Showing 102001 words to 105000 words out of 182238 words

Chapter 35 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

da kullum yake tattali ne zai zube. Daga baya ne ya tausaya masa da yawan wayar ya ɗauka ya ce ya ƙara wata guda. Saboda wasu uzurirrika da su ka taso masa. Alh. Mukhtar dai tunda ya sami amsar bawa Mami hankalinsa ya kwanta.

"Nufinsa sai waccan yarinyar ta tare sannan zai auri Salwa?"

"Ina laifi?"

"Ai kuwa akwai shi tunda nima ban zauna da kishiya ba. Ƴata ma daga ita sai miji."

***

Girki ya faɗo kan Inna ranar Juma'a. Da ta haɗa abincin Alhaji Bishir na shigowa ta ce ya kai masa. Kuma bata leƙa ɓangaren ba kamar yadda su ka saba. Mai girki za ta je ta zuba masa abinci su yi hira. Idan ya gama ta aikawa sauran matan cewa ya dawo. Duk za su zo a ɗan taɓa hira sannan su tashi.

Abinci ya yi kusan awa guda Alhaji yana kallonsa. Ga yunwa ga gajiya amma yaƙi zubawa. So yake yaga iya gudun ruwan Zainabu Abu. To dai tun bayan masallaci har la'asar bata shigo ba. Da ya dawo daga masallaci cikin gidan ya shiga ya wuce ɗakinta. Jallabiya ce a jikinsa yana danna counter mai fasalin carbi ta sama.
Babu kowa a falo. Ya shige uwar ɗakin. Yana sanya ƙafa ita kuma tana ɗora waya a kunne. Don ya san da wa take magana ta kira Taj da sabon suna.

"Angon Hamdi"

A tunanin Alhaji ko da gangan ta ɗauki wayar. Hannu yasa ya karɓe. Ganin sunan Taj da gaske sai ya miƙa mata. Ita kuwa ta saka speaker yadda ta saba idan ita kaɗai ce a ɗakin saboda wayarsu bata ƙarewa da wuri.

"Inna kina ji na kuwa?"

"Me ka ce?"

Bai san yadda za ta ɗauki maganar ba amma dole ya đauki shawarar Kamal yau. Faɗan da su ka yi da Hamdi a motarsa Allah ne kawai ya bashi ikon mallakar kansa ya buɗe mata ƙofa ya ce ta fita. Daga zuwa kai mata kati cibi ya zama ƙari. Saboda yau ta iya bakinta bata ce komai ba shi ne ya ce ba a yi mata tarbiyar godiya ba. Ai kamar jira take. Tunda ta buɗe baki ta fara surfa rashin kunya sai da yaji inama bai je gidan ba.

Gyaran murya ya yi "na ce ko za a fasa bikin?"

Alhaji da ya kama hanyar fita sai gashi ya dawo. Inna tayi sauri za ta mayar da wayar iya kunnenta ya harɗe fuska. Taɓe baki tayi a ranta ta ce ana so ana kaiwa kasuwa. Dama taji yadda ya rikice da yaji bashi da lafiya.

"Kai da ka san baka son biki ne yasa ka bari mu ka zazzage asusunmu? Haƙuri za ka yi kawai."

"Uhmmm, Inna ba bikin ba. Auren nake nufi."

Bata san lokacin da ta gyara zama ba.
"Ka fara shaye shaye ne? Auren? Saki fa kenan."

Baya son yawan tada maganar don ransa ƙara ɓaci yake. Amma dolensa ya faɗa mata gaskiya.

"Matsaloli muke ta samu. Kullum sai mun yi faɗa."

"Wannan shaiɗan ne kawai. Ku dage da addu'a." Ta ce, hankalinta ya soma kwanciya.

"Inna har marinta nayi."

Shiru ya yi yana jiran yaji me za ta ce. Ta kalli Alhaji shi ma ya kalleta.

"Taj ka sameni a gidan Yaya Malam (yayanta na biyu.)"

Ta miƙe ta dubi Alhaji da ya yi tsaye kamar an dasa shi.

"Ka yi min izinin fita?"

"Jeki."

Hijabi kawai ta ɗauka ta fita ta shiga ɗakunan su Hajiya ta ce musu ga inda za ta je. Duk su ka bata saƙon gaisuwa ga iyalin gidan. Direba ta kira su ka tafi. Aka bar Alhaji da tunani. Yadda hankalinsa ya tashi sai da yaji kamar ya ce Taj din yazo gida. Abin da mamaki ace wai shi ne da marin mace. Wace irin tarbiyya Habibu ya yiwa ƴaƴansa?

