Showing 168001 words to 171000 words out of 182238 words

Chapter 57 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

mummunan labari? So kayi ka tafi ka barni da tunanin irin halin da ka shiga yana haunting ɗina?"

A raunane Kamal ya ce "ba haka bane."

"To yaya ne?" Bai san ya fara hawaye ba "I was happy Kamal. Ina dariya ina nishaɗi saboda na auri wadda nake so kuma na samu Alhaji ya yafe min. How could I be happy. I shouldn't..."

Kamal ya marairaice masa "Da ka zauna mun yi kukan nan kawai mun share. Wannan mitar bata da amfani. Laifi ne na riga nayi kuma na karɓa. Haba Happy na Happiness." Ya kama murmushin ganin ya soma samun kansa "nace kai ma ka na kallon finafinai kenan ko? Na ga sai wani blaming kanka kake yi irin abin nan na masu ɗan uwa."

Cije leɓe Taj yayi yana harararsa. Daga ƙarshe ya yi kwafa gami da jinjina kai.
"Za mu haɗu."

Daga nan hirar ta koma kan tambayar jikin Kamal da yadda yake ji a yanzu. Motsi kaɗan zai yi Taj ya dinga tambayarsa me yake so. Shi kuwa tambayar da su Alhaji su ka yi ta kakkaucewa amsa masa ya samu ya yi.

"Happy wa ya bani ƙoda?"

Alamun alhini Kamal ya fara gani a tattare da Taj shi yasa ko da ya wayance da cewa
"Ban fahimce ka ba? Masu alhakin faɗa maka ɗin shiru su ka yi don su jiƙa min aiki?" Ya tashi zai fita "bari na kirawo maka Alhaji."

"Ka ajiye maganar wasa don Allah. I need...I must know."

Allah Ya sani bai so haka ba amma kuma rashin amsawar ba komai zai janyo ba sai tashin hankali ga mara lafiya, wanda kuma ko kusa ba a son haka.

"Kamal, Yaya ce tayi donating. Yaya mahaifiyar Hamdi."

Da wani irin yanayi Kamal ya zabura sai da Taj ya danne masa kafaɗa.

"Yaya fa ka ce. Let me go." Ya doke hannun Taj "ka sake ni mana. Taj ba fa wasa nake ba. Ka ƙyaleni na tashi."

"Ina za ka idan ka tashi? Wai ma so kake aikin ya buɗe ka mayar da hannun agogo baya?"

Kawai sai Kamal ya sanya tafukan hannunsa ya rufe fuska ya fashe da kuka. This time around fassara kukan nasa ma abin wahala ne.

"She is fine fa Happiness. Wallahi jikinta da sauƙi sosai."

"Me ya faru? Na kasa fahimtar komai."

Taj took his time ya labarta masa abin da Mubina ta sanar da shi da Hamdi jiyan bayan komawarsu masauki. Guilt ke damunta har lokacin shi ne ta zaɓi sanar dasu yadda aka yi Yaya ta fara tunanin binta daga hirarsu a jirgi. Hatta recording ɗin saƙon da ta bari ya fayyace masa.

"Na kasa murna Happy. I feel...Subhanallah" idanun Kamal cike fal da hawaye ya rirriƙe Taj "ka kai ni wajenta don Allah ko na tafi da kaina."

***

Ɗakin yayi shiru sai sautin kuka da yake fitowa daga wayar Ahmad ta speaker. Whatsapp call ya kira ta wayar Sajida. Ita da Zee da Halifa babu wanda ba ya kuka. Hamdi ma kukan take taya su. Yayinda Abba Habibu da Yaya murmushi su ke yi kawai wanda babu komai cikinsa illa dauriya. An ɗaga mata gadon ta yadda bayanta yana jingine da filo.

Muryar Halifa ce ta fito daga wayar yana shessheƙa "don Allah a mayar da kiran nan bidiyo mu ganta."

"Yanzun nan kuwa" Ahmad ya saita wayar akan Yaya bayan ya juya call ɗin.

Yaya tayi saurin gyara yanayin fuskarta gami da faɗaɗa murmushinta.

"Kun ganni fa. Wallahi naji sauƙi sosai. Ku kwantar da hankalinku."

Hamdi ta ƙara musu da cewa
"Da a ce da matsala kun san ba zan ɓoye muku ba."

