Showing 105001 words to 108000 words out of 182238 words
Chapter 36 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
ɗauko wanda ya yi boko sosai wato Alh. Mukhtar aka yi masa MD. Yana fara samu Mami ta sakarwa Ahmad mara. Babu wanda ya san maganar nan har yau.
"Ku kaini ofishinsa. Ina son magana dashi."
Da rawar jiki su ka yi gaba. Har yanzu akwai wajen kaso talatin da biyar na kuɗin da ya ranta musu da basu gama biya ba. Hankalinsu in ya yi dubu to a tashe yake.
Sun isa ofishin MD inda Alh. Mukhtar na ganinsu shi ma ya tashi da rawar jikin ganin iyayen gidansa. Aka gaisa su ka zauna. Ya miƙowa Alh. Hayatu hannu yaga babu fuska ko alamar zai karɓa. Ba shiri ya ja da baya.
"Wurinka Alhaji ya zo. Ka gane shi ko?"
"A'a" Alh. Mukhtar ya faɗi da gaskiyarsa "sai dai fuskar kamar na san mai irinta."
Muryar nan ta Alhaji a dake ta fito ya ce "Ɗana Ahmad Hayatu Sule Maitakalmi ko?"
Idanu Alh. Mukhtar ya zaro "Alh. Hayatu? Kai ne? Ikon Allah."
Ɗaya daga cikin Alhazan da su ka zo tare Alhaji ya cewa ya yi bayanin matsayinsa a garesu. Tiryan tiryan kuwa ya yi duk da sun cika da mamaki. Bayan ya gama kana ganin Alh. Mukhtar ka san ya gama rikicewa don gumin da yake ko ruwan sama albarka. Alhaji ya ce waɗancan biyun su ɗan basu wuri. Su na fita ya soma faɗa.
"A lokacin matarka ta so sabauta rayuwar ɗana. Shi yasa na ajiyeka a nan domin in kare Ahmad. To yau kuma an wayi gari taje tayi abin da ta saba tana neman shiga tsakanin wani ɗan nawa da matarsa." Ya yi maganar cikin ɗaga murya.
"Alhaji ban sani ba wallahi..."
"Ta yaya za ayi ka sani bayan kaima juyaka take yi?"
"Kada kasa su koreni. Ina da ƴaƴa wallahi." Ya ce hankalinsa na neman gushewa.
"Ka ce ni Hayatu na ce ta karya asirin. Ita ko wani nata sun yi kaɗan su tarwatsa rayuwar zuri'ata. Taj ba ɗanta bane. Idan na ƙyaleta akan Ahmad saboda haƙƙin uwa ne. Amma muddin ta sake shiga rayuwar wani nawa wallahi sai ta ɗanɗani kuɗarta. Ni da kake gani kaza ne akan ƴaƴana. Ina iya taka abuna idan sun min ba daidai ba domin su gyara. Amma idan wani ya kamanta zai sha tsatstsaga har sai anga jini. Ina fata ka fahimceni."
Jikin Alh. Mukhtar babu inda baya rawa. Bai taba ganin mutum mai ban tsoro da kwarjini kamar Alh. Hayatu ba.
"Na gane. Don Allah ka yi haƙuri."
Alh. Hayatu ya tashi "ina son ganin canji a tattare da Taj kafin sati mai zuwa. Ta karya koma me tayi don ta sanni farin sani. Akwai irin abin da bana yafewa. Taɓa min ƴaƴa yana sahun gaba. Sannan ka tashi tsaye kamar kowanne magidanci ka nemi tsari daga sihirice sihircen marasa tsoron Allah."
Ko kallon Alh. Mukhtar bai sake yi ba ya fita. A waje ya yi sallama da alhazawan nan ya kama hanyar Kano ko ruwan garin bai sha ba. Sallah kawai su ka yi su ka tafi.
***
Abu na maza, babu wanda ya yi tunanin raini ko surutu akan gidan Abba Habibu. Irin abin da mata za su yi ta gutsiri tsoma ana cewa me ya kai shi auren wadda bata kama ƙafar arziƙinsa da na iyayensa ba. Ahmad da Kamal sun zo. Sai ƙanin Inna da kuma ƙannen Alhaji guda biyu. Irin tarbar arziƙin da Abba ya yi musu ba ƙaramin daɗi su ka ji ba. Sun riga sun san ko waye, ba a ɓoyewa kowa ba. Ga amininsa Baba Maje, sai ƙaninsa Abdulƙadir da wasu ƴan uwansu maza da su ka lallabo su ka dawo rayuwarsa bayan ganin luɗufin da yake samu.
