiya. Kowa ya yi na'am da yadda zaman ya kasance. Aka rabu cikin mutumci. Bayan an cika musu ciki da daddaɗan abinci.

***

"Ba za ka ci ba?"

Hamdi ta tambayi Taj bayan ya ajiye mata wani faffaɗan plate mai kyau da haɗaɗɗiyar shinkafar da sabo yasa bai jima ba ya gama dafawa. Asalinta girkin mutanen Afghanistan ne amma ya ta sami karɓuwa a wasu sassa na ƙasashen Asia. Afghani Pulao dafaffiyar shinkafar basmati ce wadda cikin kayan ƙamshin dafata harda sinadarin cumin da cardamom. Sai kuma naman ƙaramar dabba wanda ake marinating ɗinsa da kayan ƙamshi kafin a dafa shi ya yi laushi luguf. Ita kuma shinkafar ana haɗata da caras da aka yayyanka sirara kuma ƙanana. A haɗa shi da raisin (bushasshen inibi) wanda ake soyawa sama sama da sugar sannan a haɗa da nuts.

Kansa da ya soma juyawa tun baysn ya sake arba da ita yake matsawa da hannu ɗaya.

"Ki ci kawai. Bana jin yunwa."

Ba shiri ta ture plate ɗin.

"Meye haka?" Ya ɓata rai. Zuciyar tana kuma ciwo shi.

Ita ma baki ba linzami yau ta turo shi "na san me ka zuba tunda na shiga tsakaninka da Salawaitu."

Dariyar dole ta sa Taj "Salwa ce ta koma Salawaitu?"

"Gaskiya dai na faɗa. Gashi nan ranka ya ɓaci don na canja mata suna."

"Ke za ki ji daɗi a ɓata naki?" Ya tambaya yana ƙarewa yadda take murguɗe murguɗen baki kallo.

"Mutum ya daɗe bai ɓata ba. Kuma na faɗa ɗin. Salawaitu, Salwanatu, Sal..."

Hannunsa da yake jin kamar ƙwaƙwalwar kansa gareshi, yana marmarin sake dukanta ya damƙe a da ɗan uwansa ta baya. Dukanta yake so ya ƙara yi. Rashin kunyarta da a mizanin masu tunani ma wani ko kallonta ba zai yi ba idan tana yi shi ne yake jin kamar ya kama ta da duka.

"Ki ci abincin nan kafin na dawo."

Ya kama ƙofa zai fita yana ji tayi siririn tsaki. Innalillahi...har tafin ƙafarsa yake jin ɓacin rai. Garam haka ya buga ƙofa ya sake rufeta a ciki.

Ta zauna tana ta faman girgiza ƙafa. Bata so ya fita ba tare da rigimar ta girmi haka ba. Ya saketa kawai ta huta. Ta kalli abincin ta janyo plate ɗin a fusace.

"Idan ban ci ba ma waccan Salonin zai bawa." Ta faɗawa kanta domin ta sami nutsuwar ci.

*

Mota Taj ya koma. Idanunsa jawur kawai don yaƙi biyewa zuciyarsa. Shi ya tabbatar da zai taɓa lafiyarta tabbas zai ji dama a ransa. Kamal ya kira ta whtsapp.

Bawan Allah sauƙi ya samu tunda aka fara sabon treatment. Kusan babu sauran kumburi. Sai duhu da yayi wanda a da ya ɗara Taj haske. Fari ne sosai kamar duka ƴaƴan Hajiya.

"Happiness"

Ya kira shi da wata irin murya mai rauni. Abin da yake faruwa tsakaninsa da Hamdi a ƙasa da awa biyu is not normal. Ta yaya zai dinga jin son dukanta kamar ba matar aurensa ba? Yarinyar da ɗazun nan yake jin zai iya keta bille ya aikata kowacce irin rashin kunya yau ɗinnan akanta.

Da tsokana ya ce "Happy nawa na gargajiya. Ka kai Mrs Happy gidan Sajidan ko kuwa naka gidan?"

Taj ya ɗan yi murmushi "I'm in trouble Happiness. Yaushe za ka dawo?"