"Wai me ya kai ki gidan mutane da sassafe Sajida? Nan yanzu ba na jin bakwai ta yi." Abba Habibu ya yi maganar yana duban agogon wayarsa. Awa biyu ne tsakaninsu da Nigeria. Tara saura ƴan mintuna yana nufin a can bakwai ne saura.

Sai lokacin Anti Zinatu da take ta aikin matsar ƙwalla tayi magana. Tun dare da Abba Habibu ya sanar da ita halin da ake ciki ta karɓi lambar Safwan da dabara a wajen Zee. Ta sanar da shi komai sannan ta buƙaci ya kawo Sajidan wajenta a lokacin da za a sanar da su. To ashe shi ɗin ma mutum ne mai saurin ruɗewa. Daga wayar nan bai sake yin wani abin kirki ba, ko bacci ɓarawo da ƙyar ya sace shi. Ai kuwa ana sallame asuba ya ce ta shirya su taho.

"Ni dai yanzu alfarmar da zan roƙe ku don Allah kada wanda ya tayarwa Innata hankali. Ku bar zancen nan har sai na dawo in sha Allahu. In lafiya ta samu yadda ake so ma ba sai ta sani ba."

Shawarar Yaya rabi ce ta sami karɓuwa a wajen Alhaji. Batun a rufe maganar kuma ya ce ba zai yiwu ba.

"Sadaukar da ƙoda babban abu ne wanda a halin da muke ciki yanzu da wuya maganar ta ɓuya. Idan wani bai fađa ba, wani zai iya faɗa. Saboda haka za mu jira ki sami sauƙi sai mu auna mu gani shirun da faɗar gaskiyar wanne ne yafi ko kuwa Habibu?"

Tattaunawa su ka cigaba da yi cikin lumana da girmamawa na ɗan lokaci. Hamdi ta ji duk ta takura. Zantukan nasu sun shafe su amma bai kamata ta tsaya musu a wajen ba. Tunanin dabarar ficewa ta fara yi sai ga kiran Bishir ta wayar Hajiya. Ya faɗa mata yana ƙasa tare da Mubina. Wai tana son tafiya Madina ne yau shi ne ta zo tayi musu sallama.

"Amma don ragon azanci ta kasa faɗa mana mu taho tare?"

Dariya taji ya soma yi yayi magana da zolaya "Hajiyarmu ta gargajiya kenan. Yanzu duk ɓarin hawayen da ta gama yi a asibitin nan baki gane komai ba?"

"Me aka yi?" Kafin ya bata amsa ta soma murmushi "kai Bishir ka tabbata?"

"Kin gano kenan" ya kama dariya sosai. Mubina dake gefensa ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin ɓoye murmushin dake neman kufce mata. Ta ji abin da yake cewa ta kuma gane me hakan yake nufi.

Hajiya cewa tayi su hawo da sauri sannan ta zaga bayan Mama ta faɗa mata yadda su ka yi da Bishir. Baki ya kasa rufuwa da Mama ta fesawa kowa zancen. Yaya ma daga kwance ta taya su murna. Sannan ko kusa bata yi mamaki ba. A ganinta dama soyayya ce kaɗai za ta sanya Mubina biyo bayan patient har wata ƙasar.

Alhaji da Abba Habibu ma sun nuna farinciki ƙwarai. Hamdi sai ta sake amfani da wannan damar za ta sulale ta gudu kafin su farga. Kamar haɗin baki ta na buɗewa Taj ya turo Kamal akan wheelchair.

Hirar iyayen a take ta yanke sai tambayar me yake faruwa.

"Wajen Yaya na zo." Kamal ya ba su amsa da kansa.

Murmushi Yaya ta yi masa da su ka haɗa ido "ai bai kamata ka fito a wannan yanayin ba. Taj da ba ka kawo shi ba."

"Nayi ƙoƙarin hana shi Yaya amma wallahi ya ƙi. Dole na kira wani Nurse shi ne ya ɗora shi a nan" ya nuna wheelchair ɗin.

A daidai lokacin kuma Bishir da Mubina su ka shigo ɗakin. Hankalin Kamal ya yi gaba bai kula da su ba da farko. Ya ce Taj ya matsar da shi daf da gadon Yaya. Ya tura shi kuwa jikin gadon sosai. Kamal ya miƙa hannunsa na dama dake ɗauke da canula saboda ƙarin ruwa da ake yi masa ya riƙe nata hannun sannan ya kalli Abba Habibu.

