Showing 171001 words to 174000 words out of 182238 words
Chapter 58 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
taka."
*
A cikin ɗakin kuma bayan fitar su Mubina, Kamal ya ce Taj ya mayar da shi ɗaki. A hankali ya juya wheelchair ɗin yana mai kulawa da dukkan motsin da zai iya janyo wa Kamal jin zafi.
Sallama Kamal ya yi wa kowa. Da ya zo kan Alhaji sai cewa ya yi da Taj ya tsaya.
"Na ji kana ta magana a hankali ga Alhajin ka tambaye shi da kan ka?"
Taj ya yi turus domin gabaɗaya bai gane me Kamal yake nufi ba. Ya kuma san cewa tunda ya yi haka to akwai abin da yake ransa. Lokacin wana shi ya samu. Sai ya rama ɓoye-ɓoyen da aka yi masa.
"Me ka ke son tambaya?" Alhaji ya zuba mu su ido don ya gano wayon Kamal.
"A bar maganar Alhaji. Zan dawo idan na kai shi ɗaki." Taj ya ɗan tura Kamal sai yaji kujerar ta turje. Kamal ya saki burkin tayar don kada su tafi. Ya yi kalar tausayi.
"Ai gara ka tambaya yanzu saboda ni bana so ka tafi ka barni ni kaɗai."
Abba Habibu murmushi ya yi. It is obvious Kamal a matse yake da son jin manufar maganganun Alhaji a waya. Ahmad kam dariya yake yi sosai.
Alhaji ya yi ƴar dariya shi ma
"Kamal ina jin ka. Me Taj ya ke son sani?"
"Cewa ya yi wai ya ji kamar ana maganar aure na."
Taj bai san lokacin da ya ce "Ni? Kamal yaushe?" Don bai yi tunanin tambayar da Kamal ɗin zai yi kenan ba.
Inna ta shigar wa Kamal "Ai tunda ya ce ka yi kawai ka yarda cewa ka yi ɗin don a zauna lafiya."
Da gangan Taj ya ce "Shikenan to."
Ya kalli Alhaji "na ji kamar ka na maganar aure na."
Ya yi nasarar tunzura Kamal kuwa don bai san lokacin da ya gyara masa ba.
"Aurenka kuma? Yaushe ka yi aure da har ka ke tunanin ƙari?"
"Ƙarin aure kuma Allah na tuba ai ba abu bane mai wahala."
"To wai nufin ka Hamdi za ka yi wa kishiya? Happy akan su fa ni babu ruwana da dangantaka. Hamdi comes first yanzu. Da kai da mazajen su Sajida duk ɗaya ne a wajena. Kai suruki ne, ni kuwa ɗa ne ko Yaya?" Shi ma ya rama zolayar da Taj ya yi masa.
Sai ga Taj da riƙe haɓa. Aiki ya biyo ta kan ma su gida.
"Lallai ma! Happiness kada mu ɓata daga farfaɗowarka fa. Har za ka faɗa min kusanci da Yaya?"
"Wannan ko shakka babu." Kamal ya ce kai tsaye "kai ƴa kawai ta baka. Ni kuwa ƙoda ta bani. Akwai jinin jikinta a tare da ni. Tsakanin mu ma babu haɗi.
Mayar da rigimar tasu aka yi abin dariya a ɗakin. Taj ya nemi taimakon Abba Habibu da Yaya ta gyaɗa kai tana supporting ɗin Kamal.
"Abba ka na jin sa fa."
"Ƙyale su Taj kai fa ɗan maigida ne. Shi kuwa Kamal agolan gida ne, ka san su akwai rawar kai. Gida na hannunka. Duk yadda ka dama dole a sha ko ba a so."
Dariya aka sake yi inda Kamal da Yaya su ka ce basu yarda da wannan muƙami da Abba Habibu ya bawa Taj ba. A wannan halin Hamdi da Mubina su ka dawo. Taj ya ja Kamal su ka koma nasa ɗakin. Ahmad kuma ya mayar da Mubina da Hamdi hotel. Yayinda Alh. Hayatu ya cigaba da nasa shirin daga nan. Ƴan uwansa maza ya kira ya sanar da su shawarar da ya yanke. Su ka yi na'am da farinciki. Yaya Babba ya shiga gaba su ka haɗu da ƴan uwan Hajiya, wani abokin Alh. Hayatu da ƴan uwa shaƙiƙan sauran matan mutum ɗaiɗai sai gidan Kawun Mubina. Shi ma kafin zuwan nasu ya riga ya faɗawa duk wanda ya kamata. Ana idar da sallar la'asar wanda ya yi daidai da magrib a birnin Jeddah aka ɗaura auren a masallacin unguwa.