*

Ƙasa da awa guda uwa da ɗa su ka keɓe a falon maigidan. Taj ya zayyane mata abubuwan da su ka faru. Bata ko tambaye shi me ya kai shi tafiya da Hamdi wurin sana'arsa ba.

"Idan na fahimta da kyau tun daga zuwan Salwa ku ka fara faɗan?"

"Haka ne. Na so yi mata bayanin babu komai a tsakaninmu amma ta rufe ido tana gaya min maganganu."

Inna tayi salati sannan ta ce "ya maganar azkar? Kana yi?"

Kai ya sunkuyar "ina yi."

"Ni da kai ne Taj. Ka faɗa min gaskiya."

"Allah ina ƙoƙartawa Inna." Ya kuma faɗa don ta yarda da shi.

Aikin gama ya riga ya gama. Ko yana yi dama ba zai hana ƙaddara da ikon Allah faruwa ba. Sai dai ya sauƙaƙa.
Gargaɗinsa tayi akan kada ya yarda su sake haɗuwa. Wayar ma ko ita ta kira kada ya ɗauka. Sannan mafi mahimmanci ya tabbatar kalmar saki bata shiga tsakaninsu ba.

"Ka tashi ka tafi. Za ka ji ni in sha Allah idan mun gama magana da Yaya Malam. In ma sihiri ne to in sha Allah zai koma ya ci mai shi. Addu'a, sadaka, qiyamul laili da hanyoyin neman kusanci da Allah nake so ka runguma kaji ko?"

Ya gyaɗa mata kai kamar yaro.
"Ki yi haƙuri na tayar miki da hankali. Alhaji ya kamata na nema..."

Wani irin tausayinsa ne ya kama ta. Ta dafa kansa tayi masa addu'o'in neman tsari wanda Ayatul Kursiyyu ke kan gaba. Sai da ya tafi ta fashe da kuka. Duk ya wani rame. Kana ganinsa ka san hankalinsa ne ba a kwance ba. A gidan ta zauna har yayan nata ya dawo ta faɗa masa. Ya kwantar mata da hankali.

"Kada ki ƙulla sharri akan wanda ki ke zargi. Shi zargi dama bashi da kyau a addini. Zan kira shi ya zo gobe in sha Allah."

"Yaya har zasu yi lafiya kafin bikin?" Ta tambaye shi da damuwa.

"Ke ta biki ma kike wato?"

"A'a, tsorona kada ta tare yadda yake cewa yana jin kamar yayi ta dukanta yaje ya lahanta ƴar mutane."

Kwantar mata da hankali ya yi.
"Allah zamu roƙa ba mutum ba. Shi kuma ba ayi maSa gaggawa. Tunda ya ce idan mun roƙa zai bamu to ki saka ranki a inuwa. Ko daga ina matsalar take bata wuce Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi ba."

Da ƙwarin gwiwarta ta fita daga gidan. A ranar yadda ta hana idonta bacci haka ta tada Taj. Shi kuma ya sami kansa da turawa Hamdi saƙo.

(Idan Allah Yasa kin gani kafin safiya ki tashi ki yi sallah da addu'a. Idan akwai alkhairi cikin aurenmu Allah Ya warware mana matsala.)

Sai uku da rabi ta gani da ta tashi fitsari. Ta ɗauro alwala ta zauna tana ta kuka. Zee na jinta amma ta ƙyale. Yaya ce ta bata aikin sanya mata ido saboda kwanakin nan kowa ya san ta canja.

A ɓangaren Alh. Hayatu kuwa, yana ganin shigowar Inna ya kira Yaya Malam.

"Ka biyo sahun ɗanka ne?" Malam ya faɗi kai tsaye domin duka gidansu dai haushinsa su ke ji.

Murje ido ya yi tunda in ba a nan ba babu wanda zai tambaya kuma
"A gabana ta fara wayar shi yasa. Da gaske ya mari matarsa?"

"Ƙwarai kuwa."

"Kaga abin da nake faɗa ai. Namiji mai irin sana'arsa fa ji yake kamar shi ma mace ne. Shi yasa yake daidaita tunaninsa da nata. Cikakken namiji ba zai fara kai hannu daga aure ko wata ba ayi ba."