"Abba na riga na zama ɗan Yaya shi ya sa ban nemi izinin taɓa hannunta ba."

Abba Habibu ya gyaɗa kai yana murmushin nan nasa. Ragowar kuwa duka aka yi shiru ana sauraron Kamal.

"Duk wahalar dake tattare da ɗaukar ciki da haihuwa a wurin mata a ƙarshe tana da riba Yaya. Za a kalli mace a kira ta UWA ko da ɗan ba a gabanta yake rayuwa ba. Su kan su mata abinda ya sa su ke jurar wannan wahalar komai tsananinta bai wuce domin samun wannan matsayin ba. Mace za ta zama mai cikakken iko akan wani bawan Allah da yake rayuwa da jinin jikinta." Ya ja numfashi "Allah Yana biyan wahalhalun da ta sha akan ƴaƴanta da mafi ƙololuwar daraja. Ya bata martabar da babu mai kamo ta a wajen wannan bawa har ƙarshen rayuwarsu su biyun." Ya yi murmushi idanunsa fal hawaye. Ko da ya ɗaga kai ya kalli Yaya sai hawayen ya zubo. Nata ma ya zubo...idan ka cire Alhaji, Abba Habibu, Ahmad da Taj, duka waɗanda su ke ɗakin sai da su ka zubar da ƙwalla.

"Yaya wace daraja ki ke tunanin Allah Ya tanadarwa matar da ta bawa ɗan da bata da alaƙa da shi ta jini wani ɓangare na jikinta don ya rayu? Bayan kin san cewa wahala, azabar ciwo da fargabar me zai je ya dawo a dalilin sadaukar da ƙodarki ba zai mayar dani ɗan ki ba. Taki juriyar naƙasu ce a jikinki da lafiyarki. Babu wata riba ta kurkusa ko ta nesa don ban ga abin da za a biya ki da zai maye gurbin ɓangaren jikin ki da ki ka bani ba Yaya."

"Kamal ka yi shiru don Allah. Jikin ka babu ƙwari." Yaya ta faɗi cikin kuka.

"Yadda ɗa baya yin godiya ga iyayensa akan haihuwarsa da su ka yi, haka ni ma ba zan yi miki godiya akan kyautar da ki ka yi min ba. Alfarma kawai na zo sake roƙa domin Allah."

"Ina jin ka Kamal. Don Allah ka daina kukan nan."

"Yaya idan kina lissafin ƴaƴanki ki dinga farawa daga Kamaluddeen Hayatu don Allah." Kuka sosai yake yi a wannan gaɓar.
"Idan kina da sirri irin na uwa da ɗa don Allah ki yi dani." Yaya ta gyaɗa kai.
"Damuwa ko wacce iri ce irin ta uwa da ɗa kada ki tsallake ni." Nan ma ta sake nuna amincewarta.
"Buƙata ko wacce iri ce ta uwa da ɗa ki fara faɗa min tunda kin ga Halifa ƙarami ne. Su Hamdi kuma mata ne ma su rauni."

"To Kamal" Yaya ta amsa cikin kuka.

"Idan su Sajida sun yi miki laifi don Allah kada ki ɓoye min. Ki rufa musu asiri a wajen Abba amma ki sanar dani. Zan yi mu su faɗa tamkar cikin mu ɗaya."

"Na sani Kamal, ko babu wannan abu ai kai me tsaya mu su ne."

Kamal ya girgiza kai "a da sai dai nayi kara, yanzu kuwa duk abin da ya shafe ki Yaya ya zama dolena."
Ku san sai a lokacin ya lura da tsayuwar Mubina a ɗakin. Sai ya yafito ta da hannu. Ta so cogewa amma Mama da kanta ta kaita kusa da Kamal ɗin.

"Kin amince da zaɓina Yaya? Idan na auri Mubina ƴar mu ta farko in sha Allahu sunan ku ɗaya. Sunan ta..." ya kalli Hamdi yana jiran ta ba shi amsa.

"Khadija."

"In sha Allahu sunanta Khadija."

Yaya ta rasa abin cewa. Tana gudun zaƙalƙalewa a gaban iyayensa. Gashi kuma ya tsare ta da idanu yana kallonta with so much adoration.

Alhaji ne ya yi stepping in da ya ga ta kasa magana.

"Ba ki ce komai ba game da zaɓin ɗan naki Yaya?"