Abinci ne na gani da fađa su Ƴar Ficika su ka yi. Kuma kamar yadda ya yi alƙawari tuntuni ko hanyar gidan basu zo ba shi da yaransa. Baba Maje ya yi rawar gani ya kawo dubu ashirin a bayar tukwici. Abdulƙadir ma ya kawo sha biyar. Abba ya cike ya zama hamsin. Ƴan kawo lefe kuma su ka ƙi karɓa. Sai da Abba ya ce rainawa su ka yi saboda sun gan shi a haka. Ba shiri su ka karɓa aka rabu a mutumce.
Ko rabin awa basu yi da tafiya ba gidan ya soma cika da ƴan kallon kaya. Gashi Zee bata nan. Sajida ce kaɗai take ta fama. Sai ga Iyaa ta zo da Siyama da Ummi. Ta kuma umarcesu da taimakawa Sajida wajen saka ido akan kayan da kuma aikin buɗewa mutane.
Ƙiris ya rage Ummi ta haɗiyi zuciya ta bar duniya. Dama Baballe ne ya taho dasu a motarsa. Dolenta ta taho. Yawan akwatunan da irin kayan da ta gani ya birkita mata lissafi. Zuwa yanzu ma dai sakin aure ya kamata su ji anyi. Maimakon haka sai wannan uban kaya kamar za a buɗe shago. Dole ma ta kira Salwa idan sun koma gida.
Abin baƙinciki yadda Iyaa ta ɗora mata aikin kula da wata ƙaramar jaka da aka shaƙare da sarƙoƙin gwal, awarwaraye, zobba da kuma sarƙoƙi na fashion masu matuƙar tsada. Sai da Iyaa ta ƙirga komai harda sanya Siyama ɗauka a hoto sannan ta miƙa mata.
"Ko kwali ne ya ɓata to ku ɓata tare. Ki kula dasu sosai. A nunawa mutane arziƙin Hamdi amma a kula da masu ɗan hali da mahassada."
Ummi za ta iya rantsuwar maganar mahaifiyarta da harshen damo ta fito. Bata sani ba ko tsagwaron baƙincikin da take ji a zuciyarta Iyaa ta gani. Haka nan ta karɓi jakar ba don tana so ba. Irin baƙincikin da take ji ba wai so take ta mallaki kayan ko ta sace ba. Ita da ace za su ɓace ko su ƙone ƙurmus Hamdi ta rasa da ko miliyan biyar aka damƙa mata ba za ta yi farinciki kamar haka ba.
*
Bayan tafiyar Alh. Hayatu, karatun ta nutsu Alh. Mukhtar ya yiwa kansa. Ya dinga haɗa ɗaya da biyu yana lissafin yadda yake aikata abubuwa da yawa bisa umarnin Mami kuma ba a son ransa ba. Ya yarda hannunka mai sanda Alhaji ya yi masa da zancensa na ƙarshe. Ji dai maganar Taj ɗin da ta ce dole ya auri Salwa. Gashi takanas akan yaron mahaifinsa ya zo ya yanka masa gargaɗi mai kyau.
Rasa tudun dafawa yayi ya kira babbar ƴarsa da wani tunsni ya zo masa. A gidan take shekara talatin da huɗu duk wanda ya zo da maganar aure da kansa yake gudu. Ita da duka sauran ƴan matan gidan su huɗu da samari biyu babu uwayensu mata biyu da yake aure kafin zuwan Mami sun fita ta ƙarfin tsiya. Ƴaƴan Mami a gidan huɗu ne. Salwa da ƙannenta maza biyu.
"Bushra ki ce da Mami wai na kira ban sameta ba. Kowa ya fita daga gidan zan turo mai feshin maganin sauro. Ke kuma ki zauna ki jirani. Idan akwai aikin yi ko share share bayan an gama sai ki yi."
Saƙon nasa ta faɗawa Mamin da umarninsa na ta zauna tayi aiki. Mami ta saki murmushi. Yadda ta farraƙa shi da ƴaƴan yana burgeta. Gashi yau ko tishin tauna layar bata yi ba amma ya aikata da kansa. Salwa ta kira su ka fita. Samarin dama basa nan. Ita kuma Bushra ta sanar da ƴan uwanta duk su ka tafi maƙota. Ba a jima ba Alh. Mukhtar ya dawo.