Asibitin gabaɗaya ya kaure da murna. Ma'aikatansu waɗanda su ka san Kamal da Yaya su ma duka sun taya su murna sosai.
RAYUWA DA GIƁI 40
ƘARSHE
Batul Mamman💖
Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN
A can hotel Mubina ba ƙaramar takura ta shiga ba. Aure dai an ɗaura amma kamar yadda ta ce babu kowa nata sai dangin miji. Duk sai ta koma abar tausayi. Yaya Kubra ta lura da haka sai su ka yi magana da Yaya Hajiyayye, aka kama mata ɗaki daban domin kwana biyun da su ka yi ɗakunan da su ka kama na group ne masu gado hurhuɗu.
"Hamdiyya ki koma wajenta ki tayata zama. Idan kuna buƙatar wani abu ki mana magana. Na san ba za ta sake da mu ba yanzu kuma sai a hankali."
Hamdi tayi murmushi harda rufe fuska da tafukan hannu "nima dama kunyar taku nake ji har yanzu."
Yaya Kubra ta harareta da wasa
"Ehhh lallai, wallahi ki ka sake cewa kina jin kunyarmu sai na yi mi ki handsfree a gaban Alhaji."
"Tsegumta min mana likita. Me ki ka gani? Tajo ya yi ajiya ko? Oh ni uwar babana. Aure ko wata biyu ba a yi ba. Dama na san za a rina. Taj ko kaɗan bai yi kama da salihai ba.
Hararar da take yiwa Hamdi komawa tayi kan Yaya Hajiyayye.
"Ke fa daɗina da ke sakin zance wallahi. Don Allah kina yi kina tauna magana kafin ki furzar. Me ya kawo batun salihanci tsakanin mata da miji banda abin ki?"
"Raini ya jima da shiga tsakaninmu dama Kubra. Gara ki kwaye min baya a gaban...." ta waiga babu Hamdi babu dalilinta. Can ta hangota ta kusa ƙure korido tana ta zuba sauri kamar ta kifa. Ita da Kubra su ka haɗa ido su ka kwashe da dariya. Faɗan da ba su ƙarasa ba kenan.
*
Ƙarfe tara da rabi Umma ta shiga ɗakin su Mubina. Hamdi kaɗai ta samu ta kashingiɗe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune.
Umma tayi murmushi "ƙanwar Ango ina amaryar yayanki?"
"Tana banɗaki" ta amsa mata ita ma tana murmushin.
"Ai gara tayi wank..."
Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet ɗin da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita.
"Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito."
"Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin."
"Na'am? Asibiti kuma" Ta buɗe ƙofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai ɓare-ɓare take yi. Mubina akwai ruɗewa sai a lokacin hakan ya bayyana.
Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ƙafarta ta taho ƙasar amma yau ɗaya duk ta sauya saboda alhini.
Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu.
"Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure."
"Umma ni dai don Allah" sai kawai ta fashe da kuka.
Umma ta tashi tsam ta rungume ta.
"Kamal ɗin ne ba kya so?"
Mubina ta girgiza kai.
"Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special."
Ba kunya Mubina ta ɓare baki "ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi."
Ɗago kanta Umma tayi ta ce "Tamɓali! Mubina? Shekararki nawa ne?"
Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda.
"Na fahimce ki" Umma ta sake yin murmushi "ƙarasa abin da ki ke yi ki kwanta"
Ta juya za ta fita Mubina ta kira ta kai a ƙasa saboda nauyinta da take ji.
"Umma ba za ku yi fushi ba?"