Yaya Malam dai dariya kawai ya yi. Ya shaida duk wata rigima da yake yi bata yi tasirin hana shi son ɗansa ba. Abin da yaji ya faɗa masa. Ya yi godiya su ka yi sallama.

Washegari ya san da zancen kai lefe da maza za su yi. An kira shi ya gani bayan an kammala komai. Harda akwatuna huɗun da Amma ta taho dasu waɗanda kayan ciki su ka amsa sunan kayan ƴar gata. Tunda ba dashi za a yi ba babu wanda ya sa masa ido da ya yi sammakon fita. Ko matansa bai faɗa musu inda za shi ba. Ya dai yi musu sallama ya fice. Yana zama a mota ya ce da direbansa Bauchi za su je.

"Bauchi Alhaji?"

"Ba ka san hanya bane?"

Da sauri ya hau bada haƙuri "na sani. Allah Ya kai mu lafiya."

"Amin"

Zuciyarsa a baka take da ɓacin rai. Bai runtsa ba jiya tunda ya yi waya da Yaya Malam. Arziƙin rabon Ahmad dake tsakaninsa da Mami yasa ba zai haɗata da hukuma ba. Amma tabbas sai tayi nadamar kai ɗansa gaban ƴan iskan bokayenta. Bai san bata da masaniyar abin da Salwa tayi ba.

***

Tun dare Ƴar Ficika da yaransa su ke aikin kayan kwalamar da za a tarbi masu kawo lefe dasu. Shi ya ce da Abba lallai ko ruwa kada ya siya. Za su kawo komai.

"Abin zai yi yawa. Don Allah kada ka wahalar da kan ka. Kada ka manta girma fa ya cimmana."

Yar Ficika ya karya kai yana riƙe da ƙasan jallabiyarsa.

"Haba Simagade, ina aikin yake a nan? Ai idan daɗin miya bai karya ludayi ba, wahala ba za ta karya guga ba. Ka ganni nan..." ya bubbuga ƙafa a ƙasa "digirgir nake a tsaye. Abin da zan yi in daɗaɗa maka ba zai taɓa zame min wahala ba."

Abba ya yi masa godiya. Ƴar Ficika ya koma cikin kitchen ɗinsu inda ake ta yanka naman kaza. Guda cikin yaran ya samu yana gyara wutar gashi.

"Tasalluwa me za ayi da wannan uban garwashi?"

"Ba gasa naman za ayi ba?"

Duka Ƴar Ficika ya kai masa a ƙeya "sai shegen rawar kai yawa akwalan keke. Abin da ya kamata ba shi kake yi ba. A zafin nan za a gasa nama tun yanzu a ajiye? Ba sai ya buga ba?"

Tasalluwa ya ɓata rai "daga abin arziƙi?"

"Idan aka basu naman yana hamami ai raini za ka jawowa ɗiyar tamu. Ko baka san ɗan Alh. Hayatu Maitakalmi take aure ba?"

Tasalluwa ya tafa hannuwa "eyyee, ashe abin babba ne, wai an kashe kwarkwata da taɓarya. Aikin na bajinta zamu yi."

Wani dake kusa yana jin hirar tasu ya ce "ai ke dai Allah Ya kawo kuɗi talauci yaji kunya. Nan da lokacin da za ta haihu kaji hamsin za mu babbake ba ashirin ba."

"Ahayyeeee"

Su ka dinga tafawa ana tsara irin girkin da za ayi idan Hamdi ta haihu. A cewarsu aikin yau ba ayi yadda ya kamata ba saboda tsadar rayuwar da ake fama. A haka kuma ba ƙaramin ƙaƙari Ƴar Ficika ya yi ba. Kaji ashirin za su yiwa gashin tukuba, meatpie, donut da cake duka guda ɗari ɗari yaran da su ka ƙware a nan fannin su ke yi. Sai abincin gargajiya. Tuwon shinkafa da miyar gyaɗa da kabewa wadda taji naman rago da alayyahu, waina, funkaso da alkubus kuma da farfesun kai da ƙafar rago. Sai lemon ginger da zoɓo da su ka ƙware wajen yi ana zubawa a sababbin robobi masu tambarin sunan gidan abincin nasu. Shi dai ya haƙura ya san ya makara, da wuya ya haifa. To amma fa wanda Simagade ya haifo musu sai inda ƙarfi ya ƙare.
RAYUWA DA GIƁI 26





Batul Mamman💖






***

Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya ɗauki Hamdi kafin ƴan kawo lefe su iso take yi. Zee da ƙanwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ƴan rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane taƙamaimai me yake damunsa. Halin da take ciki kenan yanzu. Tana son Taj, sannan kuma tana gudun kasancewa inuwa guda da shi.