"Faɗa min gaskiya Bushra, Mami tana da kayan asiri a gidan nan?"
Rawa jikinta ya fara. Idanunta su ka ƙara girma don tsoro da firgici.
A ƙagauce ya ce "Ba mu da lokaci. Ki faɗa min idan akwai."
Kai ta gyaɗa. Ya ce idan ta san inda su ke maza ta nuna masa.
"Ban sani ba. Sai dai mu duba."
Babbar rigarsa ya ajiye a kan kujera ya ce ta saki jiki su yi aiki da sauri. Ai kuwa yaga zafin nama. Duk gidan sun gaji da rayuwar da Mami ta ƙaƙaba musu.
Ɗakin Mamin suka fara zuwa. Yana karanto surorin neman tsari ya watso duka kayan cikin wardrobe ɗinta da kowacce durowa. Sun tsinci ƙulle ƙulle da wasu ƙwarya da tarkace guda biyar. Aka koma ƙasan gado nan ma akwai. Daga nan sai ɗakinsa. Abu ya ƙazanta. Kansa har ciwo ya dinga yi saboda tashin hankali. A ɗakin ƴaran gidan ne dai ba a sami komai ba. Kitchen ma Bushra ta nuna wani ruwa da ta kan ga Mami ta tsiyaya musu a girki. Ya ɗauka ya tuttular. Kit ɗinta inda take ajiye abubuwa masu mahimmanci ya ɗauka ya muƙa da ƙasa sai gashi ya buɗe. A nan ya tsinci laya mai sunansa da ake taunawa. Sai kuma masu sunan duka ƴaƴansa banda nata. Da kuma sababbi a leda ɗaya Taj, ɗaya Zainab (Inna).
"Wallahi Baba wannan take sakawa a baki ta ce kayi mana abu kuma sai kayi. Ko ranar da ka ce in na kuma fita zance za ka tsine min da ita tayi magana."
Haƙuri ya bawa ƴar tasa. Ya rasa matakin ɗauka na gaba. Ita ta bashi shawarar su ƙona komai. Ya ce kada ta taɓa. Da tsintsiya da abin kwasar shara ya tattara komai ya tara a tsakar gida. Ya kawo fetur ya zuba sannan ya kira Mami ya ce su dawo.
"Har maganin ya fita?"
"An fasa, sai gobe."
Masifa ta yi masa na katse mata baccin yamma sannan su ka taho gida. Ana buɗe musu gate ta hango shi daga shi sai ƴar shara a jikinsa ya sanya wasu tarkace a gaba. Su ka fito daga mota ta taho inda yake. Jikinta ne ya saki lokaci guda da ta gane mene ne a gabansa.
"Alllll....hhhhajjii? Mmmmene nee wannnnan?"
Haɗe rai ya yi sosai ya tura mata ashana da ƙafarsa.
"Ɗauki ki cinna musu wuta."
Jikinta rawa ya kama yi sosai. Tana ta gumi ta rasa abin yi.
"Ɗauki mana!" Ya daka mata tsawa.
Ta kasa motsi sai ƙullewar ciki. Salwa da taga halin da babarta ta shiga ita ma tsorata tayi. Tunda bata san kayan mene ne ba durƙusawa tayi ta ɗauki ashanar.
"Baba ni bari na ƙona."
Kafin Mami ta iya tare ta har ta ƙyasta ashana. Tana cillawa kuwa kayan nan su ka yi wata mahaukaciyar ƙara tamkar tashin gurneti. Mami tayi zaman daɓaro a ƙasa tana ihu.
"Kin kashe ni. Salwa kin kashe gidan nan."
Da faɗa Alh. Mukhtar ya ce "ta dai kashe ki ke kaɗai banda gidana."
"Mami kayan meye?" Salwa ta tambayeta ganin kuka take haiƙan. Bata sami amsa ba sai daga bakin babanta.
"Nagodewa Allah da Ya turo Alh. Hayatu gareni ya farkar dani mugun baccin da nake yi. Sai yau na gane ashe zaman waɗannan abubuwan muke yi ba aure ba."
Mami kuka kawai take yi da gurnani. Hankalinta ya kai ƙarshen tashi. Idan ya saketa bata da tudun dafawa. A zaune ta ja jiki zuwa inda yake za ta kama ƙafarsa ya janye da sauri.
"Ka rufa min asiri."