"Haba dai. Mubina ba na jin Kamal zai taɓa samun soyayya irin wadda ki ke yi masa. Kin haɗu da shi a halin ciwo kin so shi. Sannan a lokacin da dukkan wata ƙofa ta ƙulle sai Allah Ya yi amfani da ƙudurinki na biyo shi domin..." muryarta ta karye "ku yi sallama sai Ya kawo mafita. Hamdiyya kina ganin akwai..." ta juya ko sama ko ƙasa babu Hamdi sai kawai ta kama dariya "wannan ƙanwar taki ta san yakamata sosai Mubina. A duk lokacin da take jin ana buƙatar keɓewa cikin magana sai ki ga ta bar wajen da dabara."
"Nima na kula Umma."
"Idan ku ka rayu tamkar ƴan uwa tare da sauran yaran namu da matar Ahmad haƙiƙa kun gama yi mana komai."
"In sha Allahu."
"To amarya sai da safe."
Umma ta fita fuskarta babu komai sai annashuwa. Mubina kuwa wata ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ta faɗa kan gado. Yanzu da Umma ba mai fahimta bace kawai sai a wuce da ita asibiti tinƙis-tinƙis. Gobe kuma a dinga zuwa dubiya ana ganinta a ɗakin Kamal. Ai da kunya!
'Kamal' ta maimaita sunan a zuciyarta. Yanzu fa wai ya zama mijinta. Wani juyi tayi na farinciki tana ƙara yiwa Allah godiya.
*
Hamdi na fita ɗakinsu da Taj ta wuce da niyyar ta ɗauko kayan baccinta ta dawo wajen Mubina. She was just smiling idan ta tuna yadda ta baro Mubinan. Tana ji a jikinta Umma ba za ta matsanta mata ba. Nata key ɗin ta saka ta buɗe ɗakin. Tana shiga taji anyi sama da ita. Ta buɗe baki za ta yi ihu Taj ya sauketa ya jingina bayanta da ƙofar ɗakin. Ya tare mata hanyar wucewa.
"Kina yi su Alhaji za su zo kinga sai mu taru mu yi musu bayanin me ya firgita mu."
Ta harare shi "abin da ya firgita ni dai."
"Da na sani ma a toilet na ɓuya sai kin fi tsorata."
Hango irin tsoron da za ta ji tayi ta yi murmushi "da kuwa mai raba ka da yayana sai Allah."
"Kinga ki kiyaye ni da zancen yayanki ɗan kalen dangi. Yana can gadon asibiti me zai iya? Taj will do what Taj wants." Ya ƙare magana girarsa ɗaya a sama.
Kai ta girgiza "Gobe idan mun je ka maimaita abin da ka ce yanzu in koma gefe in sha kallo."
"You are looking for my trouble fa, and I will give it to you har sai kin ce ya isa."
Dariya ya bata ta kama ƙugu da hannu guda.
"Bring it on."
Janyota ya yi su ka nufi 3 sitter ɗin ɗakin su ka zauna. Ta ɗora kanta a ƙirjinsa shi kuma ya sake rungumeta.
"Ƴar caras matar Tajuddeen." Ya kira ta affectionately.
"Uhmmm." Ta amsa muryarta can ƙasa-ƙasa.
Kasancewarsu tare ya saukar mata da nutsuwa fiye da kullum a yau. Jikin Yaya yana ta ƙara kyau. Sai yanzu ta sami damar appreciating zuwa ƙasa mai tsarki a dalilinsa.
"Yau ban ce miki ina son ki ba Hamdi na. I love you."
"Ni ɗin kake so ko ƴar caras?" Ta tambaye shi bayan ta zauna su na fuskantar juna.
"Why do you ask?"
Baki ta tura kafin ta ce "Tun ina yarinya ake cewa jiki zan yi idan nayi aure. Wai ƙirar mu ɗaya da ƴaƴan Anti Zinatu."
"Ƙira kuma sai ka ce wata mota?"
"To dai ance zan yi ƙiba. Kai kuma har wani ƴar caras kake cewa. Kada na fashe nan gaba na daina burge ka."
Damuwa sosai yake iya gani tare da ita. Ya yi dariya ya kuma zolayarta.
"Ki fashe kamar wata kwalba?"
"Happy manaaaa" ta buga ƙafa a ƙasa.
He hugged her tightly sannan ya yi magana a hankali.