Yaya ta ɗaga kai a rikice ta kalli Abba Habibu tana neman agajin sa. Ita fa komai bambarakwai take jin sa tun shigowar Alhaji ɗakin nata. Ba ta son yin abin da zai sake janyo wa mijinta abin magana.

Cikin nutsuwa Hajiya ta matso ta kama ɗayan hannun Yaya a yayinda ɗayan har lokacin ya na cikin na Kamal.

"Ko ba ki karɓi tayin da Kamal ya yi miki bane na zama uwa a gare shi?" Ta haɗa hannuwanta biyu tana magiya "Don Allah ka da ki kasa yi masa wannan alfarmar. Kamar yadda ya faɗa babu zancen biya ta kowacce fuska tsakanin mu. Hakan raini ne ma akan girman abin da ki ka yi mana. Ƙara shi cikin zuri'arki ne kaɗai abin da za mu iya duk da cewa mu ne dai da sake samun riba."

"Don Allah ku daina magana irin haka. Domin Allah nayi." Ta zame hannunta dake cikin na Kamal ta nuna ƙirjinta "Karamcin Ubangina a gare ni mai girma ne. Shi Ya nufe ni da zuwa a lokacin da Kamal yake tsananin buƙatar hakan ba tare da sani ko shirin wanin mu ba. Kuma Ya azurta ni da dakewar zuciya na cika umarnin ƙaddara. Ni da har yau nake tsoron allura sai gashi na kawo kaina inda za a yanka min ciki. Na fi ku riba wallahi. Allah Ya bani ikon ceton rai sannan Ya ƙara faɗaɗa ƴaƴana." Ta sanya hannu ta shafa kumatun Kamal. Shi kuwa ya ɗora hannunsa akan nata ya lumshe idanunsa cikin farinciki.

Maimakon kuka kuma sai farinciki ya mamaye ɗakin. Mubina ta kasa daurewa ta bawa Yaya haƙuri domin tana ganin cewa ita ce ta jawo mata zuwa nan ɗin.

"Kada ki sake magana irin wannan Dokta. Mu duka mu na yin komai ne cikin tsarin Ubangijinmu. Ba ki yi min laifi ba amaryar ɗana."

Kunya ta kama Mubina. Ta koma kusa da Hamdi ta sunkuyar da kanta.

Da jindaɗi Alhaji ya ce "Tunda abin ya zo da haka ku ba ni dama na yi mu ku karambani akan Baban Khadija da Maman Khadija mana."

"Innalillahi..." Mubina ta faɗi a kiɗime da jin furucin Alhaji tana mai ƙanƙame hannun Hamdi. Ita ma dai babu halin zolaya kunyar ce ta kama ta.

"Abban Kamal ka yi shiru."

"To Alhaji mun ba ka dama." Abba Habibu shi ma dai yana cikin jin nauyin wannan sabon lamari.

Shi kuwa Alhaji dama da gayya ya yi. Yana so ne ya canja takun mu'amala a tsakanin su tun wuri saboda a sake sabon lale tun kafin su koma gida. Waya ya ɗaga a gaban su ya kira kawun Dr. Mubina, yayan mahaifinta. Ita kanta ba ta san inda ya samo numbar ba tunda bai tambayeta ba. Maganar su ta ƙarshe ita da shi sosai dai tun kwanciyar Kamal a asibiti ne inda su ka fara haɗuwa har ya ce ya san Marigayi mahaifinta.

Ya fara da gabatar da kansa wanda da alamu hakan bai yi wa kawun nata wahalar ganewa ba. Daga nan ga mamakin dukkanin su ya ɗauko maganar su da Kamal. Ya soma yi masa bayanin rashin lafiyar sa sai kawun ya ce ya gane shi. Bai dai san cewa ɗan Alhajin ne patient ɗin da ta dinga roƙonsa har ya barta tahowa duba shi da yin Umra ba.

"Tunda dai har an dace ya sami ƙodar, ina ganin kawai ta zauna ta ƙarasa ladanta. Ina fata ka fahimce ni."

A take Alhaji ya danna speaker yana murmushi sosai. Komai ya zo masa da sauƙi fiye da yadda ya yi tsammani. "Ƙwarai kuwa. Na saka ka a speaker a gaban iyalina, Kamal da ita Mubina. Zan so ka maimaita abin da ka ce domin nima dalilin kiran kenan. Ina son a san da zaman mu zuwa lokacin da Allah zai sa ya sami lafiya ya dawo gida."