Salati Kamal ya yi kafin ya hau shi da faɗa "wane irin rashin haƙuri ne da kai ne Happy? Kwana nawa ya rage ta tare? Yanzu tana ina? Allah Yasa ba hotel ka kai musu ƴa ba."

"Ba shi bane. Kai ma ka san ɗazu wasa nake maka..wata matsalar ce daban."

Hankalin Kamal kwanciya ya yi. Da safe da su ka yi waya ne Taj yace masa zai je kai Hamdi gidan Sajida. Amma fa har gidan da za su zauna sai sun je. Kamal ya dinga yi masa magiyar kada ya kunyata su amma ya dage sai sun je saboda kawai jindaɗin tsokanar ɗan uwan nasa.

"Ina jin ka to. Me ya faru? Ba dai sakin ta kayi ba?"

Kamar zai yi kuka ya ce "Marinta nayi Kamal. I slapped Hamdi har hannuna ya fito a kumatunta."

Tashi tsaye Kamal ya yi. Ya koma ya zauna sannan ya kuma tashi.

"Mari? Hamdin? Me tayi?"

Yadda ta kasance daga shigowar Salwa har fitarta Taj ya faɗa masa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."

"Sai rashin kunya take min. Ni kuma ina jin kamar na shaƙeta na huta."

"Daina faɗa Happy. In sha Allah zan yi booking next flight na taho."

"Ana haka dama? Kana son mutum kuma kaji kana son inflicting pain a jikinsa? Happiness indai haka ake aure wallahi kada kayi. It hurts...so much."

"Kuka kake yi? Happy?" Shiru bai amsa ba "Tajuddin?"

Katse wayar Taj yayi. Ya shafa idonsa yaji shi a jiƙe.

"What is wrong with me?"

Ɗazu ma sun kallon juna da Hamdi ya yi hawayen nan. Shi yasa ya juya mata baya kafin ta gani.

Bai yarda ya sake komawa saman ba sai da su ka yi jam'in la'asar yaga fitar Abba. Ya koma ya sameta tayi sallah ita ma. Kanta a ƙasa tana ta avoiding kallonsa. Hakan ya fiye masa komai.

"Zo mu tafi."

Kamar jira take ta miƙe. Ta hanyar da su ka zo su ka koma.

Salwa baƙin naci sai da taga fitar motarsa sannan ta tashi ta tafi gida. Yau yadda zuciyarta take wasai har girkin dare ta yiwa Gwaggonta.

***

Abu ya ƙara taɓarɓarewa tsakanin Hamdi da Taj amma babu wanda ya sani. Yanzu ko a waya su ke magana sai anyi faɗa. A kwana na uku wanda ranar ne Kamal ya dawo ya sanya Taj a gaba ya kira Hamdi. Irin faɗan da suke yi ya tayar masa da hankali sosai.

"Ni wannan abu ya ishe ni. Kaje ka auri Salwa. Ka cinyeta. Ka haɗiyeta ma duka. Amma don Allah ka rabu dani. Bana sonka. Bana son auren."

Guntun tsaki ya yi "matsalata dake bakinki baya shiru. Just keep quite for once. Maybe zamu iya komawa daidai idan kina kama bakinki."

"Anƙi ɗin."

"Kin san zan iya zuwa har gidan in hukunta ki ko?" Ya gargaɗeta. Kafin ya kira kuma kamar ana azalzalar zuciyarsa. Kewarta kawai ke damunsa.

"Kuma aka ce maka iyayena za su zuba ido kayi yadda kake so?" Tana wani irin cije baki ta ce " Bar ganin Abbana yana yi maka aiki. Wallahi kana kuma taɓani idan na sanar dashi zai rama min."

"Me ya kawo zancen iyaye kuma?"

"Naga ƴaƴan masu kuɗi sun raina iyayen irinmu ne."

"Allah ki kiyayeni."

Ya soma magana Kamal ya karɓe wayar. Sallama ya yi wadda Hamdi tana ji nutsuwarta ta dawo harda gaishe shi.

"Me yake faruwa Hamdiyya?"

Kuka ta saka masa. Duk tambayar duniya ta kasa bashi amsa sai "shi ne" kawai da take ta faɗi. Da ƙyar ya rarrasheta sannan ya yi mata tambaya.