"Ko me za a ce mi ki, ko me ki ka zama a gaba Hamdiyya ki sani cewa Taj is your home. You can be anything as long as Hamdin Abba Habibu ce ina son abata. Hamdi ƴar tsinke" ya fara ƙirge da yatsansa "Hamdi ƴar doguwa, Hamdi ƴar gajera, Hamdi ƴar lukuta, Hamdi mai tumbi, Hamdi shafi mulera..."
Yana kaiwa nan wata wawuyar cakuma yaji ta kai masa tana rigima ya kwashe da dariya.
"Wai ina faɗa ne don ki san cewa ke nake so ba jikinki ba."
Daga nan ya lallaɓa abarsa su ka kwanta. Sai shabiyu saura Hamdi ta farka firgigit kamar an tsunkule ta.
"Mubina tana jira na mu kwana tare. Ya Subhanallah." Ta tashi tana neman hijabi.
Sai da ta saka tukunna Taj ya ce "to amara ƙirjin biki dawo ki kwanta. Amarya tana wajen Angonta."
"Anya kuwa? Ban ga alamun za ta tafi ba." Ta faɗa masa iya abin da ta gani da Umma taje ɗakin.
Taj ya soma dariyar mugunta. Hamdi tun tana mamaki har ta koma kusa da shi tana jiran ya faɗa mata me ya kawo dariyar.
"Kaza gashin Najeriya" ya ce da ƙyar dariya na cin sa.
"Ban gane ba fa."
"Yayanki..." dariyar harda ƙwalla.
Hamdi ta kama baki "yau ina ganin ikon Allah."
Da ƙyar ya saisaita kansa "ana cewa an ɗaura auren nan yayanki ɗan kalen dangi ya sa ni fita neman kaza. Wai bai dace amarya ta zo babu wani abu da zai tuna mata al'adar gida ba." Yana kallonta ya cigaba da cewa "kin dai sanni da faɗin gaskiya ko Hamdi na...to haka na aje kunya a gefe na nuna masa rashin fa'idar nemo kazar nan saboda kada amarya ta fassara shi yana kwance magashiyan." Ya sake yin dariya.
"Ba ka da kirki fa" ita ma ta soma dariya don ta hango inda zancen zai dire.
"Rawar kai irin ta ango sabon shiga ya ce bai yarda ba. Babe, tun la'asar nake neman kaza don ya ce dole na nemo gashin Najeriya mai ɗan ƙuli-ƙuli da yaji. Kuma bai yarda na tambayi su Bishir ba duk da sun fi ni sanin gari wai kada a raina shi. To cut the story short naji a jikina. Wurin ana layi haka nayi ta zama har na samo."
"Shi ne kake yi masa dariya?" Ita ma fa dariyar take yi.
"Sai da yasa na dawo na ɗauko masa aron kayana. Ga ciwo ga wahala amma haka ya dage na saka masa shadda harda hula. A table ɗin gefen gadon na jera masa kazar amarci, juice, youghurt da biryani. Kaiiiii, wa zai cirewa Happiness kayan nan? Ko dai in kira shi ne? Ba za su yi daɗin bacci ba."
Hamdi dariya, Taj dariya. Sai sun yi kamar sun gama da sun haɗa ido sai a sake daga farko.
"Harda turaren angwanci yasa na nemo masa mai mugun tsada ya feshe jikinsa."
Hamdi ta goge ƙwallar dariya da yatsa "Ni damuwata akwai fridge a ɗakin?"
"Fridge kuma? Akwai."
"Yauwa dama don kada kazar ta buga."
Su ka sake tuntsirewa da wata dariyar that was just contagious. Da mutum zai shigo ɗakin dole ya taya su. After 1am Taj ya raka Hamdi ƙofar ɗakin Mubina. Ta shiga ta sameta tana sallah. They just smiled at each other sannan Hamdi ta ɗauro alwala ta zo ta tayar a kusa da ita.