Kawu ya maimaita "Ka fi ƙarfin haka Alh. Hayatu. Me yiwu wa ba za ka iya tunawa ba amma ni abin yana raina sosai. Mun taɓa zuwa wajen ka nema wa yaran wasu ƙauyuka kuɗin jarabawar SSCE har su ɗari da sittin da bakwai. Bayan ka biya ka ɗauki ukun farko ka biya musu kuɗin jami'a in full sannan ka sa mu ka yi alƙawarin ba za su taɓa sanin kai ne ba. Shi ya sa wasu lokutan taimako yake zuwa ga bayin Allah ta inda ba sa zato. Sadaka babban jari ce."

Alhaji ya yi ɗan murmushi kawai. Ɗan Adam ba ma'asomi ba. Kullum mu na cikin iyo tsakanin dai-dai da kura-kurai. Yawan tuba, ƙoƙarin fifita aikata ayyukan alkhairi da uwa uwa kyautatawa Allah SWT zato shi ne babbar maslahar rayuwa. Zai iya cewa a tsukin lokacin nan ya ƙara fahimtar rayuwa ta fuskoki mabambanta. Da fari ya yi karo da tsohon kuskurensa sannan yanzu ya gamu da tsohon alkhairi. FABI AYYI AALA'I RABBIKUMA TUKAZZIBAN

Kawu kuma ya ɗora maganar sa.
"Mubina ki zauna ki ƙarasa ladan ki har a sallame shi ."

Mamaki tayi sosai "Kawu aikina fa? Kuma ..." ta saci kallon su Ahmad "ba ya buƙatar zama na."

"Ai kuwa ki shirya domin kowa zai tafi ya bar ki da shi. Haɗa ni da Alh. Hayatun."

Jikin Mubina ya yi sanyi ƙalau har ta kasa motsin kirki. Zuciyarta kawai ke harbawa da daidai da fitar kalmomin godiya daga bakin Alhaji domin ya cire wayar daga handsfree. Bayan ɗan lokaci ya miƙa mata wayar.

"Je ki waje ki amsa"

Da sauri ta fita har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi. Ita kuma ganin haka sai ta nemi zare hannunta. Mubina ta dube ta da raunin murya.
"Raka ni don Allah."

*

Shiru Mubina tayi tana sauraron Kawunta.

"Alh. Hayatu ya ce zai sake kira na anjima kaɗan mu ƙarƙare magana. Idan komai ya tafi daidai in sha Allahu yau zan sauke amanar ɗan uwana, zan aurar dake ga mutumin da na tabbatar ki na so sannan ga dangin da nake fatan ba za su taɓa wulaƙanta ki ba."

"Amma Kawu..."

"Na san ban shiga haƙƙin ki ba da na yanke wannan shawarar. Soyayya ta Fisabilillahi ce kaɗai ta saka ki kusan zaucewa akan yaron nan kafin ki tafi. Yanayin ki ya bani tsoro shi ya sa ban hana ki tafiya ba da ki ka buƙaci zuwa Umra ke kaɗai saɓanin yadda mu ka yi shirin tafiyar gida cikin ƴan uwa."

Kuka ta fashe da shi.

"Ki bar kuka Mubina. Ina son amincewar ki ne domin yanzu zan tafi wajen Umman ki. Ki amince?"

Da ka ta fara amsawa sai ta tuna ba ya ganin ta shi ne ta ce "Uhm" a hankali.

"Allah Ya yi miki albarka."

Rungume Hamdi tayi bayan ta gama wayar. Hamdi ta dinga bubbuga mata baya saboda kuka ne take yi sosai. Bata taɓa zato ko da wasa akwai ranar da burinta zai cika akan Kamal ba. Ta fi karkata da tunanin cewa zuwa yanzu ya ma bar duniyar.

"Ki daina kukan nan haka Matar Yaya. Ni ce ke sujjada zan yi domin wannan babbar falala ce daga Allah SWT." Hamdi ta rarrasheta.

"Nagode Hamdi. Abin ne duk wani iri. Kin ga ana shirin aurar dani babu kowa nawa."

"Gani." Ta sakar mata murmushi "Don Allah ko da wasa kada ki taɓa yi min kallon matar ƙanin miji. Ƴan gidansu sun yi min tarbar ƴa kuma ƴar uwa ba suruka ba. Ina ganin rashin adalci ne zai sa mu kuma mu ɗauki kan mu da wani matsayi daban da na ƴan uwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login