"Ki rufawa kan ki dai" ya dubesu ita da Salwa dake tayata kuka "yauwa, Alh. Hayatu ya ce in faɗa miki ki warware abin da ki ka yiwa ɗansa har su ke rigima da matarsa. Idan ba haka ba kuma ki jira martani daga gare shi." Ya wuce ciki.
Mami ta zauna tana tumami da kuka kafin ta tashi ta bishi ciki da sauri.
"Wane ɗan? Taj? Wallahi ban yi masa komai ba."
"Ki daina saurin kama sunan Allah tunda baki san shi ba. Da idona naga laya da sunansa."
Mami ta kwantar da murya "Ayyaaa Alhaji, bamu yi amfani da ita ba. Dama na ajiye ne sai sun yi aure da Salwa. Ai ban baki ba ko...."
Ta juya babu Salwa babu dalilinta.
"Salwa? Alhaji ina Salwa?" Tayi maganar kamar wata zararriya. Tsoro take ji kada ƙona kayan nan ya janyowa ƴarta wani abu. Don dai tabbas malaminta ya sha yi mata kashedi akan kada ma wani ya gani balle a taɓa.
Ɗakunan gidan ta duba bata ganta ba. Tayi wajen gate tana faman kiranta ko kallon titi bata yi. Bata yi aune ba mota ta ɗebe ta tayi sama ta dawo. Maigadin Alh. Mukhtar da ya biyota yana son faɗa mata Salwan ta fita ne ya koma ya sanar dashi abin da ya faru. Ya fito su ka wuce asibiti tare da mai motar da ya bugeta.
Salwa kuwa tunda taji saƙon babanta hankalinta ya tashi. Indai Alhajinsu Taj ne ya yi waccan maganar kenan asirin ya kama su. Matsalar kawai tunda ake zargin Mami a hankali zsi gano ita ce. In haka ta faru kuma zai hana Taj aurenta idan su ka fara soyayya. Tasha ta wuce tunda da atm a jikinta ta ciri kuɗi sai Kano. Wurin Ummi za ta je ta taimaka mata da wanda za a rufe bakin Alhaji.
Motarsu ko fita gari bata yi ba Alh. Mukhtar ya kirata ya faɗa mata abin da ya sami Mami. Don baƙinciki sai da tayi kuka. Haka ta sauka daga motar ta tafi asibiti.
***
Mai shawara aka ce aikinsa ba ya ɓaci. Duka abubuwan da Inna ta sa Taj yi ya rungumesu hannu bibbiyu. Ƙuncin zuciyarsa ya ragu sosai. Duk da ya kan ji haushin Hamdi yana taso masa lokaci zuwa lokaci tunda fitar asiri sai a hankali, amma a zuciyarsa ya sani cewa ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba kamar yadda ya dinga ji a kwanakin baya. Banda yawan addu'a, Inna ta sa yanzu ya ware plate goma na abinci kullum sai sun bayar sadaka. Ba wai ragowar na mutane ba. Mai kyau da an gama dafawa ake packaging. Ranar farko ma na mutum ɗari biyu su ka yi aka kai asibitin gwamnati. Kusan zai rantse ma daga ranar ya fara jin canji sosai. Ciyar da mabuƙata ba ƙaramin abu bane.
Duka wani jere da gyaran gidan amarya an gama shi a farkon sati. Duk wanda ya shiga kamar kada ya fito. Hatta kayan da za su saka Kamal ya kai wa Hamdi nata ana jibi fara biki. Bayan ta shiga gida ta gwaggwada ta dawo ta same shi. Ta faɗa masa babu wanda yake buƙatar gyara. Sai kuma tayi godiya sosai.
"Yanzu yaya kike ji game da ɗan uwana?"
Kai ta sunkuyar tana murmushi. Da ya sake yin tambayar ta ce "Alhamdulillah."
"Kina ganin faɗa ya ƙare? Za ku iya zama babu tashin hankali?"
"Ban sani ba ko daga wurin shi." Ita ce amsar da ta bayar da ƙaramar murya.
"Nayi magana da shi. Ke nake tambaya kuma."
Kunya ce ta isheta ya ce gara ma ta daina domin tunda ta shigo danginsu ta sani cewa bayan shi yanzu ta sami ƙarin ƴan uwa. Kuma kowa zai tsaya mata idan Taj ya yi nufin cutar da ita.
"Zan iya in sha Allah."
"Alhamdulillah. Kamar yadda na faɗa masa ku bi komai a sannu. Kada ku ce dole a yau ko gobe ku ke son ganin alaƙarku ta dawo kamar da. Wannan zai janyo muku too much expectation, wanda kuma rashin samunsa zai sa ku zama disappointed."