***
Yau dukkanninsu su ka tafi asibitin domin daga nan za su wuce su shiga jirgin ƙasa zuwa birnin Madina. Hajiya dai ta ce da Abba Habibu babu inda za ta har sai Yaya ta fara tashi da kanta. Anyi-anyi da ita ta tafi saboda akwai kulawa sosai a asibitin amma ta rufe ido ta ce su ƙyaleta. Alhaji ya goya mata baya tunda shi ma ba tafiya zai yi ba. Kamal kuma za a bar masa Abba da amaryarsa. Duk wannan zancen kafin su fito aka gama yinsa. Alhaji ya ce da Mubina idan tafi son fara yin Umrarta a nutse cikin ƴan uwa babu damuwa. Sai kawai ta duƙar da kai. Mama ta fassara masa da cewa ta amince da zaman ne. Kuma hakan yake a zuciyarta. Tun asuba mahaifiyarta ta kira ta su ka yi magana akan yin abin da ya kamata. Wasu lokutan mutum ya kan ajiye kunya da tsammanin al'ada ya yi abin da ya dace da halin da yake ciki.
Daga ɗakin Yaya su ka rankaya ɗakin Kamal. Ango ya dinga cika yana batsewa. Taj ne kaɗai ya san dawan garin. Ya yi ƙoƙari sosai bai yi dariya ya tona masa asiri ba. Sun fara yi masa sallama a zaton sa harda Mubina a tafiyar sai ya kaɗa baki ya ce,
"Mubina matso mu yi sallama, sannan ga kazar ki nan ki tafi da ita."
"Innalillahiiii...." ta tattaro numfashi kafin ta dire "wa inna ilaihi raji'un."
Ji tayi kamar ya tsomata a cikin ruwan sanyi saboda kunya. Ɗaki ya yi tsit kamar ruwa ya cinye su na wucin gadi.
"Ku fita mu tafi. Kamal, Allah Ya ƙara sauƙi."
Ahmad ya yi ta maza ya kawo ƙarshen kallon-kallon da ake yi. Ai kamar jira su ke yi su ka fita a layi ko waige babu. Mubina ko motsi ta kasa yi.
"Da alama anaesthesia bata sake shi ba har yanzu doctor. Lamarin Happiness sai kin haɗa da haƙuri. " cewar Taj.
Kowa ya watse. Babu mutum guda da ya kalli Mubina ko ya yi murmushi ko da ƙasa-ƙasa ne kuwa. Ba su isa ba ne. Duk barkwancin yayyensu sun san Yaya Kubra ko Yaya Hajiyayye ce ba za ta ɗaga mata ƙafa ba. Sun san wasan da ya kamata su shiga da wanda bai dace ba.
"Ashe haka ka ke Kamal?" Ta faɗi baki buɗe don har yanzu tana mamakin wannan magana.
Ya juya mata ƙeya "Me na yi?"
"Babu komai." Ta rage murya tana magana a hankali amma yadda zai ji "dama Taj ya ce na lallaɓa ka da sauran allura a jikin ka." Ta sami wuri ta zauna akan kujera ta juya masa baya ita ma. Ɗakin ya koma shiru.
Da ya ga babu Sarki sai Allah sai ya sauko. Yana magana abin tausayi.
"Jiya ba ki kyauta min ba. I waited."
"Shi ne yasa ka bani kunya a gaban ƴan uwanka?"
Briefly ya labarta mata yadda jiya ta kasance a wajensa. Mubina ta dinga girgiza kai ita a dole ya bata tausayi. Ya gane sarai abin nata harda tsokana.
"Kar ki yi min dariya."
That was it! Magiyarsa tamkar zuga ta koma a gareta. Dariya ta kufce mata ta kare baki ta yi.
Kamal samun kansa ya yi da zuba mata idanu kamar haɗuwar farko. She looked so cute tana wannan dariyar. Ya ji zuciyarsa tana neman cika masa ƙirji saboda farincikin da ya samu daga abin da take yi yanzu. Da ta gama dariyar tashi tayi ta dudduba ɗakin bata ga alamun nama ba.
"Ka saka min rai kuma ni ban ga kazar ba."
"Laifin naki kenan."
"Me kuma ya na yi?"
"Na zama abin tsokana dai da alama. To ki kwantar da hankalin ki domin kema kin shiga one chance yadda na shiga jiya."
Ƴar dariyar da take yi ta daina babu shiri ta dawo kujerar gefen gadon ta zauna. Kamal ya sosa ƙeya.
"Ba na faɗa miki sai da na sa Happy