"Kina son sa?"

"Shi ma ba sona yake ba." Ta amsa da kuka.

Kamal ya kwantar da murya "wa yake ta tashi? Ƙanwata nake tambaya. Kina son Taj?"

Hamdi ta kalli ɗakinsu da babu kowa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ce sannan tayi magana.

"A da ba."

"Yanzu fa?"

"Nima ban sani ba. Salawaitu yake so. Ni kuma sai in yi ta son shi? Haka ake yi?"

Murmushi ya yi. Ya sami amsarsa koda ba kai tsaye bane.
"A'a gaskiya. Abin da nake so dake dai don Allah ki bar abubuwan nan tsakaninmu. In ki ka bari wani yaji har aka raba auren ina mai tabbatar miki Salawaitun zai aura."

Wawan duka Taj ya kai masa a baya. Baya ƙaunar zancen Salwa tuntuni balle yanzu da yake cikin damuwa shi da amaryarsa.

Ajiyar zuciya tayi "Ba zan faɗa ba"

A ransa yake auno yadda zai tsokanesu duk su biyun idan komai ya daidaita. Yana gama wayar ya koma kan Taj.

"Happy ina ganin wannan maganar fa ba tamu bace mu biyu."

"Me kake nufi? In faɗawa wani? In aka ce na sake ta fa?" Ya soma magana cikin tashin hankali.

Nutsuwa Kamal ya yi wanda yasa Taj ya gyara zama.
"Me ka ke tunani?"

"Ka faɗawa Inna."

"Inna kuma? Me za tayi?"

"Duk matsalar duniya Happy uwa ce ƙarshenta. Ko bata magance ba in sha Allahu za ta faɗa maka yadda za ka yi. Sannan ga addu'arta da bata da shamaki. Abin naku kamar asiri."

Kallonsa Taj ya yi "kai duka matsalolinka kake faɗawa Hajiya?"

"Wanda ya dace lallai ta sani ba."

Kallon tuhuma Taj ya yi masa
"Me yasa ka ɓoye mata ciwonka bayan ka san idan tayi addu'a za ta karɓu?"

Gaban Kamal faɗuwa yayi. Cikin sarƙewar harshe ya ce "ai...dama. hhhh. Saboda gudun tashin hankalinsu ne."

"I see" kawai Taj ya ce.

Kamal duk ya ruɗe "Kayi haƙuri don Allah. Ban ɓoye da wata manufa ba."

A nutse Taj ya karance shi. Inda ya dosa daban da inda yake tunanin Kamal ya dosa. Kenan akwai abin da Happiness yake ɓoyewa wanda bai sani ba? Shi ne mai dogon bakin faɗa masa komai wato.

"Akwai abin da ka ke ɓoye mana ne banda allergy da asirinka ya tonu?"

Wani gwauron numfashi da Kamal yaja sai da Taj yaji hantar cikinsa ta kaɗa. Babu shakka akwai sirrin da bai sani ba. Zai kuma sani ne don Kamal bai isa ya ninke shi baibai ba tunda ya gano da matsala.

"Shi ne. Allergy ɗin ne. A China ma ya tashi. Ba ka ga har wani duhu nayi ba?"

"Na gani. Yanzu nake shirin cewa ko man bleaching ɗin naka ne ya ƙare a can?"

Kamal ya taso ya yi kansa. Su ka gama zolayar juna sannan Taj ya koma cikin Happy Taj.

***
Shiru shiru Salwa tana jiran wayar Taj amma ko flashing babu. Hankalinta ya soma tashi. Kwanakin da aka ɗiba domin aurensu sun kusa. Ta kira Mami tana ta kuka. Mamin ta ce mata ta taho gida.

"Idan na ƙara nesa dashi ai babu lallai ya tuna dani ma."

"Ki taho nace miki. Zan sake shiri."

Ta samu Salwan ta amince za ta dawo. Sai dai bata san ta ina za ta fara ba. Alh. Mukhtar ya sake kiran Alhaji akan maganar ranar da za su je wajen kawunsa amma ƙememe yaƙi ɗauka. Baya son yi masa ƙarya sannan kuma baya son faɗa masa gaskiya. Idan ya faɗi gaskiyar girmansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login