A daren jiya ne da tana addu'a ta fara mamakin wannan sabon al'amari da ya tunkaro su. Alaƙarta da Taj ba irin wadda ake shan wahalar farata bace. Lokaci guda su ka yi clicking kamar hagu da daman mayen ƙarfe. Irin wannan rashin sakewar kafin a saba duk basu fuskanta ba. Lokaci guda su ka karbi juna a sabon matsayin da Allah Ya ajiyesu.

"HAMDIYYA!"

Firgigit ta dawo hayyacinta da jin kiran Yaya da ƙarfi.

"Tunanin me kike yi haka?"

"Babu komai" ta miƙe tsaye tana neman mayafinta.

"Me ki ke nema?" Yaya ta tambayeta.

"Mayafina."

"Wanda ki ka yafa kuma fa"

Kallon jikinta tayi ta ce "au..."

"Zauna Hamdi. Magana za mu yi."

Bata kawo komai ba tunda a tunaninta ta ɓoye yanayinta sosai ta zauna. Yaya ta tsareta da tambayar me yake damunta kwana biyu. Ta fara rantse rantse Yaya ta ce bata san zance ba.

"Idan ba wata uwar gareki a waje wadda ta dace da sanin damuwarki ba ina son sanin me ya sanyaki kwana kina sallah da kuka."

Gaban Hamdi faɗuwa ya yi. Ba za ta iya faɗawa kowa Taj ya mareta ba. Haka kawai take ganin kamar za su yi rabuwa ta har abada idan aka sani.

"Yaya babu komai."

"Kina ganin saboda lalurata da yanayin Abbanku bamu isa mu share miki hawaye idan kina da damuwa ba ko?"

Ɓacin ran uwa abin gudu. Nan da nan hankalinta ya tashi ta soma bata haƙuri.
"Ki daina faɗin haka. Wa nake da shi bayan ku?"

Da wata irin murya mai ban tausayi Yaya ta ce "Ba yau ki ka fara ba. Tun ƙuruciyarki na san kin tashi da ganin kamar bamu cika iyaye ba."

Kuka sosai Hamdi tayi. Wannan banzan tunanin tun yaushe ta ajiye shi. Ummi ta ankarar da ita girman mahaifinta a lokacin da take ganiyar gudun a alaƙantasu. Yaya ce dama tun farko bata taɓa rainawa ba. Tana son abarta a yadda take. Wannan furucin da tayi ne dai ya sake karyar mata da zuciya tayi ta kuka tana bata haƙuri.

Bayan wani ɗan lokaci da Yayan ta ce ta haƙura shi ne ta faɗa mata rabin gaskiyar zancen. Akwai mai son Taj, ta dawo da wayar da su ka taɓa yi ta ce ai matar har kiranta tayi ta tsorata ta.

"Wai idan na yarda na tare sai ta illata rayuwata."

Dariya taga Yaya tayi kafin kuma ta ce,

"Shi ne kike kuka? Kodayake Allah ki ke gayawa. Ya isar miki akan komai. Duk da haka cewa Yayi ka tashi In taimakeka. Kada ki yarda wata mace ta zama silar hawayenki a gidan miji."

"Ko da yafi sonta?" Hamdi ta tambayeta tana kuka.

Da yake Yaya bata saba ganin ƴar tata ta nuna rauni irin haka ba sai take ganin son da take yiwa Taj ne kawai bata son abin da zai shiga tsakaninsu. Kalaman da za su kwantar mata da hankali ta zaɓo. A cikin ranta kuma tana ƙudurta yi mata addu'a da sauran ƴan uwanta akan kada Allah Ya haɗa mazajensu da matan banza.

"Yafi son nata ya aureki? Ko kin manta ba tayinki aka yi masa ba?"

"Haka ne."

"Ki cigaba da addu'a sannan ki dage ki ƙwaci kanki a gidan aure. Mu bamu san boka da malami ba. Kuma bamu san makirci da sharri ba. Indai kin tsaya a tarbiyar musulunci ta zaman aure da kuma riƙo da dabarun zaman duniya za ki ga baki da yawan damuwa."

Kai tsaye ta ce "Yaya kin koya mana dabarun zaman duniyar ne?"