"In sha Allah zan kiyaye."
"Hamdiyya"
Mrs Happy ya saba kiranta. Shi yasa Hamdiyyar ya faɗar mata da gaba.
"Na'am Ya Kamal."
"Don Allah ki riƙe min Taj amana. Abubuwa da yawa sun same shi. Yana buƙatar inda zai sami kwanciyar hankali."
Ɗan murmuhi tayi "ai kana nan Ya Kamal sai mu dinga shawara. Ka fini sanin abin da ya dace da shi."
Murmushin da Kamal ya mayar mata mai matuƙar rauni ne. Da ace idanunsa ma take kallo za ta ga sun kaɗa.
"Yanzu ke ce mafi kusa dashi."
"Ba zan shiga tsakaninku ba in sha Allah" ta faɗi da sauri.
"Rayuwa da yau da gobe za su iya shiga. Ni dai na baki amanar Happy. Please Hamdiyya, give him the happiness he deserves."
Har ya tafi tana juyayin maganganunsa masu kama da sallama. Anya lafiya kuwa?
***
Idan ka ji yara na waƙar gobe Juma'a, kuturu dariya yake ko zai sami ɗan kwabo to lallai ranar ta kama Alhamis. Ta wannan satin ita ce ranar Kamun amarya Hamdi wadda iyayen ango Taj su ka yi rawar gani wurin tsara taro na burgewa. Biki ne na ƴan kasuwa kuma ƴan boko. In baka yi bani wuri. Sun tsara abinsu na yau ma mata kawai. Mazan gidansu ko mutum ɗaya ba a yarje masa zuwa ba. Daga DJ ɗinsu kuwa har mai hoto da MC duka mata ne. Daga cikin wani katari da Alh. Hayatu ya sake yi a rayuwa harda dacewa da kyakkyawar tarbiyar ƴaƴansa akan sunnar Fiyayyen halitta SAW. Ba dai a rasa nono a ruga, wani dole sai ya bauɗe. To amma dai majority a gidan sun ginu da wannan tarbiyar ta iyayensu mata. Wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Alhaji ya kan kasa yiwa wanda ya kuskure uzuri. Shi fa kusan komai Allah Ya bashi. Bai san wani nau'i bane na gwajin rayuwa. Idan ya ƙanƙantar da kai ya yarda rahama ce daga cikin taskar Ubangijinsa sai Allah Ya ƙara masa da lada mai gwaɓi. Idan kuwa girman kai da jin cewa isarsa da iyawarsa ne su ka bashi kamar yadda ya tsinci kansa yanzu, to dama Allah barin mutum yake da iyawar tasa.
Ƙarfe ɗayan rana mai kwalliya ta zo ta fara rangaɗawa Hamdi bayan tayi sallar azahar. Jiki ya sha gyara na gaske saboda haka in ka ganta sai ka ƙara kallo. Ga ƙamshi wanda da kanta ta ce a bar turara mata jiki haka nan saboda kada ta fara ɗaukar zunubi a cikin mutane.
Tana idar da sallar la'asar ta saka kaya aka ɗaura mata ashoke. Da ta fito daga ɗaki Yaya tashi tayi ta bar wajen. Bata son kowa yaga ƙwallar da ta cika mata idanu. Yau ita ce Allah Ya nufi ƴarta da auren gata irin wannan. Da bikin Sajida abin bai yi armashi sosai ba saboda tangal tangal da auren ya soma yi tun kafin a ɗaura shi.
Leshi ne haɗaɗɗe mai laushi aka yi mata ɗinkin gargajiya wato buba da zani. Ado da kyan leshin kaɗai sun wadata ba sai an ɓata ɗinkin da tarkace ba. Ruwan toka ne da adon ja kaɗan a jikin zare sai navy blue ɗin fulawoyi. Ta riƙo jar ƙaramar jaka ta amare tana kuma sanye da jan takalmi mai tsini da maɗauri. Ashokenta na ka da na kafaɗa navy blue da silver. Sai wata danƙareriyar sarƙa mai duwatsu navy blue su ma da ja. Make up ɗinta na hankali bata koma aljana a kwaba ba.
A tsakar gidan aka tsaya ana ta ɗauke ɗauken hotuna da ƴan uwa. Bata sani ba ashe Taj ya kirata ya kai sau shida. Amma ce ta turo