Yaya tayi dariya "Hamdi kenan. Da gaske ki ke son kare martabar aurenki. Hakan ya yi kyau. Lusarar mace bata taba burge miji dama." Ta gyara zama "su dabarun zaman duniya yau ce take koya maka. Sai kuma amfani da dama idan ta zo da kuma zurfafa tunani da hangen nesa. Sauri ko gaggawa a komai ɓata lamura suke. Saboda haka don wata ta kira ki tana surutu kada ki yarda ya zama dalilin da za ki ce kin gama aure ko kin bar mata miji. Ki ƙoƙarta. Sai idan kin yi naki kin ga mijin ƙwallon mangwaro ne sannan za ki jefar dashi ki huta."

Ji tayi kamar an sauke mata dutse daga zuciyarta. Ta faɗa jikin Yaya tana dariya mai haɗe da jin kunya. Yaya ta rungume abarta tana shi mata albarka. Da Zee ta leƙo domin ta faɗa musu zuwan direban da zai ka su tayi mamakin yadda ta gansu.

"Wallahi nima sai anyi dani."

Ta daka tsalle dama idan shirmenta ya motsa sai addu'a, ta faɗa kansu. Sai washhh ɗin Yaya kawai kake ji tana cewa su tashi za su ɓalla ƙashin da bashi da ƙwari.

***

Cikin ginin wani kamfanin robobi wanda a halin yanzu shi ne dukiyar taƙamar Alh. Mukhtar da iyalinsa direban Alhaji ya shiga. Akwai mota a gabansu ta wasu manyan ƴan kasuwa guda biyu wanda su ma direba ne ya kawo su. Su ne su ka yi musu jagora har wurin.

Da su ka firfito da girmamawa su ka zo wajen motar Alh. Hayatu su ka sske tarbarsa tunda dama a hanya su ka haɗu da farko.

"Alhaji ni fa ka sanya ni a duhu da ka ce mu faɗawa Alh. Mukhtar lallai ya tafi kamfani yau duk da asabar ce kana son ganinsa. Allah Yasa lafiya dai." Cewar guda daga cikinsu.

Fuskar Alh. Hayatu babu fara'a ko ɗigo ya ce masa "lafiyar kenan. Yana da kyau mutum ya dinga zaga dukiyarsa ne saboda halin rayuwa."

"Shakka babu uban Kantin Kwari da kewaye." Ɗayan ya ɗaga hannu yana jinjina masa

"Ka san na faɗa muku akwai wata alaƙa tsakanina da shi."

"Ƙwarai kuwa. Saboda ka ce kuna da dangantaka. Lokacin kuma mu duka bamu shirya barin kasuwa mu zauna a nan ba mu ka bashi. Yanzu gashi cikin ikon Allah ya mallaki kaso ashirin da takwas cikin ɗari. Kasuwa tayi albarka, shi yasa mu ka bari ya zama partner ɗinmu." Na farkon ya yi bayani a taƙaice.

Alhaji ya gyaɗa kai yana tuno wasu ƴan shekaru a baya. Lokacin Ahmad bai yi aure ba amma idan ka ganshi tamkar mai mata huɗu da ƴaƴa goma. Ya fige tamkar kazar mayu. Kullum yana rama ga zafin nema kai ka ce wani yake ciyarwa. Matan gidansu su ka shiga damuwa. Alhaji ya tsananta bincike domin a lokacin Ahmad ƙin faɗa masa gaskiya yayi. Ashe karayar arziƙi ce ta sami Alh. Mukhtar. Mami ta taso shi a gaba. Ashana wannan idan suna buƙata sai ta kira Ahmad. Ita bata yarda tayi rayuwa daidai da samun mijinta ba a lokacin. Ta ƙuntatawa yaron iyakar ƙuntata. Duk wata kadara da Alhaji ya mallaka masa ya sayar ya bata kuɗin. Idan babu yawa tayi ta bala'i da kiran za ta tsine masa.

Ranar da Alhaji ya san gaskiya sai da ya yiwa ɗansa hawaye saboda tsabar tausayinsa da yaji. Gashi kuma ya san cewa ba huruminsa bane raba ɗa da uwa. Shi yasa bai taɓa hana Inna mu'amala da Taj ba. Gidansa kawai ya hana shi shiga. To dama ya san da maganar buɗe kamfanin robobin. A wurinsa ma su ka ranci kuɗin. Shi ne ya basu shawarar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login